Skip to content
Part 63 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Kayan jikinta ta cire tare da ɗiban ruwa ta shiga wanka, ƙaramar riga ta sanya da dogon wando sannan ta faɗa saman gadon tana cewa Hafsa.

“Wash gaskiya na gaji, kaina harya fara min ciwo kinsan na tsani hayaniya.”

Dariya Hafsa tayi tare da cewa.

“Ai kuwa daga gobe ya ƙare, iwar haka dai an gama ɗaureki da igiyoyi uku, har mun wurgaki ɗakin Al’ameen.”

Dariya Ablah ta saka dai-dai Aunty Saude na shigowa ta zauna tare da cewa.

“Yauwa na manta ban sanar dake cewa munje munga kayan da Papa ya sanya miki a part ɗinki, sanina mun sanya miki wanda ummanki ta miki a bedroom sit ɗin dake hanun dama gefen kitchen ɗinki, komai yayi mahaifinki yayi ƙoƙari sosai, Ablah ki riƙe hkr dan Allah zaman Aure na mai hkr ne, kin samu gida da kuma mijin da yake tsantsar ƙaunarki naji daɗin hakan sosai.”

Kanta Ablah ta ɗaga alamun to.

“Yauwa kin cinye amaren barun nan kuwa?”

“Ehh na cinye Aunty Saude.”

“Shi kuma gabaruwan fa, kinyi tsarkin dashi?”

“Aunty Saude duk nayi.”

Tashi tayi tace.

“To shikenan sai da safe.”

Da Allah ya tashe mu Ablah ta amsa, sannan suka ci-gaba da hirarsu.

Yau Asabar da safe aka tashi da hada hadar ɗaurin Auren da za’ayi sa sha ɗaya na samu, Al’ameen na zaune duk sun shirya sun barsa bashi da ma niyyar tashi ya shiga wanka, Safwan ne ya daki kafaɗarsa tare da cewa.

“Kai uban ƴan masu girman kai wai baka da niyyar shiryawa ne?”

Idanunsa Al’ameen ya ɗaga tare da duban agogon bangon dake maƙale a cikin room din 10:05 numfashi ya sauƙe tare da tashi yana miƙewa, ganin Haidar yanda ya shirya ya danna hula a gaban goshi yasa Al’ameen sheƙewa da dariya yana nuna Haidar da yatsa.

“Kaga sarkin azarɓaɓi wai yanzu kai ashe harka shirya saurin me kake aure dai za’a ɗaurasa ba sai kayi gaggawa ba malam azagwaidu.”

Abbas dake gefe shima dariya hau yiwa Haidar, Nabil ne yace.

“Iya fa da gaskiya Aure ba wasa ba, kayi zumuɗinka iya son ranka abokina Allah ne ya nuna maka, ni da Al’ameen yamin ƙafa ai tuni yau ni nake angwancewa.”

Murmushi kawai Al’ameen yayi tare da shigewa toilet, a cikin minti sha biyar ya fito ya shirya cikin wata ɗanyar gezna mai ruwan ƙwai sosai kwalliyarsa ta zarce tasu Faruq, turare ya feshe jikinsa dashi, ƙarfe sha ɗaya saura suka fito dukkan su shida abokansa suka fito falo Inna Jumma dake riƙe da turare ta tashi ta hau fesa musu tana dariya cike da farin cikin ganin ranar Auren jikokinta, Khalifa shima ɓarin turare ya hau yiwa yayun nasa a jikinsu, abokanan wasa na famar zolaya, da ƙyar suka samu suka fita zuwa wajen ɗaurin auren, inda ya tara manyan mutane masu faɗa a ji a ƙasar, Baffa Sale shine ya amshi Auren Haidar Shi kuma Abokin abi Alhaji Mamman ya bayar yayin da Papa ya amshi Auren Al’ameen Daddy ya bayar, still dai Daddy shiya amshi na Faruq inda aka ɗaura Auren Nusaiba Ahmad Giwa da Muhammad Al’ameen Ahmad Giwa akan sadaki Naira dubu Ɗari da hamsin kacal, sannan aka ɗaura Auren Rufaida Ahmad Giwa da Aliyu Haidar Ahmad Giwa, sannan aka ɗaura na Umar Faruq Ahmad Giwa da amaryarsa Maimuna Ahmad Giwa, duk akan sadaki dubu hamsin, sanda aka gama ɗaurin auren jama’a sai miƙowa Su Al’ameen hannu ake suna musabaha suna tayasu murna Al’ameen yau sai dariya yake bakinsa ya ƙi rufuwa.

