Skip to content
Part 9 of 15 in the Series Abbakar by Fadimafayau

Haka Mahfuz yana ji yana gani police sukai gaba dashi, yana faman ihuu shi sai an fito Ummulkhairi ya tafi da ita, tuni yan kallo suka cika gurin duda kasantuwar lokacin sassafe ne.

Saida Mahfuz ya kwan ya yini a police station kafin asamu labari a gida, dan hankalinsu gabaki ɗaya ya gama tashi, anata tunanin ko lafiya, shi ba mutun bane mai kaiwa dare a waje bare kuma har s kai ga kwana,  Nasir da hajiya ne suka fara zuwa police station ɗin,  yana ganin Nasir ya hau faɗa da zage- zage “mugu azzalumi wallahi saika saketa, she is mine” ya shaqe Nasir dagyar aka fitar da Nasir ɗin daga dakin.”

Nuna ƙofar da akayi da Nasir Mahfuz yake ysna faɗin “Shine wallahi hajiya shine” haka kawai yake fade.

Hajiya ta riqe Mahfuz cikin kuka tana faɗin “shine mene?” yaci gaba da faɗe ta jijjagashi sosai “Please Mahfuz calm down, me ya faru” jijjiga shi da magana mai ƙarfin da ta yi ne yasa  k ya koma hayyacinsa fahimtar haka yasa Hajiya Dafa shi,  “ka nutsu kafadan me ya faru.”

Sosai ya bada Hankalin sa ga mahaifiyar tasa, fuskar sa ɗauke da tashin hankali yace “Hajiya yah Nasir ne yai aure, and the annoying thing about the marriage is he he married the love of my life,”  a razane Hajiya ta miƙe “haba Mahfouz “ni na haifeku gabaki ɗaya, yaushe kuma Nasir in yai aure ka,  fada min kodai wani abun ka sha ya bugar da kai?” Girgiza kai yake idanun sa cike da son ya tattabar mata bawai ƙarya yake ba a hankalin sa kuma yake, “wallahi Hajiya shine, kuma Ummun Baba Yasir, ya aura I saw them at their matrimonial home, kamo hannun ta ya yi Hajiya Please bleave me wallahi shirme nake ba shi yasa aka daureni ma” shiru tayi tana kallon sa kafin ta ce “ka tabbatar da abinda kake faɗe?”

Cike da nuna ƙwarin gwiwa ya gyaɗa kansa sannan  ya ce “eh Hajiya”

Shiru ta yi da alamu bata gama yadda da abinda ya ce ba, sai kuma ta koma ta zauna aranta tana tunanin kamar ta yadda musamman yadda Nasir ke cewa Haukacewa Mahfouz ɗin ya yi,  haba biri ya9, ” ina zuwa” ta fada kan ta fice tabar dan dakin da suke ganawar.

Nasir da ta hango daga nesa suna magana da wani police yasa ta nufar wurin, faɗa ta hau yi, ya kalleta cike da mamaki , “Hajiya wani abin nayi” cike da kufula Hajiya ta ce “bansaniba ashe kai shasha ne, da har zakayi aure bamu sani ba ka rasa wa zaka aura se yarinyar nan wadda uwatta bata ganin kowa da ƙima.”

Ya dafe ƙirji cikin tsoro da tashin hankali yake magana “Hajiya kema kin yadda ina da aure?, Ai in zan aure kin san kune zaku auran, yaushe kuka aura min?,  in inadashi ai da tuni na dena kwana agida, aje gidan da yace yaganni inyaso se agani inni inne” taɗan yi jim kafin ta koma dakin.

Mahfuz ta tambaya kwatancen gidan ya mata.

Hajiya ta so ruɗewa yarinyar kamarsu ɗaya da Ummu, sedaifa yarinya tace ita ina batasan wani Nasir ko Mahfuz, ba har gidan iyayanta ta nuna mijinta ma ko kama basu haɗa Nasir ba, police ma sun tabbatar ba Nasir ne ya kawo Mahfuz ba wanda yakawo mahfuz daban.

Koda su hajiya suka dawo da labarin komai Mahfuz ya mike yahau dukan Nasir Yana faɗin “wallahi saina kasheka wallahi shine, da hankalina ni zaku rainawa wayo.”

