Skip to content
Part 17 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Ajiye wayar Adnan ya yi ya gyara kwanciya don tuni Gaaji tayi nisa a barcinta.

Washegari

Da Asuba Adnan na dawowa daga masallaci sai ji Gaaji tayi ya saɓeta, a hankali ta bude idanunta suna kallon juna, murmishi ya sake mata yana kai bakinsa daidai kunnensa cikin raɗa a sanyaye ya ce , “Morning Beauty.”

Gaaji ta taɓe baki , “Umm ni kasan ai bansan me kana cewa ba kuma.”

“Oh Sorry, Ina Kwana Kyakkyawata ko ince Boddi Am.” Ya karasa maganar yana shigar da ita toilet din.

Gaaji ta ce, ” Yaya Me zaka mun? Ka barni zanyi alwalar da kaina ne fa.”

Adnan ya yi mata sigina kafin ya ce, “Kin manta alƙawarin mu? Wanka zamu yi tukun sai kiyi alwala kiyi sallarki shiyasa da na tashi kawai nayi alwala na tafi masallaci”

“Umm umm.”

Adnan ya ce, “Gwanda ma ki tsaya, in ba haka ba kuma inyi abun da ba kyaso.”

Cire mata kaya ya fara yi tana rurrrufe fuska ya jefa hanger toilet din.

Kunna Famfon ruwan zafi ya yi,ya cika Baf din da ruwa sannan yasabta a ciki, tana ganin ya fara tuɓewa shi ma ta rufe idanunta da hannu.

Jinsa kawai tayi daf da ita yana cire mata hannu a fuska, “Indai baki daina kunyar nan kin saki jiki ba Serious zan yi miki abun da bakya so.”

“Aa Umm Don Allah Yaayah Yi Hakuri na daina.”

Gaaji ta fada kamar zata yi kuka.

“Yawwa Beautyna ko ke fa.”

Ruwan ya fara watsa mata cikin shigar wasa a fuska a hankali, dariya Gaaji ta yi ita ma ta diba ruwan ta watsa masa.

Sai da Adnan ya yi duk abun da zaiyi wajen ganin yasa Gaaji sakewa da shi, suka yi wasa sosai ya latsa ya taɓa dukiyar Fulaninta yadda ransa keso, tun bata biye masa har saida ta biye masa musamman da jikinta ya fara amsar wasan take jin dadin hakan har cikin ranta, wani irin Farinciki ne ya lullubeta ji take tamkar ta janyosa ya kara bi da tattaba mata jiki, sai da suka yi wasansu son ransu sannan ya mata wanka tas shima ya yi.

Kamar jinjira da kansa ya kara ciro ta cikin Baf din ya lullubeta da towel shima ya daura towel din sannan ya ce , “Yanzu kiyi alwala ki zo kiyi sallah ni zan shirya ki da kaina.”

Bata ce masa komai ba illa murmushi da ta sake, ya fita shima yana yi mata Murmushin.

Yana fita ta yi Alwala sannan ta bi bayansa.

Wata doguwar riga mara nauyi da hijabi ya aje mata gefen gado tana zuwa tasa tayi fara sallah.

Shi kuwa yasa kayan ya na zaune yana kallonta yana jira har ta idar.

Tana idarwa kanta tashi ya karasa inda take da kanshi ya cire mata hijabi da rigar ya dauki mai ya bi dukkan jikinta da shi yan shasshafata a hankali sannan ya dauko wata mata kayan ciki, da kansa yasa mata bra da pant din.

Ya tsaya yana, “kin ga ni a hakan ma fa in zaki zauna kinfi mun kyau ko kawai ki zauna haka kinga daman yau weekend ba inda zanje.”

Taɓe baki tayi ta ce, “Umm Yaaya nikam ka bani kayana insa kawai ba zan iya zama hakan ba,ji be ni fa umm.”

Ta shi ya yi,ya dauko mata wata Atamfa anyi dinkin riga da sket yasa mata rigar sannan ya tayarda da ita yasa mata sket din,ba karamin kyau tayi ba tamkar a jikinta akayi dinki domin ya kamata sosai kuma ya fidda mata da shap din jikinta.

Da kaina ma zan daura miki dankwalin zaki fi kyau.

Jan dankwalin tayi tana, “Umm ni fa yau barci inaji bai isheni ba,Yaaya ka bani in saura insa hijabi inje in gaida Baffana in dawo ni barci zan koma kafin a gama abinci.”

