Skip to content
Part 18 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Imaan, kamar yadda suke kiranta saboda sunan Nuri da ta ci, in har jariri na fahimtar abubuwa zata fara gane yadda take da gata, take kuma zagaye da mutanen da ke ƙaunarta kamar rai, daga sutura da sai dai a bayar da wasu don ba ma za’a samu a saka mata ba tunda ba zata dawwama a jaririya ba zuwa kan kulawa. 

Kyawun yarinyar da girman da take da shi kamar ba ‘yar wata biyu ba yake sata shiga ran mutane da wuri, Nuri kullum sai ta aiko Aroob da driver an ɗauketa an kai mata ita, haka Fawzan da kullum in ya tashi daga aiki sai ya biyo gidan ya ganta shima. Samira zata ce bata san wahalar Imaan ba sosai, tunda basa bar mata ita, da yake bata da rikici,in ka ji kukanta yunwa take ji. 

Rafiq kuwa in yana gidan, wanka kawai yake bari ta yi mata, shima don bai iyaba, tana yi yana mata magana ta bi a hankali karta saka mata sabulu a ido, bata ce mishi komai don akan Imaan komai ma bata iya ba, kukanta in ya jiyo haka zai taso yana tambaya me ta yi mata, tun tana mamakinshi har ta bari, tana addu’a kar soyayyar da yake wa yarinyar ta rufe mishi idanuwa da yawa. 

In yana gida akan ƙirjinshi take bacci, hotunanta kuwa daga ranar haihuwa zuwa yanzun yana da sun fi ɗari, manya aka wanke mishi aka saka a frames masu kyau, ko ina ka duba a cikin gidan hotunan Imaan ɗin ne, haka bangon ɗakin su ma wani babba ne ya zama kamar wallpaper, kana shigowa shi za ka fara cin karo da shi, cikin motocin shi hotunan Imaan ɗin ne, za ka rantse kanshi aka fara haihuwa. 

***** 

Ƙofar ta turo tare da yin sallama, yana kwance kan bayanshi, Imaan na kan ƙirjinshi tana bacci, da alama shi ma baccin yake yi, shigowarta ce ta sa shi buɗe idanuwanshi yana sauke su akanta. Buɗe baki ta yi zata yi magana, Rafiq ya yi saurin katse ta da ɗora ɗan yatsan shi akan laɓɓanshi. 

“Shhh….karki tasar min yarinya…”

Girgiza kai Samira ta yi, yadda yake iya bacci akan bayanshi haka na bata mamaki, shi yasa in baya gari sai dai Imaan ta sha kukanta, in ta gaji ta haƙura ta yi bacci don ba zata iya wannan wahalar ba. 

“Shikenan ba zan yi magana ba? Wa ya ce maka tashi zata yi?” 

Daƙuna mata fuska ya yi tare da harararta. 

“Yau ta gaji sosai, tunda muka je gida Aroob bata barta ta huta ba, sai jagulata take…” 

Ɗan ware idanuwa Samira ta yi akanshi da faɗin, 

“Don Allah ka ce min baka karɓeta a hannun Aroob ba?” 

“Nuri na wajen shi yasa…”

Ya ƙarasa maganar yana turo laɓɓanshi duka biyu. Dariya Samira take yi kafin ta zagaya tana kwanciya kan gadon ta ɗayan gefen. Sosai ta matsa jikinshi ta yi pillow da damtsen hannun shi. 

“Hannuna ya gaji…”

Ya faɗa cikin raɗa yana tureta a wasance. Sake gyara kwanciya ta yi, zuciyarta ɗauke da wani yanayi na son shi da baya gajiya da bata mamaki. Lokuta irin haka na sata daɗewa bata yi bacci ba, don takan ji tsoro ko mafarki take yi, ba za ta so ta farka da wuri ba. Muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce, 

“Bansan ya zan yarda duk wannan gaskiya bane ba, lokuta irin yau na sani ji kamar mafarkin rayuwa da kaine dana saba yi…” 

Saida ya gyara wa Imaan kwanciya a ƙirjinshi yana tallabe bayanta da hannu ɗaya da ya ji ta motsa. Maganganun Samira na zauna mishi, Imaan da ke bacci ya kalla, zuciyarshi ta matse waje ɗaya. Ba zata gane yadda shi ne yake jin Imaan kamar mafarki ba, duk idan ya kalleta yakan ji kamar bai kai ace ta fito daga jikinshi ba. 

Sai ta motsa, ko ta riƙo mishi riga, ko tana ƙoƙarin riƙo mishi fuska da ƙananan hannuwanta, son ta dabai taɓa sanin akwai irin shi a duniya ba ya cika zuciyarshi taf, imanin shi yake ƙaruwa, dao iko na Allah ne yake gani akan Imaan kawai. 

