Skip to content
Part 17 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Lokaci ɗaya Ameera ta sa ki wata dariya wacce sam-sam cikin ta babu nishaɗi. Ta ce “Aure dai za ka yi Adam? Kuma Haura zaka aura ko? Sai kawai taci gaba da dariyar ta har tana riƙe cikin ta. Adam ya tsaya yana kallon ikon Allah, to ko dai Ameera ta samu matsala ne! Juyawa ya yi ya bar ɗakin cike da mamakin Ameera. Bayan fitar Adam Ameera ta tsaya da dariyar ta na kallon ƙofar da ya fita ɗin. Da sauri ta juya gurin da ta ajiye wannan wasiƙar ta ɗauka ta buɗe tana tsaye ta shiga karantawa. Bansan yaya zanyi da ke ba, na gaji da duk wannan abun da kike min, basan haka masu ciki suke komawa ba sai a kanki, yanzu zan bar miki gidan zan tafi neman magani bazan dawo ba sai Allah yayi na warke, domin na lura ke ba ƙaunar samun lafiya ta kike yi ba, Karki neme ni domin ba zaki sameni ba har sai lokacin da na dawo. Ga gidan na bar miki kiyi duk abun da kika ga dama da shi.

Ameera ta juya bayan takardar ko a kwai sauran magana, ganin babu komai ne yasa ta saki tsaki tana faɗin aikin banza ashe ma ba abun da nake nufi ba ne duk na bi na tada hankali na.

Sosai auran Nasiru da Nana yake ta natsuwa wanda yanzu saura kwanaki shida hakan yasa Ameera ƙara nisanta kanta da ga bikin domin tayi alƙawarin bazata shiga cikin sha’anin bikin yaron da ya ɗaga hannu ya mareta ba. Haka Adam ya je ya sanarwa da Najib da khadija maganar auran sa da Haura, ai kuwa nan take dukkanninsu suka nuna rashin amincewarsu akan hakan, amma shi ya ce yaji ya gani babu wanda ya isa ya hana shi auran ta. Sosai Najib da khadija suka shiga mamakin wannan masifar, yaya daga ganin yarinya sai ya ce zai aureta, ita kuwa Khadija kuka ma ta fara tana faɗin an asirce mata yaya.

Ɓangaren Ameera kuwa, duk wani tashin hankali tayi amma Adam ya ce Aure ba babu fashi, hakan yasa ta koma zagin uwarsa da ubansa da suka riga mu gidan gaskiya. Shi kuwa Adam baya ji baya gani. Itama Haura ta yarda da shi domin yana sanar da ita ta amince nan take, hakan yasa ta fara sakin jikinta a cikin gidan ba kamar da ba, domin yanzu mutuƙar Adam baya gidan to bata yarda da cin fuskar Ameera domin wannan matar da take kira da Ɓultuwa ta gama bata shawara sosai a kan Ameera ɗin. Sai dai abun da yake damun Ameera yanzu bai wuce rashin jin daɗin jikinta da bata yi ba ne, domin yanzu cikinta ya shiga wata takwas da kwanaki, hakan yasa tayi nauyi sosai, amma bakinta bai mutu ba.

Da ƙyar take tafiya har ta iso palon ta zauna tana ɗan sakin ƙara a hankali tana riƙe bayanta, waya ta ciro ta kunna data ta shiga neman littafin da zata karanta na online domin ta kwana biyu bata karanta littafi ba, take ta tuno da littafin da take karantawa na Addininmu bata gama karantawa ba. Tana cikin neman littafin taci karo da status ɗin Adam wanda yayi yau. A hankali ta buɗe tana kallo. Hoton Haura ne wanda ta ɗauka a cikin motarsa wanda yake nuni da cewar yanzu a ka ɗauki hoton domin kayan da ya saka ɗazu ne. Take ta saki wayar a ƙasa tana riƙe kanta da yay mata nauyi. Sosai take jin kanta ya riƙe afili ta furta “Adam ni za za k k ki wa”… Bata ƙara sa ba kuka ya kufce mata ta kwanta a ƙasan gurin ta fara kuka harda jan majina. Tana cikin haka ta ji shigowar su palon alamar sun dawo, da sauri ta yunƙura ta miƙe da ƙyar ta nufo gurin su wanda suma jin kukan nata ne ya tsayar da su suna kallonta. Tun kafin ta ƙarasa gurin ta gama ƙare masu kallo. Haura sanye take da rigar abaya baƙa tayi kyau sosai kasancewar ta fara. Shi kuma Adam manyan kaya ne ajikin sa harda hula, sosai kayan suka zauna a jikinsa daram, ga wani annurin farin ciki dake fita daga fuskarsa.