“Barci? Aiko yau tare zamu shiga kitchen ba zaki koma wannan barcin ba ya isa haka mai ciwon barci kawai.”

Adnan ya fada yana mata wani irin kallo.

Ita kam gwalo tayi masa tasa hijabi ta fice da dan gudunta.

*****

Tunda Adeel ya fadi a cikin dakin nan bai farka ba har safiya, ganin bai fita sallar asuba,kuma har karfe tara na safe ya yi babu motsin sa yasa Shamaki shiga ciki kawai.

Yana zuwa ya tarar da shi kamar gawa ko motsi baya yi sai numfashi kasa-kasa wanda sai mutum yaje daf da shi zai iya fahimtar yana numfashinma.

Cikin sauri da dimuwa yaje ya sanar da Uwar Soro da saurin ta tazo,tare suka rikesa suka maida shi kan Gado, Uwar Soro ta ce, “Lallai akwai matsala babba,domin Yarima ya jima bai shiga yanayi irin hakan ba,in ban manta ba tun yana yaro,kuma faruwar hakan na nunin cewa dole akwai wani abu da ke damunsa ko ya kwallafa rai akai da kuma bayyanar wani abu wanda yake sabo aransa, samuwar hakan shine mafita garesa kawai Yanzu ka koma bangarena ka dauko mun Ruwan zamzam muga ,sannan kuma kada ka kuskura ka bari labari yaje cikin Fada bare ya har ya kai ga Mai martaba ko Fulani sun sani.”

Kamar Yadda Uwar Soro ta umarceshi haka ya fita ya dauko ya dawo, yana bata ta karba ta tofa masa addu’o’i sannan ta goga masa a fuska kuma ta dan diga masa abaki.

Numfasawa tayi kafin ta ce, “In Sha Allah duk dadewarsa Yanzu ba zai zarce awa biyu ba zai farka, don tamkar barci yake, wanda azahiri zai nuna suma ya yi amman kuma indai za ayi kokarin dakile hakan sai ya dau lokaci kafin ya farka,ka zauna da shi zanje in dawo Yana farkawa kazo ka sanar dani.”

Kamar yadda ta fada kuwa haka ya kasance sai da Ya yi awa biyu cir kafin ya farka cikin wani gigitaccen yanayi yana surutu, “I love her,I said Love her, She’s My Wife,My Wife.” Yana wani irin bibbige bibbige yana kuma kokarin tashi.

Da sauri Shamaki ya fita yaje ya sanar da Uwar Soro ya farka sannan suka dawo tare.

Kafin su dawo har Adeel ya tashi zai fice.

Uwar Soro ta ce, “Ka na da lafiya kuwa Yareema? Daga tashi? Ina zaka je mu je ka zauna.”

Ta karasa maganar tana zaunar da shi.

Shiru ya yi,yana wani irin huci tare da dafe kansa gefe.

“Calm Down Please! Mene ne ke damunka? A tunanina ka ji sauki tsawon shekaru da ciwon nan bai dawo ba sai yanzu kicibis? Dole akwai abun da ke damunka, ka fadamun kada ka boye mun.”

Dagowa ya yi kawai ya kalleta da jajayen idanun sa da ya kafe kaf tamkar ba ruwa ciki,kafin ya sunkuya Domin zuciyarsa na raya masa cewa komai zai furta baza ta taba fuskanta halin da yake ciki ba da yadda zuciyarsa ke radadi.

Uwar Soro ta kara fadin , “Kwana biyun nan gabadaya ka sauya kuma innace ko maganar aurene sai kace Aa sannan kaki bude baki ka furta mun mene ne, yanzu dai kada ka sake ka fita cikin Fadar naan,ka je kayi wanka ka ci abinci, anjima zanje in sanar da liman komai koma mene ne za a magance babu abun da ya fi karfin Ubangiji ai.”

Tana fada ta shi zata fita , “Shamaki ka lura da shi kada ya fita cikin wannan halin,ya yi wanka,ya ci abinci kuma ya samu nutsuwa.”

Adeel yana ganin Uwar Soro ta fice, da wani irin sauri ya dauki Keyn Motarsa rabonsa da tuki har ya manta amman da ya figa motar cikin yan wasu daƙiƙu ya bar farfajiyar fadar, kafin shamaki ya fita ya yi nisa.

