Skip to content
Part 3 of 3 in the Series Wata Kaddara by Shamsiyya Manga

 بسم الله الرحمن الرحيم

(والسارق والسارقة فاقطعو أيديهما جزاء بما كسبا نكالا من الله،والله عزيز حكيم).{سورة المائدة} أية ٣٧.

Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a cikin alƙura’ani mai girma* *cikin suratul MA’IDA aya ta 37

 (Da Ɓarawo namiji da Ɓarauniya mace idan kun Kamasu ku yanke musu hannayen su guda ɗaya gwargwadon abun da suka aikata na game da sata, Allah mai girma ne kuma mai hikima)

*****

RAMLAT ba ita ta tashi komawa gida ba sai ƙarfe sha ɗaya na dare kamar ba matar aure ba,a falo ta tarar da MUBARAK a zaune akan sallaya da alamu salla ya idar,ya ɗaura kanshi a kan kujera kamar mai bacci,amma kuma ba baccin yake ba, ƙarar buɗe ƙofar falon da yaji ita ta sanyashi buɗe idonshi amma bai juyo ba, shigowa tayi ta ƙaraso inda yake kwancen saida tagama ƙare mishi kallo sama da ƙasa kafin taja wani uban tsaki sannan ta nufi hanyar ɗakinta.

“RAMLAT” sunanta da taji MUBARAK ɗin ya ƙirane ya sanyata dakatawa da tafiyar da take yi ɗin amma bata juyo ba balle yasa ran zata amsa mishi ɗin.

Tasowa yayi a hankali ya ƙaraso inda take tsayen magana yafara mata cikin sanyin murya.

“RAMLAT meyasa kika sanja daga ainahin matata da nasani zuwa wata daban?, RAMLAT meyasa kinsan bakya sona kika aureni?, RAMLAT yanzu tsakani da Allah rayuwar da kika zaɓarwa kanki kennan,yanzu kina ganin wannan rayuwar ta dace dake kennan a matsayin ki na matar aure,ki duba agogo ƙarfe sha ɗaya fa na dare wanda ko budurwa hakan bai dace da itaba balle ke a matsayin ki na matar aure.”

Tunda MUBARAK ya magana RAMLAT taji tsikar jikinta tana zubawa, domin kuwa RAMLAT irin matannan ce wadda suke da ƙarfin sha’awa (high libido) duk wani rashin kunyarta da rashin mutuncin ta to da zarar ance dare yayi bata iya rintsawa ba tare da MUBARAK ya biyamata buƙata ba, kafin ace yazo ya nemeta to ita zata fara kai kanta wajen shi, Allah sarki shi kuma MUBARAK bawan Allah duk yadda takai da mishi rashin mutunci shima baya iya mata musu idan ta kawo kanta gareshi,haka zai manta da duk wani abu da ta mishi ya biyeta ya mata duk abun da take so, inshAllah kuma gare yana wayewa zata ɗaura daga inda ta tsaya.

“RAMLAT ina miki magana kin mun shiru.” MUBARAK ɗin ya faɗa yana kallon cikin idanun RAMLAT ɗin.

Ai tun kafin MUBARAK ɗin ya sake cewa wani abu RAMLAT ta haɗe bakinsu waje guda ta fara kissing tun suna tsaye har abun ya gagara suka shige cikin ɗakin kamar zasu cinye kansu.

Nima da gudu na juya na bar gidan dan ban shirya ganin abun da yafi ƙarfin idona ba.

*****

“SALMA ce tsaye a bakin islamiyyar su tana jiran yaya ABDUL tun ɗazu suka tashi a islamiyyar amma har yanzu yaya ABDUL ɗin shiru, gashi har ta gaji da tsayuwa, ta saba kullum suna tashi a bakin makarantar take tarar dashi a tsaye tana fitowa sai tafiya, amma yau ta rasa mai ya hanashi zuwa har yanzu, idontane ya fara cikowa da hawaye gaba ɗaya tayi narai narai da ido kamar mai shirin kuka.

Tun daga nesa ya hangota yaga yadda ta cika tayi fam, murmushi yayi dan ya tabbatar yau akwai rigima daman SALMA ba’a taɓa ta bama yaya ake ƙarewa balle kuma an taɓota, ƙarasawa yayi inda take tsayen ta harɗe hannayen ta a ƙirjinta bata lura da zuwan nashi ba kawai sai ƙarar mashin ɗin shi da taji ya tsaya a gaf da ita, juyowa tayi ta kalleshi sannan ta juyar da kanta gefe tare da cuno baki gaba.

