Skip to content
Part 7 of 19 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

CINNAKA.

Cikin dare ya isa  jihar Maiha tare da abokan rakiyarsa guda hudu basu sha wahalar masauki ba, saboda tun kafin su iso suka yi booking daki a hotel ta online.

Da safe kuma suka yi wa cikin jami’ar LOKKO tsinke, cikin shigar da ta saje da sauran daliban makarantar.

Raba kansu suka yi zuwa ko wane department da ke cikin jami’ar suna karewa masu fita da masu shiga lecture  kallo har shida na yamma.

Sai dai  ko mai kama da Buhari basu gani ba, haka suka koma masaukinsu a gajiye.

Kashegari ma suka dora daga inda suka tsaya. Ranar kam har masallaci da wurin cin abinci suka rika lekawa namma shiru, babu mai kama da Buhari. Suka juya library nan ma ba irin Buhari.

Yau ma din dai kamar jiya, a gajiye suka dawo masaukinsu, tsabar gajiya babu mai tanka ma wani.

Shigarsu dakin hotel din ke da wuya kiran AG ya shigo wayar Cinnaka.

 “Sai Oga!” cewar Cinnaka lokacin da yake fadawa saman gadon.

Daga can bangaren AG ya ce “Me ye labari?”

“Wlh fa Oga shiru ne, wato mun shiga lungu da sako na makarantar nan amma babu yaron nan, na fara tunanin ko ma ya gama ne”

Jikin AG ya saki kamar an zare mishi kasusuwan jikinsa, kila shi ya sa komai bai ce ba. Sai Cinnakan ne ya ɗora da

“Amma ka gane, kar ka damu Oga, za a bi wata hanyar, ko ya gama ko bai gama ba zai zo hannu muddin yana raye, za mu kawo ma shi da rai ko babu Cewar Cinnaka a kokarinshi na karfafa wa AG gwiwa.

“Na fi son shi a raye Cinnaka, ba na son komai ya same shi, idan wani abu ya same shi to komai ya lalace.” cewar AG cikin hanzari tamkar Cinnaka ya fada mishi sun kama Buhari suna niyyar kashe shin ne.

“An gama Oga, ka dade ka yi karko.”

“Please Cinnaka don Allah ka yi min kokari kamar yadda ka saba”

“An gama Oga, kar ka damu ba ka da matsala”

Komai AG bai ce ba, ya yanke kiran, cike da bacin ran rashin ganin Buhari, gani yake idan aka ga Buhari kamar an ga Asma’u ne.

Yanzu yake jin takaici da bai je tare da su Cinnaka ba, ji yake har zuwa lokacin basu yi abin da ya dace ba, kudinshi kawai suke tsotsa.

Bayan AG ya yanke kiran, Cinnaka ya sauke wayar hade da kallon sauran yaranshi guda hudu da su ma shi din  suke kallo ya ce

“Ya kamata fa mu saɓe ni kaina na gaji da zama a wurin nan.”

Awilo ya ce “Haka ne Oga, zama wuri daya tsautsayi ne”

Disko ya shafa kanshi da yake cunbus da gashi yana fadin “Dazu fa saura kaɗan a ramfoni, wani ɗalibi ne ya rika min tambayoyi kure hali, cikin dabara kawai na yi mishi ta maciji da kadangare na bar shi a wurin”

Wizi da ya kwkkwalo ido ya ce “Kasa lura fa, kar ka hade mana kashi”

“Atoh! Ni ba wannan ne matsalata ba, matsalata rungumar litattafannan ne. Na dauka abu ne mai sauki ashe babu wani sauki a cikinshi. Kai karatun nan akwai wuya, gara da Allah Ya sa ma ba mu yi ba, mutum ya yi ta yawo cikin rana, ya fita can ya fada can” cewar Maiko lokacin da yake kwanciya sosai a saman gadon.”

