“Indai zaki kasance kullum a tare dani ai zan ta murmushi har sai ranar da Mumfashi ya bar jikina.”
Gaaji ta ce, “Umm to kawai kata Murmushi in kanayi kafi kyau, inko kana fuskar shanun nan abun tsoro kake zama.”
Adeel ya harareta ta gefen ido, “Daman ai kin sha cemun mai fuskar Shanu kuma zan rama ai.”
Gaaji ta Shagwabe fuska, “To ni ka dagani tunda ba mutuwar nayi ba ko.”
Dagata Adeel ya yi, sai a lokacin ya tuna da kunan bayansa da aka bi duka aka rufe da bandeji.
“Wash…”
Ya fada.
Gaaji ta yi dariya.
Yana daga kai kawai suka hada ido da Mai Martaba zaune yana kallon ikon Allah.
Da sauri Adeel ya kautar da kai yana sunkuyar wa na jin kunya ya tashi daga gadon gabadaya ya bar wajen.
Ya nufi Gaban Mai Martaba ya gaishesa.
Nurses dinne suka je gaban Gaaji suka fara duddubata suka mata wasu allurai sannan aka bata Tea ta sha.
Adeel ma shiga toilet yayi ya goge jikinsa ya yi brush ya fito shi ma ya yi breakfast.
Yana zaune kan gadonsa yana bin Gaaji da ido so yake yaje gunta amman ganin mai martaba ba,dama ita kuwa ban da dariya babu abun da take yi masa hadda gwalo.
Sai can daga baya ya tuna da Twins ya dunga waige-waige bai gansu ba a karshe ya hakura.
Misalin karfe sha biyu na rana sai gashi wata Nurse ta fito dasu kasancewar an kaisu wani dakine daban ana lura da su.
Ji yayi kamar yaje ya fisgesu amman in ga Mai martaba sai ya sunkuyar da kai Don dole.
Nurse din ta ce, “Madam tun da kin farka ya kamata ki dan basu Nono su sha duk da cewa mun basu madara amman suna da matukar bukatar shan Nonon ki ko don lafiyarsu ma.”
Mai Martaba na jin hakan ya tashi ya shiga wani daki a gefe ya kwanta.
Dayar Nurse din ce ta fito tana, “Aa Sister bara tayi wanka tukunna batai wanka ba.”
“Ok ai na zata tayine.” Ta fada.
“Yanzu dai zatayi,Madam Bismillah Please.”
Tuni Gaaji ta mike domin tunda aka fara batun bada nonon nan gabanta ke faduwa..
Adeel ya mata sigina da ido.
Ta cuno baki tana murguda masa suka shige Toilet din su biyu.
Ruwan Ɗumi da gishiri Nurse din ta sata ta fara shiga na yan mintuna kafin ta fito ta gagggasa mata jiki tukun ta barta ta yi wankan.
Adeel rike yake da Twins yana kallonsu daga Macen har Namijin kama da shi suke sak har idanunun Sexy Eyes yanayin kalar fatar jikinsune kawai irin na Gaaji.
Kakkyawane na kin karawa kasancewar su jinjiraye sai sukai tamkar ‘Yar tsana tsabar kyau.
Shi kan shi Adeel bai san lokacin da ya furta , “
a’uzu bikalimatillahi tammati min sharri ma khalaq.” A zahiri Daidai da fitowar Gaaji kenan ta kallesa,suka hada ido suna sakewa juna Murmushi.
Wata Pink din Abaya mai dan kauri wacce zata sanya mata ɗumi a jiki wata Ma’aikaciya ta bata.
Ta sa sannan ta koma gadonta ta zauna.
Tana zama Adeel ya yi saurin direwa daf da ita.
A hankali ya ce, “Momy abamu Nono mu sha.”
Gaaji ta galla masa harara , “Aa Fura za abaku.”
Ya Shagwaɓe Fuska kamar mace, “Da gaske fa nake,kin san 2 Days nayi missing dinki in kin gama basu nima sha zanyi amman dai a fara da Little Prince & Princess.”
Gaaji ta turbune baki, “Kai ka basu naka mana ai kai ma kana da shi.”
Kallon girjinsa sannan ya yi sauri ya kara kallon nata, duk da cewa yana da tudu da fadin girji amman a gaban Gaaji shi tamkar farantin da babu komai a cikine.
Ya ce, “To sai dai in zamuyi canje ki bani nakin ni in baki nawa amman in ba haka ba ai ban ga abun da zasu mamula anan ba.” Ya fada yana shafa kirjin nasa.
Kamar sun haɗa baki kuwa kuka suka fara yi bilhakki da gaskiya na jin yunwa.
Cike da jin tausayin su Adeel ya ce, “Please zizi… Yunwa suke ji wallahi kinga yadda suke kukan nan, they need you Please.”