“Nasan me kike ji, lokuta da dama nakan ji Imaan kamar ba daga jikina ta fito ba…” 

Ɗaga ido ta yi tana kallon shi, dariya ya yi. 

“Yi haƙuri, daga jikin mu, ni da ke…”

Ya ƙarasa yana dariya don har lokacin harar shi Samira take yi, saida ya hura mata iska cikin idanuwanta tukunna ta yi murmushi tana lumshe idanuwanta. 

“Samee bazan iya sati biyu bakwa kusa dani ba, bazan iya sati biyu ban riƙe Imaan a hannuna ba…” 

Yake faɗi, tana jinshi tun jiya yake maganar, bata tanka mishi bane saboda aikinta, ogansu na ganin mutuncin Baba ne sosai shi yasa ma ya barta da taje mishi da maganar rage awannin da take yi a da saboda yarinyarta, duk da haka sai da aka rage mata albashi. Ta ga alama Rafiq so yake ta bar aikin gaba daya ta dawo gida su zauna, duk inda zashi suna tafiya tare. 

Hancinta da ta ji ya ja ne ya sa ta buɗe idanuwanta da suke a lumshe. 

“Bacci fa nake son yi…”

“Kina jina ina magana…”

Ya faɗi muryarshi cike da rikicin da yake son yi mata. 

“Bansan me zance bane shi yasa.”

A hankali ya ɗago Imaan daga jikinshi yana tashi zaune, sai da ya gyara mata kwanciya a hannunshi tukunna ya kalli Samira. 

“Ki ce wani abu, bazan iya tafiya babu ku ba wannan karon.” 

Numfashi ta sauke.

“Kasan bazan iya binka ba, ka sani, me yasa kake son in ja magana dakai?” 

Kallonta yake ranshi a ɓace, bai ga me yasa ba zata ajiye aiki ba, har cewa ya yi zai dinga biyanta abinda ake bata a wajen aikin ta ajiye, sai da ta kwana biyu tana mishi fushin da baisan dalili ba. Ita bata tausayin yadda yake kewarsu, musamman Imaan da yake ji har ƙasan zuciyarshi, sati biyun nan da zai yi a Kano ba zai samu lokacin zuwa gida ba ko ɗaya. 

Idanuwanta yake kallo, faɗa ba zai kaishi ko’ina ba, don haka ya tausasa muryarshi. 

“Samee…”

Girgiza mishi kai take yi tana kai hannu tare da rufe mishi laɓɓa, yanzun zai sa jikinta ya yi sanyi da kalamanshi, yasan soyayyarshi ce rauninta, zai shagwaɓe mata yadda ba zata iya ce mishi a’a ba. 

“Raafik karka fara don Allah, ka yi haƙuri ka je ka dawo kamar yadda ka saba… Ina son aikina sosai wallahi.” 

Hannunta ya zame daga kan bakinshi yana dumtsewa cikin nashi tare da wasa da yatsunta. 

“Alfarma zaki min, wannan karon kawai. Don Allah karki sani nisa da yarinyata har na sati biyu… Ko kina so saita fara manta kalar fuskata ne?” 

Ya ƙarashe maganar yana wani bubbuɗe mata idanuwa. Dariya ta yi, 

“Ya zata manta kalar fuskarka? Ka fa barni babu inda zanje…” 

Ƙafafuwanshi ya saukar ƙasa yana janyo gadon Imaan ya kwantar da ita a ciki, kamar jira take ya ajiyeta ta farka tana fasa wani irin kuka da yasa shi saurin ɗaukarta babu shiri. 

“Dan Allah ka dinga ajiye yarinyar nan Raafik, kaga in baka nan ni kake bari da wahala… Sam ba zata kwanta ba saita fara kuka, dole sai a hannu ko a saɓeta a kafaɗa…” 

Daƙuna mata fuska yayi yana mata alama da hannu tare da faɗin, 

“Shhhh…”

Buɗe baki ta yi zata sake magana ya yi saurin katse ta da, 

“Don Allah.”

Shirun ta yi tana zuba mishi idanuwa yana lallaɓa Imaan ɗin har ta koma bacci tukunna ya zauna ya riƙe ta a hannun shi. 

“Hmmm…”

Samira ta iya cewa tana gyara kwanciya abinta, ta tabbatar ya tafi gobe Imaan zata sha kukanta ne ta gaji ta yi bacci, don ba zata iya wannan wahalar da yake yi da ita ba. 

“Sameee…mu tafi tare don Allah… Don Allah ki min alfarmar nan.” 

