Skip to content
Part 11 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Aalia Bhatt

Kyakkywa mace Aalia 

Tauraruwa ce Aalia 

Kina burge ni Aalia 

Mace mai kama da taliya 

Ga kyawun gani ga Aalia 

Ga murmushin so ga Aalia 

Ga nutsuwa gun Aalia 

Jarumar ƙasa ta India. 

Shahararrun matan duniya 

Masu tashe a wanga duniya 

Tabbas da ke ciki Aalia 

Ga ki dai ƙarama ce Aalia 

Amma da aikin manya Aalia 

Ga farin jini gun Aalia 

Kin zamo abar so ga duniya 

Wayyo jaruma Aalia. 

Aalia sanyin idaniya 

Mai sanyaya zafin zuciya 

Tauraruwar nahiyar Indiya 

Mai murmushin kaɗa duniya 

Kin zamo madubin soyayya 

Kin zamo wa mata rariya 

Ke ce mai kyawun wuya 

Aalia abar son duniya. 

Jamilu ne ni kin jiya 

Daga nan cikin Nijeriya 

Masoyin kafcen Indiya 

Saboda ke baitukan ga nas-shirya 

Fatana in wasa mashahuriya 

Fitacciyar Jaruma Aalia 

Mai haskaka ruhi Aalia 

Ina gaisheki gudaliya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 5

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 10Ba’indiya 12 >>

2 thoughts on “Ba’indiya 11”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×