Skip to content
Part 41 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Kee! Ballagaza See me!”

Al’ameen ya mata maganar cikin tsawar da sai da yasa hatta Ablah da ba ita aka yiwa ba ta razana, Nafeesa kallon nasa tayi cike da nutsuwa babu wani alamun razana tare da cewa.

“Na kalleka kayi kyau sai kuma akayi yaya, hubbyna ina son muyi magana ne ta fahimtar juna Please ka shigo ka sauƙe ni a gida sai muyi maganar a hanya?”

Nuna kansa yayi da yatsa yace.

“Ni zaki tambaya wacece ita, zaki sauya mata kammani kika ce ko, to ki gwada ki gani idan ke zaki ganu ko uwarki bazata iya ganeki ba domin kuwa ke naki kammanin da zan sauya miki iyayenki ma gagara ganeki zasuyi, ita da kike tambaya waye kike kiranta da almajira itace rayuwar Al’ameen itace dukkan farin cikin sa, Almajirar dai ta fiki matsayi da daraja ko banza shi almajiri za’a samesa da karatun addini, Al’ameen wannan almajirar yaga ta dace yayi rayuwar aure da ita nan ba da jumawa ba kuwa, kin zauna mata a sit ɗin ta, ya kamata ki fice mata daga motar mijinta saboda ta gaji da tsayuwa, kin san sauraniya ba’a son rana yana musu yawa, su kuwa bayi ai dama da wahala aka sansu musamman ma ƙasƙantattu irinki.”

Ya ƙarisa maganar yana saka hanu ya fisgota da ƙarfi ta fito daga motar ya hankaɗata gefe tare da yiwa Ablah nuni ga motar yace.

“Bismillah sarauniyar ta, wacce ta gaji daraja da ɗa’a kuma zuciyar Al’ameen ƴar lelena.”

Yayi maganar yana kallon Nafeesa dake durƙushe yana kuma sakin murmushin mugunta, tare da kanne mata ido ɗaya, wani irin ɗaci da tuƙuƙun baƙin ciki Nafeesa taji da munguwar tsana take kallon Ablah ita kuwa Ablah murmushi ta saki tare da shigewa cikin motar, rufewa Al’ameen yayi tare da zagawa ya shiga yaja motar yabar wajen.

Da ƙarfi cikin ɗacin zuciya ta ƙwala masa kira sai dai ina tuni yaja motar sa baima san tana yiba, hanunta ta dunƙule cike da baƙin ciki ta daki ƙasa, Jamila dake hangota ne ta ƙariso da sauri tare da sunkuyawa ta ɗagota, karkaɗe jikinta tayi tare da kallon gefenta Allah ya rufa mata asiri ma babu kowa a wajen wanda ya ganta.

“Jamila ya ci mutuncina ya zubar min da ajina a gaban wata jaka ƴar aji ɗaya, yau Al’ameen ya ƙasƙantar dani, saboda kawai yaga ina binsa ina gwada masa Soyayya shiyasa yamin haka abinda wani namiji bai taɓa min ba, ni nake walaƙanta maza yau kuma ni namiji ya wulaƙanta abun takaicin ma a gaban wata jaka, na rantse da Allah Jamila, Al’ameen yaci bashi kuma sai ya biya wannan bashin zan nuna masa wacece Nafeesa.”

Tayi Maganar tamkar zata saka ihu domin kuwa sosai abinda Al’ameen ya mata ya ci mata rai.

Jamila numfashi ta saki ba tare da tace komai ba ta ja hanun Nafeesa tana huci suka fita daga school ɗin adaidaita sahu suka tara, har suka shiga Nafeesa huci take, Tabbas da badan Al’ameen yana da kuɗin da take buƙata ba wallahi da bai isa ya fara mata wannan cin mutuncin ba, amma yanzu ma zai gane da ita yake, muryar Jamila taji.

“Fushi ba naki bane yanzu Nafeesa ko kin manta shirinmu a kansa ne, duk abinda zai miki ya daina damunki domin kuwa na lokaci ƙanƙani ne kafin ya dawo hanun mu, ko kin manta cewa Al’ameen nan da watanni uku muka sanya zai dawo tafin hannunki zaki rama tabbas harma ki sashi ya durƙusa miki, amma a yanzu bama buƙatar fushinki domin kuwa fushinki zai iya lalata mana komai, ki faɗa min wacece yarinyar dana gansu tare.?”

Idanunta da suka sauya kala tsabar baƙin ciki Nafeesa ta ɗago tare da amsa mata.

“Wai budurwarsa ce, ita zai Aura harya fara kiranta da matarsa, zuciyata ta buga naji ɗaci a cikin wuyana sanda ya ambace ta da kalmar matarsa, akwai Babban ƙalubale a gabanmu, domin kuwa daga ganin wannan yarinyar ba kanwar lasa bace.”

