Skip to content
Part 13 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Daga haka ta shige cikin harabar hotel din ranta na kuna, zuciyarta fal da bacin rai, daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki

“Waye zai kai ni better room 1 a cikin ku?” ta yi tambayar lokacin da take tsayawa tana fuskantarsu

Duk suka bi ta da kallo, saboda ko sallama ba ta yi ba, bare kuma  gaishe su ba, sannan ta raba hanya da ka’idojin aikinsu.

Haka nan daya daga cikinsu ya ce” Hajiya sai kin cire Face mask din fuskarki, kin kuma rubuta sunanki a kan wannan littafin. “ya kai karshen maganar hade da tura mata dogon littafin.

Ta shiga aika mishi da wani kallo, sosai ranta a bace yake, komai ma haushi yake ba ta, ji take kamar ta kama mutane ta yi ta duka haka nan. Ko kuma ta dora hannu a kai ta shiga santa-santa tana zumduma ihu. Kodai ta yi hauka, ko kuma ta mutu.

” Ba zan yi ko daya ba, daki na kama, na kuma biya kudi, kuma an ba ni lambar dakin, ba rubuta suna na zo yi ba, zuwa na yi kawai in kwana in tafi. Nan din makaranta ce, da za ace in rubuta suna in cire mask” ta karasa maganar hade da jan tsoki, lokaci daya kuma ta shiga kiran waya

“Ina nan security sun hana ni shiga” basu ji amsar da aka ba ta ba, amma sun ga ta sauke wayar hade da komawa gefe tana kara kumburi, kamar kullin masa ya fara tashi.

Tun daga nesa suka hango Lukman yana fitowa, Lukman shi ne acting manager a hotel din, “kila shi ya sa take nuna isa, ta san gadar da ta taka” Duk suka fada a zuciyarsu.

“Me ya sa kuka hana ta shiga?” Abin da ya fara tambaya kenan lokacin da ya iso

Cikin girmamawa suka hada baki “Ba hana ta shiga mu ka yi ba Oga…” suka shiga labarta mishi abin da ya faru.

Ya juya kan Asma’u wacce ta kara hade fuska, ya maido da ganinshi kan security din ya ce “Ku bar komai a hannuna, zan kula da komai, ta riga ta yi booking dakin tun dazu a online kuma ta biya, sannan da alama baƙuwa ce, ku rabu da ita”

Duk suka daga kai alamar to.

Shi kuma ya juya kan Asma’u ya ce “Mu je ko”.

*****

HAFSAT POV

Ranar da aka yi addu’ar bakwai a ranar aka raba gadon Inna, a ranar ne kuma kowa ya watse idan ban da Mama Halima, wacce ta nemi alfarmar tafiya da Hafsat.

Amma fir Malam Ayuba ya ce bai san zance ba, saboda ya san idan har ya amince ta tafi da Hafsat, to ya san za ta nade duk wata dukiya ta Hafsat zuwa wurin ta, shi kuma ba zai lamunci hakan ba, yana son ganin komai na Hafsat a tare da shi.

Duk yadda aka juya Malam Ayuba dambu ya taliya ya ce shi fa Sam bai amince ba, ta bar mishi yarshi

Yar guda daya sai an raba shi da ita. Inda yake shiga ba nan yake fita ba.

Ran Mama ya baci sosai, ta dawo dakin ƴar’uwarta inda Hafsat ke kwance kan gado tana sauraron duk abin da suke fada.

Mama ta koma gefen gado ta zauna hade da fashewa da kuka, cikin kukan ta ce “Haba mutuwa, Haba mutuwa…” sai ta ci gaba da kukan.

Hafsat kuma ta yi jugum ita ba kukan take yi ba, amma ranta ne ke mata wata irin suya.

“Kin ji yadda mu ka yi da mahaifinki ko Hafsat, ina jin kamar in yi karar shi ya ba ni ke, da idon mahaifiyarki ma wace Allah cika bare yanzu da kasa ta rufe mata idanu. Ta ya za ki rayu a gidan nan ba idon Hindatu, ta ya za ki rayu a garin nan ke kadai ba kowa. Gaskiya karar Ayuba zan yi, idan ma zuga shi aka yi, ya lalubo masu zuga shin”

Hafsat ta hadiye wani yawu mai daci ta ce “A’a Mama, don ni kada ki yi kararshi, ki kyale shi, in Sha Allah komai ba zai faru ba.”

