Shiru ya yi da takardar a hannu, kwakwalwarshi ta yi mishi jin-gim, ya kasa tantance abin da ya karanto.
Wannan ya sa ya kara maimaita karatun, still abin da ya ji da farko, shi ya ji a karatunshi na biyu.
Idanunshi ya runtse gam, yana maimaita kalmar Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un. Bai san ko sau nawa ya karanta ba, kafin daga bisani ya zame ya kwanta saman gadon yana kara bitar abin da ya karanta a zuciyarshi.
Tausayin kanshi ya kama shi, shi kuma ta shi ƙaddarar kenan, me ya sa Asma’u za ta yi mishi haka, bayan ya ɗauki dukkan yarda ya ba ta.
Wannan yana nufin da auranshi ta aikata zina.
“Wa’iyazubillah, A’uzibillahi! Ya salam!” ya shiga furtawa a hankali.
Zuciyarsa na yi masa wani ɗaci gami da zafi. Bai taɓa tsintar kanshi cikin baƙin ciki irin wannan ranar ba. Bai san yana hawaye ba, Sai da ya ji ruwa na zirara ta gefen idon shi.
Ba zai iya tuna when last ya yi kuka ba, wannan ya tabbatar mishi da lallai abun da Asma’u ta aikata ya ƙone shi sosai.
Bai san ya kwashe lokaci mai tsawo ba, Sai da ya ji muryar Hajiya na fadin “Ba dai bacci ka yi ba? Babanka yana ta jiran ka” ya so ya motsa daga kwancen domin ya tabbatar mata ba baccin yake yi ba, Sai dai ya kasa yin hakan, har Hajiyar ta karaso gaban shi, ta kuma fahimci idonshi biyu .
A tsorace ta zauna saitin kanshi, idanunta zube a kan fuskarshi tare da fadin” Magaji. Lafiya kake? kuka fa kake yi”ta kai karshen maganar hade da shafo ruwan hawayen da ke kwance a kan kumatunshi a kokarinta na gasgata abin da ta gani
Ganin da gaske kukan yake ya sanyata cicciɓo kanshi daga kwancen da yake tana fadin “Subhnallah! Me ya yi zafi haka?”
Kwanciya ya yi sosai a kan kafadarta, ba mamaki ya ji saukin abin da yake ji a kirjin shi.
Matarshi da yake so, ya yaba da tarbiyyarta ya aurota hade da kawo ta gidanshi, ya ba ta dukkan yarda, ƴan’uwanshi suka kaunace ta, ita ce take fada mishi tana dauke da cikin wani ba na shi ba, da auranshi ta je ta aikata zina. Bayan bai kasa mata ta ko ina ba idan ka dauke yanayin aikinshi da ba ya ba shi damar zama. Kuma duk da haka yana kokarin zuwa wurinta idan aka yi comparing da wasu mazan
“Ahmad!” Hajiya ta kira shi da tattausan murya jin yadda yake jan numfashi kamar suna fada.
Bai amsa mata ba, ya dai ƙara lafewa sosai a jikinta.
Wannan ya sa ta shiga shafa kanshi a hankali, zuciyarta cike da damuwar abin ya same shi.
Suna a hakan ne idanunta ya hango mata farar takardar da ke yashe a tsakiyar gadon, da hanzari ta mika hannu haɗe da ɗakkota, lokaci ɗaya kuma ta shiga karantawa.
Yadda take karatun da sauri haka zuciyarta ke bugawa da sauri har zuwa lokacin da ta kai karshen wasikar.
A cikin zuciyarta ta rika maimaita Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un.
Wani irin mamaki ne ya lullubeta gami da abin da takardar ta kunsa.
Asma’u da cikin shege, wannan abu shi ne abu na farko na tu’ajjabi a gare ta, kuma abu na farko da ba za ta taɓa mantawa ba har abada.
Maimakon ta ji tsanar Asma’u, Sai tausayinta ya kamata, daga ganin abin da ta rubuta ta san tana cikin nadama. Ita mace ce, ta san irin tashin hankalin da mace kan shiga duk lokacin da ƙaddara irin wannan ta faɗa mata, musamman ace kana da aure, dole a tausayawa Asma’u. Tana bukatar mai kwantar mata da hankali a gefen ta. Ina ma Asma’un ba ta yanke irin wannan hukuncin ba, ita ta sama ta fada mata halin da take ciki, lallai da ta yi mata abin da ba ta za ta ba. Da ta yi mata abin da kila ba a taɓa yi ma wata mai irin ƙaddararta ba
Idan har iyayenta zasu ba ta ita, to za ta rike ta, ta kuma tanadar mata komai da mai ciki ke bukata, har ta haihu, sannan ta taya ta rainon abin da ta haifa.
