Fu’ad na nan yadda ya ke. Ba zai taɓa canza halinshi ba. Ya ɗauka a shekarun nan ya karanci kuskuren shi. Saima abinda ya ƙaru. Son kanshi yana nan. Shekaru goma sha ɗaya babu abinda ya canza Fu’ad da shi.
Zee ce ta fito da cikinta da ya turo. Murmushi ya yi mata a kasalance. Ta mayar masa da martani.
"Ki bi min yarinya a hankali Zee."
Dariya ta yi.
"Wa ya ce maka yarinya ce?"
Ta ƙarasa ta dafa cinyar Lukman ɗin kafin ta zauna gefen shi. Kanta ta kwantar kan kafaɗarshi.
"Inaji a jikina. . .