“Hafsat har yanzu ke yarinya ce, ba ki hango abin da nake hange ba, kuma ba za ki hango din ba, sai ba kya ganin idona a nan gidan,”

Hafsat dai ta yi shiru ba ta ce komai ba, Sai zuciyarta da take mata zafi.

Mama Halima kasa tafiya ta yi a ranar, saboda ji take kamar ta yi zaman ta a gidan tare da Hafsat.

Washegari ma dakyar ta tafi, bayan sun ci kukansu ita da Hafsat.

Hafsat kam sai a ranar ta fahimci an yi mata mutuwa.

Ita kadai a dakin Inna kamar mayya, babu wanda yake ta ita, kowa da yaran shi yake hidima, haka ta wuni kuka a cikin daki.

Sai dakyar ta fito taba dabbobi ruwa ta kuma zuba musu abinci.

Zuwa dare zazzabi mai zafi ya rufe ta, da wani irin ciwon kai, ba ta san ma ta yi bacci ba, da safe ma haka ta tashi da zazzabin, ga amai tana ji, ta san kuma wannan har da yunwa, haka ta fita ta yi ta yunkurin aman babu komai, Sai dakyar ta samu ta yi wani yellow sannan ta dan ji dadi.

Goggo Luba ce ta dan ji tausayinta ta leka dakin ta ce “Tatuwa ba ki da lafiya ne?”

Daga kwancen ta daga kai.

“To ai ko kukan nan da kike yi ya sanya miki ciwo Tatuwa, ga shi duk jiya ba ki ci abinci ba, ki daure ki kurbi ga kokonki can a rumfa sai kuda ke bi”

Tausayin kanta ya kara kama ta, ta shiga share hawayen da suke zubo mata kamar ruwa.

Kafin ta yi magana ta ji muryar Babanta yana cewa “Me ya samu Hassatu, hala kukan take ta yi ba ta daina ba, da yake a kanta aka fara mutuwa, muma ba duk iyayenmu sun mutu din ba, kuma ga shi muna rayuwarmu”

Goggo Luba ta cafe da “Ba ta da lafiya ne Malam, har amai ta yi”

“To ba kukan ne ya kawo mata ciwon ba, kuma ba ta son cin abinci, wanda ya mutu dai ai ya mutu, duk kukanta Hinden ba dawowa za ta yi ba, da kuka na dawo wanda ya mutu da yanzu kowa ma yana raye.” cewar Kuluwa cikin halin ko in kula

“To aiko ni ba ni da kudin siya mata magani, ya fi mata ma ta warke, idan kuma ita ma mutuwar za ta yi ga hanya nan, daga nan har lahira.”cewar Malam Ayuba rai a bace

” Za ki fito ki dauki kokon na ki ko sai na shigo dakin na same ki? “ya kuma fada a fadace

A daddafe ta fito ta dauki kokon, wanda kuda ke ta bi kamar danyen tutu, ta koma daki ta zauna gefen gado tana kallon kokon cikin ido.

Daga cikin dakin ta ji muryar Nasir yana sallama, Inna Luba ce ta amsa, ita kuma ta fito jiki ba kwari ta nufi zauren.

Tun da shigo yake kallon ta, zuciyarsa na kara narkewa da tausayinta

“kin yi kuka ko?” ya fara tambaya tun ba ta ce komai ba

Tsugunnawa ta yi hade da jingina da bango ta ce “Ban lafiya ne?”

“Me ke damunki?”

“kaina ke ciwo.”

“kin yi kukan kenan Hafsat.”

Ta shiga goge sabbin hawayen da suke sakko mata.

“Kin ga hankalin Mama ya ki kwanciya a can, ita ce ma ta ce in zo in duba mata ke, yanzu idan ta ji ki haka sai hankalinta ya kara tashi. Don Allah ki rika karfafa zuciyar ki”

Ta shiga daga kai alamar ta ji, har zuwa lokacin kuma kukan take yi.