Runtse idanuwanta ta yi tana buɗe su akanshi, son shi ne rauninta, ba ko da yaushe take iya jan magana da shi ba, ta tabbata tunda ya saka ma ranshi su tafi taren nan, in bata bishi ba babu kwanciyar hankali. Kai ta ɗan ɗaga mishi a hankali kawai. Murmushin da ya yi mata yana faɗin, 

“Na gode… Ina son ki.”

Ya saka zuciyarta cika fal da ƙaunarshi. Idanuwanta ta lumshe tana barin shi don ita kam bacci take ji. Rafiq kuwa wayarshi ya ɗauka yana wa wasu cikin yaranshi saƙon su kama musu hotel, don Samee ba zata iya rayuwa a gidanshi na Kano ba, ga Imaan kuwa bayason canza musu yanayin da suka saba da shi. Tukunna shima ya kwanta, Imaan ɗin na jikinshi har bacci ya ɗauke shi. 

* * *** 

Tunda suka tashi suke shiri kamar wanda za su yi watanni ba sati biyu ba. Don sai da ma Samira ta je wajen aiki da kanta ta yi reporting, za dai su cire kwanakin ne a albashinta, ta dawo ta ƙarasa haɗa musu sauran kayayyakin da suke buƙata, don in ta Raafik ne babu abinda za su yi, Imaan na manne dashi, in ta ce ta biye wa su biyun haushi ne zai kamata. 

Ta fito falo kenan da jaka a hannunta Aroob da Fawzan suka shigo gidan da sallamarsu. 

“Aroob, Fawzan…sannun ku da zuwa.”

Cewar Samira bayan sun gaisa. 

“Yaya ne yace ba zaku biyo ta gida ba, tunda Nuri ta ce mishi ta fita…” 

Aroob ta fadi tana kallon Rafiq din. 

“Za ku ɗauke mana yarinya har sati biyu shi ne ba za ku kawo ta mu ganta ba.” 

Fawzan ya ce yana karɓar Imaan daga hannun Rafiq. 

“Ka bi a hankali Fawzan…”

Rafiq ya ce yana jin riƙon da Fawzan ɗin yai mata har cikin ranshi, kar ta je ta faɗo. 

“Na rigaka fara riƙe yara Yaya, kullum sai na riƙe a asibiti.” 

Aroob ce ta matsa kusa da Fawzan ɗin tana ƙoƙarin karɓar Imaan ɗin, ya janye hannunshi. 

“Malama baki ga yanzun na karɓe ta ba.”

Murmushi Samira take yi kawai, don lokuta da dama bata san me zata ce musu ba, kalar ƙaunar da ke tsakanin su na bata mamaki, kuma ma jikinta a sanyaye yake tunda ta tashi, zata rantse ko da ta fita tana ganin duniyar ta mata daban, kamar komai ya canza, bata kuma san dalili ba. Ga zuciyarta da ke mata rawa da wani rashin tabbas da bata taɓa cin karo da shi ba. 

“Tafiya ce a gaban mu fa.”

Rafiq ya ce ganin su Fawzan sun samu wajen zama, Imaan ɗin ma baccinta take yi hankalinta a kwance. 

“Ka barsu su ganta don Allah.”

Samira ta yi maganar tana zama kan hannun kujera itama. Dole Rafiq ɗin ya samu waje ya zauna shima, hira suke ɗan yi kafij ya ga zaman ba yi musu zai ba ya miƙe. 

“Ku tashi fa, tafiya za mu yi.”

“Me yasa ma zaka tafi da su? Ka ɗauki matar ka kawai mana.” 

Aroob ta faɗi tana turo baki, har ranta take jin Imaan, bata taɓa son yara irin yarinyar ba, bata ma san tana son yara haka ba, Zafira ce dama mai so, ita tana ganin duk wahala ce a tattare da su. Dariya Rafiq ya yi yana ficewa daga ɗakin, su duka suka bishi a baya, ya saka hannunshi kan murfin motar don ya buɗe zuciyarshi tai wata irin dokawa kamar zata fito daga ƙirjinshi. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Ya fara jerowa, jikinshi na yin sanyi liƙis, da ƙyar ya iya shiga motar yana samun waje ya zauna. Samira ma zagayawa ta yi, sai da ta shiga ta zauna tukunna Fawzan ya bata Imaan. 

“Allah ya kiyaye ya tsare hanya.”

“Amin Aroob…”

“Gaskiya za mu yi kewar Imaan sosai.”

Aroob ɗin ta ɗora da faɗi, kallon ta Rafiq ya yi. 

“Imaan kawai ko? Mu ba za ku yi kewar mu ba?”

Dariya suka yi, Fawzan ya ce, 

“Haba ga yarinyar mu, kukam kuyi ta zama.”

