Skip to content
Part 56 of 60 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Bangaren Hafsat kam tana komawa daki Mama ta kira hade da shaida mata an bar ta zuwa Ɓurma.

Cike da mamaki Mama ta ce” Lallai Hafsat na yarda ke yarinya ce, daga yi miki gatse, shi ne kika aikata, Allah Ya sa ba cewa kika yi na ce ki tambayi mijin ki ba”

Dariya ta ƙwacewa Hafsat saboda ba ta san gatse Mama ta yi mata, cikin dariya ta ce “Ni dai don Allah ku biyo ku dauke ni Mama, idan ma ba ku zo Allah tun safe zan sanya a kawo ni.”

“Sai dai kam ki sanya a kawo kin, don ni dai wlh ban zuwa ɗaukar ki” ba ta jira cewar Hafsat ta yanke kiran tana ci gaba da mita

 tsaye ta yi da wayar a hannu tana dariyar Mama kiran Ahmad ya shigo ta WhatsApp, wurin zamanta ta karasa, wato cikin bedroom a saman gado, jikin fuskar gadon ta jingina bayanta kafin ta daga kiran.

Tun da suka fara video call da shi ba ta taɓa ganin ya kira ta yana personal kayan gida ba Sai yau. Duk lokacin da zai kira ta, yana nan cikin shiri kamar ya sakkowa daga Dutsen yaƙi ko zai hau.

Yau da yake cikin kayan gida sai ya yi mata kyau sosai, gaishe shi ta fara yi, ya amsa cike da kulawa sannan ya ce “Waye ne ya ce miki nan ne ɗakin ki?”

Ta kalle shi sosai, kuma ta rufe fuskarta da hannayenta biyu kasancewar ta jingina wayar ne a jikin filo

Yadda ta yin dole ya murmusa, tare da fadin “Ba ki amsa min ba”

“Babu kowa” ta amsa din cikin noke fuskarta.

“Asad ya zo?” Yanzu kam ta dago sosai, sannan ta ce “Eh ya zo dazu da safe in ji Hajiya”

“Ba ku hadu ba”

Kai ta daga alamar eh

“Ina fatan babu wata matsala”

“Babu komai”

“Jikinki yana nuna min haka kullum. Me Hajiya take baki ne?”

Kosasshen wuyanta ta shafa kafin ta ce “Abu mai dadi”

“I see!” ya amsa ta kafin ya ce “Ta yi miki maganar tafiya Ɓurma din?”

“Eh na gode sosai, Allah Ya saka da alkairi”

“Da kyau”

Duk sai suka yi shiru, wannan ya sa Hafsat yin kasa da kanta, wani lokaci ba ta iya jure kallon shi, kodayake ba ma wani lokaci ba, ku, san duk hirar da suke yi, ba ta iya saka idanunta cikin na shi

“Idan kin je Ɓurman, ki kula da kyau”

Kai ta jinjina alamar to, shi kuma ya yanke kiran.

Safiyar Lahadi kam Hafsat da wuri ta kakkaɓe ko ina na sashenta, ta turare shi kamar yadda ta saba.

Bayan ta gama Mama ta kira hade da tambayarta ko karfe nawa za su tafi, ta shaida mata zuwa 9am.

Shi ya sa zuwa 8:30am ta fito tsab cikin ɓaƙin miski mai adon jajayen fulawa. Kallo daya za ka yi mishi ka fahimci ba da kananun kudi aka saye shi ba. Sosai kayan suka yi mata kyau, kasancewarta fara, duk da riga da zane ne hakan bai hana mata dirinta mai cike da kurciya fita ba.

Wuyanta kuma siririyar sarƙace ta gold, dan kunnen ma manne ne, shi ya sa kwalliyar tata fita simple, golden agogo ta daura a tsintsiyar hannunta.

Jan mayafi ta dora, amma sau ta yi amfani da farin takalmi da farar hand bag.

Sosai ta yi kyau, tun da ta zo gidan ba ta taɓa yin kwalliyar da ta yi kyan wannan ba. Ita kanta yau dai ta ga ƙiba da kuma kyawun da ake cewa ta ƙara.

Wayarta ta saka cikin jaka, sannan ta fito daga part din zuwa na Hajiya.

Time da ta shiga babban falo Asabe ce ke jera abinci a kan dinning, cike da sha’awa take kallon Hafsat, bayan ta mika mata gaisuwar girmamawa, ta kasa hak’ura sai da ta ce “Gimbiya yau fita za ki yi ne?”

Kai Hafsat ta daga alamar eh hade da murmushi, lokaci daya kuma tana shigewa karamin falo, nan din ma Hajiyar ba ta nan, shi ya sa ta daga murya sosai ta yi sallama.

Daga can cikin daki Hajiya ta amsa sallamar tare da fadin” Shigo ma a Hafsat, kamar bakuwa”

“Ma Sha Allah. Gaskiya kin yi kyau sosai” cewar Hajiya lokacin da Hafsat ta shigo dakin.