Tuƙi yake zuciyar sa na kurari da tafasa tamkar wanda bai son rayuwarsa motoci sai dai su kauce masa Badai shi ya kauce ba don shi bai ma da lokacin kaucewar.

Kai Tsaye Narasawa Gra ya nufa Kafin mai gadi ya gama bude masa get ya bankade ya shige da motar.

Da zafin rai ya fito ya shige cikin gidan.

Yana shiga Da Gaaji ya fara cin karo a bayan Adnan dukkaninsu kowanni fuska fal walwala.

Basu ankare da shi ba sai ji sukai yana kokarin fincikar Gaaji, “kai wane ne da har zakana taɓa mun mata?”

Adnan ya wani janye Gaaji cikin fusata yana sauketa tuni ta koma bayansa ta kankamesa.

“Matarka? Kamar haka naji ka furta ko ? Anya kwalwalarka bata samu matsala ba kuwa? Ka saketa nace maka na aureta And So?”

“Ka Aureta? Kai wani irin zahili? A ina ake saki ayi aure ba tare da idda ba? Har yanzu da iddata akanta kuma ina umartarka da ka bani matata in tafi da ita tun muna cikin lumana kada kai yi abun da zaka jawa kanka matsala.”

Adnan ya yi wata irin dariyar takaici, “Kana san matarka ce kake wulakanta ta? Kake aibatata da nunin cewa kazamiya? Kake ƙyararta? Kake dukanta? Kake bata tsoro? Kai duk ma sa wa innan a side koma miye yanzu Gaaji mallakina ce duk abun da zaka yi saidai kayi amman aure kam an daura mana batun idda kuma ai naga baka dauketa a matsayin matar da har iddarka zata hau kanta ba.”

Yana fadan hakan ya ja Gaaji suka shige ciki kuma yasawa kofar key.

Tamkar mafaraucin zafi Adeel ya fara magana, “Indai ina raye kuma ina Numfashi kasa aranka Matata baza ta taɓa zaba mallakinka ba.”

Ya fice a gidan, da kyar yake tuƙa motar har ya isa Masarauta bai ma iya Parking din ba sai Shamakine ya shigar da motar.

Yana shiga kwanciya ya yi kawai.

*****

Adeel ciwon son Gaaji da gaske kara cinsa yake ta ko ina kuma gagara sanar da hakan ganin cewa bai ma san ta ina zai fara ba.

Adnan kuwa dauketa ya yi daga lta har shi da Baffan suka bar ƙasar ma gaba-daya duk binciken Adeel ya rasa gano kasar da suka koma, kullum kara figewa yake yana fita a hayyacinsa ga biki yazo.

Yau ya kasance ranar al’adarsu ta Masarautar wacce ake yin wankan amarya da ango wanda za a iya danganta shi da sa lalle ko kamu.

Masarauta ta sha ado fiye da yadda take ada ba karamin kyau tayi ba,ko ina banda haske da kamshi babu abun da ke tashi, sai dai wani babban abun mamaki da ya kasance Khaleesa, Rumaiysa da Nasmah gabaɗayansu kala iri ɗaya sak suka sa na shigar amare.

An zaunar da su duka ya yin da aka fito da Yareema domin ya bude fuskar amaryarsa kafin sa lalle.

Tafiya yake yi tamkar ba zaiyi ba, gangar jikinsa ce kawai agun amman gabadaya tunaninsa na kan Gaaji Uwar Soro ce gefensa dayan gefen kuma shamaki.

Mai martaba da fulani Babba da fulani kilishi suna zaune a wani jeren kumbo.

Yareema na zuwa zai daga Mayafin kenan suka ji murya tamkar daga sama.

“Ba zai saɓu ba, kuma ba zai taɓa saɓuwa ba,nice mata wacce ta zam dole ga Prince Adeel Muhammad Rohaan.” Safina ta faɗa tana karasawa ciki.

Cikin Sauri waziri ya tashi yana fadin, “Karya kike Yar Talakawa, Kinyi kadan ki zam zababbiyar Mata ga Yareeema, ahir dinki da wannan furucin.” Yana karasa maganar dogarai na karasawa gareta suna tareta.

Sarkin Fada ya yi gyara murya yana fadin , “Ku barta ta furta abun da ke tafe da ita.”

