King da Masud suna tsaye suka ga kaisar ya cire rigar falmarar da ya dora akan kyakkyawwr shet din sa top jins ya kuma soma cire takalmin shi trainers yana ware agogon hannun shi itama ya ajiye akan farar kijerar da ke jere a karkashin inuwar Umbrella . kafafun shi babu ko takalmi ya nufi famfon da yake can gefen bangon gidan inda tarin shuke shuke suke saboda idan za a bayar da ruwan shukokin sai a jona tiyo ayi ta zagaye layi layi na furannin ana basu ruwa shiyasa aka jona kawunan famfo da yawa a farfajiyar gidan don haka can kaisar ya nufa ya kunna famfo ya kuma jona bakin tiyon ya taho da shi yana dauko kyalle da sabulun wankin motar ya taho yana fesa ruwa a jikin motar Yana saka kyallen yana wankewa bil hakki da gaskiya yana fatan yayiwa motar wankin da zai burge nadiya har ya zama shine mai mata wankin mota.
King da Mas ud suna tsaye suna kallon yadda yake wankin motar da darje gilasan ta da ayoyin ta
Motar alh iro ta shigo gidan aka wage mishi kofar ya shigo sai kawai ya hango kaisar yana wankin mota da iyakar iyawar sa yayin da ruwa duk ya jika mishi jiki da kayan jikin shi.
Mamaki ya kashe Alhaji iro ya kasa fitowa daga motar yana tambayar kanshi shin wani ne ya saka kaisar wankin motar nan ko kuwa shine yaga damar hakan?.
kafin ya lalubo amsar wannan tambayar yaga nadiya ta fito cikin kayan da suka fidda surar ta kanta babu ko dan kwali sai dogon gashin ta da ya kwanta a kafadar ta .
“Kai wai har yanzu baka gama wankin motar nan ba? uban me kake da har ka Kara minti takwas akan wanda na baka? wai kai in tambaye ka waye Uban ka a bauci da kake min gadara da izza Ni da gidan uba na? me yasa talakawa kuke da rainie da son ku nuna kuma mutane ne? Matsiyatan banza matsiyatan wofi shiyasa ma Allah ya barku a tsiyar ku saboda bak’in halin ku.
Wani irin bacin rai ya saukar wa alh iro wanda yake jin tamkar ya fito ya make nadiya amma sai zura mata ido Yana kallon yadda ake ta aunawa kaisar zagi shi kuma babu alamun bacin rai a tare dashi sai ma murmushi da yake Yana fadin
“Yi hakuri ranki ya dade ai na gama bani minti biyu na share laimar da ke jiki kar tayi jirwaye .
ya soma saka kyallen yana goge lemar da ke jiki yayin da mota ta dauki kyalli tana walwali .
da wani irin fushi nadiya ta shiga motar ta fige ta kad’an ta takewa kaisar yatsun kafafun shi ta fice tamkar an harba kibiya yayin da alh iro yabi bayan ta da kallo har ta fice daga gidan.
Kaisar da su king suma suka bita da kallo har ta fice.
“gaskiya in dai haka ne bakayiwa kanka adalci ba kaisar ko zakayi aiki sai kayi inda ba a san kimar ka ba?
cewar mas ud
Shi kam king ya kasa cewa komai suka juya zuwa dakin nasu inda fati ta kawo musu abinci king yana fadin
“Nifa yarinyar nan tana cizo na kaisar amma na San tafi karfi na ba ma zan soma tayawa ba amma da mamaki tarbiyar su ba irin ta waccan gwanar taka ba ita kam babu kaudi babu zalama komai nata sumple.
“In har kana son ta king zanyi maka kamfe wallahi yarinyar bata da matsala kamar yayar ta .
“Tafi karfi na kaisar ko yaro ya san nashi a cikin kaza Kai ko kafa sune nashi da yaga cinya yasan ta baba ce yarinyar can tafi karfi na.
fati da ta tsinci wannan maganar sai taji wani Abu ya tsaya mata a zuciya. menene wannan ? bata sani ba Amma koma meye baya rasa nasaba da jin irin amsar da kaisar ya bayar.
Alh iro ya fito daga motar Yana share zufa . A yau kam dole ya san matakin dauka akan Nadiya tunda har wulakancin ta ya soma zuwa inda ba zai iya jurewa ba gara ta wulakanta shi akan ta wulakanta kaisar ba zai yuwa ba.
ya rufe motar ya wuce zuwa cikin gida jikin shi a sanyaye
duk ya kasa jin dadi duk da bai sanarwa haj Aliya komai ba akan abinda Nadya tayiwa kaisar wanda ya tabbatar da bata sani ba.
babu abinda yake jira irin dawowar Nadiya .
fati ta soma safa da marwa tana jin wani abu tsaye a kan zuciyar ta musamman a duk lokacin da zatayi ido hudu da kaisar
taji hawaye yana sulalowa daga idon ta ta dafe gurbin zuciyar ta tana fadin
“Allah kai kadai kasan yadda nake ji a zuciya ta ka sanya hakan ya zama kaffara matukar babu alheri a cikin abinda nake ji . Idan kuma akwai alheri kasa abinda yake sunke cikin zuciya ta ya bayyana na san komeye shi ka kuma tabbatar dashi da rahamar ka ya Allah amma Ina wahala akan bawan nan naka Wanda na yardarwa kaina Ina son shi tun ban yarda da hakan ba har nayi giving up.
ta zauna tana fafka uban tagumi sai kuma ta mike ta dauko littattafan islamiyar ta ta wuce dakin kaisar
tuni su king da mas ud suka yi mishi sallama bayan sunci abincin suka wuce
Kaisar ya shiga wanka ya fito ya saka farar jallabiya daidai da shi ya dauko Al kur ani Yana karatu fati ta shigo
ta zauna har ya Kare ya dago kanshi yana kallon ta yana fadin
“Sister Fati Yaya dai?