Saboda a zaman da suka yi da ita, ba ta taɓa yi mata wani abu na rashin tarbiya ko rashin kunya ba. Tana girmamata kamar yadda ƴa ke girmama mahaifiyarta. Ita ɗin ma ƴa ta ɗauketa ba suruka ba. A ko ina za ta iya shaidar Asma’u mutuniyar kirki ce. Shi ya sa ta yi matukar girgiza da ganin wannan sakon nata.
A ɓangare ɗaya ma ba ƙaramin tausayin Ahmad take ji ba, Ahmad irin mutanen nan ne da za ai ta ƙwara suna ji ba za su ce komai ba. Irinsu ne idan zama ya haɗaka dasu sai su kai ka wuta saboda hakurinsu.
Ba ta so ƙaddararshi ta zo a haka ba, amma ta taya shi karɓa da hannu biyu, kuma suna yi wa Allah godiya da Asma’u ba ta rufe su ba, ta faɗi gaskiya. Wannan na ɗaya daga cikin abin da ya sa take kara jin tausayinta. Idan wata ce za ta rufe ido ta ce cikin na Ahmad ne. Ahmad kuma da shiru-shirun shin nan zai karɓa koda ya san ba na shin ba ne.
Tsakanin su biyun ba ta san wa ta fi tausayi ba.
Akwai bukatar ta karfafawa Ahmad gwiwa, ta kankantar da laifin a idanunshi maimakon ta kambama shi, hakan zai sanya ya ɗan rage damuwa.
Kafadunshi du biyun ta kamo haɗe da dago shi suna fuskantar juna. Har zuwa lokacin akwai ruwan hawaye kwance a kan dakalin fuskarshi.
Hannayenta ta sanya hade da dauke mishi hawayen kafin ta kira sunan shi a tausashe.
Bai amsa ba, amma ya dago kanshi haɗe da kallon ta.
A tausashen ta ce “Yau dai na rainawa tarin ilminka Ahmad. Musamman na addini. Tun bakinka bai bude da kyau ba kake zuwa Islamiya. Ka yi sauka ka kuma hadda, ka karancin litattafai da dama, har musabaƙa ta ƙasa ka taɓa ci , ina kuma alfahari da hakan. Sai dai yau ka ban mamaki, kai ne kake kuka saboda wata jarabawa da Allah Ya yi ma. Maimakon ka gode mishi da ya tuna da kai a cikin masu imani har ya jarabaka, kuma ka roke shi ya ba ka damar cinye jarabawar Ahmad sai ka kwanta kana kuka. “
Ta ɗan nisa kaɗan sannan ta ci gaba” Babu bukatar in tunasar da kai hadisan da kuma ayoyin da suka yi bayanin a kan jarabawa da waɗanda Allah Yake jarabawa, na san ka sani Ahmad sai dai ka tunatar da ni.
Tabbas na san akwai ciwo, akwai kuma zafi, Shi ubangijinka ya san za ka iya dauka ne shi ya sa. Don Allah ka karba da hannu biyu ko gode mishi”ta kai karshen maganar tata idanunta zube a kanshi
Doguwar ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya kuma yana nazarin maganganun Hajiyarshi, sosai yana jin zafin abin da Asma’u ta yi mishi, yana jin ciwo gami da wani irin ɗaci. Amma kam bai kamata ya manta da wannan ɗin jarabawa ce daga Mahaliccinshi ba, kuma Allah Ya kan jaraba wadanda suka yi imani ne, domin ganin kojarabawar za ta raunana imaninsu. Yanzu kam Hajiyarshi ta tunasar da shi don haka a bayyane ya furta “Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un” ya san wannan ita ce kalma ma fi dacewar furtawa a duk lokacin da abu mara kyau ya faru da bawa.