Sanda aka sanar da cewa an ɗaura Auren Ablah runtse idanunta tayi tana tuno Ummi, Allah sarki rayuwa tayi burin ganin Auren ɗanta Allah bai ƙaddara mata ba,sai dai ko yanzu alhamdulillah ta godewa Allah da ya kawo ƙarshen amarya ko yanzu ruhin Ummi zai samu salama, hannunta ta ɗaga tare da yiwa Ummi addu’ar samun rahama.

Da yamma lis Aunty Saude ta kira Ablah ɗakin Umma suka zaunar da ita, sosai suka dinga mata nasiha, musamman Aunty Saude sosai ta mata faɗa gami da nasiha da jaddada mata girman hkr a cikin rayuwar Aure, Umma itama ta mata sosai, da wajen Biyar na yamma motar abokan ango sukazo ɗaukar amarya Inna Jumma da kanta ta saka Ablah a mota, sai AMBASSADOR AHMAD GIWA ESTATE, part ɗin ta aka kaita, Sosai part ɗin ya tsaru komai na falon braune ne da Golding color, Cike da taya ƙarwata farin ciki Hafsa ke yaba kyawun part ɗin, Aunty Saude dake zaune tare da Ablah ne da daddare misalin takwas ta ɗauketa, part ɗin mahaifinta ta kaita wajen Momma, momma dake zaune cike da fara’a ta tarbesu, waje ta nuna musu tace su zauna bayan sun zauna ne Aunty Saude tace.

“Ga ƴarku mun kawo miki ki mata faɗa.”

Murmushi Momma tayi tare da cewa.

“Alhamdulillah! Wannan ranar rana ce mai cike da farin ciki a garemu, Ablah ki sani yanzu kin shiga rayuwar girma ne kina da banbanci da baya, haƙuri haƙuri! Shine jigon zaman Aure domin kuwa duk wanda kikaga ya juma a gidan mijinsa to ki sani ya riƙe hkr ne, wahalar dake cikin Aure yafi daɗinsa yawa, ba komai bane miji zai miki ki kawo ƙara, ki riƙe sirrin mijinki, ki bisa sau da ƙafa iy nayi bari na bari, ma’ana biyayya nasan kina dashi to ki ƙara akan wanda kike dashi, Allah ya miki albarka.”

Da ameen Aunty Saude ta amsa.

“Papan naku yana sama bari naje masa Magana ko.”

Kanta Ablah ta ɗaga Momma ta haura ta sanar da Papa fitowa yayi ya zauna kusa da Ablah cike da ƙaunar ƴar tasa ya mata nasiha sosai mai ratsa jiki, har part ɗin su Faruq wajen AUNTY da Abi aka kai Ablah suma suka mata faɗa daga ƙarshe aka kaita wajen Inna Jumma, itama dai sosai ta mata nasiha mai shiga jiki, kafin Aunty Saude ta mayar da ita part ɗin ta tare ƙara mata faɗa, ta tafi, ta barta da HAFSA.

Al’ameen basu shigo part ɗin ba sai kusan goma na dare tare da Safwan shine ya rako Al’ameen sayan baki har bedroom ɗin suka shiga cike raha da zolaya Safwan ke tsokanar Ablah inda kanta ke sunkuye taƙi buɗe kanta, bayan gama raha ne Safwan suka fito tare da Hafsa ya maida ta gida.

Al’ameen murmushi ya saki tare da saka hannu ya yaye mayafin Ablah murmushi suka sakarwa juna.

“Alhamdulillah! Alhamdulillah! Bini’imatul Zauji, Hmmm! Ina cikin farin ciki yau Ablah bansan dame zan misalta farin cikin da nake ciki ba, Allah ya mallaka min farin ciki na, WOW wannan rana ce ta musamman a gareni.”

