Skip to content
Part 5 of 5 in the Series Wani Rabon by Deejasmaah

I wish I could

Tun last week Tuesday rabon da in ga mai kama dashi hakan bai wani dameni ba don ba ya gabana harkokina na cigaba dayi don banda damuwa ko kad’an yau ina shigowa da sauri don nai lattin zuwa office d’in a daidai parking space naci karo da k’amshin turarenshi mai mugun dad’i lumshe idona nai sai na jiyo sallamar shi a bayana.

Waigawa nai na ganshi yana fitowa daga motarshi yana murmushi d’an tsayawa nai ina amsawa k’arasowa yai yana cewa ” yau dai munyi latti ” a gajarce nace ” aikuwa dai ” murmushi mai sauti ya kuma sakewa kafin yace ” can i see you today after work ” shiru na d’anyi kafin nace “anya kuwa ?”
“Don Allah kiy hak’uri i won’t take much of your time ” ya fad’a a daidai sanda muka hau stairs ” OK ” kawai nace masa ” thanks much ” he said grinning from ears to ears kamar na bashi wata gagarumar kyauta girgiza kai kawai nayi ina wucewa cikin office d’in kasancewar mun iso daidai floor d’in.

Ina sauri zan fice daga wurin ni na manta cewa zamu had’u dashi kasancewar yau mun shiga local markets tareda manyan maaikatan the work is really interesting yet tiring yau naga many local markets da muke dasu a kaduna sannan kuma nasan location d’insu sai dai kuma aikin ba na raggo bane don yawo ake sha ba kad’an ba don haka a mugun gajiye nake jan k’afa kawai nake yi.

Ina isowa daidai bakin complex d’in ne na jiyo mutum a bayana da sauri na tsaya ina mai waigawa shi d’inne d’an dafe kai nayi ina kallonshi murmushi yayi tareda cewa “if u won’t mind can i offer a ride?” girgiza kai nayi tareda cewa ” thanks for the offer but I’m afraid that… “Katseni ya yi da cewa “issokay, Ya alk’awarinmu?”

“Why not talk tomorrow it’s already late” na fad’a ina narke ido wani ajiyar zuciya ya sauke kafin yace” ya na iya wannan kallon ai dole ya hanani miki musu” baki na tura ina jin kamar in zane shi nisawa ya sake sannan ya cigaba ” ok tomorrow by what time and where ” d’an shiru nai ina tunani zuwa can nace ” at the secretariat after asr ” gyad’a kai ya yi yana cewa “thanks dear Allah ya kai mu goben” wuce shi nai ba tare da na tanka ba ina rolling ida nu cike da jin dad’in rabuwa da shi kallonshi da tambayoyin shi.

Zaune muke bayan ishai muna fira da Areepha k’asa k’asa yayin da fav yake kan dining yana kallon anime mu kad’ai ne a gidan dan Mamie tana clinic kasancewar yau night take yi

Labarin Salem nake bata kallona tai tare da cewa “Addah don’t tell me you are turning down this man ?” kallonta nai tare da cewa” in ban yi turning d’inshi ba you want me to disappoint my self ?, Baby that’s the only solution for my heart”.

“Addah baa cire hope fa a rayuwa who knows ko Allah ya kawo k’arshen wahalarki ne? ” girgiza kai nayi cikeda sarewa nace.” Baby mun dad’e muna wannan tunanin but were proved wrong, kar ki manta da irin abinda ya faru a baya shin hakan bai ishe mu karatu ba?

Miyau ta had’e idanunta sun fara kawo ruwa niko na cigaba da cewa ” I’m no more young Babe irgen da ake mun ya isheni hakan shi kanshi nasan in yasan wacece ni rabuwa dani zaiyi balle ‘yan uwanshi wainda sune suke da iko akanshi d’in”.


Hawayen da ya zubo mata ta share tare da cewa ” na sani Anty but u should try to hear from him first tell him everything about you,ki ji mai zai ce don’t conclude maybe ba za a samu matsala daga side d’inshi ba.

Girgiza kai na yi dan nasan ba zata tab’a fahimtar mai zan fad’i ba tunda she’s not in my position. Wayata na d’auka Ina kunna data don ban san me zan ce kuma ba daga nan kuma muka cigaba da fira jefi-jefi har 10 tayi muka kashe kayan kallon muka nufi d’aki don yin bacci.

Washegari ni ce last person da na bar gidan, Fav da Areepha sun wuce school ita CBS take zuwa shi kuma waec suke shirin yi yanzu hakan kammala gyaran gidan nayi tare da tabbatar kammaluwan lunch saboda Mamie dai sai ta huta kan ta fito.


10 dai-‘dai na shiga secretariat d’in ba mu kammala abinda muke yi ba sai around 3 mosque muka nufa da bestie hutawa muka yi bayan mun yi sallah sannan muka fara lissafin abinda za mu ci a daidai lokacin ne wayata tai k’ara dubawa nayi unknown number ne yake kira wanda hakan yasa na jinkirta kafin nai picking

“Hello princess ” aka fad’i daga d’ayan side d’in lumshe ido nayi don na gane mai magana Saleem ne” hello there ” na bashi amsa “how are you doing today”, ya tambaya a gajarce na bashi amsa da fine don bansan damu”. Ahmmmm…Kina ina ne?” He asked
cike da k’osawa nace” it isn’t yet time ai, I said after 4. Abi?” Ina jiyo murmushin shi ta side d’in turo baki nayi cike da jin haushin shi I’m surely getting r*d of him this very day takuran tai yawa.


“Yeah you said so. I’m just asking sorry!” Hararar wayar na yi kamar yana wurin “muna masjid” na sake bashi amsa muryan nan a cushe kana ji kasan dole nake maganar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce “okk dear.”

Yana fad’in hakan na kashe wayata don banda abin ce masa kallon bestie nayi da ta zura min ido ware mata nawa idanuwan nayi tare da cewa. “what?” Harara ta ta yi tare da cewa.” You asking me?! U know quite well that what you are doing ain’t good night ? Me ye laifin wanda ya nuna yana sonka “

Lumshe ido nayi a hankali ina cewa ” you blaming me?, well I didn’t see anything wrong with what I’m doing i don’t want to get attached only for me to be rejected at the end! Wanda nayi a baya ma banji da dad’i ba”

But babe not all men are the same, some will stood up with you through good and bad wasu suna jure komai for love why not give Salem a try may be he’s the right man for you ” ta fad’a tana mai dafa min kafad’a cike da son k’arfafa min gwuiwa

Dariya na kwashe dashi ina cewa “Men from tales right? Ai na riga na farka daga wannan dogon baccin nawa. Those kind of men don’t exist no more…”

Sakin baki tai tana kallona kafin ta ce” don’t lose hope jare, give love another chance” girgiza kai na yi a daidai sanda wani kiran ya sake shigowa wayata “I wish i could…” Na fad’i ina mai kara wayan a kunnena Saleem ne wai yana waje.

Ce mata nai bari in dawo fita nai na sameshi jingine da motarshi hannunshi d’auke da leda sallama nayi na tsaya ina kallon k’asa ledar hannunshi ya mik’o min yana cewa “I come to deliver this. Sak’o daga mijin k’awarki zan dawo after asr akan tamu maganar” amsar ledan nayi ina cewa thanks.

Juyawa nai na shige ina mai jin idanunshi a kaina.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wani Rabon 4

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×