Ware idanuwa Samira ta yi. 

“Fawzan har da kai?”

“Afuwan Antyna, ke ai ta daban ce, da kaɗan son da nake miki ya kusan kai na Imaan.” 

Dariya Samira ta yi, jikinta na ƙara mata sanyi. Motar Rafiq ya kunna, in ya tsaya biye wa su Fawzan ba tafiya za su yi ba. Addu’a suka sake yi musu tukunna suka wuce wajen tasu motar suma suka shiga shi da Aroob, motar su Rafiq ɗin na fita ta su ta rufa mata baya. Tafiya suke suna labari da Samira ɗin ta ce mishi, 

“Naso fa ince maka mu biya ta gidan mu.”

“Me yasa baki faɗa min ba? Na ɗauka kin biya ma da kika je wajen aiki.” 

Kai ta girgiza mishi tana jin son ganin mamanta kamar ta yi tsuntsuwa. 

“Kin huta ai.”

Rafiq ɗin ya ce yana ɗan ɗaga kafaɗarshi. 

“Ni kam naso ganin Mama.”

Ɗan kallonta ya yi tukunna ya maida hankalinshi kan tuƙin da yake yi yana faɗin,

“Sai dai in mun dawo in sha Allah…”

Kai kawai ta ɗan ɗaga mishi. Imaan ce ta farka ta soma kuka, feeder ɗinta Samira ta ɗauka tana saka mata a baki amma ta ƙi ta amsa, yau rikici take ji tun safe, tana tunanin ko bata jin daɗi ne. 

“Ko yunwa take ji?”

Rafiq ya tambaya, kukan Imaan ɗin na ci mishi rai. 

“Ta ƙi karɓar feeder ɗinta tun ɗazun, kamar bata jin daɗi ne yau.” 

“Sai yanzun kike faɗa min, mu juya a kaita asibiti.” 

Ware mishi idanuwa Samira ta yi ganin ya fara sauka daga hanya. 

“Mun wuce rabi ne zamu juya? Don Allah ka daina wasan nan.” 

Parking ɗin motar Rafiq ya yi a gefen hanya, ya miƙa hannu ya karɓi Imaan ɗin daga hannunta, da gaske yake tsaf zai iya juyawa a fasa tafiyar don lafiyarta ta fi mishi muhimmanci akan komai. Ɗan jijjigata yake yi. 

“Ina ruwanta yake?”

Ɗayar feeder ɗin Samira ta ɗauka tana miƙa mishi, da ƙyar ya samu Imaan ta ɗan sha ruwan, amma kukan ta ci gaba da yi, babu kalar lallashin da Rafiq bai mata ba ta ƙi yin shiru. 

“Ko ka dawo nan in yi tuƙin?”

Samira ta buƙata, bai yi musu ba ya buɗe motar yana fita, musayar waje suka yi, tana ja motar suka ci gaba da tafiya. Kan kafaɗarshi ya kwantar da Imaan yana ɗan shafa bayanta a hankali, har ya samu ta yi shiru, numfashi ya sauke. 

“Ko bata da lafiya ba iya faɗa zata yi ba.”

Jinjina kai Samira ta yi. 

“Wallahi kam, matsalar ciwon yara kenan, babu bakin magana…” 

Shiru ya yi yana kasa magana saboda zuciyarshi da yakeji a jagule. 

“Bansan me yasa manyan motoci sukai yawa a hanya ba yau.” 

Samira ta faɗi. 

“Wancan watan ma fa da zan tafi haka nai ta ganinsu, wasuma sun lalace a tsakiyar hanya…” 

“Matsalar Nigeria kenan, babu wata doka da ake bi, yanzun ƙasashen waje za ka fara wannan abin ne?” 

Gefe Rafiq ya ɗan kalla yana hango wata babbar mota da ta kife, da alamu sabon haɗari ne ma don ko kayan da ke cikinta ba’a kwashe ba. 

“Ki kalli wata mota ma don Allah…”

