Skip to content
Part 16 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Ya ce, “Wait.. ina zaki?”

Shigewa toilet ta yi ta turo kofar tana lekensa.

Murya a sanyaye ta ce, “Na san dukana zaka yi ko kamun wannan abun, ka yi hakuri ka ji ka ga na daina zuwa gunka, kuma na daina ma rashin kunya, don Allah kar ka kashe mun Baffana shi kadai nake da yake sona baya son kukana, inya mutu Shikenan mutuwa zanyi, adawo mun da shi ya daukeni mu koma rugarmu aradu ba zan kara ko kallon fuskarka ba, ka yafeni na tuba.” Tana maganar hawaye ya gama cika cikin idanunta, kwarara ya fara yi tamkar ruwa.

Ji ya yi jikinsa ya yi sanyi nan take ya ji tausayinta ya kamashi musamman da ta fara shesshekar kuka, jin sautin yake har cikin zuciyarsa.

Ya ce, “To fito ki daina kukan kin ji.”

Ya fada atakaice.

Shi kansa mamakin kansa yake wai har yau shine mai jin tausayin yarinyar nan haka? Yanayin da bai taba tsintar sa ciki ba don yaga wani cikin damuwa, ya san dai ya kanyi kokarin magancewa duk wanda ya kawo masa kukansa garesa amman ba wai don yaji wani abu aransa ba.

Gaaji ta taɓe baki cikin Shagwaba tana goge hawayen da ke fuskarta ta ce, “Umm umm ni nasan wayo zaka mun ka kara fasa mun jiki, na ma alkawari ni na daina yima komai kawai Baffana nake so.”

Tsayawa ya yi kawai yana kallonta sai can kuma ya kara fadin, “Ba dukanki zanyi ba, i Promise.”

“Fomisai? Ni ba kashi nake ji ba, ba zan hau masai ba, Don Allah ka barni ni ba ruwana da kai na rantse da Allah.” Gaaji ta fada.

Dariya ce ta kusan suɓucewa Adeel ya sunkuyar da kansa yana kokarin dannewa.

Kafin ya ce, “na miki alƙawari na ce.”

Gaaji ta ce, “Ka ga Allah ban fadawa Baabata cewa ka samun wannan abun ba ranar inma kazo ne kan wannan aradun Allah da gaske ina yi, kayi mun rai , ban da lafiya inka ce zaka dakeni yanzu kam zan iya mutuwa.”

Dafe kai Adeel ya yi yama rasa taya zai bullo wa yarinyar nan ke nan dai da gaske yanzu tsoron sa take.

Leƙosa take jikinta na rawa, har cikin ranta ji take tamkar ta hankadasa ya fice ya bar dakin.

Tsaki ya yi wanda har sai da sautin Ya fito zahiri ya na ayyanawa a zuciyarsa, “To me zan ma mata in ta fito? Me yasa na damu da ta fito? Me ma yasa na zo nan din?”

Dafe kai ya yi cike da takaici ya fice kawai.

Yana fita kuwa Gaaji ta lallaba ita ma ta fito ta kwanta kan Gadonta tana fadin, “Cab aradun Allah da wayona nima ai kawai kasa na fito kamun Mugunta, nikam yanzu ba ruwana da kai damuwata baffana ne kawai sai kuma Abokina na tuna shi ma yana sona.”

Adeel yaje zai fita kenan sai ga Uwar Soro na dawowa daga Fada, “Ah Yareema  kaine? Kar dai nema na kazo ka manta ina fada?”

Gaisheta ya yi kawai sai kuma ya ce, “Daman gaisheki nazo yi kawai.” Yana fada ya fice cikin sauri don gudun wata tambayar.

Ita kuwa girgiza kai kawai tayi,tana shiga tayi dakin Gaaji kwance ta sameta ta ce, “Lafiya dai ko? Na ga Yareema ya fita ina fatan ba zuwa kikai kika masa halin naki ba?”

Gaaji ta ce, “Aa nikam fa ina kwance abuna ba ruwana da shi.”

Uwar Soro ta ce, “ni dai na fada miki,ki kiyaye tom ba ruwana.”

*****

Yana komawa bangaren sai ga kiran Safina.

“Prince, wai da gaske mantawa kayi dani ko kuwa me kake nufi dani ne haka? Tun ina sharewa har abun ya fara bani mamaki.”

Adeel ya ce, “Safina Please ki barni bana da buƙatar komai.”

“Umm Wonder! Wannan zance ne,ni da nafi kowa saninka kuma, yau ina nan zuwa Daren yau ka kasance cikin shiri.” Ta fada tana wani rausaya tamkar a gabansa take.

Adeel ya ce, “Don’t Ever Try… Na fada miki bana da bukatarki so ki bar ni.”

Yana fada ya katse wayar.