Zaro idanunta Jamila tayi ko cikin mafarki batayi zaton Al’ameen yana da budurwa ba.

“Budurwa kuma lallai akwai matsala, amma babu komai zamuyi maganin abun zanyi tunani akai ta kan yarinyar zamu fara karki damu ki kwantar da hankalin ki.”

“Ta yaya hankalina zai kwanta kina ganin yadda Al’ameen yake wulaƙanta rayuwata.”

Murmushi Jamila tayi tare da cewa.

“Dama dole zaki fuskanci wulaƙanci, Saboda bake bace Yarinyar da yake so yana miki kallon wacce ta takurawa rayuwarsa ta ke neman hanasa sukuni, Nafeesa karki manta da cewa Da ɗan uwansa mafi soyuwa a garesa kika rabu kin san yana jin zafin wannan a zuciyarsa, zamuyi amfani da Haidar domin dawo da hankalin Al’ameen gareki.”

“Amfani da Haidar kuma, ta yaya hakan zata faru kinsan abinda kike faɗa kuwa, wannan ba hanya bace da zata ɓulle mana, mu nemi wata dai.”

“Itace kuwa hanyar da zata ɓulle mana, kin san me zai faru, yanzu nasan daga ya sauƙe wannan jakar Companyn su zai shige, a sauƙe mu a Companyn.”

Duban Jamila Nafeesa tayi cike da kullewar kai domin kuwa ta sakata a duhu 

“Yanzu ya gama wulaƙanta ni kuma na bisa Companyn me kike tunanin zai faru, bazai saurareni ba.”

“Zai saurareki ko dan saboda kar Haidar ya fahimci wajensa kikazo da alamu yana tsoron Haidar yasan halin da ake ciki saboda yana gudun saɓani ya shiga tsakaninsu da Haidar ya kamata mu fara haɗasu faɗa da munguwar gaba mai tsananin gaske inda kowannensu zaiji ya tsani kowa, Nafeesa idan har kika sanar da Haidar cewa Al’ameen yana bibiyarki lallai sai kin sosa shine ke kuma kikaga ya fisa dacewa dake domin kuwa ya sanar dake cewa shi Haidar ɗin mutumin banza ne bai dace dake ba dan haka shine dalilin da yasa kika rabu dashi, kika koma ga Al’ameen dan haka ya rabu da rayuwarki Al’ameen kike so.”

Da sauri Nafeesa ta ɗago ta dubi Jamila tare da cewa.

“Haidar zaiji haushin Al’ameen yaji baƙin ciki marar misaltuwa zai hasala da Al’ameen a yayin da Al’ameen zaiyi ƙoƙarin fahimtar dashi amma ba lallai bane ya sauraresa, wannan shine abinda zai faru, amma meye fa’idar hakan.?”

“Tambaya mai kyau, fa’idar sa shine faɗa da gaba zai shiga tsakanin su yayin da Al’ameen yaso ya fahimtar da Haidar yaƙi fahimtar sa, hakan zaisa shima ya hasala ya ji haushin Haidar daga nan zaiyi tunanin tunda Haidar ya kasa fahimtar abinda zai iya da wanda bazai iya ba to bari ya soki yaga mai zai faru, da wannan damar zamuyi amfani wajen jawo Al’ameen jikin mu da zarar yazo jikin mu kuwa bazamu taɓa bari ya kufce mana ba, duk abinda zamuyi domin ganin mun mallakesa zamuyi, yanzu idan munje Companyn ki fara yiwa Al’ameen barazanar zaki sanar da Haidar abinda ke faruwa.”

Dariya Nafeesa tasa tare da cewa.

“Shiyasa nake mungun ƙaunarki ƙawata kin san kan bariki, ba damuwa mu shige Companyn.”

Murmushi Jamila tayi tana cewa mai adaidaita ya sauƙe su wanda ya cika da mungun mamakinsu saboda yana sauraron dukkan maganarsu da Tabbas da yasan waɗanda ake ƙullawa wannan makircin babu makawa sai tara su ya fahimtar dasu kaidin da ake ƙoƙarin ƙulla musu, domin kuwa sharrin mace yana da matuƙar tasiri, tsayawa yayi suka sauƙa yaja adaidaitan sa yabar wajen cike da jin tsoron duniya.

“Meyasa kikace ya sauƙe mu anan ba tare da ya isar damu Companyn ba.?”

Murmushi Jamila tayi tare da cewa.

“Saboda yaji sirrin mu zai iya yiwuwa idan yaga inda zamu sauƙa yayi ƙoƙarin tona mana asiri, shiyasa na sallamesa a nan, zamu ɓatar da sawu gudun karma ya bibiye mu, mu shige gidana, muyi 30 minute kafin mu nufi Companyn nasa.”