Waziri ya ce, “Ku barta ta karaso Sarkin Fada ya yi mata lamanin saurare muji me ke tafe da ita.”

Safina ta ce, “Mai girma Mai Martaba Sarkin BENONI nice mata mafi dacewa Ga Yareema kuma ina tafe da hujojina masu karfi domin tabbatar da hakan.”

Sarkin Fada ya ce, “Muna biye da ke,ko zamu iya sanin dalilin hakan?”

Nan take Safina ta marairaice tana faduwa kasan gwiwoyinta idanu suka cicciko da hawaye araunane ta ce, “Ina Dauke da cikin Yareema a jikina.” Ta karasa maganar tana nuni da takaddun da ke hannunta.

Sai a lokacin Yareeem ya dago ya kalleta cikin wani irin yanayin mamaki da rasa gane manufar abun da take furtawan.

Wani irin kallon kallo aka fara yi a fadan wanda sai da kowa ya yi tsit ba sautin komai na tsawon second Biyar, mussaman Khaleesa da Nasmah gabadaya sun zuzuce.

Rumaiysa kuwa cike da mamaki take kallon Safina.

Wani irin bugun sauri sauri zuciyar Fulani Babba ta fara, nan take ji tayi tana kokarin gagara gane komai.

Fulani Kilishi kuwa wata irin zuface ta fara keto mata bayyananniya daga nesa za a iya jiyo sautin nishinta.

Fitowa idanun JAKADIYA zahiri sukai tamkar wa inda zasu fadi ƙasa tayi zuru-zuru.

Magajiya, Hajiya Rabi,da Hajiya Maimuna banda rawa babu abun da jikinsu keyi.

Uwar Soro sam bata amince da hakan ba ko kadan nan take taji aranta cewa babu shakka akwai wani abu da ake shirin aikatawa, amman taya za ayi Adeel da bai da lokacin mata, tunaninsu, kallonsu bare damu dasu da har zaiyiwa wata mace ciki? Macen ma wacce daga ganinta idanunta a bude suke.

Waziri ne ya dakatar da Maganar da fadin , “Karya kike ‘Yar Talakawa Kinyi kadan, kin yi kadan Yareema ya aikata barna da ke, gafara ki bawa mutane guri tun kafin ki jawa kanki Matsala,ana cikin farinciki zaki tawo mana da tuggun mugunta? To ahir dinki nace ahir dinki.”

Sarkin Fada ya kasa Magana karasawa kawai ya yi,ya karbi takaddar dake hannunta tabbas babu shakka takardar shaidar cikine a jiki ya ƙarasa yana nunawa Mai Martaba.

Sai a lokacin Mai Martaba ya yi magana duk da cewa zuciyarsa na ƙuna da zafi amman hakan ya daure ba tare da ya bayyanar da hakan ba,cikin izza ta jinin sarauta ya ce , “Kin tabbatar da cewa abun da ke cikin ki na shi ne?”

Safina hadda zubar hawaye ta ce, “Na shi ne Wallahi Mai Martaba kuma ina da Evidence din videon mu inma kana son gani zan nuna gashi nan a waya.”

Cikin Sauri Sarkin Fada ya ce, “Subhanallahi bama bukatar ganin dukkanin wata kazanta da bata ce da ganin idanunmu ba.”

Mai Martaba ya kalli Adeel ya ce, “Ka santa?”

Adeel ya amsa da eh domin ba ya taba iya yin karya duk rintsi a ko ina koda kuwa shine baya da gaskiya.

Numfasawa Mai Martaba ya yi sannan ya kara fadin, “Shin wani abu ya taɓa shiga tsakaninku?”

Sunkuyar da kai ya yi domin bai san amsar da zai bada ba wacce zata zam mafita kuma garkuwa garesa har a amince da cewa Romance kadai ya taba shiga tsakanin su ba tare da yin sex ba.

Har cikin ran Mai Martaba bai gamsu da cewa Adeel zai iya aikata hakan ba kuma bai jin tabbatuwar hakan ko kadan amman shirunsa da rashin furta komai da kuma amsawarsa a farko nunin cewa ya santa hakan ba karamin daure masa kai da tarwatsa masa tunani ya yi ba.

Hakan yasa ya kara yin gyaran murya kafin ya ce, “a bata wajen zama kuma a lura da ita tare da tanadar dukkan abubuwan bukatar ta har ya kai ga ta sauka, batun maganar auren nan kuwa an dagasa zuwa wani lokaci tukunna za ayi binciken da ya dace domin kara tabbatar da hakan.”