Ya faɗi yana ƙarasa maganar da jan tsakin takaici. Ɗan juyowa Samira ta yi tana raba idanuwanta daga titin, a zuciyarta ta fara jin wani abu mai girma zai faru da su, kafin gaba ɗaya daya jikinta yai wani irin sanyi. Wata irin dokawa zuciyar Rafiq ta yi kamar zata fito daga ƙirjinshi, bakin shi ya buɗe amma babu abinda ya iya fitowa ganin yadda babbar motar ta ƙwace tana dukan wata ƙarama da ta yi sama kafin ta dawo ƙasa tayoyinta biyu na fita tana sake faɗuwa ta gangara ƙasa, bai samu damar ganin inda ta tsaya ba saboda babbar motar suma kansu tayo, duka abin ya faru cikin mintina ƙasa da biyu, ita kanta Samira lokacin da ta juyo ta ga abinda ta ji zai faru a zuciyarta. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Shi ne abinda ta furta tana sakin steering wheel ɗin motar don ta riga ta san ikon komai na hannun Allah, Rafiq ta kalla da Imaan, yadda yasa hannuwanshi duka biyun yana riƙe Imaan dam a jikinshi, kamar yana son mayar da ita cikin jikinshi ne ya kareta daga abinda yake shirin faruwa, murmushi ta yi tana lumshe idanuwanta kafin ta ji wata irin ƙara cikin kunnuwanta da ƙarfin dukan da babbar motar ta kawo ma tasu, tasan ta rabu da kujerarta, kafij wani irin duhu ya lulluɓe duka duniyarta. 

Rafiq kuwa yana jin ƙarar dukar motar, kafin kanshi ya bugu da gaban motar, babu komai a ranshi banda ‘yarshi, banda son kareta, kukan da ta fasa yana da tabbacin mutuwa ce kawai zata mantar da shi yanayin sautin, yana jin yadda motarsu ke tsalle tana bugawa da wajaje da dama da bai sani ba, babu inda baya ciwo a jikinshi, jinshi yake kamar a wata duniya ta daban. Ya kasa addu’a, ya kasa ihu, ya kasa komai banda rufe idanuwanshi da riƙe Imaan gam, yana jin yadda kamar motar tana jujjuyawa da gilasai da ke huda duk inda suka samu a jikinshi, yana kuma jin kamar akwai wani abu a gefen haƙarƙarin shi da kuma wuyanshi amma bai san menene ba. 

Har Allah ya tsayar musu da motar cak, ɗumi yake ji a ko’ina na jikinshi, baya fahimtar komai banda son duba lafiyar yarinyarshi da ta yi wani irin shiru a ƙirjinshi. Fitowa yake son yi amma ya kasa fitowa, jinshi yake kamar yana cikin gwangwani saboda matsewar da ya yi, wani yanayi ne ke fisgarshi, shi ba a duniya ba, shi ba bacci ba, baya gane ko me yake faruwa. Baisan tsayin lokacin da ya ɗauka a haka ba kafin ya ji magana sama-sama da baya fahimtar abinda ake cewa. 

In ya ji su na mintina sai kuma ya ji komai ya ɗauke mishi, yana sake fara jinsu ya soma kiran 

“Imaan… Imaan…”

A hankali yana maimaitawa, duk sa’adda zai bar duniyar na wucin gadi ya sake dawowa abinda yake furtawa kenan, kafin ya ji hannuwa kamar ana kamashi ana ƙoƙarin fitowa da shi , ciwo yake ji a wajajen da baisan su ba, ko ina ciwo yake har cikin tsokar jikinshi, kamar a ƙasa ya ji shi kwance ana ƙoƙarin ɓanɓare hannunshi amma ya ƙi saki, zuciyarshi na gaya mishi yana riƙe da Imaan karya saketa kuma. 

“Imaan… Yarinya ta….”

Shi ne abinda yake maimaitawa. 

“Jini take zubarwa….in kana ji saika saketa don a taimaka muku…” 

Kanshi kamar an ɗora mishi mota saboda nauyin da ya yi mishi, ba sosai yake fahimtar abinda ko su waye suke faɗi ba. Yana jin suna ƙoƙarin ɓanɓare hannuwanshi, bai san daga ina ƙarfin riƙe Imaan ɗin yake zuwar mishi ba a yanayin da yake ji. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…wannan ma ai kamar ta rasu…” 

Wani ya faɗi, maganar na sa Rafiq buɗe idanuwanshi da yake jin kamar an liƙe su da gam, don da ƙyar ya samu yana buɗe su, Samira ya gani shimfiɗe kusa da shi, idanuwanta a lumshe suke, amma da murmushi a fuskarta, duk da jinin da yake fitowa ta hancinta da kuma alama har da kunnuwanta ma, yana jin ihun da yake yi a zuciyarshi duk da bai fito fili ba, so yake ya tashi ya ƙarasa inda take amma ya kasa. 

Hannun wani yake ji cikin aljihunshi baisan me yake nema ba, kafin da ƙyar a raba hannuwanshi da jikin Imaan, da idanuwanshi ya bi wanda ya ɗauki Imaan ɗin daga jikinshi, jinin da yake jiƙe da fararen kayanta nasa zuciyarshi tsayawa kafin wani irin haske ya gilma mishi ta cikin idanuwanshi komai na yin shiru. 

