Kauyen Malamawa.
Kauye ne da ke cikin karamar hukumar ALBARKAWA, da ke jihar TANGA.
Wanda ke dauke da mutane sama da dubu goma, da kuma kananan kauyukan da ke zagaye da shi.
Kaso casa’in da biyar cikin ɗari na mutanen yankin manoma ne, duk da akwai ci gaba na zamani da ya shigo yankin, kamar asibiti da makarantu na zamani, tun daga islamiyoyi, primary da kuma secondary.
Mutanen yanki sun karbi cigaban da zamanin ya kawo musu hannu bibiyu.
Kaɗan ne daga ciki suke adawa da ci gaban, har lokacin suke tafiya a kan al’ada irin ta da.
Mutanen Layin Almajirawa da ke garin, na daya daga cikin wadanda basu karɓi komai na ci gaban zamani ba, har zuwa lokacin suna tafiya ne a tsarin gargajiya.
Unguwa ce, ko layi ne mai dauke da tarin Malamai zaure ma bambanta, masu bin aƙida mabambanciya. Layin da ya hada almajirai manyan da ƙanana.
Daya daga cikin manyan Malaman da ke unguwar shi ne Alaramma, shi ne ma fi shahara da yawan almajirai, wanda yawansu ya haura dubu daya, kuma duk karkashin ikonsa suke.
Mutum ne mai zafi da nuna isa. Da kuma taƙama da tarin iliminshi,
Idan dai bangaren malanta ne to Alaramma ya shahara, ba wai iya garin ba, har da makotan jihohi, musamman da yake da katon gidan da yake kwantar da marasa lafiya, masu fama da ciwon da ya shafi jinnu.
A kaf garin da kauyukan gefensu shakkar Alaramma suke yi, basu son zare ya zarga a tsakaninsu, kun san Hausawa sun ce, “ba fada da Malam ba dare.”
Bai wai ƴan garin kawai ba, hatta ƴan’uwansa maza guda uku shakkansa suke yi, yadda ya dafa haka zasu ci, kila don saboda shi ne yake daukar 95% na dawainiyarsu.
Alaramma yana da aƙida hade da tsari, wanda kowa yake kiyayewa a rukunin nasu, ba iya rukunin ba garin Malamawa babu wanda bai san akidojinshi ba, kuma babu wanda ke ketare mishi iyaka.
Daga cikin aƙidojinshi ba a zuwar mishi gida riga-kafi ko wane iri ne, matanshi basu zuwa awo, yanmata daga lokacin da suka kai shekara 11 sun daina fita, ko karatu a cikin gida ake kara musu.
Shi ke da ikon zabowa ko wace yarinya miji, kuma ya kan zabo mijin ne a cikin dalibanshi almajirai gardawa ya hada su aure, ba maganar hira irin ta saurayi da budurwa.
Babu maganar karatun boko ga ƴaƴa maza ko mata.
Ya yaye almajirai sama da dubu daya, haka ba a yiwa yarinya aure sai ta sauke alkur’ani.
Tsari ma fi kyau a unguwar shi ne yadda ake sauke qur’ani sau uku a cikin sati daya
Litinin, Laraba da kuma juma’a, sannan duk lokacin da aka samu karuwa ta haihuwa ko aure, nan ma a kan sauke alkur’ani a daren suna ko daurin aure.
Kamar yau ma da ta kasance juma’a, ba a makaranta amma kuma rukunin ya cika da sautin karatun alkur’ani mai girma, yayin da unguwar ta yi tsit saboda dare ya fara yi, sai hasken solar masallacin da ya hasken wurin ƙwaryar kamar rana.
A daidai wannan lokacin Rumah ce kwance saman karamin gadon karfen Goggonta (Mahaifiyarta). Wani irin ciwo take ji, wanda ba ta taba jin shi ba a shekarunta sha hudu a duniya, dole ce kawai take sanya ta motsi, kamar yanzu ma da fitsari ya tilasta mata tashi, ta rika tsallaka kannenta da ke kwance a tsakar daki a hankali. A daddafe ta isa bayan gidan, ta ɗiga fitsarin da bai fi cikin kwalbar turare ba, amma jin shi take kamar zai cika karamin bokiti kafin ta yi shi.
Ta mike da niyyar fita ta ji kuma kamar tana jin bayan gida , wannan ya sa ta koma tare da tsugunnawa a kan toilet din, ta gama yunkurinta ba ta yi komai ba.
Ta kuma mikewa dakyar zuwa kofar fita, daidai lokacin wani irin ciwo ya kuma taso mata, wanda ya sanya ta dole ta kwanta a wurin, kamar mintuna biyar ta dawo cikin hayyacinta.