Duk suka yi dariya, ban da Cinnaka da yake kokarin kiran wata lamba

“Kai Mado!” ya fada lokacin da aka daga kiran

“Oga!” Daga can dayan bangaren Mado ya amsa

“Ya kana tare da kanka, ko kun raba hanya?”

“Sai Oga! Ina tare da shi Oga, zai yi amfani ne?”

“Kwarai ma kuwa. Aiki za ka yi min cikin gaggawa. Daga nan zuwa safe nake son ka gano min a garinku na Dawaki su waye suke makaranta a jami’ar LOKKO”

“An gama Oga.” cewar Mado cikin budaddiyar muryarshi.

Cinnaka ya yanke kiran yana kallon yaranshi daya bayan daya sannan ya ce “I cut the story shot. In ji turawa.”

Duk suka daga hannayensu alamun jinjina.

Cikin dare Mado ya lalubo yan garinsu masu karatu a LOKKO, ba iya ƴan garin ba har da ƙauyukan da ke gefensu.

Da sassafe ya kira layin Cinnaka ya shiga rattabo mishi sunayensu, yana zuwa kan sunan Buhari Cinnaka ya tsayar da shi tare da fadin

“Ai wannan sunan ka nemo min details din shi, ina nufin shekarar da ya shiga makarantar, abin da yake karanta da kuma wurin zaman shi.”

“Sai Oga!” cewar Mado lokaci daya kuma ya yanke kiran.

Bai zauna ba ya shiga gari wajen ma fi kusanci da Buhari, cikin salo da dabara ya samo duk abin da Cinnaka yake bukata.

Aikin Cinnaka baya sanya a cikinshi, saboda yana biya mai kyau kuma a kan lokaci.

Sai da ya samu ke babban wuri sannan ya kira layin Cinnaka ya zazzage mishi abin da ya kunso a kan Buhari.

“Aiko sai da maza ɗan….” cewar Cinnaka hade da yin wani ihu da ke nuna jin dadin abin da Mado ya fada mishi

“Cau! Cau!! Cau!!! Oga Maza maganin maza wlh” Mado ya fada cikin daga murya

“Ka samo akawun lamba, tun da kai har yanzu baho ne ba ka da akawun” Cewar Cinnaka hade da yanke kiran.

Ya kalli abokan aikin shi yana fadin “Aiki ya tashi, kowa ya shirya, kai Wizi dauko bindigogin nan, ba sai na fada maku abin da ya dace ku yi ba.”

“An gama Oga!” suka amsa a tare hade da mikewa tsaye don shiryawa.

*****

Hafsat.

JUMA’A 5:30PM

Yau kam jikin Inna da dan sauki, bayan Hafsat ta taimaka mata ta yi wanka, Sai ta shimfida mata tabarma a kofar dakinta ta ki shingida, sassanyar iskar yammar na kadata a hankali.

Lokaci daya kuma tana kallon su Kuluwa da Luba da suke ta hidimominsu a tsakar gida.

Duk wata sana’a da Inna ke yi yanzu sune suke yin ta, misalin sayar da manja, ɗanyen mai, da sauran kulle-kullen kayan miya.

Ta san ba tun yanzu wannan sana’arta ke tsone musu ido ba, wani lokaci har gwada yi suke yi, amma basu zuwa ko ina sana’ar ke lalacewa, Sai su ce ita ce ta yi musu mugun baki.

Yanzu kuma da suke yi ita tana kwance habaici ne kullum sai ta sha shi gami da gori. Yanzu ma tun da ta fito tsakar gidan suke ta ƴan waƙe-waƙensu na habaici. Ita yanzu ba ta su take yi ba, tun can ma basu gabanta bare yanzu da take fama da abubuwa masu yawa.

“Salama Alekun, wai an ce Hafsat ta zo” Cewar wani yaro daga can kofa, yana hada ido da Inna sai ya juya baya a guje.

Kuluwa da Luba suka tafa hade kwashewa da dariya, Kuluwa ta dora da “Yaro ya ga mugun abu”

“Ke dai bari, baƙin hali bai yi ba.”