“kin ci abinci?”

Ta girgiza kai a hankali

“Me ya sa?”

“Amai nake yi, ba na son cin komai”

Shiru ya yi idanunshi a kanta, ji yake kamar ya mayar da ita gidansu.

“Zan kira Maman, don Allah ki yi kokarin daidaita muryarki, ko hankalinta ya dan kwanta a can.”

Kai ta gyada mishi, shi kuma ya shiga kiran Mama.

Bayan ta daga ya sa hands-free ya mika mata

“Ina kwana Mama”

Daga can bangaren Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Lafiya ƙalau Hafsat, har na dan ji dadi, wlh jiya ban yi barci ba, hankalina na kanki. In ji dai ba kya kuka ko?”

Sabbin hawayen da suka kara zubo mata ta dauke, tana fadin “Ba na yi Mama.”

“Yauwa, ki yi hak’uri kin ji, in Sha Allah sauki na nan zuwa, kuma zan rika zuwa a kai-a kai ina duba ki. Ga Nasir nan idan kina son magana da ni, ko kina bukatar wani abu ki fada mishi ya kira ni, Hafsat ko me kike so a nan duniyar zan yi bakin kokarina wajen ganin na ba ki shi, ko menene, muddin bai sabawa addini da al’ada ba. “

Yanzu kam ta kasa rike kukanta, cikin muryar kuka ta ce” Na gode Mama”

Nasir ya shiga aika mata da harara, kafin  ya karbe wayar ya kashe ta gabadaya.

“Allah zan daina kawo miki wayar”

Komai ba ta ce ba, Sai sautin kukanta da yake fita.

“Ki koma gida, zan dawo yanzu in duba ki.”

Nan ma ba ta yi magana ba ta juya zuwa cikin gidan tana sharce hawaye.

Awakin kuma suna ganin shigowarta sai suka fara kuka suna kallon ta, sosai tausayinsu ya kamata, su ma yanzu basu da kowa sai ita, ita zasu fadawa damuwarsu da irin yarensu, kuma dole ita ce za ta magance musu ita.

Ta fasa shiga dakin ta juya zuwa wajensu, ta duka a tsakiyar turken tana bin su daya bayan daya tana shafa jikinsu, su kuma suna kara nuna mata suka yi kewarta

A wahalce ta zuba musu abinci, ta juya kan kajin da ke bin ta, ta watsa musu dawa, sannan ta shiga dakin ta kwanta tana mayar da numfashi kamar ta ci uban gudu.

Tana kwance ta kuma jin maganar Nasir, yanzu kam har dakin Inna ya shigo, ya juye mata empty tea a cup, ya mika mata hade da bread, ta rika ci a hankali har ta shanye tea din, ta aje ragowar bread din.

Sai a lokacin ya dauke idanunshi a kanta, kafin ya  fara neman jijiyar da zai kara mata ruwa, duk abin da yake yi tana jin sa ko motsin kirki ba ta yi ba, har ya gama sanya mata ruwan.

Sai bayan da ya daidaita komai ne ya ce ta shi ki gani, ta mike zaune tana kallon hannun da ke manne da karin ruwa.

Ya shiga nuna mata yadda za ta cire idan ya kare, kafin ya aje mata 1k yana fadin “idan ruwan ya kare sai ki sawo abin da kike son ci, ni zan tafi wurin aiki”

Ta gyada kai daga kwancen da take, shi kuma ya fice daga dakin.

Inna Luba ce ta tashe ta, ta cire ruwan saboda baccin da ta yi, kafin ta yi wanka, ta dauki kwano hade sa saka  hijab ta tafi sawo shinkafa da miya da kifi.

Bayan ta ci ne ta yi sallah, sannan ta zubawa awaki abinci.

Cikin kwana biyu ta warware sosai, Sai dai kawai kewar Innata wacce  ta san babu ranar da za ta daina ta. Kullum za ta yi kewar Inna, a kuma ko wane lokaci.