Kokarin fara ciro Nonon tayi amman ta ma rasa ta ina zata fara ta duburbuce.
Adeel ya tashi da kanshi ya ja mata zif din da ke gaban rigar duka biyun suka yi waje.
Ya dauki Prince & Princess yasa kowanne a bangare daban.
Kamar wa inda suka saba a tare da sauri suka cafke Nonon a baki.
Gaaji ta sake wata irin kara tana hawaye.
“Da zafi, Allah da zafi,Don Allah ka cire mun su wayyo ni….wayyo ni kam ka cire mun su.”
Ta fada tana kokarin turesu. Adeel ya rike hannayenta. Hakuri zakiyi fa a haka har zaki saba, kamar dai…..
Sai ya yi shiru yana dariya ya kalleta. Galla masa harara tayi tana hawaye ta ce, “Ai daga kai har yaranka mugayene kun iya mugunta shiyasa ma suka yi kama da kai kuta cin zallina kawai.”
“Mu dai munce adai yi hakuri Momy a ci gaba da hakuri damu.” Adeek ya fada.
Suna kara rikewa tana kara kokarin janye jikinta baya, can ta zare da karfi.
“Kai Dalla ni ku barni acici mala’ikun tauna.”
Adeel ya ce, “Amman dai duk cinsu ai basu kai Babarsu ba ko?”
Gaaji ta share shi.
Tashi ya yi yaje ya mikawa Nurses din su adakin da suke sannan ya dawo gunta.
“An gama dasu saura nima yunwa nake ji abani ko nayi kuka.” Ya karasa maganar yana riketa.
Ta sharesa. Yana kai hannun kai kirjinta ta sake masa cizo.
Bai san lokacin da ya yi wata kara ba sai da masu lura da su suka fito.
“Ranka Ya Dade lafiya?” Kunya ce ta kama shi ya sake hannun yana, “Lafiya lau ba komai.”
Gaaji kuwa me zatayi ban da dariya.
“Ai da sai ka fada masa cewa Nono ka zo sha na baka cizo.”
Harararta ya yi yana, “Zan rama ne ai kisa aranki cewa kinci bashi ne.”
Haka Ranar suna wuni Adeel na damun Gaaji kamar karamar yaro.
Ko gyara kwanciya tayi sai ya bita inda tayi.
Har dare.
Ta kwanta zata yi barci ya hau kanta ya kankame.
Gaaji ta ce, “Allah zaka fama ciwon bayanka,ni ka barni duk jikina ciwo ike mun fa.”
Adeel ya kara ƙanƙameta , “Nima ciwo jikina yake ai Amman hakan ba zai hanani jin dumin jikinki ba,ina ma ruwanki da ciwona.”
“Oh Allah na gode, Don Allah ka barni inyi barci wallahi idanuna har zafi suke mun.” Ta karasa maganar tana shagwabe fuska.
Adeel ya tura mata bakinsa yana, “Oya to kiss me, kina mun i Promise zan barki kiyi barcinki.”
Gaaji ta gyara Pilo ta kwanta abinta bata ce masa komai ba, sai jin harshen sa tayi kawai cikin bakinta yana tallafota ta baya.
Bayyadda ta iya kuma bata da zabi,hakan yasa ta biye masa suka farantawa ransu jina na tsawon mintuna, har barci ya kwasheta kafin ya sauka a hankali.
Dare Misalin karfe Goma sai ga Uwar Soro da Fulani Babba.
Gaaji har ta fara barci adakin da aka barsu ita da Adeel dake da suka farka sai Mai Martaba ya canja daki.
Fulani Babba na taka kafarta cikin bangaren tayi wata irin firgita ta farka daga barci.
Adeel daman na gun Mai Martaba ganinta kawai sukai kamar an dirar da ita gabansu. Gabaɗaya sai da suka razana.
Adeel cikin rawar Murya ya ce, “Lafiya meke faruwa?” Ko kallonsa Gaaji batai ba bare ta kullasa gabaɗaya idannunta sun juya.
Zuwa tayi jikin Fulani Babba tana wata irin karkarwa. Adeel ya ce, “Ke lafiyanki kuwa? Miye haka wai?”
Ya karasa maganar yana kokarin karasawa inda take. Uwar Soro da Mai Martaba kamar sun hada baki suka ce masa, “Dakata.” Dukanninsu tsaya sukai kallon ikon Allah.
Ita kuwa Gaaji wani irin kuka ta fara irin wanda ta saba yi in taga Sihiri a jikin Mutum.
Can kuma ta dakawa Fulani Babba tsawa cikin wata irin murya mai tsami, “Ku saketa, na ce ku saketa, ku saketa mugaye azzalumai marasa imani, ko ku saketa ko inyi maku lahani ko ni, ko ku cikin wannan Masarautar.”
