Bismillahi Rahmani Rahim
Bayanin halin da nake ciki nayi mata, cikin tausayawa ta ce, "Allah sarki Munibbah, gani nan da kike min yanzu haka wajen me shago zanje naciyo bashin garin ƙwaki domin tun safe da Baba ya fita bai dawo ba haka ma Yaya na, shine Mama tace naje 'na amso in yaso da ya shigo sai akai mai kuɗin, amma karki damu za'a san yanda za'ayi yanzu zo muje ki rakani..."
Cikin rauni na ce, "a'a Aysha karki damu dani, na gode da kulawar ki, zanje gida sabida har yanzu bana jin dadin jiki. . .