Jefar da wayar tayi tana tsaki can kuma sai ta dauka ta kira waya, “Wannan mutumin naka fa kullum karo wulakanci yake, wai nice zance masa zanzo yake mun warning kar in kuskura, ina tunanin fa bazamu samu abun da muke so ba kafin auren nan nasa, I think i have the best solution kawai.”

A ɗayan bangaren ya ce, ” Eheen ina jinki.”

Safina ta gyara zama, “Yawwa ka gane, ina tunanin hakanne kawai zai zam mafita gabadaya wacce zamu kawo karshen hakan a huta da duk wahale wahalen da ake, me zai hana kawai mu shirya cikin karya? Kodayake ma ba wai cikin karyan bama ni zan iya hakura da komai a yanzu in bari cikin wani ya shiga jikina, tunda muna da videos din romance da shi ya ishe mu evidence kawai sai in durfana gaban Mai Martaba kan cewa ya yi mun ciki, ka ga yawanci in muna romance aduk lokacin da na kunna camera ba tare da saninsa ba inna tabbatar ya fara shiga wani yanayi nima canja yanayi nake yadda duk wanda zai kalla zai ga kamar dole ake mun, inaga wannan kadai ya isa ma ace mun kashe wannan case din da shi, in yasan wata ai bai san wata ba, in an kawo batun gwaji kuma nasan zakayi duk kokarin da zakayi wajen tabbatar da cewa gwaji ya nuna cewa cikin jikina nasa ne, sannan imma hakan ba zai samu ba zamu iya dauko Baby a gidan marayu kawai muje akan cewa har ma na haifa masa yaro ko yarinya.”

Wata irin dariya mai sauraranta a wayar y fara, “tabbas Safina kince sunanki na fitilar sharri, yanzu daman kina da wadannan ideas din tun farko baki bamu ba kika tsaya bata mana lokaci?”

Ita ma dariya tayi kafin ta ce, “ai dole sai dama taki ake gwada hagu, sannan ni kaina ina matukar sha’awar kasancewa da wannan guy din don na tabbatar yadda idanunsa suka kasance sexy shi ma din can kasan hakan zai zama, kuma duk da mun samu mafita fa ban hakura ba, ko yane sai na ɗanɗanasa nayi wannan alkawarin.” Ta fada tana lashe harshenta tamkar wacce ta ci ya ji.

“Ke fa mayyace na lura da hakan.”  Na wayar ya fada.

Safina ta ce, “Ba zaka gane bane, irin wa innan mazan suke sanya mata cikin wata duniya ta musamman, dole fa mata suyi rububi kansa ya hadune ta ko ina kuma in kere na yawo na Tabbata ma zabo na yawo dole watarana za a gamu.”

“Hmm bar wannan sambatun naki, yanzu dai yadda kika fadan kawai haka za ayi, me zai hana ni kawai ki bani damar afka miki cikin, tunda gida bai koshi ba dai ai ba abawa waje ba.”

“Kai fa ka fiye son banza kuma yanzu nasan duk an gama karar ma da karfi ana neman maza masu karfi ajika da zasu iya aiki me kyau kana maganar kai.” Safina ta fada

“Ba wani nan, yanzu ni abun da zan aikata ba kowa cikin maza ma zasu iya ba, so ki bani dama kawai yarinya kila ma sai kiji na fi miki Yareeman da kike ta zuzutawa.”

Safina tayi ajiyar zuciya tana, “hhhh never ba fa zaka taba zama kamarsa ba ai jummar da zatayi kyau tun daga Laraba ake iya ganeta, anywhere aikin ai naku ne daman so za ayi yadda kake so In Sha Allah, amman dai kasan bama da cikakken lokaci tunda kace ansa ranar bikinma don haka yau ka shirya kazo kawai daman ban da wani bakon da na ba dama.”

“Okay ki tsumayeni daren yau kawai, kin sa tun yanzu har na fara shiga cikin wani nishaɗi na musamman.”

Kamar Yadda suka tsara haduwa a daren, hakan kuwa ya tabbata, Safina ta bashi hadin kai sosai wanda har suka karawa shirin nasu gishiri, Irin Kayan Yareema sak suka nemo ya saka, sannan suka seta video yadda baza a taɓa ganin fuska ba.

Bayan sun gama baɗalar su cikin zufa da gumi yake fadin, “Ni da zaki barni a koma karo na biyu da kin taimaka wallahi don sam ban gaji ba ko kadan kamar karin karfi kika karamin.”

Tashi Safina tayi jigidir tana jijjiga jiki ko ina na motsi ta ce, “Ka ci rabonka kuma ai ,kai kama gode Allah in ba makuden kudade mutum ya biya ba, bana taɓa biye masa haka har ayi abun da za aji dadi, daidai kudin mutum fa daidai sha’aninsa in akamun biyan da bai mun ba zama nake kamar fanko mutum ya gama abun da yake so da kanshi ya gaji ya tashi ya barni,kai ko ko abun tsaro bansa ba kuma na baka hadin kai duk don a samu abun da ake so lallai.”

