Skip to content
Part 50 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

*****

HAFSAT

Suna isowa garin Maƙera ana kiran sallahr La’asar, shi ya sa yana ajiye ta kofar gida ya koma masallaci, ita kuma ta shiga ciki don shiryawa.

Goggo Amarya ce ke fada mata Ahmad ya kawo musu, buhun shinkafa, cartons na taliya da maccaroni da kuma manja da Mangyada. Cikin sauri ta yi wanka hade da yin sallahr la’asar, ta shirya cikin doguwar rigar atamfa mai dauke da partern blue, shi ya sa ta yi amfani da blue hijab, da kuma agogo mai dauke da fata blue, Sai kuma ta sanya farin takalmi plat, sosai ta yi kyau, tana shirya kayanta cikin jakar tafiyarta ne ta ji Malam Ayuba na kwaɗa mata kira.

Barin abin da take yi, ta yi hade da saurin fita kofar dakin ta duka tana gaishe shi.

Bayan ya amsa gaisuwar ne ya ce “Yauwa ashe ma har kin shirya, to ki yi mishi godiya kin ji, ya kawo mana shinkafa, taliya ke har da mai. Ga kuma kudin cefane ya ba ni. Don haka don Allah Hafsat idan kin je makarantar nan ki yi kokari kin ji, kar ya kashe kudin shi a banza. Duk da na san kina da kokari sosai “

Kai Hafsat ta jinjina alamar to, ya dora da” Wuce ki karasa shirin yana jiran ki”

“To” ta amsa hade da mikewa zuwa cikin dakin. Ta karasa zuba abin da ta san za ta bukata, sannan ta zuge jakar ta sagala.

Sallama ta yi wa mutanen gidan, bayan ta jawo kofarta ta kulle hade da ba Goggo Amarya key din, saboda ita ce take dan shiga harkarta kadan.

Tun da ta fito ya bude mata dayar kofar, da sallama ta shigo, ya amsa ba tare da ya gyara daga kwanciyar da ya yi jikin kujera ba. Hancinsa ya shiga shakar humrah mai dadi hade da maya-manya da ta yi amfani dasu. Ya jima a haka yana kokarin controling din yanayinsa. Kafin a kasalance ya yi wa motar key, hade da daukar hanyar da za ta fitar da shi daga unguwar.

Haka suka rika tafiya shiru, har Hafsat ta yi mamakin canjin na shi, kamar ba shi ne dazu yake dariya ba, yanzu kuma magana ta gagare shi, ita ma sai ta kame bakinta, dama maganar ba damunta ta yi ba.

Sai da suka fara shiga garin Dawurin ne ta ji ta ga yana kokarin kiran wata lamba, ba ta san me ake mishi ba ta ji dai ya ce “Shi kenan mu hadu a asibitin “

Zuwa yanzu kam ta fara gane garin Dawuri, shi ya sa daga yadda ya mike ta fahimci asibitin zai fara zuwa.

Sun dauki hanyar asibitin ne, ta fahimci wata farar mota da ke gabansu ta yi musu signal.

Ahmad ya mayar da signal din yana murmushi, haka suka rika tafiya cikin farar motar na gaba su suna baya.

Har zuwa lokacin da aka wangale musu gate din *A&A CLINIC* special wurin parking din nan motarsu da farar motar suka nufa.

Bayan motocin sun yi parking ku san a tare kofofinsu suka bude, Ahmad da Asad suka bayyana.

Asad ma kananun kayan ne a jikinshi sai dai shi black wandon jeans ne da shirt fara.

Hafsat da ke cikin mota ta rika bin su da kallo cike da sha’awa. Haka nan ta ji sun burge ta, musamman yadda suka tari junansu ya nuna mata akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu.

Ba za ta iya jin me suke tattaunawa ba, amma koma menene ta fahimci mai muhimmanci ne.

Kamar 5mns da haduwar tasu Ahmad ya juyo wurin motar hade da bude Hafsat kofa.

Haka ta fito duk a daburce, saboda kallon da Asad yake mata. A hankali ta ce “Inawuni?”

“Alhamdulillah Amarya, ya hanya?”

Komai ba ta ce ba, illa kan ta da ta ajiye kasa cikin kunya.

Ahmad kuma ya yi kamar bai san me suke ciki ba, Sai ma cewa Asad ya yi “Let’s go!”

A tare suka jera, yayin da Hafsat ke bin su a baya, yadda suke tafiyar ne ya tuna mata da lokacin da aka kawo ta asibitin ba ta da lafiya. Tabbas Asad da Ahmad ne ta gani sun juya baya suna tafiya.

Saboda abun da ya bambanta wancan lokacin da wannan kawai kayan jikinsu ne.