Tana ƙarasawa gurin ta tsinke Haura da lafiyeyen mari ta chakumeta tana kuka tana girgizar ta tana faɗin “Tsinanniya maiya mai kuka yiwa mijina? Na ce wani irin asiri kukai masa da zai ce ke zai aura, to wallahi Allah ya fiku kuma sai kun bar gidan nan matsiyata dangin arnaku. Haura dai ta tsaya ta na kallon ta wanda badan Adam na gurin ba tsaf zata rama amma hakan yasa itama ta saki kuka wanda yasa Adam ɗin saurin ƙwace ta daga hannun Ameera ɗin ya ruƙo Hauran jikinsa ya tafi da ita ɗakin su. Ganin haka yasa itama Ameera bin bayansu tana kuka, tana zuwa Adam na dawowa hakan yasa ta kama rigarsa ta fara faɗin “Allah ya isa tsakania da kai shege mugu algungumi wanda ba zai gama da duniya lafiya, wallhi sai dai ka sake ni na koma gidan mu a kan ka auri wannan arniyar kuma maiyar. Ganin haka yasa Adam fara tafiya ita kuma tana biye da shi taƙi sakar masa rigar, sai tafiya yake yana janta amma taƙi daina zagin sa, sai da suka zo har palo kafin ya juyo ya dibeta ya ce “Yanzu sakin kike buƙata ko me? Cikin ɓacin rai dake neman hallkata ta ce “Ka sakeni na ce mugu macuci bana sonka ni kawai ka sake ni”

Adam ya ce “Tom sake ni sai na sake ki ɗin ko. “Anƙi a sake ka ɗin wallahi sai ka fasa auran wacce yarinyar ko ba ka so. Adam ya ce “Ok tom yañzu sakar min riga sai muyi magana ko?. Sai da yayi da gaske kafin ta sake shi. Ya ce “Honey ba kya jin magana, ban san mai ya mayar dake haka ba, Please ki natsu ku zauna lafiya da Haura, wallhi bata da matsalar komai kuma zata miki biyayya kaman yadda kike so. Ameera ta ce “Ko me zata min ba na so, kawai dai subar min gida shine kawai abun da na ke so. Sannan yanzu ka duba ba fa, ɗaukar ta kayi a mota kuka fita ba tare da na sani ba. “No kaya fa kawai na sayo musu ita da waccer matar. Ameera ta saki tsaki tana kawar da kai gefe. Ganin dai bata da alamar sakkowa ne yasa Adam barin gidan yana jin surutunta amma bai ko waiwayo ba.

Ɓultuwa ce tsaye cike da masifu iri-iri take zagin Haura akan yaya zata tsaya ta mareta bata rama ba. Ameera ta ce “Ni Allah so nake kawai ya sake ta amma shima yaƙi kina jin fa irin zagin da take masa amma yaƙi furta mata sakin da yake shima wawa ne. Ɓultuwa ta ce “Shi yasa nake so ayi sauri ayi auran domin kinsan idan har ta aihu komai lalacewa zai yi, dole a cikin biyu ayi ɗaya ko dai ya saketa kafin ta haihu ko kuma ayi auran naku kafin ta haihu. Haura cikin matsuwa ta ce “To yanzu ya za’ayi Kinga har zuwa yanzu bai ƙara yin maganar auran ba? Ɓultuwa ta ce “Yanzu baki tuna komai da Ammin ki ta yi akan cikin ba? Haura ta ce “Wallahi har yanzu banga komai ba kuma tabbas tana haihuwa zata dawo hankalin ta muddin bamu nemo abun ba. Ɓultuwa ta ce “Duk laifin ki ne, yaya za’ayi mahaifiyar ki na yin abu amma ba za ki so sanin komai ba, yanzu gashi ta mutu kuma ke baki san inda ta ajiye komai ba. Haura ta ce “Nifa sai nake tunanin kamar shegiyar matar tasan abun da Ammin tai mata ne yasa ta kashe ta, ai kuwa wallahi muddin na auri mijinta to itama ko dai ta mutu ko ta bar gidan. Ɓultuwa ta kalli Haura ta ce “Kema fa sai kin ƙara dagewa domin Kinga idan har baki aureshi ba har ta haihu to mun shiga uku domin kuwa shima zai dawo hankalin sa, kuma wallahi korarmu zai yi, Kinga kuwa babu inda zamu je. Haura ta yi shiru sai cen ta ce “Idan yazo da kaina zan masa maganar aure kawai nake so muyi”… Cikin sauri ta tareta da cewar “Karki kuskura ki masa magana bari da kansa zai zo. Haka dai Haura ta fasa amma dai ta matsu yazo ayi wannan auran kowa ya huta.