Hannayenta ta dora kan fuskarta tana murmushi, kafin ta duka hade da gaishe ta

Ta amsa gaisuwar tata tare fadin “Har kin shirya kenan?”

“Eh” ta amsa kanta a kasa.

“To sai ki je, ki karya, sarkin mota ya kai ki”

“To” ta kuma amsawa hade da mikawa zuwa dinning.

Bayan ta zuba duk abin da take son ci, Sai kuma ta dakko wayarta hade da bude data ta shiga WhatsApp

“Good morning Queen!”

Sakon Ahmad ya shigo

“Morning”

“How was your night?

” It was good “

“Ma Sha Allah!” ya yi reply

Sai kuma ya kira ta video call

“Wow!” Ya fara fada lokacin da ta daga kiran.

Ta yi saurin sunne kanta cikin kunya, saboda ta san dai a kan kwalliyar da ta yi ne

Ya bude idanunshi da ya lumshe tare da fadin “Kin yi kyau”

“Na gode” ta amsa lokaci daya kuma tana sipping shayin da ke hannunta

Zamanshi ya gyara a kan campbed din da yake kafin ya ce “Waye ya yi miki kwalliyar?”

“Ni ce na yi”

“Ashe kin iya tsara kwalliya haka?”

A zuciyarta ta ce “Ba dole ba, ina tare da ƴan gayu, su Aunty Safiyya lafiya ne?”

A zahiri kuma murmushi kawai ta yi

“Ya kamata a samu lokaci Asad ya kai ki, ki bude account, ga shi za ki yi tafiya babu kudi, ko kina da?”

Kai ta girgiza alamar a’a, ita tun da ta shigo gidan ai ba ta taba rike kudi nata na kanta ba.

Kuma ba ta taɓa damuwa da hakan ba, saboda dama can ita ba ta saba rike kudi ba. Abin da ke sanyata son ta ji tana da kudi shi ne abinci, to nan kuma ga shi nan kala-kala sai ta zaɓa.

“Ki jira Asad ya kawo miki kudi yanzu.”

“Ba sai ya kawo ba, me zan yi da su, Ya Tajuddeen ne zai kai mu”

“Amma yana da kyau hakan, ki jira shi yanzu zai zo.”

Shiru ta yi tana nazarin maganar ta shi, to idan kuma Hajiya ta ga kamar rokonshi ta yi fa. Ta ce ƴar mitsi da ita ta iya tambayar abu.

“Ka bar shi ni dai, babu abin da zan saya, idan ma na gani, Mama ko Ya Tajuddeen za su saya min”

“Ni ne nake da alhakin wannan ai”

“To ai…” sai kuma ta yi shiru

“Ai me?”

“Ba zan sayi komai ba.”

“Sai ki ajiye saboda zuwa school”

“Hajiya tana ba ni”

“Na ta daban nawa daban. Kuma ba za ta san an ba ki ba”

Yanzu kam hankalinta ya ɗan kwanta, shi ya sa ta yi murmushi kadan, hade da kai tea din bakin ta, tana fadin “Na gode”

Shi ma murmushin ya mayar mata kafin ya ce “Safe trip”

“Thank you! Yaushe za ka dawo ne?”

“Yaushe na tafi ma?” shi ma ya tambaye ta, shiru ta ɗan yi kafin ta ce “Ya kai wata hudu”

Ido ya waro kafin ya ce “Kai Queen”

Kanta ta kifa jikin dining table din tana murmushi, kafin ta dago hade da fadin “Ya fi ne?”

“Bai fi ba, kina son dawowa ta, please tell me”

Kamar ba za ta amsa ba, Sai kuma ta ce “Ina so mana.”

Idanunshi ya dan lumshe kadan kafin ya ce “Do you miss me?”

Kai ta jinjina alamar eh.

A karo na biyu ya kuma lumshe Idanunshi a kokarinshi na controlling yanayin da yake ji, “Amma jikinki bai nuna ba, kullum kina kan haɗa jiki”

Jin maganar Hajiya ya sanya ta sauri fadin “Ga Hajiya nan, ina zuwa” Ba ta jira amsarshi ba ta yanke kiran.

“Ba ki gama ba ne, kar fa sui ta jiranki?” cewar Hajiya

“Na gama” ta amsa ta

“To bari a yi wa Asabe magana ta kira sarkin mota a kai ki”

“To” Hafsat ta amsa hade mikewa tana gyara zaman mayafinta

Asabe ta dawo da sakon sarkin mota ya fito.

Kamar ko wane lokaci idan za ta fita sai wasu daga cikin mata dogarai sun raka ta, yanzu din ma haka ne, Sai da motar da ta shiga ta bar harabar gidan sannan suka koma

Ko 10mns basu ci a hanya ba, suka iso gidan Mama, nan din ma ta same su shirye tsab, shi ya sa tana isowa suka dau hanya.

Mama ce a gaba, Sai Goggo da Hafsat a baya, tun da suka fito garin Hafsat ke ta ware ido tana kallon da garuruwan da suke wucewa, hade da tambayar sunayensu

Tajuddeen kam ya samu abun tsokana don haka ya shiga yi, wai ƴar kauye ta shigo birni.

