Suna shiga Jakadiya ta ce, “ai ban da bin maza ba abun da yarinyar nan tasa a gaba, watarana fa ba ta kwana cikin masarautar nan, idan ta yo ciki ni da kaina ake sawa in kawo maganin zubdawar, amman fa kar ki bari kowa ya sani.”
Fulani Kilishi ta ce, “Umm babu mamaki, karki damu, ki je ke dai ta bangarenki kimun kokari duk yadda za a yi da duk wata hanya da za ta kawo tsaiko ga auren ki yi, sauran aikin kuma nawa ne nasan me zan yi.”
Jakadiya ta ce, “To, to, to ki fadamun shirin naki mana kin ga sai muyi komai a tare har mu kai ga cin nasara.”
Wata irin dariya Fulani Kilishi ta yi ta ce, “ni in fada miki shirina? Ai kin yi kadan wa inda ke gabanki ma sun yi kadan, Allah kadai ya san shirina kuma daga shi babu kari, ki yi aikinki ke dai kawai.”
Duk Yadda Jakadiya ta so da ta ji shirin Fulani Kilishi ta kasa samun galaba haka ta fice zuciya fal takaicin Fulani Kilishi domin bala’in wayo gareta za ta iya shan cikin kowa ta ji abun da ke ransa amman ita baza a taɓa jin ko tarinta ba har sai ta so hakan.
*****
Sai can wajen karfe tara na dare Adnan da Prince Adeel suka koma cikin masarauta.
Gaaji na tsaye jikin window taga shigarsu da sauri ta fita, Adnan ya fara shiga Adeel ne ke kokarin shigewa rike masa hannu ta yi cikin shagwaba ta ce, “Aboki ba ka mun alƙawari zaka dawo mu yi wasa ba?”
Dake dukkaninsu bakaken riguna ne a jikinsu, hakan yasa bata iya bambamcewa ko tunanin cewa Prince Adeel ne ba Adnan ba
Adeel ya juyo da sauri yana yi mata wani irin kallo nan take ta razana jikinta ya fara rawa.
Fisge hannunsa ya yi, cikin tsawa ya ce, “tafi anan.”
Adnan na ji ya tashi da sauri tana kokarin komawa da gudu kenan ya ce,
“Gaaji? Me ya faru?”
Tsayawa tayi daga nesa bayan Adeel ya shige ta ma Adnan alama da hannu, “jo ka ji.”
Yana zuwa ta ce, “ni fa na za ta kaine shine na rike masa hannu shi kuma yamun tsawa kuma ya ba ni tsoro da wannan idon nasa.”
“Bai gane ki bane ina ga fa, yanzu madadin sa na ce miki ki yi hakuri to, kin hakura?”
Murguda baki ta yi ta ce, “ai ni shi nake so ya ba ni hakuri ba kai ba wa ya ce ya mun tsawa tom.” Ta karasa maganar tana taɓe fuska.
Murmushi Adnan ya yi ya ce, “Oh Gaaji to ba ni ba ne abokinki?”
Baki a cune ta ce, “kaine mana, ai shi ba ruwana da shi.”
“Yawwa To ki yi hakuri kin ji .” Adnan ya fada.
Alama da kai ta masa tana kara shagwabe fuska.
Ya ce, “Yawwa to yi mun murmushi mu ga.”
“Umm umm ni sai kace za ka zo muje muyi wasa da yarana sai inyi ma Murmushin.”
Adnan ya ce, “Eh na yarda to yi murmushin.”
Washe baki tayi wanda ya bayyanar da asalin kyawunta da dimple dinta da ya shiga ciki.
“Yawwa To Oya Give me five.”
Adnan ya fada.
Tsira masa ido tayi bata san me ya ce ba.
Ya yi dariya , “Au to ba ni biyar mu tafa.”
Mika masa tayi dukan su suna dariya.
Ya rike mata hannu suka koma ɓangaren Uwar Soro.
Ta ce, “ai na hango ku shiyasa ma na zauna ina jira ta dawo gwanda da ka biyota ka ga ta gama cin abinci wanka zata yi ta yi brush take gudun nan.”