Duk kokarin ta na tashi bisa kafafunta ta kasa, dole ta rarrafa zuwa tsakar gida, daidai lokacin da ta isa tsakiyar gidan ne, wani ciwon ya kuma taso mata fiye da na baya.
Gam ta rike turmin dakan da ke kusa da ita,
“Yaya!” cikin daga murya ta shiga kwalawa Innah kira(kishiyar mamanta kuma uwargida)
Yaya da ke bacci ta rika jin muryar Rumah cikin kanta, firgigit ta sakko daga gadon tare da lalubo dankwalinta ta yi tsakar gidan ba tare da ta daura shi ba.
“Rumasa’u lafiya?”
A firgice Inna ta yi tambayar
Rumah ta sake turmin tare da rarrafowa inda Innah ke tsaye tana fadin “Wayyyo Allah Yaya zan mutu, wayyyo Allahna…”
Dole ta katse maganar saboda aman da ya taso mata, ta shiga kwarara shi kamar ana juye ruwa cikin tukunya.
Yaya ta karaso wurin ta a rude tare da rarumarta cikin tashin hankali take magana “Ruma me ya same ki, ba ki da lafiya ne dama?”
Amai kawai Rumah ke kwararawa yayin da Yaya ke ta aika mata da sannu, kamar ita ce za ta warkar da ita, kodayake Hausawa sun ce sannu ba ta warke ciwo amma tana da dadi.
Bayan aman ya tsaya ne Inna ta debo ruwa ta shiga wanke mata fuska, tana aika mata da wata sannun.
Rumah kam numfashi take saukewa kamar ta yi gudun tsere.
wani irin nishi hade da yunkuri kamar akuya za ta haihu ta rika yi, yayin da ta kankame Yaya kam jikinta na wani irin kakkarwa.
tuni Yaya ta sadaƙar Ruma gamo ta yi da aljanu, ciwon ya fi mata kama da haka.
Saboda yanzu ko sannun ma ba ta iya aikawa da Ruma ita, shiru kawai ta yi tana kallon Ikon Allah wai mai tsaida wando ba zariya in ji Hausawa.
Yayin da nishin Ruma ya ƙaru ne, Yaya ta ji wani abu mai sanyi ya taɓa kafafunta, a hankali kuma jikin Ruma ya fara saki, har ta zare hannuwanta daga rikon da ta yi wa Yaya ta fadi gefe yaraf.
A lokacin ne ta samu damar ganin jaririn da ke yashe a kasa kusa da kafafunta
Ba yau ta fara ganin haihuwa ba, ita kanta haihuwarta takwas, amma yau sai ta ji duk wani ilmi da ta sani gami da haihuwa ya bace mata.
Daga tsayen take kallon jaririn a yanayin da ta kasa fassarawa tsoro ko mamaki.
Ta dauke kallon ta daga kan jaririn ta mayar kan Ruma wacce ke kwance wan-war kamar gawa, ta kalli zaren cibin da ya hada Ruma da jaririn, sai a lokacin ma ta lura da yadda cibin ya nade wuyan jaririn.
Cikin rashin kuzari ta duka da niyyar warware mishi zaren cibiyar, Sai kuma tsoro ya kamata ta mike tsaye da sauri.
Har yanzu ta kasa gasgata abin da take gani, kashi 90 cikin kaso dari na rayuwar Ruma tana yin ta ne a dakinta, amma ba ta taba lura akwai ciki a jikin Ruma ba. “Anya wannan ba wani sha’anin aljanu ba ne?” ta tambayi kanta da kanta. Saboda suna ganin abubuwa mamaki game da al’ajabi ta dalilin ayyukan mazajensu na tu’ammali da aljanu. Amma a wannan karon abun tsoro da mamakin ya bambanta da wanda suka saba gani.
Cikin tafa hannuwa na rashin sanin abun yi ta ce “To idan ba aljanun ba kuma, ina yarinyar nan ke zuwa? Daga gida sai gida, ko makaranta basu zuwa bare kuma aike, sannan ba hira take fita ba. To ina za ta samu ciki ni Halima?”
Ta karashe maganar tare da kallon Ruma da jaririnta wanda suke yashe a tsakar gida kamar gawa.
” Na shiga uku ni Halima “ta fada da dan karfi, ko me ta tuna kuma, sai ta yi hanyar fita da sauri.
A hankali ta zare sakatar kofar gidan ta leka, babu kowa sai haske da kuma karatun Kur’anin da ke fita ta cikin speakern masallacin.
Haka ta rika zarya tsakanin cikin gida da kofar gida, har zuwa lokacin da Allah Ya taimake ta wani ya fito daga masallacin rike da buta.
Ta fito sosai daga cikin gida, ƙasa-kasa ta rika cewa “Yayansu!”