Bai yi ƙarya ba kam, ba ta  taɓa wuce Dawuri ba, shi ya sa ta kyale shi. Ya yi ta tsokanarshi.

Da suka zo jihar Nasara ne Hafsat ta ce “Ina ma ace nan ne garinmu Mama”

“Kin ji ƴar ƙauyen ko, da wasu manyan kumatunta” Cewar Tajuddeen

Baki Hafsat ta zunbura hade da harararshi, ta cikin mirror ya hango ta, shi ya sa ya juyo yana fadin “Allah zan sace ki. Wannan luhu-luhu din ba ƙiba ba ce, kumburi ne”

Cikin dariya Goggo ta ce “Ka sanyawa Hafsat ido Tajo”

“Don ba ki san yarinyar nan ba ne da can, ƴar tsigigiya da ita, amma kalle ta cikin wata hudu yadda ta zama kamar ana sanya mata yeast. Ta je ta bude ciki tana ta lodar abinci.”

“To sai in ki ci?” cewar Hafsat

“Atoh!” Goggo ta fada cikin dariya

“Mama, wai don Allah ya na zama, muni na yi ne?” cewar Hafsat lokaci daya kuma tana taɓa kumatunta

Juyowa Mama ta yi hade da kallon ta ta ce “Ke rabu da shi, ba wani munin da kika yi, sosai ƙibar ta yi miki kyau”

Tajuddeen ya fashe da dariya yana fadin “To ki yarda da maganar ta, kin san dai ai ba za ta fada miki gaskiya lamari ba.”

Kan Goggo Hafsat ta juya tare da fadin “Goggo don Allah muni na yi?”

“Allah ba ki yi muni ba Hafsat, ina amfanin rama, amma ke kam ga ki nan bul-bul gwanin sha’awa”

Ta juya kan Tajuddeen harara ta aika mishi hade da murguɗa baki.

“Bari mu sauka, zan rage miki iska”

Duk suka yi dariya.

Misalin karfe sha biyu da rabi na rana suka isa kofar gidan Mk

Gida ne madaidaici, da aka yi wa ginin zamani, sosai gidan ya yi kyau, horn biyu Tajuddeen ya yi Ruma ta iso wurin gate din ta bude, fuskar nan cike da fara’a da ke nuna jin dadin ganin baƙin na ta.

Mama ta fara rungumewa sannan ta rungume Goggo, kafin ta koma kan Hafsat, har zuwa lokacin bakinta bai rufu ba.

“Ya, Tajuddeen sannunku da zuwa, ya hanya?”

“Alhamdulillah! Ya jiki da kuma karin hak’uri?”

“An gode Allah” cewar Ruma

“To Allah Ya mayar da rayayye”

“amin” ta amsa hade da jan su Goggo zuwa cikin daki, aka dasa sabuwar gaisuwa hade da jajanta mata a kan abun da ya faru, sannan ta kawo musu ruwa da abinci, bayan sun ci abinci kuma suka yi sallah, aka ci gaba da taɓa hira kafin la’asar, tun da ana yin la’asar za su tafi. Hirar tasu duk a kan abubuwan da ke faruwa da Ruma ne, Hafsat dai nata kunne, ta fi mayar da hankali a kan kallo, da kuma chat da suke yi ita da su Nabila, saboda group gare su, su uku, a nan suke hirarsu.

Misalin karfe uku da wasu ƴan mintuna aka rika kwankwasa gate din a hankali.

“Ana buga kofa” Cewar Goggo

Ruma ta mike zuwa kofar Goggo kuma ta ce “Gaskiya aiki ya same ku, ni yaushe zan iya wannan, ace duk wanda zai shigo sai na mike na bude mishi kofa, duk irin dadin zaman da na ji”

Hafsat da Mama suka yi dariya, daidai lokacin ne, kuma Ruma ta dawo tare da bakuwar

Haka nan Hafsat ta ji gabanta ya fadi lokacin da suka hada ido da ita, ba Hafsat ce kadai ta ji haka ba, hatta bakuwarma ta ji irin abun da Hafsat din ta ji.

Da kallo ta bi ta, doguwa ce, irin tsawon nan mai kyau, tsawon bai hana kibarta mai kyau bayyana ba, tana da hasken fata, wacce ke nuna jin dadi da rashin yin aikin wahala.

Jikinta sanye da Abaya irin ta manyan matan nan, ta nade kanta da veil din a bayar, kallo daya za ka yi mata ka fahimci ba ta shafi ƙauye ba, sannan akwai wayewa ta zamani hade da wayewar ilmi a tare da ita.

Dayan hannunta rike da karamin yaro wanda bai wuce shekaru biyar ba. Yaron sanye cikin suit baƙaƙe na yara, takalmin kafarshi ma baki ne cover mai kyau.

Hafsat ta dauke kanta daga barin kallon bakuwar a lokacin da take zama kan kujera.

Bakuwar ma satar kallon Hafsat take yi, ta rasa ina ta santa, amma sosai ta na yi mata kallon sani.