“Hakane farin ciki na, ni kaina bazan iya misalta farin cikin da nake ciki ba, Tabbas kai haske ne a gareni.”

“Ki tashi kije kiyi alwala muyi nafila mu godewa Ubangijinmu.”

“Bara naje bedroom ɗina na rage Wannan kayan jikin nawa nayi alwala ina dawowa.”

Kanta Ablah ta ɗaga alamun to sannan ya fita itama tashi tayi taje ta ɗauro alwala, bai juma da fita ba ya shigo, da kansa ya shimfida musu sallaya sukayi raka’a biyu, goshinta ya kama ya mata addu’o’i kafin ya sakar mata kanta ya mata tambayoyi game da addinin ta, dukkan tambayar da ya mata sai da ta amsa masa, ledar daya shigo dashi ne ya jawo ta, tare da buɗewa naman kaza ne sai 5alive tashi yayi da kansa ya ɗauko plat da cup a kitchen ya juye tare da cewa Ablah.

“Bismillah! Nasan yau wuni guda daƙyar idan kinci abinci.”

Murmushi Ablah tayi tare da sanya hannunta ta ɗauki kazar kaɗan taci sannan ta ture plet ɗin alamun ya isheta, tattarawa yayi ya mayar kitchen tare da saka guntuwar kazar a fridge, dawowa yayi ya buɗe drowern ta ya ɗauko mata wata ƙaramar rigar bacci blue yace ta je ta yi wanka ta sanya su sannan ya fita sanda ya fita Ablah ta saka hannu ta ɗago rigar shara shara, wacce ta ɗan wuce gwiwwa kaɗan, numfashi ta saki tare da ɗaukar rigar ta shiga tollet wanka tayi, ta sanya rigar tare da saka hijab ta fito humra ta shafa ta kwanta tare da duƙunƙunuwa a cikin hijab ɗin, babu jimawa bacci ɓarawo ya saceta, Al’ameen sanda ya gama komai nasa ya gama aikinsa a system sannan ya tashi ya ɗauki wayarsa ya nufo bedroom ɗin Ablah, tana kwance baccinta yayi nisa tuni hijabin ya fice daga jikinta santala santalan cinyoyinta duk sun bayyana murmushi Al’ameen yayi yana ƙare mata kallo, gefenta ya zauna tare da saka hannu ya shafa kanta, kiss ya manna mata a goshinta, yana jin wani irin ƙauna da sha’awarta na fisgarsa, hannu yasa ya shafa cinyarta tare da saka hannu ya fara balle maɓallan rigarta cikin bacci Ablah taji tamkar ana shafata, gyara kwanciyar ta tayi ita duk zato take cikin mafarki ne sai famar miƙa take tana jin dadin abinda yake mata, hannu tasa ta ƙanƙamesa cikin bacci, shi kuwa Al’ameen ya dage sai lalubarta yake Shi kaɗai yake kiɗarsa yake rawar sa, sanda Ablah taji ƙasanta ya fara mata zafi sannan ta buɗe idanunta a firgice, tana ƙoƙarin ture Al’ameen daga jikinta sai dai duk wayon amarya dole sai ansha romonta, a wannan daren Al’ameen ya mayar da Ablah cikakkiyar mace tasha wahala sosai kasancewar gyaran da aka mata.

Da asuba da kansa ya haɗa mata ruwan zafi tare da saka gishiri kaɗan ɗaukarta yayi tamkar jaririya ya sanyata cikin ruwan zafin runtse idanunta Ablah tayi tare da yunƙurowa zata tashi ya dannata yana riƙe da ita, idanunta ta rufe gam cike da kunyarsa, sosai take jin zafin ruwan sai dai zuwa can sai ya daina mata zafi ya dawo sai daɗin ruwan take ji, ganin haka ya sashi fita ya barta cikin toilet yayi bedroom ɗinsa wanka yayi tare da wankan tsarki yasa jallabiyarsa ya shige masallaci.

