Skip to content
Part 27 of 28 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Hafsat.

Amaryar Malam Ayuba dai da sabon salonta ta zo, sabon salon da ya shafi kowa a gidan.

Da farko dai ba ta hulda da kowa sai mijinta, abincinta daban, ruwan shanta da bana. Hatta bayinsu zuwanta sai da aka shafe shi da siminti aka buga mishi kwano. Wai ita ba ta iya shiga ya yi kazanta. Kuma wai Kar tana wanka a fara ruwan sama.

Ba ta aiken kowa a gidan sai mijinta. Hatta debo ruwa shi ke daukar bokiti ya debo a kanshi ya kawo mata.

Su Inna Kuluwa sun zama yan kallo, ba ta su yake ba. Wannan abu ba karamin yi wa Hafsat dadi ya yi ba. Saboda yadda ta ga ran su Inna Kuluwa na baci da wannan salo na amarya.

Wani abu kuma da wani lokaci yake ba ta dariya shi ne yadda Babanta ya koma kamar wani ƙaramin yaro. Umurni kawai yake amsa ko yana so ko ba ya so.

Sati biyu da zuwan amarya gidan ba karamin saiti ya dauka ba. Saboda abin da take so a gidan shi take yi, koda kuwa kowa ba ya so.

Girki ma ba ta hura wuta, da risho (stove) take amfani, idan nama ta ce tana so shi Malam Ayuba zai nemo ya ba ta.

Shi ya duk wasu kadarorinshi na gadon da aka ba shi ya siyar. Gonaki duk ya bayar da jingina. Su ma a hankali yake bi yana kara karbar wani abu. Kudaden da ya karba baya da hanyar biyansu. Kuma kullum kara karba yake.

Hafsat dai na ta ta shirya ta tafi makaranta. Bayan ta dawo ta je ta yo wa dabbobinta ciyawa. Daga nan ta yi wanka ta shige dakinta ta kwanta, tana duba littafinta saboda gabatowar exam. Ga kuma debate da aka ba ta, saboda prizes and giving day na karshen shekara da za su yi a makarantarsu saboda masu fita.

Ba iya debate din aka ba ta, akwai program da dama wanda ku san duk tana ciki. A cikin program din career day, ita ce likita. A cikin cultural dance kuma tana cikin fulani. Kuma still ita ce Fulani a cikin nuna al’adun gargajiya na kasarsu. Ga quize da za a yi tsakaninsu da SS1 kuma tana cikin participant. Wannan ya sa ta zama busy, ba ta, da lokacin damuwa mai yawa.

Yau kuma da ya kasance asabar babu makaranta, gari na gama wayewa rana ta fito ta tafi ciyawa. Yau kam sawunta biyu ma. Daga nan ta yi wanka, ta je shagon Maman Iyabo ta karbo abinci. Sannan ta shige dakinta hade da dakko takardar debate dinta tana bita.

Kamar daga sama ta ji sallamar Mama Halima da su Nabila. Ai a 360 ta rarrafo ta fito daga dakin kajin ta kwasa da gudu zuwa inda su Mama Haliman suke ta shiga rungumesu daya bayan daya cike da murna.

Mama Halima ba ta kawo komai ba ganin Hafsat ta fito daga dakin kaji, ta dauka wani abun ya kai ta.

Kai tsaye Mama Halima ta doshi dakin ƴar uwar ta.

Hafsat kuma ta shiga laluben abin da za ta fada. Kafin ta lalubo tuni Mama ta daga labule. Ganin sabon jere sai ta sake laluben hade da juywowa tana kallon  Hafsat.

“Dakin Goggonmu ne, Baba ne ya yi aure” cewar Hafsat cikin rashin nuna damuwa.

“To ke yanzu a ina kike?” Mama ta tambaya idanunta a kan Hafsat

“Ga shi can” Hafsat ta nuna dakin kajin da kuzarinta ba tare da damuwa ta bayyana a kan fuskarta ba

Nabilata yi yar dariya kafin ta ce “Can ɗin ne dakinki, dakin kajin”

Juwairiyya ma dariyar ta yi kafin ta ce “To ta ya zamu shiga kenan?”