Cikin kuka Ameera ta dauki ƴar ƙaramar jakarta ƴar hannu tana tafiya tana kuka Kamar wacce a kaiwa mutuwa. Tana zuwa ƙofar get ɗin gidan taga get ɗin a rufe, tana gani tasan adam ne ya rufe. Hakan yasa ta zauna a gurin ta ɗaura hannu a kai ta fashe da kuka. Sai da tayi mai isarta kafin ta juya ta dawo gidan ta ɗauki waya ta kira Umma har kira biyar amma babu amsa. Ta lalubo lambar Nana ta kira, ai kuwa kira ɗaya amarya Nana ta ɗaga tana sallama. Take Ameera ta fashe da kuka ta cikin wayar harda ihu da kiran waiyoooo Allah da na shiga uku duk a lokaci ɗaya. Nana da take tare da Nasiru suna shawarin yanda zasu gudanar da komai na dina taji irin kukan da Ameera ke yi.

“Lafiya dai anty Meera? Ta faɗa ta na sauraron irin gunjin ihun da Ameera ke yi. Nana ta ƙara cewa “Anty Ameera wai me ke faruwa ne pls sanar mini mana kodai wani abu ne ya samu Adam ɗin?

“Dan Allah Nana kizo gidana yanzu Please zan mutu ki taimaka ki zo tare da Umma wallhi Adam zai kashe muku ni. Jin haka yasa hankalin Nana tashi ta kashe wayar tana faɗin ganinan zuwa yanzu. Tana gama wayar ta kalli Nasiru da ya wani haɗe rai ya na jiran ta kawo masa wata maganar yanzu su hau sama su faɗo. Cikin ɗan rikicewa da halin da taji yayar tata ta ce “Please ko zaka sauke ni a gidan Anty Ameera wallahi ba lafiya ba kaji fa har kuka ta ke yi. Nasiru da yake jira azo gurin ya ce “Wallahi babu inda zaki je koma mai zai faru ai ita da mijinta ne, ko kin mata irin zagin da tai min kuma ta ce bazata taɓa zuwa bikin mu ba, saboda da haka kema ba zaki je gidan ta ba wallahi muddin na isa da ke.

Nana ta ce “Ƴar uwata ce fa, kuma yayata amma kake faɗin haka, to koma me tai maka sai ka hanani zuwa zuwa gidan ta?. Nasiru ya ce “Ni dai idan na isa da ke to karki je, ki bari har sai mun gama abun da muke yi na tafi sai kizo. Nana kuwa da hankalinta duk ya gama tashi da halin da yayar tata ta ke ciki ta ce “Gaskiya bazan iya ƙin zuwa gidan yayata haka kawai ba, kuma sai ka bari sai ka aureni kafin ka kafa min sharuɗan zuwa wani gurin da baka so, amma yanzu dai gaskiya sai naje naji halin da take ciki sai dai kayi haƙuri yayata ce bani da kamar ta koma me zata min.

