Skip to content
Part 11 of 23 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“Daddy dan Aikin gidan mu zan bawa hakuri? haba daddy kar ka sa ya raina ni mana ? Don na zage shi daddy ko kashe shi nayi me za ayi  dan talakawa wanda bashi da galihu.

A fusace daddy ya kifa mata mari yana fadin, “Ai na fada miki idan kika sake tozarta wani mutum akan ido na sai na baki mamaki duka ki bashi hakuri wallahi.

“Wallahi daddy ba zan bawa wannan matsiyacin hakuri ba tunda na gane kafi son shi dani duk da ban san abinda yayi maka ba.

A fusace daddy ya figo bulaliyar da ya tanada ya mikawa Kaisar yana fadin

“Karbi nan ka zane min yarinyar nan har sai na ga tana sharbe hawaye da majina.

da sauri kaisar ya dubi daddy yana fadin

“Ayi hakuri daddy a kyale ta na yafe mata.

“Kai karbi nan kaji so nake kayi mata dukan tsiya in kuma ba haka ba har kai zan hada in buge wallahi kaji na rantse.

Kaisar ya karbi bulaliyar yana nufar nadiya wacce take duban shi da wani kallo na in ka dake ni zakayi nadamar abinda kayi.

ya daga bulaliyar ya yafa mata sau uku .

“Ba irin wannan dukan nake so ba wanda zan tabbatar da doku har tana share hawaye da majina in kuma ba zaka iya ba to kai zaka fanshe ta da jikin ka don ni zan dake ka tamkar kurar bara.

“Kayi hakuri daddy na yarda zan fanshe ta . mace ce mai rauni kuma bana son abinda zan tab’a fatar ta .

“To kuwa zakaji a jikin ka .

Daddy ya fada yana fige bulalar daga hannun kaisar inda nadiya take zaton daddy din zai rufe kaisar da duka amma ga mamakin ta sai taga daddy ya rufe ta da duka abinda bai tab’a yi mata a tarihin rayuwar ta ba don tsakanin su sai rarrashi babu ko tsawa mai karfi bare kuma duka amma Wai a yau  saboda wani matsiyaci ana jibgar ta duk da taso kwacewa ta gudu amma daddy yayi mata rukon da ta kasa kwacewa yayi ta dukan ta tamkar ba Daddyn ba wanda yake nuna mata so da kauna.

Da gaske kuww daddy sai da yaga nadiya na sharben hawaye da majina duk da hakurin da kaisar ke bashi bai saura ra mata ba sai da kaisar ya rike bulalar kafin daddy ya sake ta ta aunaa guje tana gunjin kuka.

“Wannan yarinyar na saka kafar wando daya da ita tunda na kula idan na ci gaba da saka mata ido zata kai ni jahannama da mugayen ayyukan ta alhalin ni banyi zunubin shiga wuta ba amma yarinyar nan zata jawo min janhurun masifa to an gama wallahi .

Kaisar yayi ta baww Daddy hakuri shi kuma yana ta fada haj Aliya ma tana zaune tana fadin

“Ai yanzu ka farka daddy tun tuni nake nuna maka yarinyar nan sai da saiti amma tana Rarrashin ta .

“Ai na gama rarrashin ta Aliya tunda ta zama Yar iska ban sani ba ashe haka wulakancin yarinyar nan ya kafurta ban sani ba? to ba zan yarda tafi karfi na ba.

“duk ranar da yarinyar nan ta kuma zagin wani a gidan nan aliya ki fada min fatima ko ji kikayi ta fadawa wani bakar magana ki fada min wallahi yarinyar nan zan bata mamaki.

Kaisar ya mike yana daukar kayan shi da key din motar Yana Kara bawa daddy hakuri.

“Kaisar ko kallon banza yarinyar nan ta kuma yi maka don Allah ka sanar dani taga kalar wulakancin da nima zanyi mata sai ta gwammace bata budi ido ta San wulakanci ba .