“Tabbas hane kina da gaskiya mu tari wani adaidaitan muje.”

Kallon sa Ablah tayi tare da cewa.

“Meyasa zaka mata ƙarya, abinda ka mata sam bai kyautu ba.”?

Al’ameen hankalinsa naga mota yace.

“Kafin na amsa miki tambayarki yanzu ina ɗaya zan sauƙeki gidan naku zaki ko gida zamu shige.?”

“Gidan mu zaka sauƙe ni na sanar da Inna Jumma zan kwana a gida Umma bata jin daɗi zanje naga yanayin jikin nata.”

“Okay, Meyasa kikace na yiwa wannan dabbar ƙarya, hmmm duka maganata babu ƙarya a ciki, ko da baki bani dama ba, ni kece rayuwata kuma farin ciki na matar da nake son na Aura, to meye ƙaryar a cikin wannan maganar, Ablah daga yau karki kuma cemin nayi ƙarya domin kuwa matsayina ya wuce ki furta min wannan kalmar miji nake ƙoƙarin kasancewa a gareki, dole ne ki girmamani dan nace ina sonki ba shine zaisa ki rainani ba, sannan amsar tambayar ki ta biyu itace, babu kyautatawa tsakanina da wannan Yarinyar domin kuwa baki san munguwar kunama bace ita.”

Shuru Ablah tayi cike da jin kunyarsa da nauyin Maganar da ta faɗa masa, sai yanzu ta fahimci maganar da ta faɗa masa sam bata dace ba, kanta na ƙasa ta furta.

“Kayi hkr na fahimci maganar dana faɗa maka bai kyautu na gaya maka ba, ranka ya ɓaci kayi hkr, sai dai yaya Al’ameen babu soyayya a zuciyata ka daina sakawa a ranka cewa ni ce matarka ka fahimci ban dace da rayuwarka ba, ni ba tsararka bane kafi ƙarfina ta ko ina.”

Murmushi Al’ameen yayi yana cigaba da driving ɗinsa yace.

“Babu ruwana da dacewa ko cancanta, soyayyarki kawai na ke nema sai dai idan kece kikafi ƙarfina amma ni banfi ƙarfinki ba, kije kiyi shawara idan kinje gida zan jira amsar soyayyata daga nan zuwa ki dawo.”

Numfashi Ablah tayi tare da kaɗa kanta dai-dai sun iso ƙofar gidan nasu bisa mamakin Ablah gani tayi gidan su an cire wannan langa langan an kewaye da ginin block da block har da get aka sanya musu a ƙofar gidan, da kallo Ablah tabi Al’ameen tana tunanin anya kuwa gidan su ne.

“Yaya Al’ameen anya kuwa nan gidan mu ne.?”

Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Shakka babu gidan ku ne ya sauya miki ko, ni zan shige sai Allah yayi dawowarki gobe ki jira idi zaizo ya kaiki school.”

Da to ta amsa shi kuma ya shige cikin motar yaja yabar wajen cikin gidan ta shige Umma na zaune a baranda tana tsinkar ganyen zogale kusa da ita ta zauna tana dariya itama Umma dariyar tayi tace

“Ablah kece tafe yanzu, ɗazu kuwa mukayi waya da Aminu bai kuma sanar dani cewa zaki zo ba.”

“Ummana dole ai nazo Inna Jumma tace min bakiji daɗi ba.”

“Zazzabi ne da ake ta fama dashi yanzu amma da sauƙi ai sosai wannan ganyen zogale da kikaga ina tsinkewa dafawa zanyi na tace ruwan na dinga sha kin san yana maganin zazzaɓi sosai.”

Kanta Ablah ta girgiza tare da miƙewa ta cire hijabin ta, ta je ta ijiye da bag ɗinta sannan ta fito ta hau taya Umma aiki suna zancen duniya nan ne ma Umma take sanar da ita Hafsa bata da lafiya ta kwana biyu tana kwance.

Da la’asar suna zaune a falon Umma take sanar da ita Al’ameen ya saka aka gine mata katangar gidan nasu, harma ya bata dubu ɗari Uku ta fara sana’a sosai Ablah taji daɗin karancin da Al’ameen yake yiwa mahaifiyarta, Umma ce tace.

“Ablah ya Amarya kuwa abubuwan nata da sauƙi dai ko?”

“Hmmm! Umma ina wani sauƙi, Amarya ai bazata fasa halinta ba, Umma kinsan ma me tace min, hmmm! Wai sai ta sakani a cikin bala’i munanan maganganu iri iri, Umma ta tabbatar min da cewa sai ta kashe Al’ameen da duk wanda ke cikin gidan ni kuma ta sani cikin bala’i.”