Saƙƙowa yayi daga kan mashin ɗin nashi sannan ya zo ta gabanta ya tsaya tare da haɗa hannayen shi waje guda alamar neman afuwa, ƙara juyawa tayi da kanta gefe ta haɗe fuska ko kallon fuskar shi batayi ba.

To fah! Babbar magana ya faɗa ya zuciyar shi domin kuwa yasan yau akwai drama, ƙara zagayowa yayi ta gabanta, tana ƙoƙarin ƙara juyawane yayi saurin zube gwaiwowin shi a ƙasa tare da haɗa hannayen shi waje guda dan yasan hakan kawai zaiyi tayi gaggawar saƙƙowa,ganin da tayi ya zube a ƙasan ne ya sanyata saurin riƙoshi tare da ƙoƙarin ɗaga shi tsaye,noƙe kafaɗa yayi alamar bazai tashi ba.

Cikin shagwaɓe fuska ta fara magana tana mai waigawa baya ganin har mutane sun fara kallon su.

“Yaya ABDUL ka rufamin asiri ka tashi kaga ana kallon mu.”

Shima shagwaɓe fuskar yayi sannan yace,

“A’a nikam bazan tashi ba har sai kincemun kin haƙura kuma kin daina fushi dani.”

“Shikennan to yaya ABDUL ka tashi dan Allah mu tafi kaga mutane suna ta kallon mu nikuma kasan bansan kallon mutane.” Ta faɗa kamar zata yi kuka

Dariya ce taso kufcewa yaya ABDUL ɗin ganin mai fushi lokaci ɗaya har ta saƙƙo daman yasan abun da bataso kennan shiyasa yayi hakan.

“To ai baki ce kin haƙuri ba,kuma ma nikam ina ruwana da wasu mutane da suke kallon mu ai ba zunubi muke aikatawa ba” Ya faɗi irin bai damu ɗinnan ba.

“To shikennan naji na haƙura nidai dan Allah yaya ABDUL ka tashi mu tafi.” Ta faɗa tana mai jan shi dan ita burinta kawai su bar wajen.

Dariya yayi sannan yace.

“SALMA rigima Allah dai ya barmu tare.”

“Ameen ya Allah yaya ABDUL ɗina” SALMA ta amsa mishi tana ɗanewa bayan mashin ɗin.

Basu ɗauki tsawon lokaci ba suka ƙarasa unguwar tasu kasancewar basu da wani nisa tsakanin su da islamiyyar su SALMA ɗin, shima kuma ABDUL ɗin a unguwar yake gidansu yana gefen nasu SALMA.

A tare suka shiga cikin gidan bakin su ɗauke da sallama inda suka tarar da Umman SALMA ɗin tana gindin murhu tana tuƙa tuwo.

Amsa musu sallamar tayi tana cewa

‘kaga ƴan islamiyya an dawo kennan”

“Eh wallahi Umma mun dawo” Cewar yaya ABDUL ɗin tare da jan kujera ya zauna.

“kuji bakin shi a nan wajen wai sun dawo sai kace islamiyyar yaje, kabari nida naje islamiyyar na amsa mana” ‘ta faɗa tana harar shi.

“To yau dai da alama za’a ji kanku ABDUL dan irin wannan harara da naga an watsama to da alamar tambaya” Umman ta faɗa tana dariya.

“Uhmmm Umma kede ki rabu da SALMA kinsan halinta ai ba’a rabata da rigima,wai fa wannan fushin da kikaga anayi da ni duk wai saboda banje na ɗakkota da wuri bane ba” yaya ABDUL ɗin ya faɗa.

“Hhhhh kudai kuka sani nanda sati biyu dai kuna can an kaimaka ita sai taje tamaka rigimar a can, yawwa SALMA ni bama wannan ba mai gyaran jiki fa ta aiko kijeki ɗazu wai tajiki yau shiru.”

“Wayyo Allah nah wallahi Umma na gaji da wannan gyaran jikin anfi wata uku fa ana abu ɗaya gaskiya nikam yau bazanje ba.” SALMA ta faɗa tana mai zare hijab ɗin islamiyyar da yake jikinta saboda zafi da take ji.

“To nidai ke kika sani ruwanki ne idan ma kika ce bazaki ƙara komawa ba ruwanki nidai banida case.” Cewar Umman tana mai fara kwashe tuwon da ta tuƙa ɗin.