Suka kuma kwashewa da dariya, daidai lokacin kuma Asma’u ta aje littafin Hausar da take karantawa ta fito waje.

Sanye take cikin riga da zane na atamfa masu kyau.

Fuskar nan fayau ba kwalliya sai yar ramar da ta yi wacce ta kara fitar da doguwar fuskarta mai dauke da dogon hanci.

“Waye yake kiran ki kuma?” cewar Inna tana kallon Hafsat cike da kulawa, saboda Hafsat din dai babu inda take zuwa daga gida sai gida.

Idan ka ga ta fita to magani ta tafi siyawa Innar shagon Nasir ko an so littafin Hausa a wurin Nasirun.

Shi ke aro mata ya ba ta, saboda ita ko ta je aron ba za a ba ta ba. Ga shi kuma tana son karatun sosai.

“Ban san waye ba.”

“To ko kin yi wani abun ne jiya da kika fita siyen magani?”

Ta girgiza kai alamar a’a

“Ko malaminku ne da ya ji shiru ba ki je makarantar ba ya biyo hanya?”

“To kila”

“Je ki ki gani” Inna ta ba ta umurni.

Duk maganganun da suke yi, su Kuluwa suna jin su, Sai bayan da Innar ta yi shiru ne, suka kwashe da dariya.

“Ta shi in kama ki zuwa daki Inna” cewar Hafsat, ba tare da ta bi takan su Luba ba

Hankalinta ba zai kwanta ta bar Inna a waje, za su iya yin amfani damar wajen ja mata wani sharri.

Dakin a gyare tsaf sai, kamshin tsintsiyar kamshi da yake ta shi, ta zaunar da Innar gefen gado tare da fadin kin ga Inna da kin iya karatu sai in ba ki ki karanta kafin in dawo zai debe miki kewa”

Inna ta yi murmushin da ya bayyana hakoranta tana fadin “Ba tun yau kike cewa haka ba Hafsa”

Ita ma dariya ta yi mai sauti a lokacin da take sanya dogon farin hijabinta.

“Yanzu zan dawo Inna”

“To ki fada mishi gaskiya dai, tun da ya damu da ke, kar yay ta zuwa babu dadi, ko kuma kawai ki hak’ura ki koma makarantar”

Ido Hafsat ta gwalo kafin ta ce “Ba zan koma ba wlh Inna…” ta yi saurin dakatar da abin da ta yi niyyar fada, ba ta son tana tunawa Inna abin da ya faru, da ace tana da iko da ta shiga kwakwalwar Innar ta goge komai.

Saboda kullum Inna sai ta yi kukan abun, tana fadin “Allah ka saka min”

Ta juya tsakar gidan inda su Kuluwa ke ta hada-hadari kasuwancinsu, suka bi ta da kallo hade da taɓe baki.

Ita kadai ce mace a gidan, sauran yaran gidan duk maza ne, Kuluwa na da uku Luba na da biyu.

Tun da ta yaye murfin kofar ta hango Uncle Najib tsaye jikin bishiyar cediyar nan, cikin shigar farar shadda dinkin zamani na ƴan birni, kamshin turarenshi mai dadi ya cika wajen.

Yau ma kamar waccan ranar daga nesa da shi ta duƙa cike da girmamawa ta ce “Uncle good aft… Ina wuni?” ta fasa fadin abin da ta yi niyyar fada da farko

Ya mayar da hannayensa kan kirjinshi yana kallon ta cike da tausayawa, saboda yanzun kam ya san tarihinta ya kuma san matsalarta, ya san abin da ya sa ba ta zuwa makaranta, ya san dalilin da ya sa take ware kanta.

Yau sauke numfashi a hankali cikin sarkakkar murya mai cike da tausayi ya ce “Come!”

Ta mike a hankali ta kara matsowa daf da shi “Me ya sa ba ki je makarantar ba”

Shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba

“I’m asking” hawayen da take boyewa suka fi karfinta ta hanyar gangarowa kan kyakkyawar fuskarta

Cikin kukan ta ce “Innata ce ba ta da lafiya”

Ba ya son ya ga ana kuka shi ma sai ya ji zai yi kukan, duk yadda ya so hana kanshi kukan, hakan bai hana idanunshi yin maiko ba.