Ta damƙo gashin kanta ta gefe. Sannan ta ci gaba da magana, “Zan hallakaku kuma in hallaka banza, marasa imani wa inda basa tausayin kansu bare wani, a makaskanta zaku kare har karshen rayuwarku muddin baza ku canja hali ba.”
Ta kara dawowa goshinta tana yi kamar tana shafa abu, can sai Fulani Babba ta fadi kasa.
Ta kalli Uwar Soro ta ce, “A dauketa a kwantar da ita, inta tashi daga barci zata dawo da muryarta da komai nata da ta rasa da izinin Allah, sannan a dage da addu’o’i kar ayi wasa, Mai Martaba ina shawarartarka da kayi gaggawar sanar da tawagar son zuciyarka cewa kana raye ,in ba haka ba dukkaninsu suna daf da shirya babban lamarin ba zai iya yin wuyar fuskanta bare magancewa.”
Adeel ya kalli Uwar Soro cikin yanayin Rashin Fahimtar meke faruwa. Aljanun jikin Gaaji suka yi wani irin Murmushi ta gefen fuska suna kallonsa sannan Ta ce, “Umm Angon Wata Bakwai, gashi kuma harda Yaran Wata Bakwai.”
Uwar Soro ma tayi Murmushi ta ce, “Aikuwa dai kam.” Sosa ƙeya Adeel ya fara yi na jin kunya. Mai Martaba yana kallonsu shi dai bai ce komai ba.
Ta ci gaba da magana, “Duk da cewa duk rintsi na san sai ka nemo Gaaji domin ita din wani bangare ne na wannan masauratar ka tafka babban kuskure na amincewa da saki a karon farko,mun so mu wahalar da kai matuƙa Don har mun so dauketa a duniyar nan sai kuma Allah ya taimakeka kana da Aminin kirki aminin kwarai duk da cewa bai san wace ce ita ba,amman yana ji a jikinsa cewa ita ce kai, zuwanta gunka ba a banza bane duk da cewa sanadine ya kawota Amman domin ka ne da kuma Masarautar nan Ubangiji ya kawota.” Sai a lokacin Mai Martaba ya yi magana.
“Niko zanso in san yadda akai wannan auren ba tare da saninmu na.”
Murmushi ta kara yi a karo na biyu.
“Lallai mu muka sa masa cewa ya Aureta ba tare da ya san dalilin hakan ba, duk da cewa ya tsaneta a farkon ganinsa da ita kuma hakan ma dalili, ya Aureta shi kansa bai san me yasa ya Aureta ba,haka kuma da kanshi ya fara sonta ba tare da kowa ya tursasa masa ba, ko a lokacin da ya rubuta mata takardar saki yana tsananin kaunarta cikin ransa amman izza ta jinin Sarautan da ke yawo a jikinsa yasa shi kasa bijirewa hakan, daga baya kuwa ya nemota da kanshi ko ba haka aka yi ba.”
Adeel ya girgiza kai kansa na ƙasa. Ta ce, “Zan tafi ina tunanin cewa na kammala komai da ya dace amman kunnuwanku su shirya sauraren abubuwan da bakwa zato,haka ma idannuwanku su shirya cin karo da abubuwan da basu shiryawa kallo ba, Zainab zata iya karawa da duk wata makira a cikin Masarautar nan ba tare da shakkar komai ba, kasancewar su cikin dakin Duhu ma wani Shirine babba wanda Ubangiji ne kadai yasan fassaran hakan amman muna tare da ita.”
Ta kara kallon Adeel” Angon Karni sai mun zo suna.” Tana fadan hakan ta koma daki da kanta ta kwanta.
Tana kwanciya kuwa Fulani Babba ta farka tana, “Yareema, Mai Martaba kuna ina? Ku zo in ganku Don Allah,ku zo in ganku yanzu ina ganin komai gashi ina magana, da inna rufe ido wasu abubuwa nake gani zasu kashe ni, sun ce kasheni zasu yi wai…
Da sauri Uwar Soro ta riketa tana, “Addu’a zakiyi Fulani ki daina sambatun nan sannu.” Ta karasa tana shafa mata addu’o’i.
Mai Martaba ya ce, “Alhmdu Lillah, Alhamdu Lillah, tabbas ya tabbata cewa za a shedawa al’umma cewar ina raye kuma su ganni tare da iyalaina duka.”
Rungume Adeel tayi tana kuka.
Ya share mata hawaye yana fadin, “Kiyi shiru In Sha Allah komai yazo karshe Momy.”
Tare dukkanin su suka kwana a Part din ranar, Uwar Soro ta shiga wani dakin,Yareema kuma ya koma dakinsu.
Yana zuwa yaga Gaaji nata barci hankalin ta kwance.
Bargo ya ja mata shi ma ya shige ciki.
Washegari
Da sassafe ta ko ina hayani suke ji ana kai kawo za a daura auren Waziri da Fulani Kilishi….