Ablah itama wankan tayi da na tsarki ta fito ɗaure da towel tana runtse idanunta domin kuwa har yanzu tana jin zafi kaɗan kaɗan, sallah tayi tare da saka riga da wando na bacci ta kwanta ta duƙunƙunu baccin wahala ya kwasheta.

Washegarin da safe Al’ameen ya riga Ablah tashi, a falo ya zauna tare da kunna tashar alzajira yana kallon News, yaji ana ƙwanƙwasa ƙofa, da kansa yaje ya buɗe, Samira ce tsaye hannunta riƙe da basket ta kawo breakfast.

“Good morning Yaya Al’ameen.”

“Morning Samira waya baki abinci ki kawo.?”

“Inna Jumma ce tasa Ladiyo ta girka.”

“Okay kije ki ijiye a daining sai kizo ki gyara min falon nan maza.”

Da to samira ta amsa tare ijiyewa cikin minti talatin ta gyara falon tayi mopping ɗinsa sannan ta tafi, Ablah sha ɗaya da kwata ta farka da baccin da take, toilet ta faɗa tayi wanka tare da shiryawa cikin jan atampa chiganvy wacce tasha ɗinkin stone work, ta feshe jikinta da rurare a falo ta samesa yana zaune gefensa ta zauna cikin kunyar abunda ya faru daren jiya tace.

“Good morning dear.”

Murmushi Al’ameen yayi tare da jawota jikinsa ya amsa da.

“Morning My heart sai yanzu kika tashi?”

Kanta Ablah ta ɗaga masa alamun ehhh.

“Kinyi kyau sosai, kunyata kikeji ne yau kuma kike sunkuyar da kai.”

Dariya Ablah tasa tana tashi daga jikinsa tace.

“Kaga bara naje na haɗa mana breakfast.”

“Breakfast bayan Inna Jumma ta aiko, muje daining ɗin.”

Yayi Maganar yana ijiye remote ɗin suka ƙarisa dining, zama sukayi tare da yin breakfast ɗin cikin raha da kaunar juna.

Can ma gefen su Haidar cikin farin ciki suke, musamman Haidar da yake jin da ya yadda Rufaida ta suɓuce masa da yayi babbar asara.

*****

Sati biyu da Auren su Al’ameen ya fara fita Office, suna zaune cikin farin ciki da ƙaunar junan su, a yanzu basu da wani tsoro ko far gaba a cikin Rayuwarsu, rayuwa suke mai cike da tsafta.

Lokacin da Ablah ta cika wata ɗaya da Aure Umma ta amince ta dawo gidan ɗakin ta, sosai Ablah taji daɗin hakan ga Abdu yana can Paris Daddy ya sama masa gurbin karatu.

Yau weekend kasancewar babu aiki Al’ameen yana zaune a falo Ablah ta fito daga kitchen tare da faɗawa jikinsa tana cewa.

“Dear ya kamata mu shiga part ɗin Inna Jumma fa yau weekend”

“Yauwa My heart kinsan me kuwa.?”

Kanta Ablah ta girgiza alamun a’a murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Ni fa so nake Daddy ya auri Aunty Saude, zamansa haka nasan baya jin daɗi, kuma Aunty Saude na lura macece mai hkr tun hidimar bikin mu na lura da hakan.”

Ƙara kwantar da kanta Ablah tayi jikin Al’ameen tace.

“Da kuwa naji daɗin hakan amma kasan me zai faru Inna Jumma zakaje ka yiwa maganar ita tasan yadda zata ɓullowa lamarin.”

Dariya Al’ameen yayi yana manna mata kiss yace.

“Shawara mai kyau my Heart, jeki ɗauko hijab ɗinki muje cikin gidan.”

Da sauri Ablah ta tashi tare da ɗauko hijab ɗinta.

 Koda suka shiga part ɗin Haidar da Rufaida suna zaune sai comedy suke sha da Inna Jumma gefenta Ablah ta zauna tare da cewa.

“Kai INNA Jumma wannan abinci da kika saka a gaba duk ke ɗaya zaki cinye sa.”

Harararta Inna Jumma tayi tace.

“Umm kaji ƴar saka ido, duk cina na kai wannan mijin naki ne mai ci da aljanu.”

