Skip to content
Part 39 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Riƙe haɓa Ruma ta yi kafin ta ce “Tabbb! Ai, Goggo mune muke musu kallon bassa karatun Mahammadiyya. To wallahi idan kika ji suna rera karatu ki dauka Makka kika je. Su da har da hadisai ma da sauran littattafai suke yi. To ranar Aminatu kanwar shi (tana nufin Mk) da tana koya min wani littafi wai Tajweedi na ji kamar ma ban iya karatun qur’anin ba. Gaskiya ni dai Goggo makaranta zan shiga. Ko Baba Alaramma bai sani ba”.

“Ni dai ba ruwana, kin san dai halin shi. Kuma ina son sanar miki zan yi aure ni ma”.

A firgice Ruma ta dago tana fadin “Aure kuma Goggo, wa za ki aura?”

“Wani ne a can Dawuri, shi ma babba ne a boko, daga ya zo kauyenmu duba makarantu shi ke nan  ya ce yana sona”.

Shiru Ruma ta yi komai ba ta ce ba, saboda abun ya zo mata a ba zata, wai Goggonta za ta yi aure. Ikon Allah.

HAFSAT

Hausawa sun ce wai laifin dadi karewa, to hutu dai ya kare.

Duk da ita din ma dai ba ta huta ba, saboda aikin gonar Mama Halima, sati uku da suka yi suna hutun kusan duk a gona ta yi shi. Rugar ma sai ta kwana biyu ba ta leka ba.

Shi ya sa Dawurin ma da take ta son zuwa ba ta samu dama ba.

Sai dai duk wani hatsi da Mama Haliman ta noma tuni ya je Dawuri, Sai wanda ta ba Malam Ayuba kyauta.

Abu ma fi dadi a wurin Hafsat shi ne yadda Mama Halima ta shawo kan Malam Ayuba wajen a gina mata daki, saboda yanzu squatting suke yi ita da su Inna Kuluwa, don ma ruwan ya yi sauki, amma duk da haka bassa kwana dakin, za dai su yi hidimominsu iya rana, dare kuma su dawo dakin Kajin Hafsat din su kwana.

Shi ya sa zaman dakin ba dadi, ga su Danladi na fitsarin kwance ga shi kuma babu isasshen windows da iska za ta shiga ta koro fitsarin, shi ya sa kafin asuba hancin Hafsat yake banuwa ya lalace, ita din nan da ba ta raina wari.

Ba iya dakinta kawai za a gina ba, har da gyara na Inna Kuluwa.

Ita dai masu gina dakin Hafsat daga Dawuri za su zo, na Inna Kuluwa kuma a nan cikin garin ne.

Kamar ko wane lokaci haka ta tafi school ba a dama musu kokon safe ba.

Inna Luba ce mai aiki, kuma wani tashen rashin mutunci take yi yanzu a gidan, komai sai ta ga dama take yi. Idan ma ta yi din sai ta kwaɓashi mai ci ya ci, wanda bai ci kuma ya bari.

Hafsat dai bi take yi, tana nan shiru a gidan, iyakacinta dasu gaisuwa.

Idan akwai wani abu da baya mata dadi shi ne yadda suke nuna babu ruwansu da duk wani abu da ya shafe ta. Dan wani guntun ciwo sai ta gama shi tas ba tare da sun sani ba.

Karin Maganar nan wai ba ruwan kowa da kowa, bakuwa a dakin mahaukaciya.

AHMAD

Yau kimanin kwanaki 12 kenan da ya ga Juwairiyya, kullum cikin zaman jiran tsammanin jiran kiran mai Pos yake amma shiru.

Bai san ta ya zai kamanta kwanaki 12n nan ba, ji yake ya fi duk sauran kwanaki shiga damuwa da kuma tashin a hankali.

Duk yadda zuciyarshi ke tursasa mishi zuwa gida ya ki bin umurninta, kila shi ya sa ya fi shan wuya, har wata ramar dole ya yi. Kila kuma don saboda ciwon kan da yake yawan yi ne.

Yanzu ma zaune yake a gefen gadon, hannayenshi du biyun dafe da kanshi, office yake son zuwa amma ya kasa tashi ya shirya, bare ya nemi abin da zai ci. Saboda shi da kanshi yake girkinshi, bai faye sayen abinci waje ba.

Bai san dalilinshi na fitowa saman entrance din ya yi tsaye ba. Lokaci daya kuma yana kallon sojojin da ke tafiya wurin aiki, wasu kuma suna dawowa, duk wadanda suka hango shi, Sai sun zo sun kawo gaisuwa.