“Kin ga nima zan biya koma nawa kikeso ki dawo don Allah kar kice zaki maida kayanki tunda naga ba niyar yin wanka kike da ba, ki dawo wallahi zan biya kinji na rantse, ni ai bansan haka kika kware ba, na zata zaman kwalta yasa duk an kwashe armashin.”

Wata irin dariya Safina tayi tana, “Shegiya Bariki wanda bai san ciki da wajenki ba ya yi asara, ni tsaya ma, amman dai dole a kara mun kudi ko? Batun cikin nan da zanyi kasadar dauka, ahto tun sau ɗaya da na taba wasa da damata aka dambara mun na sha azaba kan in zubda rike ciki fa ba wasa akwai wahala gaskiya.”

“Ah ah… Kema dai kinsan ko nawa ne za a iya kashewa wajen tabbatar abun da muke nema, Ni dai yanzu kawai ki dawo ko inzo in kamoki haba zan biya ke matsalarki kudine,kuma ma ai bamu da tabbacin cewa at once ciki zai iya shiga jikinki yanzu, kila karawan nan da za ayi sai ki ga an dace And inma tun farko an dace yanzu a kara su zama yan biyu.”

Safina ta ce, “Waya ce ma hakan? Jiya na kammala period so yanzu mahaifata a bude take daidai lokacin daukan ciki, duk abun da nake cikin lissafi nake ka gane kadai kawai kace yau ka sha giyar da ta fi karfinka, Don haka in fara jin dumus.”

Taɓe fuska ya yi kafin ya dauki wayarsa yana, “Oya duba wayarki yanzu mu ga.”

Tana dubawa ta sake Baki tana kallonsa , “Awwwn irin hakan nake so ai tabbas dole aje da kai, irin wannan alert mai fasa waya ai in kaso ma kullum kana zuwa anayi.”

Shi dai bai ce komai ba ya cafkota suka ci gaba da tambaɗewa.

Niko na hito waje aguje ganin cewa abun na manyane yafi karfina batun cikin dakin gwanda in baku wata gulmar.

*****

Safina Al-hassan Imam budurwace kyakkyawa ajin farko, fara Sol doguwa mai diri da ɗaukan hankali ga dukkan namijin da zai ganta yayin da surarta take a bayyane, ta taso cikin maraicin Iyaye, tun tana jinjirar wata guda Mahaifiyarta ta jefar da ita sakamakon ciki aka yi mata, tsintarta a hanya yasa aka miƙata gidan marayu, tana shekara shida wasu manyan maza daga cikin gidan suka fara neman yin badala da ita, tun bata saba ba, har hakan ya zame mata jiki wanda ita da kanta takan nema da tayi da kananun yara sa’anninta dake gidan, fahimtar hakan da shugabar gidan tayi yasa aka koreta tana da shekara goma sha biyar suko sauran manyan mazan da suka kasance musababbin fadawarta cikin hakan juya mata baya sukai tare da nunin cewa basu san hakanma na faruwa da ita ba,har da su a ingiza cewa lallai a koreta domin kuwa zata iya bi ta lalata dukkanin sauran yaran, Safina na fitowa duniya kuwa idanunta suka kara budewa ta koma zaman kanta da kanta maza sai ta zaba wanda zatai hulda da shi wannan kenan.

*****

Kuka Nasmah take ba kakkautawa tana kwance jikin Hajiya Maimuna.

Basmah ta ce, “Kuka? Akan So? Ni wallahi kuna bani mamaki miye abun damuwa anan? Ance za a aura masa Khaleesa,kuma ita ma yar uwarmuce ba sai mu tayasu fatab Alkairi ba, amman tunda aka fara shirye-shiryen bikin nan kin bi kin dagawa kanki hankali kullum cikin kuka, ko shi kadai ne Ɗa namiji a duniya yaci ace ki hakura ai.” Ta karasa maganar tana tsaki.

Cikin Muryar kuka Nasmah ta ce, “Mami kin ganta? Ina gani ace wai Khaleesa ce zata auresa wallahi ni yake so ba ita ba,yama fi kulani ko naje gunsa baya so ita tazo.”

Hajiya Maimuna ta ce, “Ni dai nace miki kiyi shiru,indai ina da rai da numfashi Khaleesa bazata taba Auren Yareema ba sai dai ke ki auresa ki daina kuka kiyi farinciki kuma muma zamu fara shirye-shirye kamar yadda suke yi,ni nasan me zanyi.”

Da sauri Nasmah ta dago tana fadin, “Don Allah? Da gaske Ammie?”

Murmushi ta yi tana , “Eheen kar kiji komai kidaina kuka ai mu keda Yareema basu ba, ni sam abun nan bai dameni ba,kuma bai taba ni araina ba.”