“Ikon Allah” ta fada a bayyane. Shi ya sa aka ce tsakanin hak’uri da rashin hak’uri ɗan taƙinsu kaɗan ne. Sannan rabonka kana zaune yake iske ka har gida.

A wancan lokacin ta matsawa kanta ganin fuskokinsu sai ga shi Allah Ya kai mata fuskar har gida. Cikin iko da buwayarsa, har zai zarga igiya mai karfi a tsakaninsu, wacce za ta dunkule su wuri daya.

Tun da suka shiga asibitin nurses din ke kawo gaisuwa, suna karba, wata kuma ba sa amsawa a haka har suka isa kofar office din, sai a lokacin ne kuma Ahmad ya juyo, yana kallon ta, da ido ya yi mata alamar ta ta biyo shi ciki, shi kuma ya shige.

A cikin ta same su tsaye gaban wasu cumputers, saboda koda ta shigo basu juyo ba, sosai ta shagala da kallon su, yadda suke abu cike da kwarewa gami da ilmi.

Babu wanda zai kalli Asad da Ahmad bai fahimci suna da tarin ilmi ba, apart from that ma, za ka fahimci akwai shakuwa gami da fahimtar juna a tare da su.

Sallamar wata nurse ne ya sanya Asad juyowa, sabanin Ahmad da ya yi kamar bai ji an yi sallama ba.

Da hannu ya nuna Hafsat, dalilin da ya sanya nurse din nufar Hafsat din, hannun rike da ƴar karamar robar daure hannu idan za a ja jinin mutum, Sai kuma sirinji (syringe)

“Kawo hannun” cewar nurse din

Jikin a sanyaye Hafsat ta mika hannun, karfin hali kawai take yi, amma kam ta tsani abin da zai huda mata jiki.

Cike da jin zafi ta bude idanunta da suke rufe sakamakon tsira mata sirinjin da aka yi, da sauri ta janye su, sakamakon hada idon da suka yi da Ahmad wanda ya yi tsaye a hannayenshi a cikin aljihun wandonshi yana kallon su.

“An ɗiba Sir” cewar nurse din

Rubutu Asad ya yi a wata yar farar takarda ya mikawa nurse din.

Bayan fitar nurse sai suka jona a tattaunawarsu, wacce Hafsat ba ta fahimtar komai.

Gajiya ta yi da zaman office din ta fito waje ta zauna, tana ganin yadda mutane ke zirga-zirga a cikin asibitin.

Masu kudi da talakawa, 6ar birni da kuma na karkara irin ta.

Wajen awa daya da tafiyar nurse din sai ga ta ta dawo, hannun rike da takarda.

Ko minti daya ba ta yi a office din ba ta fito, Sai da ta dan waiga sannan ta ce “Yi hakuri don Allah zo mu yi magana” ta yi maganar kamar mai raɗa.

Cikin wani daki suka shiga, Hafsat duk a tsorace take “Sunana Hassana”

Kai Hafsat ta jinjina alamun ta fahimta

“Ke kanwar Oga Ahmad ce”

Kan Hafsat ta kuma jijjigawa alamar eh

“Yauwa don Allah wani taimako za ki yi min, ki ba ni lambarshi ƴar kanwata don Allah”

“Ai ba ni da waya” Hafsat ta amsa ta kamar wata mara wayau

“Oh my God!” cewar nurse din cike da takaicin abun

Sai kuma ta ya go wata farar paper ta yi rubutu a kai hade da nade ta, ta miƙawa na Hafsat tana fadin “Don Allah ki taimaka min ki ba shi.”

Kai ta daga mata alamar to, daidai lokacin kuma Asad ya leko cikin dakin fuska babu alamun wasa ya ce “Me take yi a nan?”

“Cewa ta yi za ta sha ruwa, shi ne na ba ta” cewar Nurse Hassana.

Ya juya kallon shi kan Hafsat wacce reaction dinta Bai nuna abin da Nurse Hassana ta fada ba ya ce “Muna jiran ki”

Bai jira cewar ta ba ya juya.

Ita ma sai ta biyo bayan shi.

Bayan kammala interview din, exam office ya tura su, a can ta cije komai hade da yawa n thumbprint, yayin da ta baro Asad yana biyan kudaden da za a biya.

Cikin motar ta shiga hade da sauke glass tana kallon yadda daliban ke yi shiga wani wuri da aka rubuta dinning Hall.

Ta shagala sosai da kallonsu, wayarta ta shiga vibration alamun kira, da sauri ta daga kasancewar Ahmad

Ya amsa sallamarta hade da tambayar “Kun gama ne?”