* * *** 

Wani irin kuka Aroob take yi kamar zata shiɗe, tunda aka bugo wayar Nuri da maganar haɗarin da su Rafiq ɗin suka yi take kuka, bata san yadda takai kanta King’s Hospital ba, tunda Nuri ta ce nan za’a yo da su Rafiq, ta kira Fawzan ya fi a ƙirga baya ɗaga wayar, tunda ta zo take cikin mota tana kuka. Wayarta ta ji tana ringing, da sauri ta ɗauka bata ma tsaya duba ko wanene ba. 

“Aroob, kin kira na bar wayar a office… Lafiya dai ko?” 

Kuka take yi tana kasa magana, ɗayan hannunta riƙe dam da inhaler & inta, kukan da ya ji tana yi ne yasa shi faɗin, 

“Menene? Aroob me ya faru don Allah?”

“Ya… Ya… Yayaa… Yayaa Rafiq.”

Ta samu tana fadi dakyar. 

“Me ya same shi? Kina ina?”

Fawzan ke faɗi cikin ɗaga murya da tashin hankalin da yake ciki. 

“Aroob don Allah kina ina? Ki min magana? Kina ina?” 

Numfashinta take ƙoƙarin ya saitu kafin ta samu can ƙasan maƙoshi ta ce, 

“King’s… Ina King’s hospital…”

Fawzan bai jira ta ƙara cewa wani abu ba ya kashe wayar daga ɗayan ɓangaren, kanta ta haɗe da abin tuƙin wasu sabbin hawayen na sake zubo mata. Bata gane tafiyar lokaci, yau ta san menene tashin hankalin da takan ji ana faɗi, yanzun kam in ana bada labarin fargaba zata zo gaba gaba don tana da tabbacin ta fi kowa fahimtar kalmar. Bata ji buɗe motar da Fawzan ya yi ba sai da ta ji ya dafa ta. Ɗagowa ta yi tana sauke jajayen idanuwanta akanshi, hannu ya miƙa mata ta kama tana saukowa daga motar. 

Jikinshi ta faɗa tana sakin wani irin kuka. Mukullin motar ya kai hannu ya zare ya rufe, tukunna ya kamata, kuka take har jikinta na kyarma. Bai ce mata komai ba sai bayanta da yake dan bubbugawa cikin son lallashin ta. Sai da ta ɗan ji ta samu nutsuwar da zata iya magana tukunna ta ɗago daga jikinshi tana faɗin, 

“Su Yaya ne sukai haɗari…”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”

Fawzan ya faɗi yana ci gaba da maimaitawa, tukunna ya tuna wa Aroob abinda ya kamata ta yi kenan. Hannunta ya kama yana riƙewa dam cikin nashi, zuciyarshi na wata irin dokawa, su dukkansu sun zuba wa gate ɗin ido suna jiran su ga ta inda su Nuri za su ɓullo, motar Daddy suka fara hangowa ta shigo tukunna ta Mummy ta biyo bayanta sai motar asibiti, da gudu ita da Fawzan suka ƙarasa suna tsaitsayawa. 

Daddy ya fara fitowa, kallo ɗaya za ka yi mishi ka fahimci tashin hankalin da yake ciki, kafin Nuri data fito itama, fuskarta a kumbure take, tana ganinsu wasu irin hawaye masu ɗumi suka zubo mata, hannuwanta ta miƙa musu, Fawzan da Aroob ɗin suka ƙarasa suna riƙewa, jansu ta yi jikinta tana rungume su, tana rasa yadda duniyarsu ta birkice a rana ɗaya haka. Kukan da take yi ya dawo dana Aroob sabo, Fawzan kam zuciyarshi ke wani irin zafi amma hawaye sun ƙi zubar mishi. 

Rafiq ne Aroob ta ga an fito da shi daga bayan motar ana ɗora shi kan gado, babu inda ba jini a jikinshi, gaba ɗaya fuskarshi ta sauya halitta, tana ganin abinda aka tallabe kanshi da shi ya gama jiƙewa da jini sharkaf, likitoci ne akanshi, ɗaya daga cikinsu na maganar da bata isowa kunnuwansu. A hankali Aroob ta raba jikinta dana Nuri idanuwanta kafe kan Rafiq ɗin da ake gungurawa. Haka Fawzan ma sakin Nuri yayi yana ƙarasawa wajen motar asibitin. 

Hannu yakai zai kamo Samira da ake shirin fitowa da ita, da abin numfashi maƙale a fuskarta, wani cikin likitocin zai mishi magana, ID card ɗin da ke wuyanshi ya ɗaga yana nuna wa likitan, ɗan kamawa ya yi ya duba ya ga Fawzan ɗin ma likitane don haka ya ƙyale shi, suka kama Samira ɗin suna sakkowa da ita, ɗagowa ya yi idanuwanshi na sauka kan Imaan da ke naɗe cikin towel ɗinta da ya gama ɓaci da jini. Da sauri ya kai hannu yana ɗaukota ganin duka likitocin hankalinsu baya kanta. 