Ruma dai yaron da ke rike a hannun baƙuwar shi ne ya fi ɗauke a hankalinta, tun daga lokacin da ta bude mata kofa.

“Sannu da zuwa” Cewar Ruma a lokacin da take ajiyewa baƙuwar ruwa a gabanta

“Yauwa, na gode” baƙuwar ma ta amsa hade, mikawa Runa gaisuwa, kasancewar ta gaishe da su Mama.

Sai da ta dan yi sipping din ruwan kaɗan Sannan ta ce “Nan ne gudan Mk? Ina nufin Muhammad Kamal Bashir”

Kai Ruma ta jinjina alamar Eh

“Yana nan kuwa?”

“A’a gaskiya baya nan.”

“I’m sorry please, ya yi nisa ne?”

Cikin rashin ƙosawa da tambayoyin Ruma ta ce “A’a, yana nan cikin gari.”

Baƙuwar ta mike tsaye, cike da farin cikin jin abin ta da shirya shi ya faru, don haka ta ce “Don Allah ki kira shi a waya ko shaida mishi Asma’u ta zo daga Jama’a, amma ya same ni can cikin gida, ina nufin gidansu”

“To!” Ruma ta amsa hade da mikewa tsaye da zummar yi wa bakuwar rakiya.

Bayan Ruman ta dawo ne Goggo ta ce “Amma wannan ƴar’uwar mijinki ce ko, na ga yaron da ke rike a hannunta sun yi kama da mijinki sosai”

57

“Da alama ƴar’uwarshi ce. Amma ni ban san ta ba. Kila na a nan kusa take ba, su din nan akwai yawan dangi”

“Muma ai sai mu yi sallah, mu ɓulla gidansu Mk din a gaisa mu kama hanya, yanzu kin ga Tajuddeen ya dawo”

Cewar a Mama

“Gaskiya kam”

Goggo ta amsa

Asma’u na fita AG ya bude mata kofar motar ta ciki.

Bayan ta shiga ne ta kwantar da kanta jikin kujera, hade da lumshe ido, Sai kuma ta saki murmushi hade da bude idon a kan AG ta ce “Mu je gidansun”

Kan motar ya juya zuwa hanyar da za ta sada shi da Family house na su Mk. Saboda kafin ya kawo Asma’u sai da ya yi bincike sosai ya gano gidan Mk da kuma gidan iyayenshi.

Kasancewar Baban Mk Reps ne a wannan lokacin, shi ya sa gidanshi yake da tsaro sosai, sai dai kallon Abdallah da ke rike a hannun Asma’u ya zame musu ID card, kuma gate pass. Don haka ba a tsananta musu bincike ba suka wuce, har bangaren Hajiya Fatima aka yi wa Asma’u jagora, yayin da AG ya tsaya cikin mota yana jiran fitowarta

Ruma kam bayansu Mama sun shiga yin sallah Mk ta kira a waya hade da shaida mishi sakon Asma’u .

Kwatanta tashin hankalin da ya shiga, ba zai yiwu ba, saboda har ji ya rika yi baya gani, shi ya sa cikin sauri ya nufo gidansu a ruɗe.

Asma’u kam da sallama ta shiga babban falon Hajiya Fatima, a lokacin zaune take tana amsar kiran, shigowar Asma’u da kuma arba da fuskar Abdallah da ta yi, ya, sanyata yanke kiran cikin sauri, idanunta a kan Abdallah, saboda Mk take gani a lokacin da yake yaro, komai na yaron na Mk ne, tafiyarshi, structure na jikinshi, gashin kansa, hatta idanu da yanayin kallon shi irin na Mk ne.

Kasa Asma’u ta zauna hade da mikawa Hajiya Fatima gaisuwa, ta amsa gaisuwar a sanyaye, tun ba ta ji abin da ke tafe da Asma’un ba.

Jin shirun ya yi yawa ne ya sanya ta fadin “Baƙuwa ban shaida ki ba”

“Sunana Asma’u, daga jama’a na zo wurin Mk ne”

Gaban Hajiya Fati ya shiga dukan uku-uku, har wani fitsari take ji, a zuciyarta take fadin “Me kuma ya hada Mk da wata Asma’u a garin Jama’a, ga ta har da yaro mai kama da shi” kafin ta gano amsar Mk ya sako kai cikin falon a matukar kidime.

Kai tsaye idanunshi a kan Asma’u suka sauka, wacce take zaune a kasa ta lankwashe kafafunta, kanta a kasa, Sai Abdallah da ke gefen ta

Shigowarshi ya sanya ta dago kai kwayar idanunsu suka hadu, ta janye nata a hankali, bayan ta aika mishi da wani kallo.

Saman kujera ya zauna, yanzu kam idanunshi a kan Abdallah wanda ya zama kamar kumbo kamar katanta ko kamar ya yi kakinshi ya ajiye.

Gabanshi ya ci gaba da faduwa lokacin da Hajiya ta ce “Yauwa, ga baƙuwa ka yi, wai daga jama’a.”

