A kwanaki biyun nan ciwo take da ba shi da alaƙa da asibiti, ta rame ta yi zuru-zuru da ita. Bata san me yasa son Tariq ɗin ya taso mata haka ba lokaci ɗaya, tunda abu ne da ya jima tare da ita, kusan da shi ta girma a zuciyarta. Da Tasneem ta tambaye ta ce mata ta yi gujumniyar makaranta ce, kuma tana jin kamar zazzaɓin dare take yi, ta ce mata ta je asibiti ta amsa da zata sha magani in zata kwanta in bai yi ba sai ta je, dole Tasneem ɗin ta ƙyale. . .