Alƙali ya tsawatarwa Asabe tare da yi mata barazanar ɗauri idan ta sake yin magana ba tare da izini ba.
Bayan Alƙali ya gama sauraron duk wata shaida daga bangaren Malam Hassan, sai ya kalli Lauyan Asabe ya ce ko yana da abin cewa. Tashi tsaye ya yi ya ce, "Ba ni da abin cewa ya mai shari'a."Alƙali ya yi rubuce-rubucensa sannan ya ɗago ya kalli jama'ar kotun ya ce,"Kotu ta ɗage wanann shari'ar zuwa ƙarshen wannan watan. Sannan kotu ta ba da izini a je asibiti a yi gwajin DNA. . .