Da kai kawai yake amsa musu, ko ya daga musu hannu, ya kwashe tsawon mintuna talatin a wurin kafin ya koma cikin gidan nashi.

Wanda yake dauke da katon falo, da aka malale shi da koren carfet hade da lemon green cottons masu tsananin kyau da tsada.

Sai katon plasma da tuntaye na sarauta zube a kan carfet din

Daga nan sai kofar da za ta kai ka  bedroom, bau komai a cikin bedroom din sai katuwar katifa wacce ta ji lallausan bedsheets gami da bargo lumtsumeme. Sai wardrobe da kuma shoe rub, akwai toilet a ciki mai girma wanda ya kawatu da komai na zamani.

Duk a cikin falon, akwai wata kofa da za ta sadaka da wani dakin wanda babu komai a ciki sai katifu biyu shimfide a saman tiles.

Sai wani ɗan corridor daga cikin dakin wanda zai kai ka kitchen.

Idan ka dauke sansanyan kamshi fresheners masu dadi da ya hadu da sanyin Ac babu komai a gidan.

Wanka ya fara yi, cike da kwarewa ya shirya cikin uniform din Shi nevy blue, rank din Shi na assistant vice Air Marshal ƴa fita das a kan kafadarshi.

Kallo daya za ka yi mishi ka fahimci he is gallant officer, and very young soldier.

Kitchen ya nufa a tsaitsaye kawai ya hade tea ya sha. Kafin ya fita, saboda tuni ya ji zuwan motar kai shi office.

Yana a cikin motar ne kira ya shigo wayarshi

Yanzu ba ya ƙi daga bakuwar lamba, yana jin tsoron wuce sa arshi, don haka ya yi receiving call din

Tun kafin su gama gaisawa ya fahimci mai muryar, Sai kuwa ga shi wancan din ya ce “Sunana Nura, ni ne ka ce in binciko ma wannan yarinyar ko AK”

“Na fahimta” Ahmad ya amsa a hankali.

“Yauwa, dama Ina son fada ma ne na samu AK din, sai dai ba shi da lambar waccan yarinyar. Kuma ya ce bai san gidansu ba, amma tare suka yi secondary school”

“Zan zo jibi sha Allah, zan neme ka, Sai ka nemo min shi” Ahmad ya kuma fada kamar ba ya so

Daga haka kuma suka yi sallama ya sauke wayar a hankali daidai da fitar ajiyar zuciyarshi, Sai kuma ya dauke kanshi zuwa gefen titi inda sojoji ke ta aiko mishi da gaisuwa, wasu kuma sara mishi suke yi, hade da daga murya su ce “Morning Sir!”

*****

ALARAMMA

Shawara ta fi dubu wane ɗari, goma sha biyar din banza, haka Alaramma ya rika tufkawa yana warwarewa, tsoron shi kar ya ga tsulum ya ga kuma tsame, tun da dai zaben nan ya taho, shi kanshi yana da yakinin Alhaji Bashir zai kai bantenshi, saboda dan siyasa ne da ludayinshi yake a kan dawo.

Misalin karfe takwas ya fita don zagaya gidan marasa lafiyarshi, yayin da mukarrabanshi suke take mishi baya, yana shiga kwana ya hadu da Malama Aisha, hannunta rike da dan karamin yaronta cikin uniform din primary ta kudi.

Karon farko da ya ji shigar kayan makaranta ta burgeshi.

“Likita bokon Turai, ba ku so a mutu ba ku so a yi lafiya”

Malama Aisha ta yi dariya hade da gaishe shi, suka gaisa faran-faran kamar ko wane lokaci

Ya rike hannun Aiman yana mishi wasa kafin ya ce “Malama ina ko son magana da ke”

Cikin mayar da hankalinta a kanshi ta ce “Ina jin ka Malam”

“Maganar ta zama ce don haka zan zo har gida in same ki idan ba damuwa”

Cike da fara’a Malama Aisha ta ce” Allah Ya kawo ka, ina jiranka “

Shi kuma ya yi godiya suka wuce.

*****

HAFSAT

Yau kwalemar komawa sabon ɗakinta take yi, da Mama ta zuba kudi aka yi mata gini ba na wasa ba.

Katon daki ne dauke da bathroom a ciki, Sai kuwa wani ƙaramin daki kamar kitchen, duk a cikin dakin, tun daga cikin toilet din zuwa ƙaramin dakin da kuma babban shafe yake da tiles mai kyau da tsada, sama kuma roba silin ne golden mai kyau.