“Ban sani ba ko akwai sauran wani abu, amma dai har thumbprint din na yi.”

“Interview din fa?”

“Shi ma na yi.”

“Kina ina yanzu ?”

“Ina nan cikin mota”

“Asad din fa?”

“Yana can office… (shiru ta yi ganin Asad din yana zuwa, don haka ta ce) shi ma ga shi nan zuwa”

“OK.” ya fada hade da yanke kiran.

Sauke wayarta tata ba dadewa Asad ya karaso.

Sannu ta yi mishi hade da godiya, ya amsa hade juya kan motar

Shi ma AMI ya fara zuwa da ita, ya ce ta shiga ta dauki abun da take so

Tare suka shiga suka rika zagaye store din, komai ba ta dauka ba, shi ne ya daukar mata kalolin biscuit da chocolate hade da turarurruka irn wanda ya ga Maman Zarah na amfani dasu, sannan suka fito.

Bayan ya dire ta ne ya ce, “Zuwa karfe biyar za a zo a mayar da ita gida, ba zai samu zuwa ba, saboda akwai wasu ayyuka da zai yi a asibiti, yanzu haka jiranshi ake yi.”

Kai kawai ta jinjina alamar to, hade da yi mishi godiya ta shiga cik gidan.

Bangaren Ahmad kuwa bai samu damar bude videon da Asad ya ce ya tura mishi ba, sai misalin karfe biyu, lokacin da yake zaune yana jiran isowar gwamna da za su gabatar da wani meeting a kan matsalar tsaro.

Relaxed ya yi a kan kujera hade da bude videon, yadda Hafsat ke amsa tambayoyin ba karamin burge shi hade da fitar da shi kunya ta yi ba, ai ban san lokacin da ya dago bayanshi daga kan kujerar ba, yana kara tattara duk hankalinshi a kanta

“Wowwww!” ya fada lokacin da videon ya kare, ya tsinci kanshi da maido shi baya, ya kuma kalla.

Lambarta ya lalubo hade da doka mata kira, sai dai ba a daga ba, don a lokacin Hafsat bacci take yi.

Haka ya ci gaba da kallon videon har sai da aka sanar mishi isowar gwamna.

Hafsat kam sai hudu Mama ta tashe ta, shi ya sa a gurguje ta yi sallah, bayan ta idar wanka ta kara yi, Mama ta kuma zuba mata abinci ta ce ta ci.

Tana cin abincin yayin da Mama ke haɗa mata kayan ta.

Biyar da mintuna ta ji ana horn, dalilin da ya sanya Mama ce ma mata ta leka.

Wata jibgegiyar mota ta gani, ire-iren wanda Ahmad ke hawa, Sai dai yanzu wani mutum ne ya fito, sanye da kayan fada, da sauri ya kai kasa yana zabga mata kirari, daga karshe ya ce”An ce in zo in kai ki gida Ranki-ya-dade. “Hafsat da ta saki baki kamar saukar markaden farko, gida ta juya cike da mamakin mutumin, tana isa kuwa ta fara fesawa Mama labari.

” Ikon Allah kenan Hafsat, ina ma ace Hindatu na da rai ta ga wannan rana, lallai da ta yi farin ciki mara misultuwa. “cewar Mama cikin wani irin yanayi mai wahalar fassarawa.

Hafsat ma duk sai jikinta ya mutu, wannan ya sa ta juya zuwa dakin su Nabila inda ta sanya wayarta caji a lokacin da za ta yi bacci.

Hawayen da suka tarar mata ta sharce, hade da daukar wayar tana kallon missed called din da aka yi mata

Akwai na Juwairiyya da Nabila, Sai Ya Tajuddeen, Sai na Ahmad wanda bai wuce 10mns ba, karon farko da ta yi attempting kiranshi, kiran na shiga ya yanke hade biyo baya.

“Assalamu Alaikum”

Sallamar ya amsa da ɗan bacin rai ya ce “A ina kika ajiye wayar”

Yanayin muryarshi ya sanyata kara nutsuwa ta ce “Na sanya a caji ne, Sai kuma na yi bacci”

“Da kika tashi fa?”

“Sallah na yi, hade da yin wanka sai kuma na shirya” ta kuma amsawa

Daga can ya ce “Ba na son ina kiran wayar mutum baya dagawa, always your phone is with you. Idan Kuma ba caji before ki kai cajin ki sanar min, da lokacin da kike tunanin amsowa”

“To” ta amsa

Ya ɗan rage fushin muryar tashi, saboda da gaske ya ji haushi, ya tsani ya kira mutum sama da daya a lokuta mabanbanta kuma ba a daga ba “Akwai wanda ya zo daukar ki yanzu?”