Cikin dariya sosai Nabila ta ce “Wai kina nufin da rarrafe za mu shiga dakin naki, mu fito da rarrafe kamar dakin boka”

A tare suka tuntsire da dariya.

Mama kuma takowa ta yi zuwa tsakar gidan inda su Inna Kuluwa ke baje da yaransu. Ta bi su da kallo daya bayan daya. Kafin ta goge hawayen da suka gangaro mata. Cikin tashin muryar dake nuna tarin damuwa ta ce “Kuluwa yanzu Hafsat ce ke kwana a dakin kaji. Ga ku ku uku a cikin gida, amma a rasa wanda zai dauke ta ya jefa a dakin shi. Kar ku manta mahaifiyarta mutuwa ta yi ba fita ta yi ba. Kenan abin da ya faru da ita kuma zai iya faruwa da ku. Ku mutu ku bar yaranku, za ku so su rayu kamar Hafsat? Yanzu kenan da ba dakin kajin a waje za ta zauna ga damuna” cikin kuka ta karasa maganar.

Jikinsu Inna Kuluwa ya yi sanyi, musamman yadda suka ga Mama Halima na kuka sosai. Cikin kukan ta ce “Babu komai. Duk abin da ka yi ma wani dai kai ma za a yi ma. Sannan inda Hindatu ta je kowa ma zai je. Ba ta yi sauri ba, mu kuma ba mu yi nawa ba.”

Ta juya kan kayan da aka zube a tsakar gida da kuma cikin zaure kamar na mahaukaciya, su kadai sun isa sanya ta kuka. Sai ta kara fashewa da kuka.

Wannan ya sa su Juwairiyya fashewa da kuka su ma, sabanin dariyar da suka fara da farko.

Jiki ba kwari Inna Kuluwa ta ce “To wlh ni dai ban hana ta shiga dakina ba, ita da kanta ta ta zabi dakin kajin.”

Shigowar Malam Ayuba ta hana Inna Luba kare kanta

“Yaya! Yaya!! Lafiya ake ta kuka kamar an yi mutuwa? Yaya Halima saukar yaushe? Ya da kuka haka kuma?”

Cikin kuka Mama ta ce “Ba dole in yi kuka ba Ayuba, yanzu ace da ranka ba mutuwa ka yi ba, amma ace Hafsat ba ta da arzikin dakin da za ta shiga ta kwana gari ya, waye ta tashi. Yanzu ace kayan Hindatu haka a wulakance a waje? Malam Ayuba inda fa Hindatu ta je kowa ma zai je”

Sai jikin Malam Ayuba ya yi sanyi, a sanyayen ya ce “wato Yaya Halima, ba za ki gane halin Haftsatu ba ne, wlh taurin kai ne da ita da rashin sabo, amma babu yadda ba a yi da ita ba a kan ta zabi dakin da za ta zauna amma ta ƙi”

Komai Mama Halima ba ta ce ba, illa share hawayen da take yi

“Ya za ku tsaya a tsaye, ku shigo mana” ya yi maganar hade da nuni da dakin amarya.

Suka bi bayanshi, ba yabo ba fallasa amarya ta tarbesu, yayin da su kuma suka baje, suka shiga hira.

Hirar tasu yau duk a kan taron graduation din da, za a yi a makarantarsu Hafsat ne. Kasancewar makarantar ba ta taɓa yayewa ba sai bana. Shi ya sa suke ta shirye-shiryen da zai kayatar. Mama kam ta yi wa Hafsat alkawarin sha Allah za ta zo.

Basu tafi ba sai karfe biyar na yamma, karon farko da Mama ta kawo mata ziyara ta tafi ba ta yi kuka ba.

*****

ASMA’U

Tun dare take fama da labour, shi ya sa asubar fari suka nufi asibiti. A ranar ne ta san abin da ake kira da wuya. Ranar ta bambance kalmar wahala da kuma wuya. Saboda ita kam wuya ta ci ba wahala ba

Ranar ta zagi Mk ya fi kafa dari, ta kara yin nadama fiye da sau shurin masaki.

