Wata irin ihu Shuraim ya saki yayo gurin Widad ta fadi a hannunsa, Abdullah da ya karbi kayan juyawa yayi ammq ihun Shuraim ya dakatar da shi, yana duban abunda ya rike .
'Yan sandan kansu suka yo , shikuwa ko kalansu baiba ya cicibeta yana kiran Abdullah tada mota muje kar na rasa ta pls kayi sauri , ba musi kuwa ya tafi yasa bintu a gaba , ya tada motar san nan ya bude baya , Shuraim ya shiga 'yan sanda guda biyu suka shiga domin rakiyar su.
Suna zuwa wani asibitin da yake kusa suka tsaya , ma`aikta suka karbeta cikin gaggawa. . .