Ala dole su hajia suka yadda tabbas Mahfux ya haukace hakan yasa suka amshe shi  suka wuce asibitin kula da kwa kwalwa.

Duk wani bincike anyi anman ba’agano komi ba wato kwakwalwarsa normal take, sai dai Hajiya ta gaza yadda normal yake. yadda in yaga Nasir yake tuburan dole hajiya yasa  ta yadda ya haukace. Wannan yasa ta ce a ɗauke shi a kai shi asibitin kula da marasa hankali dan ya ba fara bata tsoro, sam ya dena cin abinci sai faman faɗin shi wallahi da hankalin sa ace Nasir ya sakar masa masoyiya.

Duk halun da ake ciki Abbakar baya da labari sai, yau hankalinsa ya tashi danshi be yadda Mahfuz ɗinsa ya haukace ba.

Kai tsaye asibutun ya wuce, Mahfuz ɗin na ganinsa yahau kuka tausayinsa ya cika Abbakar, yadda kwana biyu kawai yaga Mahfuz ɗin duk yai baƙi ya rame kamar bashi ba.

Ya hau rarrashinsa, cikin kuka Mahfuz ya riƙo hannun sa “dan Allah aminin kaje kacewa Hajiya wallahi da hankalina, Allah ban haukace ba kai nasan zaka yadda.”

Yadda yake maganar yaƙarama Abbakar kwarin, gwiwa tabbas Amininsa da hankakinsa wata maqirqisa kawai aka shirya masa. Dan shima yaga Nasir ya kuma san shi ya gani sai dai in duk su biyun suka haukace kenan.

“Naji nayadda da hankalinka, anman garin yaya me yafaru har aka kawoka nan dole da abinda ka yi yasa Hajiya ta yadda baka da hankali,” bashi labarin komai Mahfuz ya yi, shiru Abbakar ya yi tabbas raina musu hankali yarinyar nan take, abin kuma ya isheshi yau zai maganin komai, dan yanasan abokinsa, yanaji yana gani baza’a mayar masa da Amininsa mahaukaci ba.

Ya kwantarma da Mahfuz hankali kafin ya fito daga gidan masu rangwamen hankalin.

Kai tsaye gidan Su mayhfuz ya wuce, baibi ta ko inaba yai bangaren Hajiya abinda yake ba sabonsa ba shiga cikin falon gidan kai tsaye.

Yai sa’a tana falo suka gaisa kafin ya mata jaje, ya ɗora da fadin “yanzu Hajiya kina kallo za’a maida Mahfuz mara hankali, bazaki magana ba?”

Tai dan murmushi “Habu kenan ai ba maidashi akaiba, ya haukace din ne, mutumin da ke ƙoƙarin kashe ɗan uwansa”

Girgiza kai Abbakar ya yi “wallahi Hajiya bai haukace ba, da hankalinsa”

“Uhum haba Habu taya zakace bai haukace ba, mutumin da yake ikirarin kashe ɗan uwansa agabana fa,ai inda yana da hankali ko Nasir ba wansa bane a ganan mahaifiyar sa bai ci yace zai kashe shi ba gaskiya.”

Nisawa ta yi ta cigaba “Yana ihuuu, yana shine ajalinsa, yace yai aure alhalin ƙarya yake masa, yace yaganshi alhalin bamashi bane, bakajin wannan duk ba alamomin hauka bane?.”

“Wallahi hajiya shi yagani, we saw him together am very sure shine”

Hajiya taja tsaki “daman ai abokin ɓarawo ɓarawo ne, ina yabonka ashe kaima ka fara shan kwayar da yake sha, nasan itace ta fara tambayar ku, inzaka tashi katafi to, inkuma anan zaka kwana sekayi tayi” ta miƙe tai sama tana faɗin ” dan wallahi kaima ban yadda dakaiba kar inje a afkamin.”

Ya miƙe yabar gidan takaici fal cikinsa.

Gidan da sukaje da Mahfuz yai inda sukaga Nasir da Ummun.

Yaro ya aika amasa sallama da me gidan yaron ya fito wai baya nan can saigata tafito.

“Wake nemansa?” yai saurin Ɗagowa daga daddanna wayar da yak,e dan ko a ina yaji muryarta sai ta gane nine ya fada.

Kamar ba ta taɓa ganin sa ba ta ce “oh baya nan sedai inzaka jira” ta faɗa lokacin da ta fito.