“Sai kun kawo wani gadon…”

Fawzan ya faɗi yana kasa gane muryarshi, saboda ya raba zuciyarshi da aikinshi a yanayin, ceto su farko tukunna duk wani abu ya biyo baya. 

“Ta rasu tun kafin mu isa.”

Likitan ya faɗa mishi yana ɗan dafa kafaɗarshi tukunna ya wuce. Yarinyar ya ji ta kara wani irin nauyi a hannunshi, yara sun sha mutuwa a hannunshi, Imaan ba ita bace gawa ta farko daya riƙe, amman itace ta farko da take da kusanci da shi. Numfashi ya ja ya sauke yana kuarasawa ya miƙa wa Nuri gawar. Cikin tashin hankali take kallon shi. Kai ya girgiza mata, yana kallon yadda hawaye ke bin fuskarta lokacin da ta karɓi yarinyar, yana kuma jin gunjin kukan Aroob. 

Wucewa ya yi, cikin kanshi yake maimaita yadda aikin shi ne farko yanzun kafin wani abu, da gudu ya bi inda ya ga an yi da wani gadon, sai da suka shiga ɗakin tukunna ya ga Samira ce, duk wani ƙoƙari da za su iya suke yi a kanta, ganin ta ƙi tashi yasa Fawzan matsawa kawai, a zuciyarshi ya fara jin yadda Allah ya riga ya yi ikon shi, lokacin ta ya yi, a rana ɗaya ita da yarinyarta. Juyawa ya yi kawai yana fita daga ɗakin. 

Ko hanya baya gani sosai sa’adda ya fito, su nasu lokacin ya riga da ya yi, Rafiq ne ya yi saura yanzun. Hannun Nuri ya ji ta riƙo shi. 

“Fawzan….Samira ɗin fa?”

Sai lokacin ya ɗago ya kalleta, ya kula ba ita kaɗai bace, har da mahaifiyar Samira ɗin da ƙanninta da kuma babban yayansu. Wannan shi ne yanayi mafi wahala a aikinshi, lokacin da zaka kalli idanuwan makusantan mutum ka faɗa musu labarin mutuwarshi. Ba zai iya ba, baya jin zai iya faɗa musu. 

“Ta rasu ko?”

Maman su Samira ta tambayeshi tana kallon cikin idanuwanshi da nata da suke a bushe da tashin hankali. Shirun da ya yi ne yasa ta faɗin, 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Tana durƙushewa a wajen, yaranta na yin kanta. 

“Yayaa… Ina aka yi da shi?”

Fawzan yake tambaya. 

“Bansani ba… Wallahi ban sani ba Fawzan…” 

Nuri take faɗi tana jin numfashinta baya kaiwa inda ya kamata saboda tashin hankali, kuka take amma ta kasa samun sauƙin abinda take ji, tana kallon shi ya bar wajen yana shan wata kwana, nan ta tsugunna itama suna wani irin kuka ita da ‘yan uwan Samira, suna rasa lokacin da rayuwa ta kawosu inda suke yanzun. 

Bata taɓa sanin tashin hankali irin na yau ba, kallon dangin Samira take yi tana rasa abinda ya kamata ta faɗa musu, in har ita tana jin raɗaɗin nan a zuciyarta, batasan me suke ji ba, ba zata misalta zafi na rashi ba, don tunanin rasa Rafiq kawai na barazanar sakata ta shiɗe, shi yasa ma ta daina, ba zata bari tunaninta ya kaita nan ba, ta rasa jikarta, ta rasa surukarta duk a rana ɗaya, in ta rasa ɗanta kuma bata san abinda zata yi ba, tunda suka iso dama Yayan Samira ya karɓi gawar Imaan daga hannunta. Yanzun kuma suma za’a fito musu da ta Samira a haɗa musu. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Shi ne abinda take furtawa ko Allah zai kawo musu sauƙi cikin lamurran su. 

* * *** 

Da ƙyar ya gano inda Rafiq ɗin yake, Daddy ya samu zaune, Aroob na maƙale jikinshi tana kuka. Magana zai musu ya ga wani likita ya fito daga ɗakin da Rafiq ɗin yake, kafaɗarshi ya kamo yana faɗin, 

“Ya yake?”