“Uhum wallahi zaman shirun ne ya ishe ni nace bari nazo ma ka kara min karatu Yaya kaisar.
“to ke sister fati kika sani ko na san wani abu ne a littattafan naki?.
“Ai da baka sani ba da Ubangiji ba zai kimsa min ilhamar tunkarar ka ba.
“Haka ne to bari mu gani idan zan iya
turyan turyan kaisar yake karawa fati karatun Al amarin da ya kuma rikirkita fati domin kuwa a wannan zaman karatun ya tabbatar mata da lallai son kaisar take bata bukatar wani dogon bayani
Daddy goye da hannayen shi a bayan shi yana cike da bacin rai a yau din nan
Kaisar ya shigo inda fati ke biye a bayan shi don kiran daddy ne ya sa makarantar karatun ta tashi
ya iso yana dukawa a gaban daddy yana fadin
“Daddy sannu da gida ban ji shigowar ka ba.
“Eh na jima kaisar Yaya gidan?
lafiya lau alhamdulillahi daddy.
“Masha Allah ga jaka nan Kaya ne na saka adun ka maka kala hamsin ne idan kana bukatar wasu kalar sai Kayi magana .
cike da mamaki kaisar ya ke duban daddy Yana fadin
“Wallahi daddy wannan ma sun Isa nagode Allah ya kara girma.
Haj Aliya ta shigo daidai da daddy yana direwa kaisar jakar kayan ya fito dasu dunki mai daraja disigner kalar yan Abuja.
“Mama ga dunki daddy yayi min don Allah a taya ni godiya.
“Kai masha Allah kaisar na taya ko godewa kam Allah ya sa ka kashe da kanka.
“Ameen ameen mama .
nadiya ta shigo gidan bakin ta dauke da wata banzar waka marar albarka wacce show ya rera .
Idon ta ya sauka akan kaisar da ke daga kayan yana gani haj Aliya kuma tana taya shi godiya wurin daddy.
da sauri nadiya ta Isa ga daddy tana fadin
“Daddy motar nan tana da dadi wallahi gashi duk garin nan babu mai irin ta sai ni thank you daddy sai dai ba a saka min plate number ba?.
ya kalle ta yana fadin
wace mota ce take da dadi?
tayi maza tace
“Wacce sulele ya kawo high land din nan fara?.
“Ayya wannan motar ba taki bace ta kaisar ce shi na siyawa kice kin dano mishi mota to kin nemi izinin shi ne?.
Ta juyo a kidime tana kallon daddy.
“Banji abinda kace ba daddy? wane haka kaisar? wai daddy waye wannan matsiyacin da kake saka shi yana Jin kan shi a wata tsiya? dan aikin daddy ka siyawa wannan motar?.
“Ban hana ki kiran mutane da matsiyata ba Nadiya? wane irin kunne ne da ke ? bani key din motar nan !
Ya fada da tsawa yana mika mata hannu ta mika mishi key din jiki na kyarma .
ya karba ya mikawa kaisar yana fadin
“ga mota kaisar na siya maka tun last week amma bata iso ba saboda halin yau sai jiya shine aka kawo ta yanzu ga ta nan ka tsayar da shawara zaman ka a hakan ba zai yuwu ba dole ka karbi wani sashi na daga dukiya ta ka kula dashi.
“To Daddy yadda kace haka za ayi.
ya mika mishi key din motar ya karba yana godiya yana nunawa haj Aliya itama cike da farin ciki take godiya yayin da Nadiya taji wani bakin ciki yana shirin sumar da ita.
“Waye wannan shegen da yayi min shiga hanci da kudundune?
ta fada ba tare da ta san a bayyane maganar ta fito akasin tambayar da zuciyar ta kadai ta zaci tayiwa?.
Daddy ya dube ta yana fadin
“Wato ba zaki daina wulakanta mutane ba ko? kin san Ina cike dake akan abinda kikayi wa Ade na kone ta da ruwan zafi ? kin san ba kyale ki nayi ba? kin san Ina cike da ke akan mutumin da kika banke kika gudu baki tsaya ba ? ta dube shi a razane don batayi zaton ya san anyi hakan ba.
“Kin San Ina cike dake akan abinda naji kina fadawa kaisar a dazu? ,kece ke saka shi wankin mota har kina zagin shi ? kin kuwa san waye kaisar? To ZINARE ne duk yadda kike daukar kanki wallahi baki Kai darajar AZURFA a wurin kaisar ba . shi kuwa idan akwai abinda yafi ZINARE da Lu u Lu u da jauhari to Kaisar ya wuce Ina mai tabbatar Miki bakai kaisar komai ba bare ki fishi . lalacewa kawai kika fishi don haka daga yau idan kika kuma gaya mishi bakar magana zan nuna miki fin da yayi miki a wuri na don zan nuna miki nafi son shi sau dubu akan ki don haka maza ki zube a gaban shi ki bashi hakuri har sai ya yafe miki in kuwa baiji zai iya yafe miki zagin wulakancin da kikayi mishi ba wallahi zan bashi dama ya lakada miki shegen duka kuma duk yadda yace yana so hakan za ayi a ciki kuwa har da mika ki gidan gyaran hali don na kula sai an sabunta miki hali ko a gyara miki shi maza duka a gaban shi ki nemi yafiyar abinda kikayi mishi ko kuma yanzu wallahi na bashi bulaliya ya lakada miki shegen duka wanda ba a taba yi miki shi ba.