Rugumeta Nasmah tayi tana, “Shiyasa nake sonki Mamina.”

Basmah tayi tsaki, ” daurawa kai wahala kawai.”

Nasmah ta ce, “Ohon miki dai kema rashin samune da zaki samu tuni zaki amshe.”

*****

Gidan Sarauta ko jidali yanzu kuma wai munka nufi Dakin Magajiya ko me zai hwara?

Ku dai biyoni ku ba idanunki abun mamaki don lamuran nasu kara girmama suke ana kokarin toshe wata kofa, wata kuma na barkewa…

Tsaye take tana zagaye dakin ta kasa zama taje ta dawo taje ta dawo tamkar wacce ake tsikara basir ya gama cinyeta.

Ganin abun bana kare bane Rumaiysa da ke karatu gefe ta dago tana fadin, “Umma Lafiya dai ko? Naga tunda kika dawo daga Fada yau kin kasa zama tun tuni sai yawo kike adakin nan wani abu ya farune kuma?”

Magajiya ta ce, “ke neke kokarin nemawa mafita kuma in inganta miki rayuwa kamar yacce kowacce uwa ke kokarin ingata rayuwar ‘Yarta.”

Cike da mamaki Rumaiysa ta ce, “Ni kuma? Me na rasa ? Ai inajin cewa rayuwata Alhmdu Lillah Umma komai na tafiya daidai kuma cike da inganci.”

Zama tayi daf da ita tana dafa kafadarta ta ce, “Aa da saura, ba zan zura ido kifi ya yi mana kafa cikin ruwa ba mu zam yan kallo, ke zaki Auri Yareema.”

Cikin rashin Fahimta Rumaiysa ta ce, “Ni Yareema? Ba Khaleesa ce ke sonsa ba? Kuma shi zata aura ai, nikam ma banda tunanin aure a yanzu, Allah ya sanya alkairi kawai.”

“Ke… Wata tsawa ta mata sai da ta firgita

Kafin ta ci gaba da fadin, “Ana nuna miki haske kina ga duhu yafi dadin zama, to ki fita a idanuna tun muna cikin lumana,na Tabbatar da cewa in kyaune ba wata yarinyar da ta kamoki bare ta fiki kaf cikin Masarautar nan, bare kuma akai ga batun ilimin addini dana boko uwa uba tarbiyya da girmama mutane shi kansa Mai Martaba ya sheda hakan, ina sanar dake da babbar murya in ma baki son Yareema daga yau kuma yanzu ina umartarki da ki sanya soyayyarsa cikin zuciyarki domin kuwa babu wata wacce ta dace da Yareema bayanke, ke ce gimbiya kafin Mai Martaba ya sauka a kujera inko ya sauka kece Fulani ki kara dasa hakan cikin ranki.”

Tana fada bata jira amsar Rumaiysa ba kawai ta fice cikin sauri.

Binta da kallo Rumaiysa tayi kawai zuciyarta na saƙa mata abubuwa da dama na ban mamaki.

*****

Gaaji na kwance kan gado adakinta kamar daga Sama ta jiyo Muryar Adnan yana sallama, Uwar Soro ta amsa.

Fitowa tayi da sauri fuska fal farin ciki ko bari su gaisa bata yi ba ta ce, “Kaine? Kaki zuwa guna ko? Baabata ta ce mun kana gun Baffana ka dawo mun da shi ne?”

Adnan ya yi Murmushi ya ce, “To Yanzu wanne kike so in amsa miki ciki ne? Ba gani dai na zo ba? Baffanki kuma yana lafiya zamu je ki gan shi.”

Yana karasa maganar ya kalli Uwar Soro ya ce, “Ranki Ya Dade zamu dan je bangaren Prince dake in ba matsala Please.”

Tashi ta yi tana, “Alright ba matsala muje din to.”

Adnan ya kalli Gaaji ya ce, “Yawwa kema tawo muje.”

Tsayawa tayi alamun jikinta ya yi sanyi kamar zata yi kuka ta ce, “Aa ni kuje ku dawo ina jiranku anan.”

Adnan ya ce, “tare zamu je kizo.”

“Duka na zai yi, ni tsoronsa ina ji kuma…” Sai tayi shiru kuka na shirin suɓuce mata.

Uwar Soro ta ce, “ba gamu ba? Ba zai dake ki ba Zainabuna muje.” Ta karasa maganar tana rike mata hannu.

Tare duka suka shiga Part din.

Jin Shigarsu yasa Prince Adeel dagowa ya na binsu da kallo ba tare da ya ce komai ba.

Adnan ya sa hannu a aljihunsa ya ciro takarda yasa masa a gaba da pen.

Da mamaki cike da rashin fahimta ya dago yana kallonsa.

Adnan ya ce, “Our Deal…yau WATA BAKWAI cif da aurenku kuma a yau kayi alkawarin sakinta in aureta.”