Kallon Fawzan ya yi, da kayan da suke jikinshi, kafin ya ce, 

“Bazan iya cewa komai yanzun ba, akwai ciwuka a waje da ciki, yana buƙatar aiki don saukar da kumburin da ke faruwa cikin kanshi…” 

Kai kawai Fawzan ya iya jinjina ma likitan, ma’anar abinda yake faɗi na zauna mishi, kafin ya dawo kusa da su Daddy ya zauna, fuskarshi ya dafe da hannunshi duka biyun, yana maida numfashi. Samira ta rasu, Imaan ta rasu, Rafiq kuma sai abinda Allah yayi, buɗe fuskarshi ya yi, muryarshi can ƙasa yake cewa, 

“Samira ta rasu…”

“Me? Me ka ce?”

Daddy ya tambaya yana jin jikinshi na ɓari, gaba ɗaya hankalin shi na kan Rafiq, tunda aka yo waya suka zo suka ɗauki likitoci a asibiti suka wuce babu komai a ranshi sai ɗanshi, ko da suka isa ma baya ganin kowa sai Rafiq ɗin, sai yanzun da Fawzan yake magana yama tuna cewar Rafiq ɗin na tare da iyalanshi ne.

“Ta rasu Daddy, Imaan ma haka…”

Ɗago da kai Aroob ta yi, ita da Daddy na kallon Fawzan ɗin kamar yana wani yare ne daban da basa fahimta, kafin Aroob ta yi wani murmushi, hawaye na zubar mata. 

“Mafarki ne… Zamu tashi… Mafarki ne ko Yayaa?” 

Ta ƙarasa tana goge hawayen da ke zubar mata. Kallonta yake yi yana addu’ar Allah yasa mafarkin ne suke yi su dukkansu. Saboda zuciyarshi ta kasa ɗaukar rasuwar Imaan da Samira. Baisan ta ina zai fara ɗauka ba, yana kallon Daddy ya cire hular kanshi yana fifita da ita, da yadda Aroob ta sake kwanciya a jikinshi tana wani irin kuka. Za su ce awa shidan da suka ƙara a wajen ita ce mafi tsayi a rayuwarsu gaba ɗaya. 

Kafin wani likita ya fito yana ma Daddy magana, miƙewa Daddy ya yi suka wuce, daga Aroob har Fawzan babu wanda ya yi ƙoƙarin tashi daga inda yake. Daddy ya daɗe bai dawo ba, lokacin daya dawo kallon su kawai yake yi. 

“Shima ya rasun ne?”

Aroob ta tambaya. Kai Daddy ya girgiza mata. 

“Na sa hannu ne za’a fita da shi India…”

“Tare zamu tafi…”

Fawzan ya faɗi da sauri. Kai Daddy ya ɗan ɗaga yana faɗin, 

“Babu wanda za’a bari, mu duka zamu tafi… Ku zauna in dawo.” 

Kai suka ɗaga mishi suna kallo ya wuce, jikin Fawzan Aroob ta koma tana takurewa, sanyi take ji, don ko ɗankwali babu a kanta balle takalmi, riga da wando ne a jikinta sa’adda aka kira haka kuma ta fito, Fawzan ne ya kula da sanyin da take ji ya cire farar rigar da ke saman kayanshi ya bata ta saka.

“Yaya Fawzan na kasa yarda da abinda yake faruwa damu, wallahi na kasa…” 

Numfashi ya sauke, yau ko motsin Asthma ɗinshi bai ji ba, ita kanta ta ɓoye tunda ta ga abinda ya fi ƙarfinta. 

“Cikin ƙiftawar ido Allah zai iya birkita maka komai Aroob, da safiyar yau Imaan na hannuna, tana riƙe a hannuna fa…” 

Cewar Fawzan ɗin yana jin zazzaɓin tashin hankali na rufe shi. Shiru Aroob ta yi, sabon imani da tsoron Allah na shigarta, in ɗan adam bai hankalta da yanayin mutuwa da rashin tabbacin rayuwa ba bata ga lokacin da zai yi hankali ba. Da safiyar yau inda wani ya ce musu za su rasa Samira da Imaan ba za su taɓa yarda ba. Zama su yi rigima da wanda ya faɗa ne, amma yanzun gashi komai ya canza. 

Su za’a kaisu kabarinsu, rayuwar kenan, aikin banza, komai na aro ne, ga Rafiq kuma a kwance yana kokawa da tashi rayuwar, aron lafiyar da Allah ya bashi ya ƙwace abin shi. Runtsa idanuwanta Aroob ta yi tana ci gaba da neman yafiyar Allah, tana ƙara jin ita kanta numfashinta zai iya tsayawa a yanzun nan, wani irin tsoro na shigarta. Tana jin Fawzan yasa hannunshi cikin nata yana dumtsewa, kan kafaɗarshi ta ɗora kanta, hawaye masu ɗumi na zubo mata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 17Alkalamin Kaddara 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×