Adnan ya kalli Gaaji yana zaro ido, “Daman wanka kike gudu? To ni bana kawance da mara wanka da brush gaskiya, ba ruwana dake daga yau, mu kunce ma.”
Ya karasa maganar yana mika mata hannu.
Tuni idanunta suka cicciko kamar zata yi kuka ta ce, “Aa zan yi, amman wannan abun Buroshe din fa kwashe mun jini yake zan mutu ne, kuma ni kar ka yi fushi da ni kace baka kawa da ni.”
Adnan ya ce, “dattin bakinkine yake fita ba jini ba, in dai da gaske ni abokinki ne to ki je kiyi ina jiranki.”
A shagwaɓe ta ce, “tom ni dai saibdai kai kamun muje tare.” Ta fada tana rike masa hannu.
Adnan ya ce, “Aa za dai ai mi ki ai namiji baya yiwa mace wanka, ba kyau in ganki haka fa ki je a mi ki ina jiranki har ki fito.”
Gaaji ta ce, “tom kar ka tafi ka ji ina zuwa yanzu zanje a mun.”
Da kanta ta shiga toilet din, Uwar Soro ta bita tana murmushi domin tasan da ba Adnan sai dai su yi ta dambarwa da kyar ta yarda.
Aikuwa Uwar Soro na mata wanka tana surutai tana ba Adnan labari yana amsawa a dole kar ya gudu.
Har ta fito aka shiryata sannan ta koma parlour gunsa.
Adnan ya ce, “Yawwa ko ke fa Good girl.”
“Mene ne? Ni ba gudu nake ba fa.” Ta fada.
Dariya Adnan ya yi ya ce, “Cewa Na yi Good girl ma’ana yarinyar kirki.”
Ta washe baki “to kai ma guduo gu tunda kai ma yaron kirki ne ba irin wancen Yareeman ba.”
Adnan ya yi dariya kawai yana bin ta da kallo ita kadai ta ce wannan ta ce wancen magana daya biyu sai ta ce Baffanta wanda hakan ya kara tabbatar masa da cewa ba ta da kowa fiye da baffanta.
Ta ce, “ka ga kullum Baffana sai ya mun tatsuniya nake barci tunda ya fara ciwo kuma ya daina mun shikenan.” Tana fadan hakan yanayinta ya canja damuwa ta bayyana a fuskarta.
Tsantsar tausayinta Adnan ya ji har cikin ransa ya ce, “yanzu zanna miki tatsuniya madadin Baffa kafin ya ji sauki kin yarda?”
Da sauri ta ce, “Eh da gaske kake?”
Ya ce,”Ehen.”
Gyara zama ya yi, itama ta matsa daf da shi.
Ya fara yi mata tatsuniya ban da dariya ba abun da Gaaji take yi, a haka har barci ya kwasheta ta fada jikinsa.
Dakansa ya dauketa ya kaita daki ya kwantar da ita, sai da ya shafa mata addu’a kafin ya fita.
Gidansu ya nufa kawai ganin dare ya yi bai koma bangaren Prince ba.
A wannan tsalelen daren. Motar safina ce a gefe tana ciki waya take tana fadin “ina ta kiransa fa bai dauki Kiran ba ni kam na gaji zan tafi.”
A dayan bangaren aka ce, “kar ki damu ba sai ya dauka ba, na tabbatar yanzu dai ya ci abincin daren da aka kai masa, inma bai ci ba to ya sha drinks din ko ruwan so ki na shiga komai zai tafi daidai don Allah karkiyi mana wasa da wannan damar domin ita ce ta karshe a garemu.”
Dariya Safina ta yi, ta ce, “an gama tabbas yau akwai shagali kace mun ka gama naka aikin saura nawa.” Ta karasa maganar tana katse wayar tare da cizon bakinta.
Kai tsaye ta shige ciki tana shiga kuwa ta tarar da Prince Adeel kwance ga dukkan alamu yana cikin wani yanayi hannunsa akan gabansa yana juyi .
Tsayawa tayi daga nesa tana wani irin Murmushin Mugunta.
Adeel na jin alamar ta ya dago cikin wata irin gigitacciyar murya ya ce,
“Safina Am in need Please.”
Yana fada ta kara kwantawa.
Karasawa gare sa ta yi cikin jin dadi.
Ta dagosa tana…