Ina ma ace wannan wuyar a hanya mai kyau ta ci ta. Ina ma ace abin da za ta haifa ya zama abun alfahari ne ga kowa, Sai dai Kash ba ta san ko iya mutane nawa ne ke addu’ar kar ya iso duniya da numfashi ba.

Ita dai ta raba kafa, idan da ran ko ba ran ya zo duk tana maraba, saboda haka nan koma menene yake masifar ba ta tausayi. Tun bai iso duniyar ba ya fara haduwa da kalubale. Saboda ko irin awon cikin nan da scaning ita ba ta taba zuwa ba. Abin da ke cikin yana lafiya ko akasin haka ba damuwar kowa ba ne. Yanzu ma sai da Aunty Hajara ta ga dai abu ya ki ci ya ki cinyewa sannan ta taso ta zuwa asibiti.

Ba ta haihu ba sai magriba, zuwa lokacin ta gama jigata, ta ci wuya har da baƙar wuya.

Nurses din suka kanga mata baby boy dinta santalale, ita da ta san ubanshi, ta san babu abin da ya bambanta su. Sai dai Mk ya girma wannan kuma jariri ne.

Ba a sallame su ba sai kashegari da safe. Fuskar kowa ba kuka ba guda. Don Momy har kuka ta yi lokacin da ta rungume jaririn. Wai ita ce rungume da ɗan Asma’u ba ta hanyar aure ba.

Haka suka rungudo zuwa gidan Aunty Hajara, a kai ta tsugunne tashi. Saboda da dai ga Baby kato tubarakhallah ya iso cikin aminci, Sai dai ba a san ubanshi.

Shawara ta fi dubu, Momy dai cewa ta yi a tasa Asma’u har Nasara ta je ta kaiwa Mk ɗanshi

Dady kuma ya ce wannan tamkar kisan kai ne. A dai jira Asma’un ta kara dawowa hayyacinta saboda sosai ta ci wuya. Daga nan sai a san me ya kamata a yi. Tun da su ukun nan kacal suka san cewa cikin Asma’u ba da aure aka same shi ba.

Asma’u ba ta fara dawowa daidai ba, Sai ranar da aka wayi gari da kwananta biyu da haihuwa. Sannan ta fara gane kanta.

Misalin karfe takwas ta fito wanka, wanda Aunty Hajara ta taimaka mata.

Sannan a gaban Aunty Hajarar ta kintsa jikinta, ta dauki lafiyayyen tea gami da bread da kwai ta zauna kan kujera yar tsungunno tana karyawa.

Yayin da idanunta ke kan Aunty Hajara wacce take yi wa Baby wanka, har ta gama ta shirya shi tsaf cikin fararen overall masu taushi. Sosai sai ya yi kyau ga kamshi jarirai na ta fita jikinshi mai dadi. Ita kanta Aunty Hajarar sai da ta kasa hak’uri ta ce “Ma Sha Allah! Fine baby wlh. Ina ma ace ta tsabtatacciyar hanya ka zo.”

Komai Asma’un ba ta ce ba. Saboda ita ma abun da take fada kenan a zuciyarta.

Mika mata yaron ta yi hade da mikewa tana fitar da kayan wankan.

Sai da tabbatar ayyukan Aunty Hajaran sun koma tsakar gida, sannan ta gyara zamanta sosai hade da dakko wayarta ta yi snapping babyn mai kyau.

Idanu ta zubawa innocent face din shi. Tausayin kansu su biyun ya kamata. Wani irin kaunar yaron ke ratsa gaɓa-gaɓa gami da ɓargon jikinta. Tana jin a yanzu za ta iya sadaukar da rayuwarta don kare tashi. Shi din bai san komai ba, bai san zai zo a hanyar da ya zo ba. Kuma bai isa ya hana kanshi zuwa ba. Wannan dai ya zame mata aya gami izna, da nan gaba ba za ta taba barin irin wannan ƙaddarar damar kutso rayuwarta ba da iznin Allah

Ko iya nakudar da ta sha aka bar ta da ita ya ishe ta. Mk yana can kwance yana ta baccinshi koda mutuwa ta yi ba sani zai yi ba. Tun da rabon da su yi waya ma ya kai sati daya. Chat din ma ko magana doguwa bassa yi.