Khaleesa ce ta fara ihu cikin hargagi tana fadin, “Wannan ba gaskiya bane karya take, kawai basa so ne ayi auren nan ,tuggu aka hada wannan ba gaskiya bane,nice Matar Yareema ni kadai na dace da shi.” Tana gama fadin hakan ta fadi kasa a sume.

Nasmah kuwa zuban hawaye kawai take ta ma rasa abun fadi jikinta na karkarwa.

Uwar Soro ce ta rike Yareema ta na girgiza shi, “ka yi magana Please! Ka sanar da mai martaba cewa baka aikata wannan mummunan aikin ba,na san bazaka taba aikata hakan ba,ka karyata hakan Don Allah ka karyata hakan.”

Duk jijjigar nan da take masa ko motsa baiyi ba,bare ya daga kansa,idanunsa na kasa gabadaya tunaninsa na kan Gaaji ita ke haskawa cikin zuciyarsa kawai.

Ganin wajen taro na shirin barkewa da rikice tuni Sarkin Fada da dogarai suka dakile kowa, Mai Martaba ya koma Fada, Sannan Safina ma aka shigar da ita cikin masarauta.

Fulani Babba ta kasa jure hakan da kanta ta bisa bangaren Uwar Soro.

Yana zaune tamkar gunki Cikin yanayin damuwa da ɗimuwa hawaye na kwarara daga idanunta ta ce, “Don Allah in mafarki nake yi kayi gaggawar farkar dani, bana fatan sake yin aringama da mummunar bakar rana mara kyau da fasali irin wannan,ko da baza ka bude baki ka fadawa Kowa ba ina so ka furta mini cewa ba kai kayi wannan cikin ba,ka fadamun hakan ko Zuciyata zata yi sanyi in daina jin radadi da zafin da take yimun.”

Yanzun ma Kansa na kasa duk abun nan bai dago ba , Uwar Soro ta rike kafadar Fulani Babba tana, “Fulani dole sai dai ayi hakuri a yanzu kam, amman ni dai ko da wasa ban aminta da zancen nan cikin raina ba kuma bana jin cewa zai iya yin hakan abu ɗaya na sheda da cewa akwai wata kullalliya da ake kullawa kuma na fara ganin alamun hakan tun kwanakin baya a garesa, ki kwantar da hankalinki kada kisa komai arai In Sha Allah za abi ayi kokarin kawo maganin kowacce irin matsala.”

Share hawayen da ke zuba a fuskarta tayi ta tashi ta na daga hannunta sama ta ce, “Ubangiji na,kana ji kuma kana gani fiye da kowa,ina rokon ka ci gaba da tsare mun rayuwar Ɗana daga sharrin sheɗan da ma sharrin dukkanin mai sharri.”

Ta shafa afuskarta shi ma ta shafa masa sannan ta fice cikin sauri.

Tana fita Shima Adeel ya fice daga Ɓangaren Uwar Soro,Part dinsa ya nufa yana shiga ya kulle kansa.

*****

“Wane ne ya aiko wannan Yarinyar? Wane ne ya turo ta? Ta san tsawon shekarun da na dauka ina tanadar zuwan wannan ranar kuwa? Tasan shirin wa ta wargaza kuwa? Anya ta san cewa tamkar kirawa kai mutuwa nake kuwa? Hmmmm lallai tsuguno bata kare ba,kuma yanzu za a fara asalin wasan domin sai nayi fito na fito ga dukkan wanda yake son batamun shirina babu shakka tsarin zai canja haka kuma tafiyar ma ya zam wajibi ta sauya.” Cewar Hajiya Maimuna wacce shigowar wata Kuyanga ne ya dakatar da ita.

Ranki Ya Dade Mai Girma Fulani ta ce tana nemanki.

“Too…to.. ki ce mata ina nan tafe yanzu.”

Tana karasa fadan hakan ta bi bayan kunyangar.

Yanayin yadda ta ga fuskar Fulani cikin damuwa hakan yasata canja yanayin fuskarta nan take ta nuna yanayin jimama da rashin jin dadi.

Jiki a sanyaye ta zauna tana fadin, “Abu dai kam baiyi dadi ba, gabadaya gwiwowina sun sake har wani irin zazzabi nake ji.”