“Wata bakwai?” Adeel ya. Fada cike da bazata.

Adnan ya ce, “Eheen wata bakwai kenan cif yau kaga yanzu zaka saketa kenan kamar yadda yake A deal dinmu.”

Kallon Gaaji ya yi, cikin sauri ta koma bayan Uwar Soro alamun tsoro ya gama bayyana karara a jikinta da fuskarta.

Ya sunkuyar da kai kuma ya yi shiru.

Adnan ya ce, “ko in kara tunatar da kaine, Auren Wata Bakwai ne kuka yi daman sannan kace mun baka bukatarta muka yi deal kan cewa data cika wata bakwai zaka saketa ni kuma in aura.”

Duk sa hakan Adeel bai kara dagowa ba, kuma bai ce komai ba, zuciyarsa ce ta fara raya masa, “To akan me zan tsaya? In rubuta mata sakin magana wannan dirty Fulani Girl din nan ban da damuna ma me take? Me yake damuna ne ma wai? Adeel Go on please wannan ma ai babbar damace gareka zaka yarda kwallon mangoro ka huta da kuɗa, Go On Please…”

Janyo Paper ya yi, ya rubuta mata saki ɗaya ba tare da ya daga kai ba,yana gama rubutawa Adnan ya dauki Takaddar , uwar Soro ta rike Gaaji suka fice da Part din.

Uwar Soro ta ce, “Yanzu ke nan zaka tafi da ita da gaske?”

Adnan ya ce, “Eh hakan nake so bayan an daura mana ina so in sanyata a makaranta ma.”

Shiru Uwar tayi  na dan lokaci sai kuma ta numfasa ta ce, “Amman ko zanyi kewar diyata Sosai sai nake jin cewa dama ka barmun ita anan, amman kuma dole nasan tana matukar bukatar kasancewa da Baffanta, Don haka Ina yi maku fatan Alkairi a duk inda zaku Kasance, aikin Alkairi daka sa agaba kan wannan yarinyar Ubangiji ya baka ikon iddawa cikin Nasara.” Ta kalli Gaaji sannan ta ci gaba da Magana, “Uwata na san dai yanzu girma ya zo amman dai a kara kiyayewa kinji ban da rashin ji.”

Gaaji ta ce, “Na Daina ai In Sha Allah ba ruwana da kowa yanzu.”

Dakanta Uwar Soro ta shiga ta hada mata kayanta cikin wani akwati ta fito da su.

Sai da ta rakasu har suka shige mota kafin ta dawo.

Adeel kuwa tsaye yake jikin Glass din window yana kallonsa har sai da suka bace.

Gaaji ta ce, “amman dai gun Baffana zaka kaini ko? Ina so in gan shi.”

Adnan ya ce, “Eheen ki sake ranki in ba kya murmushi ba zan kaiki gunsa ba.”

Washe baki Gaaji ta fara tana, “Zanta murmishi har mu isa inga Baffana nikam.”

Tafiya suke titi samɓal har sai da suka isa NASARAWA G.R.A,  wani babban gida kayatacce wanda haduwarsa ma daga waje kan sa a tsure ya shigar da motar.

Suna shiga Ya fito ya bude mata kofa.

“Yawwa to zo mu tafi.”

Suna shiga babban Parlourn gidan da Baffanta ta fara cin karo shingide akan kujera.

Da gudu ta karasa tana Rungume sa, “Baffana ka dawo? Ka ji sauki yanzu ko…?”

Tana karasa maganar hawaye na zuba daga idanunta.

Murmushi Ya yi yana share mata hawaye ya ce, “Na ji Sauki Gaajin Baffa, ki daina kuka kinji in ba wai so kike in koma ci gaba da ciwon ba.”

“Umm ummm ummm ni bana so ka ci gaba da ciwo kaji sauki kenan In Sha Allah.” Gaaji ta fada tana kara rugumesa.

Adnan ya ce, “Wato anga Baffa an manta ma dani?”

Da dariyarta ta dago ta ce, “Ina dai yanzu zamu koma Rugarmu ne da Baffa?”

“Aa kam nan ne sabon gidanku kuma anan zamu zauna duka.” Adnan ya fada.

Gaaji ta kalli Baffanta tana, “Wai da gaske?”

Girgiza mata kai ya yi alamar eh yana murmushi.

Adnan ya sanar da baffan Gaaji komai dake wakana kuma ya nemi da ya bashi Aurenta kuma ya bashi don haka daurin aurene kawai ya rage tunda sunsa ba wata alaka da ta taɓa shiga tsakanin Gaaji da Adeel don haka bata da idda akansa.

Haka kuwa aka yi washe gari da sassafe  sallar asuba aka daura auren Gaaji da Adnan cikin masallaci.

Dawowarsu daga sallah kenan Adnan ya wuce dakinta kai tsaye tana kwance sai ji tayi an miskuleta a razane ta farka tana hade fuska.