“Come Hafsat, come and tell me something about you please, me yake damun Inna din? “

Karon farko da wani bayan Innarta da Nasir ya yi mata magana cikin tausayi da nuna kulawa, hade da kiran Innarta Inna, bayan ita da ƴaƴan Mama (Yayar Mamanta da ke aure a Dawuri) babu mai kiran Inna da Inna.

” Me ya sa ake zargin Inna, just tell me the truth please, may be I will help you.”

Mamaki ya bayyana a kan fuskarta, dalilin jin maganarsa

“Yes! I I know everything Kawai Ina son in ji daga bakinki ne.”

Duk suka yi shiru, Sai ita da take dauke hawayenta lokaci zuwa lokaci.

“Ko ba ki yarda da ni ba” ta shiga girgiza kai a hankali, saboda Uncle Najib na daya daga cikin masoyanta da suka nuna mata so a lokacin da kowa ke gudunta

Daga lokacin da ya shigo makarantar zuwa yanzu da suke tsaye ya yi mata alkairai masu tarin yawa, ya kuma ba ta kariya a bangarori masu yawa.

“Shi kenan zan tafi.”

Cikin sauri ta ce “Ka yi hakuri don Allah” ta kai karshen maganar hade da kokarin daidaita muryarta.

*****

Tun misalin karfe bakwai da rabi na safe Cinnaka da yaranshi suke cikin department din da suka tabbatar a nan Buhari ke daukar darasi, amma har Shadaya na safe babu Buhari.

Kallo daya za ka yiwa fuskokinsu ka tabbatar rayuwakansu duk a bace suke, musamman Cinnaka da ya kasance ja gaban tafiyar. Bai taɓa yin aikin da ya ɓata mishi rai ba irin wannan wasa-wasa yau kwanansu uku suna sintiri a cikin makarantar nan, ban da ya dade yana harka da AG tabbas da ya fita batun neman Buhari, amma idan ya tuna yadda AG ke bude musu hannuwa a duk lokacin da harka ta taso irin wannan sai ya hak’ura.

Amma kam idan suka samu Buharin sai yaɗumama mishi jiki ladan wahalar da ya basu.

Ko jiya ma da yamma nan suka wuni amma basu same shi ba.

Kai karshen maganar zuci tashi ke da wuya, idanunsa suka hasko mishi Buhari da ke shigowa harabar department din, kafadarshi sagale da jaka madaidaiciya ta daliban da suke karatu a jami’a.

Da alama ma su Wizi sun ga shigowar Buharin, saboda a take suka dago ido daga inda suke suka dora a kan Cinnaka wanda shi ma su din suke kallo. Domin ganin suna aikinsu da kyau, kodai kawai zaune suke a wurin hankali da tunaninsu yana wani wuri daban.

Cikin sauri kuma suka mayar da idanunsa a kan wayarsu da suka lalubo hoton Buhari, suka kuma juyawa inda Buhari yake, yana kokarin shiga lecture hall.

Shigar shi ta yi daidai da mikewar su Wizi, suka nufo inda cinnaka yake.

“Ya Oga! Ta fada ko?” suka hada baki a tare.

“Kunama ta fadi, ku dai ku zama cikin shiri, and take care in ji bature ” Cewar Cinnaka yana kallonsu.

Suka kuma rabuwa a duk wata kofa da Buhari zai iya bi ya fita.

Suna zaune a wurin har daya saura, sannan su Buhari suka fito lecture, daga wurin lecture masallaci ya wuce, a tsakiyar su Disko ya bi jam’i ba tare da sanin shi ba.

Tun da ya fito suke bibiyarshi har zuwa lokacin da ya fita daga cikin makarantar, zuwa rukunin  dakunan Dalibai da ke wajen makaranta na haya.

