Sunyi nisa sosai a mota masu bacci nayi masu kalle kalle nayi cikin masu kalle kallen harda ummu gabaki daya ji take ranta babu dadi ji take kamar tasa motar ta tsaya ta sauka.
Duda kasantuwar garin yanayin sanyi gashi dare ne kukan tsin tsinye kawai kakeji gwanin dadi sai dai ita gun ummu ba abinda ke mata dadi baccin ma kwata kwata batajinsa juyawa gefenta tayi taga ummi nata sharar baccinta ta kalli hannunta inda danta ke maqale a qirjinta shima baccinsa yake har yana dan murmusawa akaro na biyu da tausayinsa ya cikata.
Tun randa aka miqo mata. . .