Ganinsa yasa ta sakin Murmushi can kuma sai ta taɓune fuska, “Umm ni ina barcina ka tasheni kuma ni ba ruwana da kai.”

Adnan ya ce, “Sorry Albishir nazo miki da shi.”

Gaaji ta ce , “Da gaske?”

“eheen gyara zama ki bani kunnuwanki, Albishirinki.” Adnan ya fada.

Gaaji na dariya ta ce, “Goro fari sol ma kuwa.”

Adnan ya gyara zama daf da ita ya ce, “Yau An Daura mana Aure ni da ke,kin zama matata.”

Wata irin kunyace ta lallube ta cikin sauri ta rufe fuska.

Adnan ya cire mata hannayen ya ce, “Oya yanzu kafin komai fada mun guda nawa ne farillan alwala? Kuma ki lissafo mun su.”

Zaro ido Gaaji tayi tana sa yatsa a baki kawai tana kara sunkuyar da kai.

Adnan ya ce, “In baki fadamun ba fa ba ruwana dake kuma ba zan saki a makarantar da za a koya miki turanci ba.”

Shagwabe wa ta yi ta ce, “Ummm Guda Bakwai ne Baffana ya fadamun.”

“To lissafomun su inji daga na Ɗaya har zuwa bakwai din.”

“Na Ɗaya: Niya.”

Sai ta yi shiru

Can kafin ta kara fadin.

Na biyu kuma:Ummm Ummmm yawwa akwai wanke fuska, da wanke hannaye.” Tana fadan hakan tayi shiru.

Adnan ya ce ce, “kin fada uku sauran fa to?”

Cikin Shagwaba ta ce, “Umm ni bai karasa koyamun ba ya fara ciwo kuma bana zuwa ko ina,agida nake zama da shi.”

Adnan ya ce, “Tom shikenan daga yau bake ba zama wasa sai kinyi karatu sosai da kaina zanna koya miki karatun Addini na bokon ma zan fara miki lesson a gida kafin in saki Skul, In kina son zama matar kirki kuma wacce Yaranta zasu yi alfahari da ita sai kin kasance mai ilimi, ko kina so ki haifi yara suzo suna ki koya masu abu ki kasa?”

Gaaji ta girgiza kai.

Adnan ya ce, “Yawwa My Gaaji Beauty kin ga zaki yi karatu har ma ki zama likita kina duba lafiyan Baffanki da kanki yadda ciwonsa ba zai kara tsanani ba In Sha Allah, kuma kinga sauran farillan alwala sune

• Niyya

• Wanke Fuska

• Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu

• Shafar kai

• Wanke kafafuwa

• Cuccudawa

• Gaggautawa.

Kinji su ko? Kuma ina so ki rike su banda wasa.”

Murmushi ta yi masa ya ce, “kin ga na manta ma bakiyi sallah ba ko? Maza tashi kije kiyi ko alwalanma sai na nuna miki?”

Tashi tayi tana , “umm umm Baabata ta Masarauta ta koyamun na iya.”

Tana shiga toilet din shi kuma ya fice daga dakin.

Bai koma barci ba, duk da cewa da kwai masu aiki cikin gidan Mussaman bangaren Baffan Gaaji amman Adnan da kanshi ya shiga kitchen ya hada masu breakfast.

Kafin karfe takwas ya kammala komai ya kaiwa Baffa na shi sannan ya haɗa masu nasu a daining shi da Gaaji.

Tayi wanka kenan ta fito zaune gefen gado tana shafa mai daga ita karamin towel din da ta tarar a toilet din an tanada domin ita.

Ta daga towel din kenan zata shafa mai a kirjinta sai ga Adnan kamar an hankadosa.

Daga shi har ita mutuwar tsaye suka yi, domin duk da kasancewar karamar yarinya hakan baisa ta rasa arzikin fulani ba ko ince tunda jininsu ce gaba da baya ai sai dai kuma su bada sadaka ba dai abasu ba.

Kusan minti guda can jikinta ya fara rawa ganin yanayin idanun Adnan ya sauya nan take taja towel din ta rufe kirjinta tana kankame jiki, ba abun da idanunta ke tunasheta sai abun da Adeel ya mata, yanayin tsoro ne ya bayyana gareta ƙarara tamkar zata yi kuka.

Adnan na fahimtar hakan ya fara kokarin danne kansa murmushi ya yi ya ce, “Kisa kaya kizo kici abinci ko?”

Muryarta na rawa ta ce, “Tom ka fita, ka fita Kar ka ganni Don Allah.”