Maiko ne ya shiga gidan  yin surveying , Wizi da  Awilo kuma su ka yi surveying din yanayin unguwar.

Duk wannan ya faru ne a cikin kankanen lokaci.

Daga can nesa da gidan suka tsaya suna jiran umurnin Maiko da ke cikin gida.

Basu ji ma ba, ya leko hade da dago musu hannu.

Cikin hanzari suka karaso wajen, Awilo da Cinnaka suka fada cikin gidan kai tsaye.  fuskarsu sanye da facemask sai facing cap. Dakunana ne guda sha biyu a jere, tsakar gidan ba kowa, cikin hanzari suka lalubo lambar dakin da Maiko ya fada musu Buhari ya shiga.

Awilo ne ya kwankwasa kofar dakin a hankali.

Daga ciki dakin Buhari ya ce “Waye?”

Maimakon Awilo ya amsa sai ya kuma kwankwasawa da dan karfi.

A fusace Buhari ya ce “Wai waye ne, dalla kofar a bude take”

Awilo ya juya yana kallon Cinnaka da ya kankance idanu sakamakon tsawar da Buhari ya yi musu. Ji yake kamar yana shiga ya fara zubar mishi da hakora.

“Easy dai Oga” cewar Awilo a hankali.

Karar kofar ta sanya Awilo juyawa da sauri, Buhari ne daga shi sai gajeran wando ya leko.

Kallon rashin sani yake musu, kafin ya yi wani abu har sun tura shi cikin dakin sun mayar da kofar sun rufe

“Lafiya, su waye ku, wa kuke nema?”

“Kai muke nema.” Cinnaka ya amsa shi, cikin wata irin murya da ta razana Buhari, ta kuma sanya shi shiga taitayinshi.

Cike da tsoro yake kallonsu, har zuwa lokacin da Cinnaka ya nuna mishi wani hoto tare da fadin “Ka san wannan?”

Shiru Buhari ya yi yana kara kare musu kallo hade da hoton da ke kan wayar Cinnaka

“Kai ba ka ji ne?” Awilo ya daka mishi tsawa

“Ban san shi ba” Buhari ya amsa cike da karfin hali

Wani irin kallo Cinnaka ya aika mishi kafin ya ce”Kana son a yi maka da yaren da za ka fahimta ne? “

Ya kai karshen maganar hade da daga rigarshi kamar bindiga ta bayyana.

Tsoro sosai ya bayyana a fuskar Buhari ya dauka abun wasa ne, Ya yi saurin ja da baya a tsoroce, Cinnaka ma ya matsa har zuwa lokacin bai rufe bindigar da ya bude ba.

” Ka san shi?”

A zabure ya ce,” abokina ne, dakinmu daya kafin ya gama makaranta”

“Da ka ce ba ka san shi ba, da na fasa kanka na kwaso kwanyarka ita sai ta amsa min duk tambayoyina.” Cewar Cinnaka cikin muryar da ke nuna ranshi a bace yake.

” Za ka sanya kaya ko a haka za ka bi mu” Cinnaka ya kuma fada babu alamun wasa

A tsorace Buhari ya dire kafafunshi ya shiga rokon su yi mishi rai, don Allah su kyale shi.

Tsawar da Awilo ya daka mishi ce ta sanya shi mikewa ya shiga sanya kayan jiki na rawa.

“Kwaso min wayoyinka” Cewar Cinnaka a kausashe

Jiki na rawa Buhari ya mika mishi wayoyin.

“Oya! Mu je, kuma ka nutsu, idan ka bari wani ya san halin da muke  zan fasa kanka.”

Da kai Buhari ya rika amsawa umarnin.

Yanzu kam a tsakar gidan Salihu ne ke wanke – wanke, kasancewar ba su da wata alaƙa da Buhari da ta wuce zaman gidan, gaishesu kawai ya yi, Buhari ya amsa kamar ba komai, sannan suka fice daga gidan.

<< Abinda Ka Shuka 6Abinda Ka Shuka 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×