A hankali ya kuma maimaita kalmar yayin da yake jin wani bigire na zuciyarshi yana rage cushewar da ya yi mishi
Hajiya ba ta dakatar da shi ba, har sai da ya yi shiru don kanshi, kafin ta ce “Ina kyautatawa Asma’u zato, tabbas wannan abun da ya faru da ita, ita ɗin ma jarabawa ce, za ka fahimci haka daga wasikarta. Sannan daga yadda ta gudu da kuma yadda ta fada maka gaskiya. Idan wata ce za ta rufe ta bar ka ka ci gaba da renon ɗan wani ko ƴar wani. Amma sai ta zaɓi ta faɗa maka gaskiya. Don Allah kar ka riƙeta da zafi, dukkanmu mu ɗauki wannan a matsayin ƙaddararmu. “
” Ban rike ta ba, Sai dai ban ji daɗin abin da ta yi min ba Hajiya. Akwai ciwo sosai, ina jin zafi a zuciyata, ji nake kamar za ta fashe. Ban taɓa tunanin wannan zai faru da ni ba” yadda ya yi maganar da yadda ya ƙarasata sai idanun Hajiya suka cika da ƙwalla, Ahmad mutumin kirki ne, mai shiru-shiru mara son hayaniya mai ɓoye damuwarshi yana da hak’uri sosai da daukar komai ba komai ba. Haka Allah Ya yi shi, shi ya sa ita da kanta ba ta son ta yi mishi abin da ba zai ji dadi ba. Wancan halin nashi na ɗaya daga cikin abin da ya hanata tirsasa mishi ya auri Mami. Ba ta son yi mishi duk wani abu da ba ya so, saboda yanayin shi. Haka ba ta son kowa ya yi mishi abu mara dadi, Sai ta ga kamar da gayya ake mishi saboda anga yana da hak’uri kuma baya magana.
Numfashi ta sauke a hankali tare da fadin
“Komai zai wuce Sha Allah. Muna fatan Allah Ya sa haka ya zama ma fi alkairi a tsakaninku. Tashi mu je wurin mahaifin naka.”
Ya mike jiki ba ƙwari, yayin da ita kuma ta sarkafo hannunta cikin na shi suka jero zuwa wurin Hakimi.
Tun da suka shigo yake kallon yanayinsu, har zuwa lokacin da Hajiya ta zauna a kan daya daga cikin kujerun alfarmar da suka zagaye falon.
Ahmad kuma ya zube kasa cike da girmamawa ya shiga gaishe da mahaifin na shi.
Shi ma amsa cike da kulawar, yana ƙara tambayarshi hanya da yadda ya iso.
Tun kafin Hakimi ya ce wani abu Hajiya ta mika mishi takardar da ke hannunta tare da faɗin “Asma’u ce ta rubuta”
Duk da hasken da ke falon, Sai da ya kara da hasken touch light din wayar shi.
Ya gama karanta wasikar hade da sauke ajiyar zuciya, ya jima ba tare da ya ce komai ba, saboda abun ya so mishi a bazata, bai taɓa tsammanin wannan shi ne dalilin da ya sa Asma’u ta bar gidan ba.
Ya ɗago kanshi a hankali daga shirun da ya yi kafin ya ce “Alhamdulillah! Allah shi ne abun godiya a ko wane yanayi. Babban abun farin cikin farko dai shi ne ganin wannan wasikar, ko ba komai za ta rage mana damuwa da muke yi a kan me ya same ta, a ina take .
Abun farin cikin da ya hadu da bakin ciki shi ne dalilin tafiyar nata
Farin ciki da ke cikin kuwa shi ne yadda ba mune muka cuceta ba. Kuma ita da kanta ta shaida Ahmad mutumin kirki ne. Sannan ba ta bari mun raini jinin wani ba. Lallai a wannan gaɓa ta yi mana adalci, kuma mun farin ciki sosai.
Abun baƙin cikin kuma shi ne ƙaddarar da ta sanya ta barin gidan, lallai abun baƙin ciki ne ace a zuriyarmu an samu wannan. Zina kamar bashi ce, amma ba na jin a cikinmu akwai wanda ya ci wannan bashin. Idan ma akwai to wannan ya zama izina, a kanmu. Ita shu’umin zunubi ne, kakan, kakanka ma sai ya aikata ta, zunubin ya shafi jikanshi na ashirin saboda Annabinmu Muhammad S. A. W ya ce
KAMATUDDEEN… TUDAAN. Allah Ya gafarta mana ba ki ɗaya. Ya kara tsare mu da zuriyarmu ba ki daya. “
Duk suka amsa da amin a hankali. Shi kuma ya ɗora da ” Ahmad ka yi hakuri ka ji, a ɗauki wannan a matsayin ƙaddarar, ƙaddarar da ba ka isa ka guje mata ba. Lallai na san akwai ciwo, to amma ya mu ka iya, haka Allah Ya hukunta.”
Ko motsi babu wanda ya yi a falon har Hakimin ya ɗora da “Game da ita kuma yarinyar, Sha Allah zan sanya wani Malami a can ƙauyen Malamawa zai yi mana aiki, duk inda take kwana biyu ya yi yawa za ta bayyana a gida. Daga nan kuma sai mu san matakin da zamu ɗauka. “
Daga Hajiya har Ahmad babu wanda ya yi magana, shi ma Hakimin shiru ya yi, wanda ya dauke su tsawon lokaci, kowa da abin da yake tunani. Shi ne dai ya kara katse su da faɗin
” Ina rokonku da mu bar maganar nan iya mu uku, kar mu fitar da ita. Wannan din abun kunya ne musamman a idon makiyanmu.