A karo na biyu Mk ya kuma dora idanunshi a kan Asma’u, Sai dai a wannan karon ba ta kalle shi ba, idanunshi ya dauke ba tare da ya ce komai ba

Jin shurun ya yi yawa ne Hajiya ta ce “Asma’u ga Kamaladdeen, ko ba shi kike nema ba?”

Daga  yadda take ta ce “Shi ne” a hankali.

Wani shirun ya kara ratsa falon, a wannan karon Hajiya Fati ba ta kara cewa komai ba, har lokacin da Asma’u ta mike hannunta rike da Abdallah, a kan cinyar Mk ta dora shi tare da fadin “Zai yi hutu a nan, idan hutu ya kare zan zo in dauke shi” Daga haka ta, daga kafa da niyyar ficewa daga falon

Hajiya Fati ta yi saurin fadin “Waye zai yi hutun a nan, waye shi?”

Cikin rashin fahimta ta yi tambayar

Komai Asma’u ba ta ce ba, kafarta ta kuma dagawa da zummar ficewa cikin falon.

Da sauri Hajiya Fati ta riko ta tare da fadin “Ina za ki je? Waye wannan yaron”

“Ɗanshi ne” Asma’u ta amsa

Ba iya Hajiya Fati ce kawai ta ji maganar kamar dirar kibiya a kirji ba, har da su Ruma da suke niyyar shiga dakin, shi ya sa cak suka tsaya, without any making sound.

“Ɗanshi?” Hajiya Fati ta tambaya a kiɗime

Kai Asma’u ta jinjina ba tare da ta ce komai ba, Hajiya Fati ta sauke idanunta a kan Mk tana fadin “Da gaske ne abin da ta fada?”

“Innalillahi Wa’inna IlaihirRaji’un!” ta shiga maimaitawa, saboda shurun da Mk ya yi ya, tabbatar mata da Abdallah yaronshi ne, ko ba haka ba ma, kammannin da ke tsakaninsu ya isa ta gasgata Asma’un

“Auran ki ya yi?”

Kai Asma’u ta girgiza lokaci daya kuma tana ficewa daga falon idanunta na zubar da hawaye.

A nan ta yi kicibis da Ruma, Hafsat, da su Mama wadanda suka yi kamar an zana su.

Da ido suka bi ta da kallo har ta ɓacewa ganinsu, kafin suka saka kai cikin falon, saboda tuni Hajiya Fati ta gansu, Idan ka dauke kukan Abdallah ba komai da ke motsi a falon.

Cikin rashin kuzari Hajiya Fati ta ce “Sannunku da zuwa”

Su ma a kasalance suka amsa, sannan suka yi mazauni, aka shiga gaisawa, Mk dai ko kanshi bai dago ba bare ya hada ido da kowa a cikinsu, har suka gama gaishe-gaishensu suka fita Hajiya Fati kuma ta fita don yi musu rakiya.

Jiki babu ƙwari Ruma ta yi sallama da su Goggo, su kansu su Goggon jikinsu a sanyaye yake, shi ya sa tafiyar tasu ba ta yi armashi ba, kamar lokacin da suke zuwa.

Har kofar gida suka aje Hafsat, kafin suka wuce.

A bangaren Hajiya ta yi sallahr magariba da isha’i ta ci abinci, kafin ta koma sashenta, saboda a gajiye take likis, chat ma sama-sama ta yi da Ahmad ta kwanta.

*****

Mk

Zuwan Abdallah zuriyar Alhaji Bashir abubuwa da yawa sun faru, wadanda duk marasa dadi ne, musamman bangaren Hajiya Fati, ta fi jin zafin abun, kowa ya sani, Mk shi ne ɗa ma fi soyuwa a wurin Alhaji Bashir, har ya kasa boye wannan soyayyar da yake mishi ta fito fili. Shi ya sa Mk din ya yi bakin jini a wurin wasu ƴan’uwamshi musamman wadanda suka hada uba. Basu kadai ba har da abokan zaman Hajiya Fati. Shi ya sa daga Hajiya Fati zuwa Mk kullum cikin kokarin ganin Mk bai yi wani abun aibu ba suke. Yanzu kam da wannan batu ya fito, ta tabbata ko ba su nuna jin dadinsu a zahiri ba, to a badini har Allah ya ƙara sai sun yi.

Shi ya sa cikin kwanaki kankane da kawo Abdallah Hajiya Fati ta sha ruwa ku san leda goma, kadan za ace sai an kara mata ruwa.

Mk kam kunya har baya son fita, tun da aka kawo Abdallah bai yarda sun hada ido da Alhaji Bashir ba. Ba iya shi kadai ba, hatta Ruma kunyarta yake ji, koda yaushe yana daki kwance, saboda yana jin kila zuwa yanzu a garin nasu kowa ya sani, musamman su da dama kadan ake jira a fara talla da su.

Ruma dai tuni Goggo ta kira ta a waya, ta yi mata gargadin ahir ta tayar da hankalinta a kan wannan batun, nata ido, kar allura ta tono garma, tun da ita ma tana da nata guntun kashin a duwawunta.