Fulani Babba ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce, “Hmm amman kina ganin da gaske Yareema zai aikata hakan?”

Hajiya Maimuna ta gyara zama kafin ta ce, “To Ba ace ba, ba a shedar halin Ɗan yau.”

Wani irin kallo Fulani ta mata cikin sauri da jajayen idanunta wanda suka rine tsabar kuka.

Cikin Sauri Hajiya Maimuna ta canja tsarin jawaban nata, “amman kuma duk da hakan nafi zargin cewa wani tuggu ake kokarin haɗawa Yareema kuma a cikin Masarautar nan ne,kila kuma wacce aka zaba mai a matar ne baza ta taɓa zama tasa ba domin bata dace dashi ba hakan ya faru, ina da shawara in an bani dama.”

Fulani Babba ta ce, “Haba Hajiya Maimuna ke kinfi kowa sanin cewa banda Aminiya kuma abokiyar shawara fiye da ke, dalilin hakan yasa na kiraki ai ina saurarenki.”

*****

“Abu na farko kamar yadda muka taba magana auren yareeema ya kasance cikin sirri domin indai ba hakan ba anta samun matsala kenan, ya kasance sai an daura auren ma kafin kowa ya sani, sannan ita kuma wannan yarinyar ki bar mun lamarinta a hannuna kawai , na fahimci cewa auren ne kawai ba aso aga ya yi.”

Fulani Babba ta ce, “Amman kuma ina ganin koda za ayi auren nan sai dai a bar batun Khaleesa a gefe a hadasa da Nasmah a yanzu wanda za ayin in komai ya daidaita yaga yana da bukata sai ya Auri Khaleesan, zan je in tuntubi Mai Martaba bayan ya samu nutsuwa don yanzu na tabbatar da cewa abun na matukar damunsa aran shi.”

Wani irin dadi Hajiya Maimuna taji ganin anzo daidai inda take da bukata kasa boye Murmushin da ke fuskarta tayi har sai da ya bayyana azahiri ta ce, “Hakan zai fi dai kam tunda Nasmahn ma naga sunfi samun fahimta da shi Yareeeman.”

Fulani Babba ta ce, “Ni babbar damuwata ma yanzu da ya kasa furta komai kan waccer yarinyar din da tazo duk da cewa daman Asalinsa ba son magana yake ba amman duk rintsi wannan lamarin ai ya kai mukurar da duk miskilancin mutum zai iya bude baki ya tanka,hakan ke razana ni cewa kodai da gasken hakan ya tabbata.”

Da sauri Hajiya Maimuna ta katseta, “Aa kam fa nace miki wannan batun ki barsa a hannuna dole gaskiya ta bayyana duk rintsi duk wuya.”

*****

Cike da damuwa Safina ta ke Magana, “Ni kam fa duk shirin mu ban san da cewa haka abun zai zurma dani ace wai za a rikeni cikin Masarautar nan ba, Nikam fa bazan jure ba wallahi kasani sarai ban saba rayuwar takura ba, akan wannan takurar tsaf zan iya bayyanar da gaskiya kowa ya huta.”

Wanda take wayar da shi ne ya ce , “Subhanallahi karki kuskura ki fara hakan, Ni kaina nayi tunanin cewa za abarki ki tafi ne kawai dawainiyarki za a dauka, amman yanzu dai kiyi hakuri za asan yadda za ayi tunda aka gama mai wuyan ai duk sauran masu sauki ne.”

“Ni kam tsaya! Kasan lokacin da nayi Maganar nan ya dago ya kalleni na matukar razana kuwa? Wallahi sai da hanjin cikina suka kada lallai Yareema akwai kwarjini tsorona kar ya ƙaryata ni kuma naji yyi shiru ya sunkuyar da kai.” Safina ta fada

Dariya ya yi yana fadin, “Lallai naki lamarin wasa ne,ai tuni aka rufe masa baki, ko shekara dari zakiyi bazai taba iya furta cewa ba shi ya yi miki ciki ba,kuma karki manta duk wasu da za asa su dubaki dole akwai sa hannuna ciki,ke dai ki kwantar da hankalin ki ki fara cin arziki iya son ranki kawai.”

*****

Shigowar JAKADIYA yasa tayi saurin katse kiran tana aje wayar gefe.

