Beelah ce taja kunnen ailah wadda take rike da kayan gugan da tayi taa fadin"dan allah beelah ki sakeni, wallahi ni ba sata nayi ba.
"idan ba sata kikai ba uwarki kikayi dashi, shegiya mai kama da kafirai.
Dik da tana hannu hakan bai hanata fadin" ni wallahi ba kafira bace ai ina sallah kuma kowa ya sheda.
Bata ankara ba taji ta wullata a daki,yayin da kanta ya daki bango,a take kayan gugan suka zube kasa.
Dagowa tayi tana kuka wiwi tana kallon kayan wankin data gige ga wata azababbiyar yunwa wadda dama can saurin taje. . .