Gabaki ɗayansu dariya sukayi, sun dan juma suna hira kafin Maimu ta shigo, Suna hirar Al’ameen cikin dabara ya shigarwa da Inna Jumma maganar Daddy da Aunty Saude ai kuwa tayi na’am da Maganar tare da cewa zata tuntuɓi Daddyn.

*****

Wata biyu da Auren su Ablah ta fara wani mungun zazzaɓi da ciwon ciki ga murɗa, kwananta Uku cikin ciwon taƙi yadda suje asibiti.

Ranar Lahadi da safe sai ta tashi da amai sosai ga ciwon kai da murɗawar ciki, ganin ta fita hayyacinta ko ɗan yatsanta bata iya ɗagawa yasa Al’ameen tilasta mata dole sukaje asibiti, koda sukaje asibitin likita ya tabbatar musu da cewa tana da shigar ciki harna tsawon wata ɗaya da sati biyu, kuzo kuga murna da farin ciki a wajen Al’ameen, shi kansa likitan sai da ya masa kyauta, magani likitan ya rubuta musu tare da basu shawarwarin yadda zasu reni cikin, kafin suka dawo gida.

Tun daga wannan ranar kulawa ta musamman Al’ameen ke bawa Ablah ko Office ya fita hankalinsa yana kanta kasancewar cikin yana bata wahala wuni yake yana kiranta harya dawo cikin gidan.

Yau Ablah tana zaune ta sanya fruit a gaba tana ci, Rufaida na gefenta suna hira sukaji anyi nocking ɗin ƙofa, Rufaida da itama take da cikin sai dai ita nata sam babu laulayi ta tashi taje ta buɗe ƙofar Nafeesa ta gani tsaye ɗan zaro idanunta Rufaida tayi tare da cewa.

“Nafeesa kece, ki shigo.”

Tayi Maganar a daƙile shigowa Nafeesa tayi ta zauna a gefe tare da fashewa da kuka, zaro idanunta Ablah tayi tare da cewa.

“Nafeesa lafiya meke faruwa ?”

Cikin kuka da nadamar rayuwa Nafeesa tace.

“Ablah nayi danasani da takaicin ƙazamar rayuwa da nayi sannan na tuba na koma ga ubangijina, Ablah rayuwata babu daɗi babu namijin dake kallona kowa gudun fuskata yake dan Allah ki rufa min asiri ki taimakeni ki roƙa min alfarma wajen mijinki dan girman Allah, ina son ku biya min kuɗi a sauya min fuska ina tsoron karna rasa mijin Aure.”

Shuru Ablah tayi cike da tausayin Nafeesa tace.

“Kiyi shuru Nafeesa ki daina kukan, tunda kin tuba ai ubangiji gafururrahim ne, zai yafe miki, insha Allah na miki alƙawarin cewa za’a fitar dake waje za’a miki aikin kiyi haƙuri da rayuwa babu yadda bata juyawa bawa zaki samu mijin Aure da yardar Allah.”

Kanta ta rausayar cikin kuka take yiwa Ablah godiya bata juma ba ta tafi, sosai ta bawa Ablah tausayi.

Ko da Al’ameen ya dawo da ƙyar Ablah tashawo kansa ya yadda zai ɗauki nauyin sauyawa Nafeesa fuska. Ablah sanda cikin ta ya cika wata Huɗu sannan laulayin ya mata sauƙi a yayin da cikin Rufaida ke da wata biyar, Maimu ce dai ita Allah bai bata cikin ba, inda zasu koma can American tare da Daddy da ita da Faruq ɗin, Cikin ikon Allah Daddy ya Yarda ya amince da Auren Aunty Saude kasancewar matsa masa da Inna Jumma tayi, a cikin sati Uku aka ɗaura Auren Aunty Saude ta dawo Ahmad Giwa Estate da rayuwa kusa da ƴar uwarta Umma.

Haka rayuwa ta dinga tafiya cikin walwala da jin daɗi inda ya biyawa Nafeesa kudi za’a sauya mata fuska sai dai akwai asibitin da sukace zasu sauya mata ba dole sai an fitar da ita waje ba..

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 65Aminaina Ko Ita 67 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×