Wani abu daya da ya tsare shi ne yana aiko mata da kudi, ba kuma sai ta nuna tana bukata ba. Wannan ne kadai yake mata dadi, sabanin wasu da suke banzatar da mace da zarar sun samu abin da suke so.

Ta mayar da wayar kasan filo da sauri hade da, kwantar da Baby jin takun Aunty Hajara. Ba ta son ta shigo ta kama ta tana kallon yaron.

Aunty Hajaran ta zauna kan carfet din da ke yashe a tsakar dakin da ya zama mallakin Asma’un.

Ledar hannunta ta ajiye, wacce kaya ne second hand masu kyau Mamanta ta aiko mata dasu. Saboda har yaron ya iso duniya ko pant ba a siya Don shi ba. Sai bayan an haihu Dady ya siyo mishi kala biyu, wadanda aka sanya mishi a asibiti, da kuma wadanda aka sanya mishi yau.

Aunty Hajara ta rika daga kayan yadda Asma’un za ta gani. Bayan ta gama ne ta mayar da su cikin ledar tana fadin “Kin ga ai an samu na canjawa”

Komai dai Asma’u ba ta ce ba. Duk abin da ya shafi yaron ba sosai take tankawa ba. Daga haihuwarta zuwa yanzu za ta iya ƙirga maganar da ta yi.

A hankali ta mike zuwa wajen handbag din ta da ke sagale.

ATM ta ciro hade da mikawa Aunty Hajara tana fadin “Dame-dame ake bukata wa yaro da kuma ni kaina?”

“Me ya faru?” Aunty Hajara ta tambaya a sanyaye

“Babu komai ina son ji ne kawai” Asma’u ta amsa

Jin Aunty Hajara ba ta ce komai ba ya sa Asma’un fadin “Akwai kudi a cikin wannan account din. Duk wani abu da kika san Baby yana bukata Aunty, ina nufin ƴan gatan yara, kar ki ji komai ki dakko. Komai da komai nake nufi. Akwai isassasun kudi a ciki”

“Kin yi fushi ne Asma’u?”

Kai ta girgiza alamar a’a

Murya a tausashe Aunty Hajara ta ce “Idan ma kin yi fushin ne, to ki yi hak’uri. Sannan ki duba irin zafi da kuncin da iyayenki ke ji. Isn’t easy Asma’u ace yarka ta haihu ba tare da aure ba. Iya ciki ma yana daga hankali ballantana haihuwa. Mahaifiyarki yanzu haka ba ta da lafiya sosai duk saboda wannan. Kin san su waye iyayenki Asma’u. Idan da ace yaron nan ya zo a hanya mai kyau ne, tabbas daga ke har shi za ku gata. Shi ya sa na so a cire cikinnan mahaifinki ya ki. Da tuni kila ma kin yi auran ki.”

Hawayenta ta ci gaba da daukewa da bayan hannu, cikin murya kuka ta ce “Aunty ban yi fushi ba, sannan ba na jin haushi kowa. Hasalima kunya da kuma tausayinku nake ji. Ban kyauta muku ba abin da na yi. Tabbas na tozartaku gami da zubar muku da mutumci. Amma ya na iya ƙaddarata ce ta zo a haka. Wlh ko mafarkina bai taba kawo min zan aikata wannan ba. Na yi dama, na yi danasani aikata abin da na aikata.

Yaron nan tausayi yake ba ni Aunty. Shi bai san komai ba, bai san a wace hanya ya zo ba. Sannan bai isa ya hana kanshi zuwa ta hanyar da ya zo din ba koda ya sani. Yanzu wannan yaron nawa ne, saboda ko wanda yake da alhakin zuwan shi duniya gudun shi yake yi. Kada abun ya yi mishi yawa. Ga rashin gata ga kuma zuwanshi ta hanyar da ba dace ba.

<< Abinda Ka Shuka 26Abinda Ka Shuka 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×