Skip to content

About Us

Bakandamiya Hikaya (ko Hikaya) taska ce daga cikin taskokin Bakandamiya, wacce aka kirkira don masu sha’awar rubuce-rubuce da karance-karancen littattafai, musamman na adabi da sauran fannonin ilimi..

Kowa na iya karanta littattafai daga shahararrun marubuta daban-daban. Akwai littattafai na kyauta da dama, sannan akwai littattafan da sai an biya kudi ta hanyar subscription za a iya karanta su.

A latsa nan don ganin wasu daga cikin litattafan da muke da su. Ga masu son yin subscribing, sai a latsa nan.

Hanyoyin sanya littattafai

Marubuta na iya dora littattafansu a Hikaya ta hanyoyi guda biyu kamar haka:

  1. Ta hanyar dora littafin nasu babi-babi (series) don masu karatu kyauta. Ga masu sha’awar yin hakan, da farko sai a yi rajista, a yi login, sannan sai a je main menu a latsa publish. Ba za a iya ganin ‘publish’ ba idan har ba a yi login ba.
  2. Ta hanyar sayar da kammalallen littafi ga Hikaya don itama ta dora ta sayar wa makaranta ta hanyar subscription. A latsa nan don karanta sharuddan sayar da kammalallen littafi da kuma yadda za a aiko da littafin.

Don karin bayani game da amfani da taskar sai a je FAQ page namu ko kuma a tuntube mu kaitsaye ta contact page. Kana kuna iya ziyartar ofishinmu No. 15A Tabarakallah Mash’Allah Plaza, Opp. Rijiyar Zaki Motor Park, Gwarzo Road, Kano.

Har ila yau, don sannin ka’idojin amfani da taskar sai a ziyarci terms and conditions ko kuma privacy policy.

Mun gode.

The Bakandamiya Hikaya Team