Ko ba haka ma, babu kyau yaɗa zunubin wani, musamman irin wannan, yaɗa zunubin wani kansa Allah Ya jarabaka da irin shi. Musamman ku mata, idan an ce ma bakinku ne ya jawo mana wannan ba za a yi gardama ba. Saboda kun iya yada gami da maganganu marasa kyau, a kan duk wanda irin wannan makamanciyar ƙaddarar ta fada mishi” ya rufe maganar idanunshi a kan Hajiya da duk jikinta yake a mace.
Ganin ba ta yi alamun magana ba ne ya ce “Yaushe za ka koma wurin aikin naka?” idanunshi a akan Ahmad, wanda ya aje kai a kasa kamar shi ne Asma’un.
A yadda yake ya ce “Gobe idan Allah Ya kai mu.”
Cikin sauri ta ce “Haba gobe dai, ai ka tsaya ko kwana biyu ka yi, ka kara hutawa”
Hakimi ma ya katse ta da fadin “To zaman me zai yi? Ai gara ya koma wurin aikinki, ke da bakinki kika ce satar hanya ya yi”
Yadda Hajiya ba ta ce komai ba haka Ahmad, Hakimin ma sai ya ya yi shiru, kowa shi ya san abin da ke zuciyarshi.
*****
MONDAY TUSHEN AIKI
HAFSAT
Zaune take gefen gado, sanye ciki uniform wanda ya sha guga, ya kasance blue, da kuma farin hijab, kafarta sanye cikin fara kal din socks da sandals. Yayin da kamshinta na sassanyar humrah da Mama Halima ke aiko mata ya cika dakin, ba iya dakin ba har tsakar gidan kamshin kan leka.
Fuskarta fayau, sai farar powder da ta murza, yanayin kan fuskarta nata ya nuna ba yabo ba fallasa.
Yau dai da kewar Innarta ta tashi, kamar yadda ta yi bacci ita jiya. Ranta yana mata ba dadi yau saboda rashin Innarta, amma yadda ta fita fes din nan cikin uniform, da ace Innarta na gefenta ba ta jin akwai abin da zai ɓata ranta.
Horn mashin ɗin Nasir ne ya katse mata tunani, ta mike jiki ba ƙwari hade da saba school bag dinta a baya. Sai da ta rufe kofar, sannan ta nufi tsakar gidan, a lokacin ne Inna Luba ke dama kokon safe
“Na tafi.” cewar Hafsat daidai lokacin da ta isa wurin Inna Lubar
“To.” ita ma ta amsa hade da ci gaba da abin da take yi.
Ran Hafsat ya kuma ɓaci, wannan halin ko in kulan da suke nuna mata, ba ƙaramin ɓata mata rai yake yi ba.
Ta ce ta tafi, wai an ce mata to, ko irin ba za ki tsaya ki karya ba. Kullum tana kara gane muhimmanci uwa, da ace Inna na da rai ba za ta bar ta ta fita ba ta karya ba.
Daidai lokacin ta saka kafarta wajen gidan, Nasir da ke kan mashin ya zuba mata ido har ta ƙaraso
“Me ya faru kuma?”
Maimakon ta amsa hawaye ne suka shiga ziraro mata da gudu.
Idanu ya zuba mata, idan akwai hawayen da saukarsu ke kashe mishi jiki to na Hafsat ne, a sanyaye ya ce “Me ya faru, ko ba ki son makarantar ne?”
Ta shugaba girgiza kai alamar a’a. Lokaci daya kuma tana dauke hawayen da bayan hannu.
“Mene ne to?”
Jin ba ta amsa ba, ya fahimci ta tuno Innarta ne, tana ma kokari, tana da Juriya sosai, bai yi tsammanin za ta warware haka da wuri ba.
Daga yadda yake ya mika hannu haɗe da sakko jakar da ke bayan ta.
Babban zip din ya fara budewa litattafanta a shirye, ya rufe tare da bude karamin zip din. Nan kuma biscuit guɗa biyu manya cikin irin wanda yake sawo mata sai ledar pure water guda ɗaya. Ya rufe hade da mika mata yana fadin “To kin gama kukan ne mu tafi, ko a samo tabarma mu shimfida jikin bishiyar ceɗiyar can, mu zauna ki gama?”
Fuska ta narke ba tare da ta ce komai ba, lokaci daya kuma tana hawan mashin din.
“Kin ci abinci ko?”
Da kai ta amsa mishi alamar eh.
Saboda ta san idan ta ce mishi ba ta ci ba, kai tsaye wurin masu shayi zai zarce da ita, ko ya ce ta koma gida ya sawo mata abun kari.