“Waya fada miki Mata nayiwa Majinta kauran jiki? Da kai da fata ai duk mallakan wuyane, don haka dake da duk wani abu da kika mallaka jikinki nawa ne a yanzu ai.”Adnan ya fada a zuciyarsa kuma ta wani bangaren yana fadin, “Lallai wannan a zahiri da dabi’unta ne kawai na yarinta amman tabbas jikin manya gareta kuma duk wani Ɗa namiji da ya sameta Ubangiji ya gama yi masa komai, Alhmdu Lillah Allah na gode maka duk da cewa ba niyar komai araina amman hakan kuma na son zame mun Alkairi tun kan aje ko ina na fara fahimtar hasken dake nufoni.”

Katse masa tunani tayi da fadin, “Umm umm ni ni….kai ma irin…..” Tama gagara maganar kawai ta fashe da kuka.

Take tausayinta ya fara ratsashi,har cikin zuciya yake jin kukanta da Sauri ya fice yana, “shikenan kiyi shiru zan fita, in kinsa kayan kizo ina jiranki a parlour.”

Sai da tasa kayan kafin ta fita Parlour a hankali take tafiya jikinta a sanyaye babu kwari, yana zaune yana jiransa yana danna waya jin taku a hankali yasa shi dagowa yana murmushi, “Ah kin gama? Yawwa to maza kici abincin nan inaso mu fita mu dawo kan lokaci.”

Zama tayi zata ci abincin kamar ba zata ci ba, hakan yasa shi matsawa yana bata da kanshi har ta danci sannan ya ce taje ta dauko hijabi su tafi.

Saloon ya fara kaita aka wanke mata kai aka mata kitso kananu masu kyau tukun suka shiga cikin wani babban Shago ya yi mata siyayyan kayayyaki.

Suna hanyar komawa Gaaji ta ce, “to wai kai baka da Baffane? Ina baffanka da innarka suke? Ni kaga Innata ta mutu.”

Adnan ya ce, “Nima Baffana da Innata sun jima da rasuwa kuma su ba yan kasar nan bane amman ai yanzu zaki bani aron Baffanki ko?”

Tana shan Ice cream ta saki Murmushi ta ce, “Eh mana zan baka tunda kai dai ba ruwanka ba irin wancen mugun bane.”

*****

Shagalin biki ake tayi ta Kowanni bangare amman banda bangaren ango wanda sam bai dauki abun da mahimmanci ba bare yasa aransa ko hakan ya damesa illa yanayin wani sabon sauyi da yake kara ji a jikinsa na kewa jin cewa akwai wani bangare da ya rasa na rayuwarsa, ga uwa uba kuma Sha’awar da ke addabarsa a kullum kamar ana kara masa jin hakan ne inya gagara daurewa sai dai ya kira Safina ta rage masa zafi da Romance amman har yanzu ya kasa kai wa ga cen makura.

Biki ya rage saura sati biyu kamar yadda sati guda kenan da barin Gaaji a masarautar.

Kamar yadda yake ganin dare haka yake ganin rana a kullum idanunsa basa iya rufuwa koda na second ne bare akai ga batun yin nisa har ayi barci, alamar damuwa ta gama bayyana a jikin Yareema domin duk ya canja kuma ya rame, ko da Uwar Soro ta zaunar da shi tana tambaya kan ko batun auren ne baya so ba abun da ya furta illa , “Babu komai kuma babu abun da ke damunsa.”

*****

Rayuwa ta ci gaba da tafiya tsakanin Adnan da Gaaji kullum yana kokarin Fahimtar da ita rayuwa da koya mata wasu abubuwa da dama, da kanshi yake mata karatu duk lokacin da yake gida, inko ya fita ta kan koma bangaren Baffanta su sha hira Sai dare in Adnan ya dawo su koma bangarensu inko girkine tare da mai masu abinci suke komai tana gani tana tayata a kitchen.

Yau ma kamar kullum ya dawo daga office kenan ya bi Part din Baffa suka gaisa sannan ta bisa suka koma bangarensu.

Suna shiga Adnan ya nufi toilet zaiyi wanka, Gaaji na zaune gefen gado, ya manta da towel na Parlour bai shiga da shi ba kasancewar an wanke yana gama wanka ya fito haka, suna hada ido da Gaaji ta kwallara wani ihu sai da shi kanshi ya razana ta tashi zata gudu.

Tsawar da ya yi mata ne yasa ta saurin tsayawa jiki na karkarwa tana nuna gabansa, “Kai ma….. Kana da wannan?…..humm humm.” Gabadaya ta birkice.

Fahimtar abun da ya razanata yasa shi saurin saka kaya kafin ya dawo ya riketa yana fadin, “wannan abun tsoro bane zaki ji tsoro, kowanni Ɗa namiji na da hakan ya kamata ace yanzu kin sani, ko dan ban taɓa zuwa miki a matsayin miji bane har yanzu? Hakan ba shine a gabana amman na ga alamar lallai akwai bukatar tabbatar miki da hakkin miji akan matarsa da ma yadda zamantakewar Auren take, kuma zan nuna miki amfanin abin da kike tsoro domin tabbatar miki da cewa ba abun tsoro bane a daren yau.”