Cikin ɓacin rai ya ce “To wallhi muddin kika bar gurin nan bamu gama abun da muke yi ba to babu ni babu ke har abada, kuma aure na fasa domin bazan auri matar da bata jin magata ba. Dama tasan za’ayi haka domin ta lura da take-tsken sa kenan dama. Ta ce “Allah ya sa hakan shi yafi alkairi. Tana faɗa ta juya zata tafi amma Nasiru ya kamo hannunta ya juyo da ita ta fuskance shi da kyau ya ce “Wallahi idan har kika bar gurin nan aure dani dake ya fasu kenan har gaba da abada. Ya faɗa yana kallon idonta da har ya fara taruwan ruwan hawaye. Kafin tayi magana har sun gangaro kan kumatunta ta ce “Idan ka fasa sai me? Allah yasa kaine kaɗai na mijin da yayi saura a duniya. Ganin zata tafi yasa ya ƙara juyowa da ita ya ce “Wallahi baki isa ki je gidan wannan munafukar yayar taki ba. Cikin jin haushin kalmar munafuka da ya kira Ameera da ita ta ce “Duk abun da zamuyi da kai karka ƙara zagin kowa nawa domin nima bana zagin kowa naka, saboda haka bazan jura ba, kowa ya girmama dangin kowa shine mutuncin.

“To ƙarya nake ba munafukar bace? Matar da take cewa ta tsaneni kuma bata sona da ke, to wallahi ni dai sai na ce mata magulmaciya kuma munafuka. Nana ta ce “Sai dai kaine munafiki amma ba itaba…” Kafin ta ƙara sa ya buge mata baki ya ce “Ni kike kira munafuki. Cike da jin zafin buge mata bakin da yayi ta fara magana “An faɗa maka ɗin, kasan babu dadi ni ka faɗa wa yaya ta. Hakan da tayi yasa hankalin mutane fara dawowa kansu, dama kaf anguwar kowa yasan wannan halin nasu. Ƙarshe dai sai da aka yi dokeni in dakeka kafin suka rabu kowa yayi alwashin ya fasa auran ɗan uwansa. Shi Nasiru ma harda faɗin yanzu zai turo a karɓi komai da ya kawo mata.

Haka Nana ta shirya bata ko sanar da Umma ba ta nufi gidan Anty Ameera ranta a mugun ɓace. Lokacin da ta isa gidan ta tarar da ƙofar a rufe hakan yasa ta kira Ameera ta ce mata gata a waje. Ameera ta kira Adam akan yazo ya buɗe wa Nana gida amma Adam ya ce “Yanzu baya kusa, tunda har ta kori mai gadi ai sai dai tayi hakuri har ya dawo ya buɗe. Ta cikin wayar ta ce “Nana ce fa da Umma suka zo duba ni. Adam ya ce “Idan zasu iya jira har na dawo to su zauna a ƙofar gidan, idan kuma ba zasu iya ba to su koma gida har sai na dawo. Yana faɗa ya kashe wayar. Ameera ta bi wayar da kallo tana jin wai anya kuwa yaji abun da ta ce masa. Take ta shiga ɗakinsa domin dubo ko zata samu wani makullin da ya a jiye na get ɗin. Babu inda bata dubaba a cikin ɗakinsa amma babu komai. Hakan yasa ta koma ɗakin ta, tana duba gurin da yake ajiyar takardun sai kuwa ta ga makullin get, kasancewar tasan irin sa yasa ta ɗauko ta nufi waje wanda Nana take ta kiranta akan ta gaji da tsayiwa.

Da ƙyar ta iya buɗewa Nana ta shigo gidan duk ranta a ɓace, ga abun da Nasiru yayi mata ga barinta a waje da a kayi yanzu. Tana shiga suka haɗa ido da yayar tata wacce rabon su da su haɗu ido da ido sun kwana biyu. Take Ameera ta nufo ta tana jin wani sanyin daɗin ƴan uwantaka. Nan take ta fashe da kuka. Nana ma kukan ta kama tana ƙara tuno abun da Nasiru yayi mata. Haka suka shiga cikin gidan wanda suna shiga Haura da Ɓultuwa suna fitowa daga cikin ɗakin su da niyyar kama Ameera su mata gargaɗi a kan dukan Haura da shiga sabgarsu. Turus kowa yayi suna kallon juna, Nana tayi mutuwar tsaye tana kallon Haura da Ɓultuwa.

<< Ameera Da Adam 15Ameera Da Adam 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×