Usman da ke kokarin shiga bayi ya fasa, tare da juyo inda yake jiyo sautin murya da take kiran sunan shi.
Ganin mahaifiyarshi ba ko lullubi bare takalmi, da hanzari ya karaso wajen ta yana fadin “Lafiya kuka fito cikin daren nan?”
“Ina fa lafiya. Zo mu je gidan.” kai karshen maganar tata ya yi daidai da wucewarta cikin gidan, Usman kuma ya bi bayanta, suka yada zango a inda Ruma ke kwance.
A ruɗe Inna ta ce “Kalli kanwar ka”
Touch light din wayarsa ya kunna, tare da haske Ruma, cikin rashin fahimta ya ce “Me ye wannan din?”
Yaya ma cikin rashin fahimtar ta ce “Ni ma ban sani ba.”
Duk suka yi shiru, kafin Usman ya yanke shirun nasu da fadin “Wai haihuwa ta yi ko me?”
“Oho!” Yaya ta kuma fada a sanyaye.
Usman ya juya sosai yana kallon ta kafin ya ce “To ku in haihuwar ta yi ba ku sani ba, ko ba ku taba ganin an haihu ba?”
“Na taba gani mana” ta amsa a kasalance
“To ita haihuwar ta yi?” Usman ya kuma tambaya
hannuwa ta kuma watsawa tare da fadin “Oho!”
“Af!” cewar Usman yana kallon ta.
“To idan ba haihuwar ta yi ba, wannan jaririn na waye?” Usman ya kuma tambaya yana kallon ta
Ta mayar da hannayenta kan kirjinta, cikin jimami ta ce “Oho!”
Usman ya zubawa mahaifiya ta shi ido yana kallon yadda ta rude lokaci daya, abu take kamar ba cikin hayyacinta ba.
Ya kuma katse shirun nasu da fadin “To ita Ruman tana da rai kuwa ko suma ta yi?”
Sai a lokacin ta tuna akwai suma akwai mutuwa, ta kuma tuna yadda Ruma ta zare jikinta daga nata ta fadi kasa, ta kuma tuna jaririn ma tun da ya fado bai yi kuka ba.
Take wani tsoron ya kara kama ta, da hanzari ta duka saitin fuskar Ruma a kokarinta na gano tana numfashi ko a’a.
A firgice ta dago tana fadin “Wlh ba ta numfashi. Yau mun shiga uku.”
Da ruwan butar da ke hannunsa ya yi amfani wajen shafawa Ruma a fuska, tare da tofa mata duk wata addu’a da ta zo bakinsa.
Cikin abin da bai gaza mintuna biyar ta ja dogon numfashi, Inna da Usman ma suka sauke numfashin a tare.
Ta rika bin su da kallo daya bayan daya.
A hankali kuma abin da ya faru ya rika dawo mata cikin kanta.
Cikin matsanancin tashin hankali ta fashe da kuka, kokarin tashi take, Usman na danne ta, ta rika fisgewa tana ihu.
Inna ce ta danne mata baki hade da fadin “Don ubanki ki yi shiru kar ki tara mana jama’a.”
“Na shiga uku Inna, Baba Alaramma kashe ni zai yi idan ya ji abin da na yi, wayyyo Allahna na shiga uku” Cewar Ruma cike da tashin hankali.
“To ki yi shru kar ya jiyo kukanki, kin san suna masallaci.” ina ta kuma fada bayan ta dauke hannunta daga kan bakin Ruma
Cikin wani kukan Ruma ta ce “Inna ku rufa min asiri, ku saka yaron nan a cikin masai kar Babanmu da Baba Alaramma su ji, zasu kashe ni wallahi.”
A lokacin ne Inna ta tuna ba ta yankewa yaron cibi ba.
Cikin sigar lallashi Inna ta ce “To ki nutsu, sannan ki daina daga murya kar su ji ki su shigo”
Hannu ta sanya hade da danne bakinta, a hakan take fadin “To na yi shiru Inna, daukar shi ki saka cikin masai, kar su shigo gidan”
Inna dai hanyar daki ta yi hade da dakko reza ta dawo inda suke, Ruma na ta gunshekin kuka, Usman kuma na kan turmi zaune, har zuwa lokacin hannunshi na rike da butar nan bai aje ba.
Daga inda yake zaune, yake kallon Inna wacce ta yanke cibiya, ta kuma nade yaron cikin zane ta nufi dakinta da shi.
Bayan ta dawo ne Usman ya ce “To yanzu ya za a yi?”
“Mu jira gari ya waye, sai ka sanar da Baba Malam, amma idar da sallah ka zo ka fita da Ruman gidan Iya (kakarsu)”
Usman ya jinjina kai cikin rashin kuzari kafin ya fice daga gidan.