“Ga shi can a waje yana jirana”

“OK.” ya fada hade da yanke kiran.

Shiru ta yi tana kallon screen din wayar, Sai kuma ta koma gefe gado ta zauna, ta shiga rubuta mishi sako kamar haka “_Ka yi hakuri don Allah, ba zan sake ba. Kuma na gode sosai da dukkan dawainiyarka, Allah Ya saka maka da mafificin alkairi_”

Zaune yake a lokacin yana kara tausar zuciyarsa, sakon ya shigo, kamar ba zai dau wayar ba, Sai kuma duba, ajiyar zuciya ya sauke, yayin da maganganun sakon ke bin ko wace gaɓa tashi suna narkawa, a take ya yi melting. Duk wani fushi ya babu, ya ji babu wacce yake son gani sai ita, yayin da jikinshi ke muradinta, duk da ya sha gargadin jikin na shi a kan son kasancewa da ita, har yanzu jikin na shi bai karbi gargadin ba. Duk lokacin da zai kasance shi kadai, zai tsinci kanshi da son jin Hafsat a tare da shi. Ba Ya son hakan, saboda kallon karamar yarinya yake yi mata.

A kasalance ya aika mata da na shi sakon kamar haka “_It’s OK. Safe trip”

Sakon ya shigo ne daidai motar su Hafsat na haurawa kan titin zuwa Maƙera, game din da take yi ta dakatar hade da bude sakon ta karanta.

A cikin sakon ta rasa me ye ya yi mata dadi, duk da ba wata magana doguwa ya yi ba, ko wasu kalamai na soyayya irin wanda take karantowa a novel, amma sai ta tsinci kanta da maimaita karanta sakon duk bayan wasu mintuna.

*****

ASMA’U

Misalin karfe goma na dare ta ji alamun naƙuda, wannan ya sa ta yi wa gidan Maman Nawwara tsinke, Maman Nawwara ita ta yi ta fama, da taimakonta Asma’u ta sako kyakkyawan yaron ta zuwa duniya, da misalin karfe biyu na dare.

Kallo daya za ka yi mishi ka fahimci AG ta haifa, har da hasken fatar.

Sai kuma a lokacin AG ya samu nutsuwa, yadda ya nuna damuwa har sai da hakan ya tafa zuciyar Laɗifa sai dai kawai ta daure, amma tabbas ta ji zafi

Sai Asuba Asma’u ta koma gidanta, bayan an gyare su tsab ita da Baby.

A lokacin ne kuma aka rika sanar da ƴan’uwa da abokan arziki.

Zuwa karfe goma na safe gidan Asma’u ya fara karbar yan ganin Baby, musamman ƴan’uwan AG.

Ganin status din Asma’u da sabon Baby ba karamin tayarwa Mk hankali ya yi ba, abun da yake nema ido rufe, ga Asma’u ta samu, da kanshi ya ce kodai hakkin Asma’u ne ke bin shi? Da kuma hakkin Abdallah?

Ido ya runtse cike da tashin hankali, koda yana son dawo da Abdallah kusa da shi, ba abu ne mai sauki ba, zubewar kima da mutumci yake gudu, ga kunyar iyayen shi, ga ta matarshi ga kuma ta sauran mutanen gari. Akwai wahala a dakko Abdallah. Zai dai tuntubi Asma’u idan ta amince ya rika daukar responsibilityn Abdallah amma yana a hannunta. Kila hakan zai sa a wannan karon Ruma ta haihu lafiya ya kuma samu damar daukar abin da Ruman ta haifa har ya raine shi.

A yanzu ne Asma’u ta san ta yi haihuwar gata, maimakon ɓoye-ɓoye da jimami yanzu kowa fada mishi ake yi, hade da alfahari.

Lallai abun alkairi yana da dadi, sakamakon na barna, da ake boye shi, da ƙi bayyana shi

Sosai sai Abdallah ya rika ba ta tausayi ganin shi duk ya rasa irin wannan gatan na uba da kuma dangin uba

AG kam ya yi rawar gani, dama kullum cikin taka ta yake, a kan Asma’u, AG miji ne da ko wace mace za ta so samu, idan dai a kan kyautatawa zamantakewa ne, yana kokarin sauke duk wani nauyi da Allah ya dora mishi, bai taba gazawa ba.

Abin da kawai ya kasa zama a wurin Asma’u shi ne maye gurbin Ahmad, har gobe tana kewar shi, da kewar abubuwa da yawa da suka shafe shi. Karamcin Ahmad da iya kula da mace ya fi karfin mantuwa.

<< Abinda Ka Shuka 49Abinda Ka Shuka 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×