Kyawawan samari ne wanda kallo daya zaka yi musu kasan ya'ya wasu ne saboda irin shigar kayan jikin su na kamfanin Lois Vutton. Su uku ne suna zaune da kofunan barasa mai dan karen tsada mai suna Cool Fire a saman teburin da suke zagaye saman kujera suna rike da kofunan suna kurba yayin da daya daga cikin su kuma bai ko bi ta kan barasar ba ga alama yana da damuwa.
Ya soma cuda sumar kanshi cike da wata irin damuwa wacce yake jin tamka ya amaye zuciyar sa har yana cizon leben sa. Babu abunda kunnuwan sa. . .