Wannan gini ba karamin tayar da hankalin matan gidan ya yi ba, don basu yi tunanin haka za a yi shi ba. Sun dauka dan karami za a yi. Musamman tiles din da aka sanya da roba silin din.

Hatta Inna Kuluwa da ta ci arziki aka hada da nata har da rufin kwano aka yi mata hakan bai hana ta jin zafin abun ba.

To bare su Inna Luba kuma, Inna Luba kam yau ma a sama take kamar hancin gauta, don tuni suka fara haurawa da kashin duwawunta wato Inna Kuluwa, tun suna yin ciki har da suka daga murya, inda Inna Kuluwa ta ce, Inna Luba baƙin ciki take yi mata an buga mata kwano.

Cikin masifar da ta dade tana cin Inna Luba ta ce “Ina kudan yake bare romanshi, me kika aje wanda ban aje ba da zan yi miki bakin ciki Kuluwa. Komai da kike ina da. Abun daya ne ban da shi ban haifi dan iska gantalalle ba, wanda baƙin halinshi ya kore shi daga gidan uban shi”

Ita ma Inna Kuluwa cikin salon na ta bala’in ta ce “Karya kike yi Luba, na aje abubuwa da yawa wadanda ba ki aje ba, ba kuma ki isa ki ajiye ba. Kuma dan’iska gatallale da kuke magana idan yanzu Malam ya mutu sai an kasa ya dauka sannan ku dauka, ni ina son abuna, tun da yunkuri na yi na haifi abu na. Ku kuma da kuke min gori, ku ci gaba, mai ƴaƴa mata dai ba ya rufe kofa”

“Ni na rufe kofa ta rufe wlh, kuma mugun bakinki ya koma bisa kanki, dama kin aje abubuwan da ban ajiye ba mana. Tun kina dauke da mugun hali, hassada da mugun nufi, su kadai kika fi ni”

Cikin shewa Inna Kuluwa ta ce “Wlh gaba kika yi na biyo baya, idan kuma zama fara bankada ne Bismillah, ni din nan warwareki zan yi tas wlh, kin san dai komin ki a tafin hannuna yake.”

“Ke ma na ki a nawa tafin hannun nawa yake, kuma kin san ke din nan kin fi ni mugun hali, duk ba bakin halin naki ne ya koma kan ɗanki ba, ga yarinyar da kika so illatawa nan, bayan kin gama jawa uwarta sharri Allah Ya jikanta Ya mayar a kan ɗanki”

“To! To!! To!!! Sarakan fada, kaji garin ya waye ko, za ku fara.” cewar Malam Ayuba da ya shigo kamar an jeho shi.

Cike da takaici Inna Kuluwa ta ce “Luba ce, tun da aka gina dakin nan take baƙin hali…”

“Ai ba sai kin fada ba, na sani kuma na fada mata ni a ginin dakunan nan biyu wlh kwandalata babu a ciki. Yaya Halima ce ta ce ta gaji da ganin kayan ƴar’uwarta a waje da kuma ganin ƴar ƴar’uwarta tana kwana a dakin kaji. Ban san ko sau nawa zan maimaitawa Luba wannan zance ba. To da rabon zaman wannan dakin da kike ciki ma ya gagare ki, Sai ki koma can gidanku a gina miki irin wanda kike so”

Ya ɗan tsahirta kadan kafin ya ce “Kar ku fasa maganar ku ci gaba har ku tara min makota, ni kuma in hada da mokatan in kore ku wlh. Kun ga Murjanatu duk ta fiye min ku”

Amarya da ke cikin daki sai ta saki shewa hade da kwallara guda ka rantse da Allah amarya aka dakko, daga cikin dakin ta shiga rera wata waƙa “Hadari ya yi banga-banga bai taso ba, ni ma na yi banga-banga bakin garka…”

Hafsat dai aikin shigar da kayanta take yi, sai kuma Farida da Na’im da suka shigo a lokacin da Baba ke fada, suka shiga taya ta.

Duk wasu tarkace cikin wancan dakin mai kama da kitchen suka loda su.

Cikin main bedroom din Kuma suka saka gadajen karfen guda biyu, suka da lafiyayen zannuwan gado masu taushi amma marasa nauyi.

Dayan bangon kuma sif mai biyu (Mama Halima ta sa aka yi mata) suka sanya da mirror, yayin da suka dora jakunkunan Hafsat can saman sif din, suka zuba sabbin coffee color na sabbin labulaye da Mama ta kawo mata.