Shi ya sa ta kame bakinta shiru, ko sau daya ba ta taba tunkarar Mk da maganar ba. Iyakaci idan Abdallah ya zo ta yi mishi wanka, ta ba shi abinci hade da sake mishi fuska.

 Abdallah kam  ba shi wurin Ruman ba shi wurin Hajiya Fati, duk wancan tashe-tashen hankalin shi bai shafe shi ba. Yana samun duk wata kulawa babu hantara, saboda a hankali soyayyarshi gami da tausayinshi ke ratsa zukatan ginshikanshi, Hajiya Fati, Mk da kuma Alhaji Bashir.

Yanzu ma kwance  yake kusa da Hajiya Fati a akan makadaden gadon ta na alfarma, lokaci daya kuma yana cin biskit din datebase.

Hajiya Fati ce kwance a gefenshi, wani irin ciwo kanta yake mata, tun daga lokacin da aka kawo Abdallah ba ta ƙara lafiya ba, ciwon yau daban na gobe daban

Jin ta take yi duk ta muzanta, wanda ya taɓa riskar kanshi a situation din da take ciki ne kawai zai fahimci yadda take ji.

Amma duk lokacin da ta kalli Abdallah yana wasanninshi a tsakiyar dakinta, ta tuna jikanta ne da aka samar mata ba ta hanyar aure ba, Sai ta ji komai na duniya baya yi mata dadi, ko baƙi ba ta son ta ga an yi a gidan. Shi ya sa idan har za a yi taro take tura shi gidan Ruma.

Mk ya turo kofar ya shigo, a sanyaye, tun daga lokacin da Asma’u ta duro rike da Abdallah kawo yanzu ya koma mara kuzari babu karsashi ko kadan a tare da shi.

Da ido Abdallah ya bi shi har zauna kan stoll din mirror, Saboda hat Yanzu saba dasu ba, rashin uwa ce ya sa yake uwar rana da su.

“Ya jikin?” ya tambaya a sanyaye

“Da sauki, har yanzu dai kan ne yake ciwon” Hajiya Fati ta amsa shi

“Sannu, Allah Ya ba ki lafiya, ki dan rage damuwa”

Yumkurawa ta yi hade da mikewa zaune, cikin yanayin damuwa ta ce “Damuwa dole ce Kamal, Idan aka ce ma kar inda mu to an raina min hankali. Ba ka yi tunani me zai je ya zo ba Sam. Ka manta yadda muke zaune a cikin gidan nan? Kullum neman kuskurenmu ake yi. Ba iya cikin gidan nan ba ma, ka manta waye mahaifinka, haka nan ma an sawo sharri a kasuwa an lika mishi barantana abu da reference. Kuma Kai kanka, ka san me za ka zama nan gaba? To wannan tabon zai iya, shafar siyasarka a nan gaba. Sannan yaron nan me ye makomarshi Kamal, me zamu fada mishi idan yi girma? Wannan shi ya fi damuna “

Ta karasa maganar cikin kuka mai cin zuciya. Abdallah ya mike zaune sosai yana kallon ta. Sai kuma ya juya kallon na shi a kan Mk yana fadin” Ka tafi ka sanya ta kuka”

Haka ya mike hade da han hannun Mk zuwa falo, Sai Mk din ya yi sama da shi hade da nufar part din matasan gidan.

Dakin kannenshi ya bude, kan katifa ya kwanta hade da dora Abdallah a kan cikinshi. Zuciyarshi babu dadi, kukan da mahaifiyarshi take yi, da kuma yawan ciwon da take yi yana matukar daga mishi hankali

“A kira ma Ummee?” cewar Mk ganin Abdallah na niyyar kuka, saboda ya fi sakewa da Hajiya Fati. Ganin ta yake kamar Mommyn Jama’a.

Layin Asma’u ya shiga kira, karon farko da zai, kira ta tun bayan da ta kawo Abdallah.

Gab kiran zai yanke ta daga, shiru ba ta ce komai ba, shi ma Abdallah ya kanga ma wayar bayan ya sa a, handsfree

“Hello Ummee!” Cewar Abdallah da muryar yara

Numfashi ta sauke a hankali kafin ta ce “Little! Kana lafiya?”

“Eh.” Ya amsa kafin ya ce

“Ki zo mu tafi gida Ummee, ban son nan”

“To Little, next week Sha Allah zan zo in dauke ka ji ko”

“To!” ya fada cikin ɗoki.

Mk ya karbi wayar yana fadin “Next week din za ki zo ki dauke shin?”

“Ka ƙosa ne?”

Duk da damuwar da yake ji hakan bai hana shi murmusawa ba kafin ya ce “No. I’m just asking”

“Ranar da ka shirya ka yi min magana in ba ka address ka kawo shi” Daga haka ta yanke kiran.

Ya bi wayar da kallo, wani murmushin ya kuma yi, hade da kwantar da Abdallah a jikinshi. Shi fa sosai yake kaunar yaron, idan ma za ta bar shi zuwa yanzu kam bai damu ba. Tun da aikin gama ya gama.