Nadiya tsaye a gaban mirror tana hawaye tana kallon jikin ta da yayi burdin bulaliya da mamakin kalar wulakancin da zatayi wa kaisar a gidan Nan har ya iya dukan ta kuma a karbe mota ace tashi ce bayan ta gama shelantaww duniya cewa tata ce ?

Ta zauna tana goge hawaye fati ta shigo ta ajiye littattafan ta  bata tanka mata ta soma gyara kayan dakin wanda Nadiya ke yin watsi da komai sai dai ita ta gyara in kuma bata gyara ba to  a haka dakin zaiyi ta zama

haushi da takaici ya ishi Nadiya ta soma aunawa Fati zagi tana fadin

“Shegiya mayya kaska marar zuciya matsiyata masu gadon talauci.

Fati dai bata tanka mata ba tayi ta gyaran dakin ta baww banza ajiyar ta abinda ya kuma fusata Nadiya kenan sai kawai ta tashi tana rufe fati da duka da son ta huce fushin ta akan fatin.

Fati tayi tsaye tana kallon ta ba tare da tace mata ko uffan ba haka kuma bata Kare dukan ba bare ta rama.

Haj Aliya ta na tsaye tana kallon Nadiya da dukan fati da take amma vata ce mata komai ba har ta gaji ta kyale ta.

“Fati jeki ki fadawa daddy irin zagin wulakancin da tayi maki wata kil bata bugu bane  shiyasa tayi miki hakan.

“Mama kyale ta har ta kure hakuri na inda zata san shuru shuru ba tsoro bane kawar da Kai ne amma tunda daddy ya gane hanyar da zata biyu ai shikenan ko ban fada ba wani zai fada ni kuma duk ranar da ta kuma duka na ban mata laifin komai ba wallahi zan bata mamaki amma duk wanda ta kuma yiwa gorin talauci ko ta wulakanta shi da gudu zan fadawa daddy.

“To da kin burge ni kuwa

Cewar haj Aliya wacce ta juya dama ta san sai nadiya ta nemi hucewa akan fatin

Kaisar ya iso sashin nashi yana jin zafin dukan da daddy yayiwa nadiya a kan fatar jikin shi don wallahi Yana Jin zafin dukan ajikin shi  fiye da zafin da Nadiya taji.

Ya soma zarya a falon babu abinda yakke son sani sai halin da nadiya take ciki amma ya san bai Isa ya sani ba tunda ba sauraran sa take yi ba.

Wata hikima ta fado mishi ta kiran wayar Fati .

ya kira fati wacce ta saka mishi lambar ta a dazu

Fati na ganin kiran taji wani sanyi smma tana dauka yace mata

“Fati idan nadiya na kusa da ke don Allah hada ni da ita mana?

Cike da firgici fati ta juya ta kalli Nadiya da ke shafe jikin ta da yayi burdin bulaliya da coco botter ta mika mata wayar tana fadin

“Ana magana.

tayiwa fatin wani shegen kallo kafin kuma ta karbi wayar don tayi zaton mama ce ko daddy.

tana Kai wayar a kunnen ta taji muryar na fadin

“Masoyiya don Allah Ina son ganin ki.

ta dauke wayar daga kan kunnen ta tana duba fuskar wayar duk da bakuwar lamba ce babu suna.

“Waye wai yake min hauka? wacece masoyiyar ka?.

“Kaisar ne don Allah in ganki minti daya mana akwai sakon da zan baki.