“Ok ba matsala” yace tamkar shima bai san ta ba, yayin da ita kuma ta koma ciki.

Ya kusa minti goma sha biyar, mutumin ya parkee motarsa ƙofar gidan, ga mamakin Abbakar ba Nasir bane, anman yaɗan daurewa mamakinsa ” Assalamu alaikum, barka sannu ko, yawwa kai kake nema na?” Mutumin ya faɗa tare da malam miƙa masa hannu lokacin da yazo daf da Abbakar.

“Eh nine”
“Ok muje daga ciki ko” suka shige.

Bayan ya shiga ya fito riƙe da yaronnan da kodaga bacci Abbakar ya tashi saiya, ganeshi dan tabbatar da abinda ke masa yawo arai na shakku yasashi miƙa hannu “kawoshi.”

Ya amsheshi daɗinsa da yaron kwai fara’a, ya sunansa?,
“Mahfuz” Mutumin yace ataƙaice

“Allah sarki Allah ya rayashi”

amin yace ya miƙo hannu ya amshe abinsa.

Muskutawa Abbakar ya yi kafin ya ce “Nikam Kamar nasanka wataƙil dan kwanaki dai munzo da abokina mahfuz ne”

Aɗan fusace Mutumin ya ce “oh naganeku kune yan iskannan masu shigarwa matan aure gidako?”

Abbakar yaɗan cige leɓe dan yaji zafin kiransu da yan iska dayayi ya dai basar “ehto koma me kakiramu ni ba hayaniya nazo ba nazone dan inasan yin magana dakai da matarka.” Abbakar ya faɗa a dake.

Ya miƙe a fusace “what dan mene sai da ita zakai magana, inbazaka iyayi dani ba, my wife is mine, haramin alaik.

Girgiza kai Abbakar ya yi “no maganece ta fahinta nakeso muyi kan abokina da kuka haukatar.”

Ɗaga masa hannu mutumin ya yi, “Kaga nafiskanci baka da aikinyi, pls tashi kabar min gida tun kan kadaga hankalin matata.

Haɗa hannun sa wuri guda Abbakar ya yi “pls give me a chance, this matter da nake muyi magana will save life, please reconsider.”

A fusace Mutumin ya miƙe ” wai baka ji me nace maka bane, ko sai na haɗaka da police ne kaima, na sassauta maka ne dan kawai na fiskanci kafi abokinka kamala.”

Abbakar ya miƙe ” kasani I will be back for sure in Sha Allah, ka kwanda sanin inna dawo dole I will speak to her, mark my words, i bleave that will be the reason wannan rainin hankalin zai ƙare” ya faɗa tare da yin waje.

Taɓe baki mutumin ya yi “to muzuba nidakai dan halak ka fasa”

Tunda yahau titi tunanin muhawarsu da mutumin yake, yasan babu ta yadda zai iya magana da matarnan indai mutumin nan nanan, but za’a iya kamashi inyaje ya shigar musu gida suka masa ihuuu gabaki ɗaya tunaninsa a cunkushe yake ya rasa mafita.

Sauri kawai yake ya tafi sch ko breakfast ɗin kirki bai ba ya bar gida.

Ko a office ma jira yai kawai takwas tayi ya wuce inda zaiyi lecture ɗinsa ta morning, bayan ya gama kan ya fita yace “wadda aka kawon complain bata da lafiya tazo yau for her make up” ya fice be jira amsar student dinsa ba.” Ya yi waje

Aikuwa kamar tare suke yana shiga office ɗin ta shigo riƙe da babyn ta, yadan kalleta ya kalli babyn ya tsorata ta, ” zaki iya zama” yace taja tazauna, yai saurin murɗa makullin office ɗin gami da zareshi ya zura a aljihu, jikinta ya ɗauu rawa ta mike ya daka mata tsawa, ” koma ki zauna, kuma kika ce tak kome ya faru dake ke kika jawo,” yadawo gabanta dab da ita tana kallonsa yana kalkonta yazauna har yana iya jiyo faduwar gabanta suka haɗa ido ya daka mata harara tai saurin kawar da kai…

Zan cigaba in sha Allah.

<< Abbakar 8Abbakar 10 >>

1 thought on “Abbakar 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×