*****

Hafsat

Yau kam shirin zuwa Maƙera ta yi, karo na farko da za ta je gida tun bayan auran. Shigar sarauta Hajiya ta sanya ta yi, har da alkyabba gami da dogarawa ƴan rakiya. Mota biyu a ka ba ta. Misalin karfe shadaya na safe suka Isa Maƙera, Hafsat wani irin dadi take ji mara misultuwa, ba ta jira dogarawa sun bude mata kofa ba, ta ɓalle murfin kofar hadewa da kwasawa da gudu zuwa cikin gidan

Cikin sa a kuma ta yi karo da Malam Ayuba tsaye a tsakar gida, cikin murna ta makale shi. Shi ma sai ya kasa rufe baki, ya shiga wangale bakin yana karewa Hafsat kallo, wacce ta kara kyau gami ƙiba mai cika ido. Ba shi kadai ba, duk matan gidan da yaran gidan kallon ta suke yi cike da sha’awa, yau ga Hafsat diyar Hindatu ta zo tare da rakiyar fadawa, ita kanta Hafsat din sai ta rika jin  ko iya nan aka tsayawa ita kam ta godewa Allah, mutanen da suka tsane ta, hade da gudun hada hanya da ita, yanzu kuma ta fi karfinsu.

Kai tsaye dakinta da yake rufe Goggo Amarya ta bude mata.

Saman gadonta ta fada cike da kewar dakin, ba bata lokaci ta yaye alkyabbar nan ta shiga gyara dakin, zuwa azhur ya fito fes. Wanka ta yi hade da cin abinci lokaci daya kuma tana taba hira da yaran gidan suna ba ta labarin abin da ya faru.

Daidai lokacin Malam Ayuba ya kuma shigowa gidan, har ɗakin Inna Kuluwa ta bi shi, suka sake sabuwar gaisuwa, hankalinshi ya tattara kanta yana fadin “To Hafsat babu dai wata matsala ko?”

A nutse ta shiga girgiza kai alamar a’a

“Mai gidan na ki bai dawo ba?”

Kan ta kuma dagawa alamar eh.

“To ki rika yi mishi addu’a kin ji, Allah Ya tsare shi, ya dawo da shi guda lafiya. Duk wanda aka ce miki ya je Kasar waje yaƙi ai dole a rika yi mishi addu’a”

Gaban Hafsat ya shiga dukan tara-tara. Saboda ba ta san yaƙi ya tafi ba, kawai dai an ce mata yana wurin aiki. Shi ya sa idan ya kira video call, Sai ta ganshi cikin wasu kaya irin wanda sojojin Kasar waje ke sanya idan suna yaki.

Take tsoro ya kamata, tun da ya tafi ba ta taba shiga farga ba irin ta yanzu ba. Idan aka kashe shi kam ai ta shiga uku.

“Ki zauna da kowa lafiya kin ji, mijinki da danginshi mutanen kirki ne, kin ga duk wata sai sun aiko min da kayan abinci.”

“Mun gode” Hafsat ta amsa a aanyaye

“Ya makarantar?”

“Saura sati biyu mu fara jarabawar fita gabadaya”

“Ma Sha Allah! Allah Ya taimaka”

“Amin” ta amsa, shi kuma ya ci gaba da yi mata nasihohi masu rasa zuciya, duk sai jikinta ya kuma mutuwa, haka ta baro dakin babu  kuzari.

Sai da aka yi sallahr la’asar sannan ta yi shirin shiga gari.

Dogarawan nan basu bar ta, ta tafi da kafa ba. Ko ina a mota suke kai ta. Gidansu Farida, gidansu Ni’ima. Har wurin Tukur. Shi ya sa sai 6pm suka dawo.

Zuciyarta ta dan yi wasai, musamman da Tukuro ya ce mata Ahmad yana lafiya, kuma kwana nan zai dawo.

Tun da ya fadi haka, jikinta yana ba ta akwai makamancin abin da ya fada a tare da Ahmad din.

Basu baro kauyen ba, Sai ana sallahr magriba, boot dinsu dauke da tsarabar nono mai kyau, fura da manshanu

Sai kubewa busassa, wake, daddawa, kuka har da dakakken yaji.

*****

Tun daga lokacin da ta ji cewa Ahmad yaƙi aka tura shi hankalinta bai sake kwanciya ba, abinci da take ci da yanzu kam ba ta iya cin shi, bacci ma sai dakyar take yin shi, shi ya sa take yawan tashi sallahr dare.

Ba ta san ta damu da shi ba sai a wannan lokacin, shi ya sa always tana online checking on him. Har abun mamaki ya rika ba shi, da shi ne yake nemanta, yanzu kam ita ce take neman shi ko wane lokaci.

Da zarar ya dauki some hours baya online zai zo ya samu sakonninta da yawa.