“Ka kaiwa uwar sakon ni kana da abin bani ne? matsiyaci irin ka yaushe kake da abin bani? Ina ce a gidan mu akayi maka alfarmar da uwar ka da uban ka basuyi maka ita ba? In ka kuma kira na da wannan sunan na rantse maka sai na fasa maka kai kuma dukan da akayi min saboda kai zaka ga abinda zai faru har kaine ke buga min bulali don na zage ka to na zage ka din .

ta datse wayar tana wurgawa fati wayar tana fadin

“In kika kuma nufa ta da wannan abun da kikayi min a yanzu wallahi zan ci uwar ki ne wannan ta kauyen misau din wacce fatara da tsiya suka Kare a kanta.

fati ta dauki wayar ta ta fice don tuni zuciyar ta ke zafi musamman sunan da taji Kaiser ya ambataww nadiya wai masoyiya. wannan tashin hankalin yafi komai firgici a wurin fati ba zagin wulakancin da Nadiya tayi mata ba in da sabo ta saba amma wanna bak’on Al amari  ne da yake neman mayar mata da saman ta ya koma k’asa.

hawaye suka ciko idon ta don hasashen ta kan ya cika cif zuciyar da take son mallaka tana wurin yar uwar ta nadiya kaisar ba ita yake hari ba Nadiya yake hari .

A wannan rana zukata uku sun kwana cike da Al amari mabanbanta kowace zuciya da kusurwar da ta makale tsakanin kaisar da nadiya da kuma fati . Yayin zukata biyu suke kukan so wato Kaisar da fati. Ita kuwa Nadiya mugun alwashi ta kwana sha akan kaisar.

da safe kaisar ya fito Yana shirin wanke motar da ya wankewa Nadiya a jiya don a yau kam Yana son bata mamaki.

ya gama wankin ya kuma goge lemar tana ta kyalli ya koma ya zauna kamar mai jiran tsammani sai ga Nadiya ta fito ga Alama kuma fita zatayi amma ta manta da babu mota a hannun ta sai da ta fito ta fara hango motar nan high land sai ta tuna da wulakancin da daddy yayi mata na kwace key din motar.

takaici ya ishe ta da ta ga tata motar duk gilasai a far fashe tana shirin juyawa ne ta koma ciki don bata ga kaisar ba shi kuma ya zuba mata idanu ya shagala da kallon ta yana jin ba a jarrabe shi da komai ba sai soyayyar nadiya wacce yakke gani a aljannar duniya.

ta juyo sukayi arba da juna yana mata murmushi.

“Fatan kin tashi lafiya masoyiya? ga key din motar nan Ni na baki shi kyauta irin ta masoya  nadiya ina son don Allah ki soni koda bai Kai yadda nake son ki ba kuma don Allah ki fada min aibu na ko yadda kike so na xama matukar yadda kike son na zama bata saba da halittar da Ubangiji yayi min ba nayi miki alkawarin zama irin mijin da kike so kuma kike so zan baki shi in sha Allah.

ta watsa mishi wani shegen kallo tana fadin

“Me kake tunanin bani alhalin mune suturar ka? wace tsiya kuke da ita da zaka bani? Idan ka kuma kira na da wannan sunan masoyiya wallahi zanyi kwallo da kai har wani namiji ne nan kai? ai ka rike wanna a ranka kafi kama da mata maza da wannan karamar halittar taka kake nufin aure na? da Allah malam bani makullin mota ai Kai da kanka ka san kaci uwar karya ka kwana da yunwa a baka wannan motar a gidan mu ai gara na kyasta ashana na kone t da dai ka hau ta .

ta fige key din motar daga hannun shi ta wuce tana auna mishi rashin mutunci.

ya zauna yana kallon ta ta figi motar aguje ta fice

ya sauke ajiyar zuciya yana shafa sumar kanshi cike da damuwa me yasa so yake da sab’ani ne wanda kake so ba lallai ya soka ba? me yasa baiyi  sa ar samun soyayyar Nadiya ba? me zaiyi ya zamo ya samu soyayyar ta a rayuwar sa?

ya mike ya nufi cikin shi inda sukayi kicibus da fati da littattafan ta zata shiga wurin shi.

<< Azurfa Da Zinari 10Azurfa Da Zinari 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×