“Umma ƙyaleta bara naje nayi wanka a gida zanzo na kaita da kaina” Inji yaya ABDUL ɗin yana nufar ƙofar fita daga gidan.

“Badai ni zaka kai ba saidai ka nema wadda zaka kai.”

SALMA ta faɗa tare da shigewa cikin ɗaki.

*****

“MUBARAK kuwa bashi ya ƙyale RAMLAT ba sai ƙarfe ɗaya daidai,duk ya gaji sosai amma ita kuwa ko a jikinta domin kuwa da zai cigaba da yi ma ita kam bazata hana shi ba a yanzu hakanma da ƙyar ya ƙwaci kanshi, tashi yayi ya nufi toilet dan tsarkake jikinshi, ita kuwa RAMLAT tana kwance a inda ya barta ɗin bata da alamar tashi.

Saida ta tabbatar ya shiga toilet ɗin har ta fara jin ƙarar ruwa alamar ya fara wankan, gani nayi ta tashi ta tsaya a tsakiyar ɗakin a yadda take babu ko sutura a jikin nata,idonta ne naga ya fara komawa green colour,wani green colour ɗin abune ya fara fitowa daga cikin idonta sannan ya zagaye duka ɗakin ma’ana duk ɗakin ya zama green colour ɗin, kallon inda MUBARAK ɗin ya kwanta tayi sannan wannan green ɗin abun ya tafi yaje ya yaryaɗu akan gadon iya dai-dai wajen da MUBARAK ɗin zai kwanta har fillon da zai kwanta ɗin, jin kamar alamar MUBARAK ɗin ya gama wankanne ya sanya RAMLAT ɗin saurin komawa gadon ta kwanta.

Fitowa yayi daga toilet ɗin yana goge ruwan kanshi sannan ya kalli inda RAMLAT ɗin take kwance yace,

“RAMLAT kije kiyi wanka tunda na fito ko.”

“Kai MUBARAK yanzu da wannan uban daren wankan mai zanyi kawai ka barni saida safe” Ta faɗa tana ƙara gyara kwanciyar ta.

Baiyi mamakin abun da yaji RAMLAT ɗin tace ba domin kuwa wannan ba sabon abu bane ba,duk ranar da suka gama mu’amalar aurattayya to bata wankan tsarki sannan idanma ta shiga wankan to saidai ta watsa ruwa kawai ta fito bazaka ga ko ɗigon ruwa ɗaya a kanta ba.

“Haba RAMLAT najasa ce fa a jikinki kina nufin cewar da…”

Maganar tashi ce ta maƙale sakamakon ɗagowar da RAMLAT ɗin tayi ta watsa mishi kallo da green colour ɗin idanunta.

Ji yayi duk wani abu da zai faɗa ya manta take yaji wani tsoronta ya mamaye shi tare da wani bala’in sonta, haka ya ja jikin shi ya ɗauki sallaya ya shimfiɗa ya fara gabatar da Sallah, daman MUBARAK baida wasa Indai wajen ibada ne kawai dai WATA ƘADDARA ce da kuma jarrabawa Allah ya ɗauro mishi da ita.

Washe gari ta kama sunday, inda tun ƙarfe bakwai MUBARAK ya tashi ya shiga wanka saboda a ranar zai koma wajen aiki inda yake aiki a Abuja daman duk weekend ne yake dawowa gida, har ya fito daga wankan RAMLAT tananan a kwance a inda ya tafi yabarta, jijjiga kai yayi sannan ya nufi wajen closet ɗin kayanshi,wasu ƙananan kaya ya ciro farar riga ce sai baƙin wando,Saida ya shafa mai mai ya sanya kayan kafin ya nufi bakin gadon fara bubbuga filon da RAMLAT ɗin take kai yayi a hankali yana ƙiran sunanta kamar mai tsoron yin magana.

Buɗe idonta tayi a hankali sannan ta zuba su a kan MUBARAK ɗin da yake tsayen,miƙa tayi babu ko addu’a daman ba iya tayi ba ko nace daman ba damunta tayi ba, miƙewa tayi ta zauna tare da jingina bayanta da jikin gadon tana kallon shi sama da ƙasa.

“RAMLAT ki tashi ki shirya kin san zamuje shopping gashi yau nake son wucewa zan koma wajen aiki” MUBARAK ɗin ya faɗa yana sanya agogo a hannun shi.

“Oh haka fa ni nama manta wallahi, bara naje nayi wanka ka jirani, naji kana cewa zaka koma yau amma dai tare zamu tafi ko,dan gaskiya nagaji da rayuwar kaɗaici” ta faɗa tana miƙewa tsaye.