Babu abin da take so irin ta ji yaushe zai dawo, shi kuma sai dai ya ce mata soon in Sha Allah

Kamar yau ma da ta kira shi a video call din korafin ba zai zo ranar graduation din ta ba take yi mishi

Salon yadda ta yi maganar ne ya sanya shi lumshe idanu kafin ya ce “Yaushe ne graduation din”

“Next Saturday”

“Saura 9dz kenan?”

Kai ta jinjina a hankali alamar eh.

“Allah Ya kai mu, ko ban zo ba, akwai Mama, akwai Hajiya, akwai Asad, ga Aunty Safiya, ga Aunty Ju. Duk basu ishe ki ba?”

Narke fuska ta yi kamar za ta yi kuka, komai ba ta ce ba.

Murmushi ya kuma yi, kwanakin nan sosai take kara shiga ranshi, musamman canjawar da ta yi, na yawan neman shi da take.

Cikin sigar lallashi ya ce” Shi kenan zan duba in gani “

Fuskar tata ta shiga warwarewa, hakan sai ya kara sanya shi murmusawa.

Fatan ta kawai shi ne ya, zo din, saboda yanzu babu abin da take so irin ta gan shi.

MK

Address din da Asma’u ta turo mishi ya rika bi, har zuwa lokacin da ya yi parking a gaban katon gate din gidan. Ya juya yana kallon Abdallah wanda yake ta murna sakamakon ganin gate din gidansu, kokarin bude kofar motar kawai yake yi ya fita.

Mk ya kai wayar kunnen shi sakamakon daga kiran da Asma’u ta yi “Ga ni a kofa”

“OK” ta amsa hade da yanke kiran.

Tsakanin yanke kiran nata da fitowar AG bai fi 5mns ba. Sanye yake cikin jallabiya milk colour’s.

Wani abu mara dadi ya soki zuciyar Mk, har yanzu yana jin zafin AG ba kadan ba.

Kofar ya budewa Abdallah, saboda tun da ya ga AG ya fito yake buga murfin alamun dai yana son fita.

Da gudu kuwa ya karasa jikin AG, shi kuma ya daga shi cike da farin cikin ganin shi, kafin ya sauke shi yana fadin “Je ka ciki Ummee ta gan ka”

Da gudu kuwa ya nufi gate din

AG kuma ya shiga cikin motar yana mikawa Mk hannu a lokacin da ya zauna.

Hannun kawai Mk ya mika mishi ba tare da ya ce komai ba. Ko lokacin da ya kai Asma’u gidan irin wannan gaisuwar Mk ya yi mishi.

Numfashi ya sauke a hankali kafin ya ce “Na san na yi maka abubuwa marasa dadi, da kila kake ganin ba za ka yafe min ba, ko kuma duk abin da na yi maka ba zan burge ka ba, amma ka sani ni da kai yanzu mun zama daya. Sati uku baya ni ne a kofar gidanku, yanzu, kuma tarihi ya maimaita kanshi ga ka a kofar gidana. Kuma ka san yau ne farko ba kuma ka san ranar karshe ba”ya dam tsagaita yana kallon Mk, wanda ya jingina bayan shi da kujera yana sauraro maganganun.

“Ka duba farkon labari, aka daga hotel za a siyar, Sai na siya, ashe saboda kai na saye shi, ta wannan hanyar ce kadai zan iya ganin Asma’u a matsayin matar da zan aura. Ranar da na je hotel din ba ranar zuwana ba ce, ashe kai ne za ka zo a ranar. Sai kuma ga shi ka zo din, tare da Asma’u. Daga ranar ban kara samun nutsuwa ba, Sai da na, ganta a dakina a matsayin mata. Wannan duk wasu kaddarori ne da Allah Ya tsara, kaddararka ta neman Asma’u ta hadu da tawa ƙaddarar, ta hanyar kaddararka kawai zan same ta. Abu na biyu. Don haka ka manta da komai, mu hada hannu wajen rainon little, ni din zan wanke duk wani laifi nawa ta hanyar rike maka little, abin da kawai muke so, shi ne ka san akwai shi a raye, haka ma, ƴan’uwanka, ni ban kai Little wurinka da niyyar tozarci ba. “

” Na gode “karon farko da Mk ya yi magana.

Sai kuma ya fita, hade da dakko ƙaramin akwatin little ya ajiye. Wannan ya sa AG ya sakko hade da jan akwatin zuwa gida.

Cikin motar Mk ya koma, maganganun AG na yi mishi zagaye, wato ƙaddarar wani, na iya yi ma hanya zuwa ga ta ka ƙaddarar. Allah Ya kaddara ta hanyar shi AG zai hadu da Asma’u. Shi kuma baya jin akwai wata hanya ta haduwarsu da AG idan ba a wannan hotel ba. Bai taba ganin mai kama da shi ba. Yanzu ga shi a kofar gidanshi.

Tabbas ko don rikon da ya yi wa little ya kamata ya yafe mishi duk wani abu da yake jin da can ba zai ya fe mishi ba.

Da wannan tunanin ya bar kofar gidan.

<< Abinda Ka Shuka 55Abinda Ka Shuka 58 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×