Gaaji na jinshi tana numfarfashi tamkar mai nakuda bata ce komai ba, Kawai ya tashi ko kashe wutar dakin bai ba, ya hullar da rigarsa gefe ita ma yajata ya cire mata ta ta.

Tana turtur jeyawa yana kara janta.

Romance ya shiga yi da dukiyar Fulaninta wanda daman shi duk yafi tsole masa Idanu, “Yaaya Don Allah ka bar ni ka bari bana son abun nan ni bana so Nikam ban so ka daina matse mun kirjina da zafi,Wallahi Allah da zafi.”

Jin yadda ya koma taɓa mata jiki yasa nan take ta jita cikin wata duniyar.

Shiru tayi tana lumshe ido yadda take jin dadin hakan har cikin ranta gabadaya ta sake masa jikinta, hakan ya kara basa kwarin gwiwar ci gaba da abun da ke gabansa.

A hankali ya fara kai hannunsa gabanta yana zare mata sket, da dayan hannu kuma yana kokarin kawar da zif din wandonsa.

Yana jan zif din idonta na kaiwa gun ta dawo seti a take ta yi wata irin miƙa ta ce, “Kar ka samun ni ba wannan nake so kar kasa mun indai wannan ne Auren Wallahi Na fasa Yaaya na ce na fasa auren bana so na fasa kawai kar kasa mun abun nan cikin jikina.” Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.

Tsayawa kallonta Adnan ya yi, domin ya gama kaiwa makura mussaman shi da yake wata alaka bata taba hadashi da wata mace ba Yau dinma kuma ganin abun nata na son cutararsa yasa shi kokarin aiwatar wa don yaso sai ya bari ta kara girma, amman fahimtar inya ce hakan kila ata tafiya batare da ta fahimci komai ba yasa shi aniyar hakan, kuma gashi Silarta ya fara jin kansa a duniyar da bai taba riskar kansa ciki ba kuma ya ji dadin zama amman sai dai kash tana so ta hanashi isa inda ya dace.

Ajiyar Numfashi ya yi ya ce, “Zainab… Wannan yana daya daga cikin manyan hakkin miji ga matarsa kuma Ubangiji na fushi da duk matar da bata son bawa miji hakkinsa, ba zan taba miki dole ba, duk ranar da kika ga ya dace shikenan amman ka da ki manta hakan babban hakkin mijine ga matar sa wanda yakan iya janyo halaka ga duk ma’auratan da basa biyawa junansu bukata, ba wai fata nake yiwa kaina ba, ban taba zina ba,kuma bana fatan farawa amman Kinga inda tsautsayi silar kin amincewarki yasa na iya shiga cikin wani hali,ki daina kuka, na miki alƙawari ba zan miki komai ba har sai da amincewar ki In Sha Allah, amman da kwai sharadi ɗaya daga yau tare zamu dunga wanka har sai kin daina jin tsoron kin yarda?”

Gaaji ta ce, “eh.” Murya a sanyaye.

Maida kayansa ya yi ita ma ya tattara nata zai bata tasa, taba jikinta da zaiyi yaji wani irin zafi dan tsoratan da tayi har zazzabi ya kamata.

“Oh My God kin ga tsabar tsoron ki da rashin jarumta yasa zazzabi ya kamaki yanzu gyara in maida miki kayan sai kisha magani ki kwanta ko?”

*****

Cikin daren nan kawai Adeel yaji ba wacce yake so kuma yake son gani fiye da Gaaji da a tunaninsa sha’awarta yake amman yanzu zuciyarsa babu abun da ke raya masa illa tsantsar kishinta da kaunarta a zuciyarsa.

Wani irin zafi yake ji acikin ransa zuciyarsa na bugawa, duk kokarinsa na ganin ya rike kansa kasawa ya yi, daukan waya ya yi kawai ya dannawa Adnan kira, har sun kwanta jin ringing ya tashi da mamaki yaga Number Adeel cikin zakuwa da fatan Allah sa lafiya ya dauka.

Yana karawa a kunne cikin wata gigitacciyar murya Adeel Ya ce, “Where is she?”

“Wace ce kenan?” Adeel ya fada cikin yanayin rashin fahimta.

Adeel ya kara fadin, “My Wife ka dawo mun da ita.”

Adnan ya yi wata irin ajiyar zuciya ya ce, “Your Wife? Point Of Correction Your Ex Wife, yanzu kam aure ne akanta kamar yadda na sanar da kai tun farko.” Yana fadin hakan ya katse kiran.

Shi kuwa Adeel idanunsa fara rufewa suka yi yana neman daina gani, ga wani irin azazzaban ciwon kai, zazzaɓi da jiri duk suka hade masa lokaci guda nan take ya fadi sumamme.

<< Auren Wata Bakwai 16Auren Wata Bakwai 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×