"Ni dai ba surutu ba. Yunwa nake ji ka zo ka ɗauke ni please."
Dariya Lukman ya yi ta cikin wayar sannan ya amsa da,
"Ni na ce ka zo babu sanarwa. But seriously ban sa ran zuwan ka yau ba. Duka satinka uku ko?"
Daƙuna fuska Fu’ad ya yi tare da faɗin,
"Oww Lukman. Surutun nan in ka zo mun yi. Ka taho ni dai."
Ɗan jim Lukman ya yi kafin ya ce,
"Ba wani ɗan ladabi?"
"Please..."
Fu’ad ya faɗi yana kashe wayar da alƙawarin shaƙe Lukman in ya ƙaraso.
So. . .