“Hmm ki dago ki kalleni kawai kisan in ke karamar dangace wajen kulle-kulle to ni nan uwarki ce ko ince uwar uwarki ma, na zo ne muyi tattaunawa ta Mussaman kafin kowa ya riskeki ni na fara, ban damu da cewa cikin jikinki gaskiya ne ko karyane Yareema ne ya miki ba, abu Ɗaya nake so, ki je ki furta cewa ba ciki ya yi miki ba biyan ki kudi Magajiya da Waziri suka yi kan lallai cewa kizo kice Yareema ya miki ciki,ni kuma na miki alkawarin baki duk kudaden da kikeso komin yawansu a duniyar nan,saɓanin amsa hakan kuwa ko bayyanarwa da wani zancen da na miki babu shakka zaki iya yin sanadiyar rayuwar ki, domin duk numfashinki yana cikin tafin hannuna ne cikin wannan Masarautar innaso dakilewa cikin second guda zan datse .” Jakadiya na gama fadan hakan ta fice adakin

Wata irin zufar wahalace ce ta fara ketowa Safina nan take ta fara gagara gane komai.

Fitar Jakadiya da yan mintuna sai ga Hajiya Rabi shigar nlbayi tayi ta dauki abinci domin kaiwa Safina, wani irin mummunan kallo take bin Safina da shi sama da kasa sannan daga bisani ta ce, ” Ban damu da sanin waye ya aiko ki ba da kuma jin gaskiyar zance, kashedi Ɗaya zuwa biyu gareni nazo miki da shi, kiyi gaggawar bayyanar da cewa turoki Hajiya Maimuna tayi kawai Domin ki yi sanadiyar hana Auren Yareema da Khaleesa ba zan fada miki makomar ƙin yin hakan ba Amman ki sani rashin samuwar hakan babbar barazana ce ga rayuwarki.” Dire mata farantan abincin tayi ta fice.

Suman zaune mai dauke da abun al’ajabi Safina tayi yau gata aduniyar mutanen da suka fita iya makirci da sharri, gata a cikin tsaka mai wuyar da bata san hanyar bullewa, rawan da jikinta ya fara yi ta fahimci cewa ashe ma sanyi take ji, takurewa tayi waje guda tana kankame jikinta.

*****

Tunda Adeel ya kulle kansa a Part dinsa bai bude sai karfe Ɗaya na dare.

Yana budewa ya yi saurin ficewa daga Masarautar ba tare da ya bari angansa ba.

Mota ya dauka ya wuce Airport

Direct ya hau prvt Jet ya yi Cyprus.

Sai da safe suka isa yana isa kuwa Gidan Adnan na cen ya fara nufa, zaune suke suna breakfast cikin Nishaɗi Gaaji ta ce, “Yaayah Sorry.” Tana maganar cikin Shagwaba.

Kallonta Adnan ya yi ya ce, “Aa ai kam sai kin ci abincin nan fa in ba haka ba yau ko karatu ba zan miki ba munyi fada bani ba ke.”

“Ummm Please Yaayah ni fa banso ne Allah banso kawai na ƙoshi Don Allah.”

Dagowa ya yi ya kalli tsukekken bakinta da yadda take maganar ya ce, “in kika gama zama baturiya fa shikenan inaga ni kaina sai kin fini iya turancin nan.”

Zata yi magana kenan suka ji an hankado kofa.

Adeel na shigowa Adnan ya tashi cikin hanzari.

Bangajesa ya yi kawai yana kokarin jan Gaaji.

Adnan ya riketa yana fadin, “Wai kai yaushe zaka bar wannan shirmen ne? Baka da hankaline, ka sake mun mata ta nace ka sake ta.”

“I can’t…. Matata ce.” Adeel ya fada yana kokawar fisgeta.

Gaaji kuwa tun tana shiru har ta kasa jurewa kuka take tana fadin, “Yaayah Don Allah kace ya sakeni zan balle, na shiga uku zaku ballani .” Ta kara fashewa da kuka.

Ci gaba da fisgarta sukai dukan su ,da tayi wata ajiyar zuciya tuni jikinta ya sake ta daina motsi.

Cikin dimaucewa Adnan ya ce, “Shikenan ai gashi ka kasheta ka huta ka kasheta.

Adeel ya riketa hannu biyu yama kasa magana da gudu ya fita a gidan, Adnan ya bisa suka.

<< Auren Wata Bakwai 17Auren Wata Bakwai 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×