Sai kuma katon enlargement na hoton ta wanda aka dauke ta ranar graduation din makarantarsu sanye da kayan Fulani ta rungume kwaryar Fulanin daidai saitin kugunta.

Ba za ka taba yi wa hoton kallo daya ka kawar da kai ba. Saboda kyan da ya yi sosai Hafsat din ta fita kamar ba ita ba. Kitson Fulanin nan ya kara fito mata da yawan gashinta ga mi da tsawon shi. Sai ta dan saki leben kasanta kaɗan Sai ya zama kamar tana shagwaba ne.

Sai kuma wani abu enlargement din hoton Inna, tana sanye da farin hijabi, kallo daya za ka yi mata ka fahimci ita ce ta haifi Hafsat saboda kamanninsu, ga shi ba ta tsufa sosai ba, sosai yarintarta ta fito a hoton.

Haka su Na’im sukai ta yaba komai na ɗakin, Sai dai kunyar duniya ta ishi Hafsat, yadda suka wuni zur a gidan suna taya aiki ya kamata ace kafin su tafi sun ci abinci. Shi ya sa jikinta duk ya yi sanyi, yake kawai take buga musu. Sune suka fara rare bayan gidan suka yi wanka,suka shirya cikin kayan Hafsat, Hafsat din kuma ta zuba nasu a laundry basket da ke cikin toilet din, Sai ta wanke ta kai musu.

Ganin za su tafi babu komai sai ta kasa jurewa ta fashe da kuka, ina Innarta ko Ya Nasir na nan, ta tabbatar sai sun fita kunyar bakinta ayau da suka yi mata karamci mai tarin yawa.

Kukan da ya tashi hankalinsu Farida suka yi ta tambayarta menene, Sai dai ta ce ba komai, dakyar suka lallashe ta rage yawan kukan sannan suka tafi.

Sai ta rasa abin da ke yi mata daɗi, shi ya sa ta haye saman gadonta ta rungume hoton Inna duk da bayan sallahr la’asar ne hakan bai hana bacci dauke ta ba, to ga gajiya ga yunwa tun abincin safe.

Bari mu leka Madiddi (AHMAD)

AHMAD

Alhamis 5:00pm

A daidai wannan lokacin Ahmad ya fito sanye ciki yadi coffee color mai taushi, wanda ya kwanta jikinshi hade da fito mishi da hasken fatarshi. Kamshinshi mai dadin shaka ya cika farfajiyar gidan. Fuskar nan very innocent, kallo ɗaya za ka yi mishi a fahimci akwai nutsuwa a tare da shi

Duk kirari gami da gaisuwar da dogarawan ke mika mishi bai bude bakinshi da niyyar amsawa ba.

Shi ba miskili ba ne, amma haka nan magana ke mishi wahalar yi wani lokaci.

Sannan ya tsani hayaniya, bata mishi rai take yi.

Yanzu haka sai da ya ji zuciyarshi ta dan sosu, idan so samu ne idan ya fito kar wanda ya ce mishi komai sai idan shi ne ya bukaci hakan, amma sun kasa ganewa.

Calmly ya fice daga gidan cike da kwarewar tuki, kai tsaye kuma shagon Nura mai Pos ya nufa. Bai fi awa daya da sauka garin na Dawuri ba, abinci ma a tsaitsaye ya ci, sannan ya watsa ruwa gami da shiryawa don zuwa shagon na Nura.

Da fara’a Nura ya tarbe shi gami da girmamawa, can cikin shagon ya shigar da shi hade da ba shi wurin zama, lokaci daya kuma yana fadin “Bari in kira AK din, ba ka sanar min kana zuwa yanzun ba, da na kira shi tun kafin ka zo yallaboi”

Komai Ahmad bai ce ba, Nura kuma ya shiga kiran da layin Ak.

“Yana zuwa yallaboi” cewar Nura lokacin da ya gama wayar da Ak, Sai kuma ya juya kan kostomominshi.

Ahmad kuma ya shiga taba wayar shi.

Ba jimawa kuwa sai ga Ak ya shigo shagon, cikin yarensu na samari masu tashen kuruciya ya ce “Ga ni, kaya sun sauka ne?”

Nura ya juya ganin shi zuwa wurin  Ahmad, da ya yi kamar bai san Ak ya shigo ba, ya ce “ga mai neman ka nan”.

Take Ak ya koma cikin nutsuwarshi, kafin ya yi wani abu kuma har Nura ya ce “Ranka ya dade ga shi nan”.

<< Abinda Ka Shuka 38Abinda Ka Shuka 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×