“To nidai yanzu ki shirya muje muyi shopping ɗin mu dawo”

“To ai gwanda na sanar da kai dan bazan ƙara yadda ka tafi ka shafe sati ka barni a nan ba.”

Bai kulata ba sai ma juyawa da yayi ya nufi falo,itama tashi tayi ta nufi toilet ɗin dan yin wanka,bata wani daɗe ba ta fito daga wankan,shiryawa ta fara yi cikin wata doguwar riga ta fitted gown wadda ta kamata sosai kamar ba matar aure ba wani ɗan figigin mayafi ta ɗakko ta sanya wanda dashi da babu duk ɗaya,haka ta juya tana tafiya da ƙyar kamar kice firit rigar ta yage,nikuwa nace ikon Allah wai hakan suna matar aure Allah ya shirya.

A kan kujera ta tarar da MUBARAK ɗin yana waya da Deede, tun da ta fito yake kallonta tun daga sama har ƙasa zuciyar shi ce yaji tana mishi wani irin zafi kamar zata faso ƙirjin shi ta fito,zuwa tayi ta zauna a gefen shi,sallama sukayi da Deede ɗin sannan yace mata zasu zo suje shopping.

Sauƙe wayar yayi daga kunnen shi sannan ya juya ya kalli RAMLAT ɗin yace,

“Yanzu RAMLAT mai kike nufi, tsakani da Allah wannan shigar ta dace ki fita da ita a matsayin ki na matar aure, ko ba matar aure ba budurwa ma mai tarbiyya bazata yi wannan shigar ta fita da ita ba” Ya faɗa yana kallon RAMLAT ɗin.

Itama kallon shi tayi sannan ta kalli kanta tace.

“MUBARAK ban fahimta ba mai shigar tawa tayi bafa tsirara zan fita ba kaga malam in zaka tashi mu tafi ka tashi in kuma baka shiryawa tafiyar ba sai ka sanar dani dan inada abun yi.”” ta faɗa tana zaro wayarta ta shiga dannawa.

“Amma RAMLAT ba iya wajen shopping zamuje ba hadda gidan mu kina ganin ya dace kije gidan a haka?”

“Au dan zanje gidanku sai akace wata shiga zanyi daban,ikon Allah! to bari kaji babu uban da zai sanya na sanja wannan shigar da nayi in faɗama ko mahaifina kaga dai shine kat ko to da in sanja shigarnnan gwanda ka fito kace mun RAMLAT bazan fita unguwarnan dake ba,fine amma nikam bazan sanja shigar da nayi ba”””” ta faɗa tana wulla cingom bakinta.

Shiru yayi yana jin duk abun duniya ya isheshi,shikam wannan wana kalar rayuwace wannan.

“Shikennan tashi mu tafi.” Ya faɗa yana ɗaukar key ɗin motar shi tare da ficewa daga cikin falon.

Itama miƙewa tayi sannan ta nufi hanyar fita a falon tana ƙunƙuni.

“Haka kawai mutum da rayuwar shi za’a takura mishi.”

Shidai bai kulata ba haka ya nufi mota,itama ƙarasowa tayi sannan ta buɗe gidan gaban motar ta zauna,tayar da motar yayi suna suka fice a cikin gidan,direct gidansu MUBARAK ɗin suka fara zuwa,basu tarar da kowa a falon gidan ba,zama RAMLAT ɗin tayi a kan kujera kafin shikuma MUBARAK ɗin ya nufi Bedroom ɗin Deede ɗin,bai sameta a Bedroom ɗin ba saidai yaji ƙarar ruwa a cikin toilet alamar wanka akeyi,fita yayi a ɗakin yaje ya zauna shima a falon kafin ta gama wankan.

Bai wani daɗe sosai da zama ba sai ga Deede ɗin ta fito sanya cikin doguwar riga ta abaya ta yane kanta da ɗankwalin abayar, ƙarasowa tayi inda su MUBARAK ɗin suke ta nemi kujera ta zauna, saƙowa ƙasa MUBARAK yayi sannan ya fara gaishe da Deede ɗin.

“Ina kwana Deede fatan na sameki lafiya.”

“Lafiya ƙalao MUBARAK alhamdulillahi.” Deede ɗin ta faɗa tana kallon inda RAMLAT take zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya bata da niyyar saƙowa balle ta gaishe da Deede ɗin.