Yanzu kam awakin gidan sune abokan Nishadinta, da safe za ta share makwancinsu, ta zuba musu abinci, wani lokaci sai ta shimfida tabarma a tsakiyarsu ta yi kwanciyarta tare da kananan ƴaƴansu.

Gidan dai babu mai shiga harkarta, ko miko min can babu mai sanyata, kowa harkar gabanshi yake shi da yaranshi, dama-dama Goggo Luba ita ta kan dan shiga harkarta wani lokacin.

Amma Inna Kuluwa kam kamar ba ta san da zamanta ba a gidan ba, iyakaci idan ta gama abinci ta zuba mata ta bar shi a nan. Idan ta ga dama ta dauka ita dai ba ruwanta.

Dakin Inna shi ne ya zama na Hafsat, ba a cire komai ba, kullum a gyare tsab ba ta barin shi da kazanta.

Malam Ayuba kam dama ba zama gidan yake ba, ya fita tun safe to sai dare, idan ban da gaisuwa babu abin da ke shiga tsakaninsu.

Nasir ne kawai da Najib ke kokarin saka ta a cikin farin ciki, Nasir kam rawa da yawa yake takawa a wurin ta, shi din na musamman ne, yana nan kamar uwa, kamar yaya, kamar uba, kamar aboki, kamar ƙawa, kamar kuma fitilar mai haske da yake haska mata duk wani duhu da yake son shiga gabanta.

Wannan kenan. Bari mu leka Asma’u…

*****

ASMA’U POV

Ta shiga  karewa hotel din kallo, har zuwa lokacin da Lukman ya isa kofar wani daki ya sanya key ya bude.

“Bismillah!” ya fada lokacin da yake shiga

Asma’u ta bi bayan shi  cikin rashin kuzari.

“Dakin ya min girma, tsoro nake ji” ta fada da alamun tsoron a kan fuskar ta

Ya dan murmusa kadan kafin ya ce “To ai shi kika yi booking Hajiya”

“Ai ban san room and pallor ba ne”

“ok. To yanzu single kike so?”

Ta daga kai alamar eh.

“ok, so please wait a minute”

Kan ta kuma dagawa, shi kuma ya fice daga dakin.

Dakin ta rika bi da kallo, a  falon kujeru ne guda biyu, 3 sitter da 2 sitter, tv da karamin fridge, Sai kuma table na cin abinci mai dauke da kujeru guda biyu

A cikin bedroom din kuma katon gado ne, tv drower da katon toilet.

Ban da ya mata girma da ta zauna, ina ace ba matsala ce ta kawo ta ba, haka nan ta bukaci hutu ta zo nan, lallai da ta huta son ranta.

Kofar da ta ji ana taɓawa ne ya sanya ta dora idanunta a kan kofar har zuwa lokacin da Lukman ya bayyana

“Hajiya ga wani dakin can an samu”

Bayan shi ta kuma bi har zuwa wani dakin, wanda yake dauke da madaidaicin gado, wardrobe, center table, TV, da kuma fridge.

“Wannan dakin ya yi?”

Ta shiga gyada kai, alamar ya yi mata.

“To wannan din 30k ne, sabanin 50k da kika biya da farko. Yanzu kina da 20k canji”

“Ba na so” ta fada a lokacin da take ajiye jakar hannunta a kan center table din

Yanzu ma murmushin ya yi hade da fadin “To me kike so a kawo miki”

“Ruwa, kankana da ayaba, Sai ice-cream.” ta fada lokacin da take zama a, gefen gadon

“To Hajiya” cewar Lukman hade da juyawa zuwa waje.

Bai jima ba, Sai ga shi da duk abin da ta bukata har da kaza gasasshiya.

“Nawa ne kudin?”

In ji Asma’u tana kallon abin da ya ajiye din

“Har yanzu akwai canjinki a wurinmu ai.” daga haka ya ja mata kofar ya fice

Saman gadon ta kwanta, sanyin  A.C da iskar fanka na busa ta, ta lumshe idanunta a hankali ta kuma bude su a kan agogon da ke cikin Tv. 7pm ya nuna mata.

<< Abinda Ka Shuka 12Abinda Ka Shuka 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.