Murmushi Umma tayi tare da girgiza kanta kafin tace.

“Wasu suna mantawa da cewa ba’a taɓa sauya ƙaddara ko a murɗata baya yiwuwa duk zanen ƙaddarar da ubangiji ya zanata to babu makawa wannan zanen bazai goge ba har sai alƙalami ya ƙarasa aikin sa, Duk sharri da makircin masu makirci Ablah muddun Allah ya kareka to fa basu isa su muzantaka ba, ina son ki dinga imani da ƙaddara ki kuma yi yaƙini da ubangiji zai kareki to ina tabbatar miki da babu abinda zai sameki sai alkairi, ki jajirce Ablah ki saka a ranki zaki iya kawo ƙarshen zaluncin Amarya, Ablah dukkan abinda ya faru da ke har police station da aka kaiki naji komai duk da kin ɓoye min baki sanar dani ba, shi Al’ameen ya sanar dani sannan ya bani haƙuri ya tabbatar min da bai yadda kece kikayi wannan aikin ba yamin alƙawarin cireki daga matsalar da kika faɗa, ko iya wannan masifar da kika faɗa kuma kika fita to hakan ya isa ya tabbatar miki da cewa zakiyi Nasara akansu, ƙarya bata taɓa danne gaskiya Ablah, adduata tana tare dake zai kareki daga duk wani sharri ina da yaƙini akan wannan.”

Murmushi Ablah tayi idanunta yana cikowa da hawaye Tabbas tana alfahari da samun Umma a matsayin mahaifiyarta domin kuwa itace Abokiyar shawaranta taka bata ƙwarin gwiwwa a duk halin da take ciki, duk da baƙin ciki da dangin mahaifinta dana mahaifiyarta suka ɗurawa Umma hakan baisa ta sare da rayuwa ba, ta cigaba da rayuwa da ƙwarin gwiwwa, har abada bata son Umma ta waiwaici Niger domin gudun dawo da baƙin ciki rayuwarta dalilin da yasa bata ƙaunar Maganar Aure domin kuwa duk sanda akace anzo zancen aurenta dole za’a nemi dangin mahaifinta, idanunta ta runtse tare da cewa Umma.

“Hakane Umma kullum da ƙwarin gwiwwar ki nake rayuwa sai dai Umma a wannan karon Al’ameen kansa yazo da abubuwan da suka girgiza ni, cewa yayi wai yana sona Umma.”

Murmushi Umma tayi tare da cewa.

“Dama nasan haka zai faru Ablah, domin kuwa ni naga hakan a idanunsa ko ta yadda yake mutuntani ya isa na fahimci yana sonki, ki amshi Soyayyar sa, amma da zuciya ɗaya kuma saboda Allah ba saboda abin duniya ba, amsar soyayyarsa shine zai baki damar karesa cikin lumana, Ablah Al’ameen mutumin kirki ne na Tabbata zai riƙeki bisa gaskiya da amana, sai bana son ki dinga tambayarsa wani abu nasa, a wannan lokacin domin kuwa hakan zai zamo tamkar abin hanunsa kike so, kin fahimceni.”

Kanta Ablah ta ɗaga tare da cewa.

“Eh Umma na fahimta, amma Umma ni bazanyi Soyayya ba, babu wani Aure da zanyi Saboda bana son na tuna miki da dangin Baba, bana son wani abu ya sake haɗaki dasu Umma idan har zanyi Aure to shakka babu dole sai kunyi tarayya da dangin Baba ni kuma bana son Tarayyar ku, ba wai bana son Yaya Al’ameen bane Auren ne bana so.”

Murmushi Umma tayi tace.

“Burin ko wace Uwa ta gari Ablah shine ta Aurar da ƴarta shine cikar mutunci da kamalar Mace duk abinda dangin babanki zasu min a bayan na da ne, Ablah tunda na haihu dasu na san dole komai jimawa zamu sake haɗuwa, nasan da wannan Ranar dole zata zo, kuma na shirya mata, ina baki umarnin tunda kina son Al’ameen ki amshi Soyayyar sa, ki kuma kasance mai jajurcewa da haƙuri da kuma ƙarfin zuciya domin kuwa ba’a samun nasara sai da waɗannan guda ukun dana lissafa miki, nasan dole zaki fuskanci matsala a wajen amarya muddun ta fahimci Al’ameen yana son Auren ki.”

Da sauri Ablah ta ɗago idanunta tana kallon Umma zan fuskanci matsala a wajen amarya kuma akan Al’ameen yana son, to meye damuwarta da hakan…

<< Aminaina Ko Ita 40Aminaina Ko Ita 47 >>Aminaina Ko Ita 43 >>Aminaina Ko Ita 42 >>Aminaina Ko Ita 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×