Murmushi Deede ɗin tayi sannan tace,

“RAMLAT ina kwana”

Saida RAMLAT ɗin ta ya tsina fuskarta kafin ta juyo inda Deede ɗin take zaune sannan tace.

“Oh ashe fa kin fito Ina kwana”

“Eh ai naga kamar baki lura da fitowar tawa bane shiyasa na gaisheki ni”

“Deede ɗin ta faɗa ba tare da ta nuna ɓacin rai ko kuma damuwa da abun da RAMLAT ɗin ta mata ba.

Har MUBARAK ya buɗi baki zai yi magana Deede ɗin tayi saurin dakatar dashi ta hanyar ɗaga mishi hannu tare da jijjiga mishi kai sannan tace,

“Ku tashi mu ƙarasa dining muci abinci dan nasan wannan fitowar wurin da kukayi baku ci abinci ba”””” ta faɗa tana mai miƙewa tsaye tare da nufar hanyar dining area ɗin.

Aikuwa RAMLAT kamar jira take ta tashi ko kunya babu ta bi bayan Deede ɗin.

Wani uban takaici ne ya lulluɓe MUBARAK ɗin yana jin kamar ya haɗiyi ya mutu gaskiya yau RAMLAT tana son kaishi maƙura kuma zai taka mata burki dan zai iya jure komai amma banda a taɓa mishi sanyin idaniyar shi watau Deede, haka dai shima ya daure ya tashi ya nufi wajen cin abincin.

A nan ma RAMLAT tana ganin Deede tana serving ɗin su amma ko a jikinta,sai shi MUBARAK ɗin ne ya karɓi serving spoon ɗin a hannun Deede ɗin ya zuzzuba musu abincin.

Basu wani ɗauki tsawon lokaci ba wajen cin abincin suka gama sannan suka miƙe inda ƴar aikin Deede ɗin ta zo ta fara tattare kayan wajen.

Shirya suka ƙara yi sannan suka tashi har Deede ɗin dan tafiya wajen shopping ɗin,a mota MUBARAK sai cika yake yana batsewa ƙiris yake jira RAMLAT ta taɓoshi ya sauƙe mata kwandon rashin mutunci kawai Sa’a ɗaya taci kasancewar da Deede a cikin motar,amma ya ƙudirta a ranshi yau sai ya haife cikin RAMLAT ɗin domin kuwa yau ya gaji Allah ya maidasu gida lafiya zataga yadda zai yi da ita.

A haka suka ƙarasa wani Babban Mall inda zasuyi siyyayyar ,shiga wajen sukayi sannan suka ɗauki basket suka fara jidar duk kayan da suke buƙata ɗin,sun ɗan daɗe kafin suka gama.

Saida suka nufo hanyar wajen biyan kuɗi kawai idon RAMLAT ya sauƙa akan wani takalmi mai shegen kyau aikuwa hannu ta miƙa ta ɗauka tare da sanyawa a cikin jakarta,sunyi gabama ta ƙara cin karo da wata sarƙa wadda kana ganinta kasan zata kai ɗaruruwan kuɗaɗe hannu ta sanya ta ɗauki sarƙar sannan ta sanya a jakarta tare da bin bayan su MUBARAK ɗin,duk abun da take yi ɗin ma’aikatan wajen suna kallonta ta cikin CCTV camera ɗin su,kunsan daman irin manyan Mall ɗinnan ba’a cika barin su babu CCTV camera ba.

Ƙarasowa wajen sukayi sannan su MUBARAK ɗin suka miƙa duk kayan da suka siya akayi calculating,wani daga cikin ma’aikatan cikin Mall ɗinne ya kalli MUBARAK sannan ya nuna RAMLAT yace.

“Bawan Allah tare kuke da wannan matar?”

Ya jefawa MUBARAK ɗin wannan tambayar.

Kallon juna MUBARAK sukayi dashi da Deede sannan suka kalli RAMLAT da hankalin ta ma baya wajen su.

“Eh tare muke lafiya ko wani abune ya faru?” Cewar MUBARAK ɗin.

“Eh ka sanar da ita ta fito da abubuwan da ta ɗauka ta sanya a cikin jakarta domin kuwa CCTV camera ta nunamana ita.”

Wani bugawa ƙirjin MUBARAK ɗin yayi a lokaci guda suka kalli juna shida Deede sannan suka kalli RAMLAT da babu wani alamar tsoro ko rashi gaskiya data nuna.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Wata Kaddara 2

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×