Skip to content
Part 13 of 23 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Akan idon Daddy duk abubuwan suka faru amma babu wanda  yafi tsayawa daddy irin da nadiya ta kifawa tsohon ta kuma hankada shi ya kife har yana hantsilawa.

Da sauri daddy ya biyo bayan tsohon wanda a take ya shaida tsohon nan ne da nadiya ta banke abin mamakin ma ta yadda ya zo gidan ya kuma shigo kai tsaye.? lamarin tsohon Yana da ban mamaki anya kuwa?.

Da sassarfa daddy ya isa ya dauki kudin da su kaisar suka bashi ya kuma dauki sauran abincin da yake cikin kwanon tsohon ya fita inda sarkin gida ya auno aguje zai karbi uban gidan nashi amma Daddy ya wuce sarkin gida don yana jin akwai Al amari a tare da tsohon nan ba kawai yake ba.

Ya fito get din inda duk masu tsaron kofar suka taso da azama amma daddy ya soma dube duben inda zai ga tsohon amma sama ko kasa babu shi babu dalilin sa abinda ya kuma tsorata daddy kenan don ya san mutum dai bai Isa shanye hanyar ba duk saurin sa kuwa to amma waye tsohon nan?

Ya gama dube duben shi ya juyo rike da kwanon tsohon da kuma kudin sa da ya zubar.

tuni Nadiya ta koma cikin gida don ta manta da daddy Yana gidan sai kuma gashi yaga abinda tayi.

jiki a sanyaye daddy ya ajiye kwanon da kudin Akan center table.

“Aliya na soma nadamar abinda nayi wanda na tabbatar da yana dab da zob’e min lada ta duka. Ina tsoron tuhumar da yarinyar nan zata sa Ubangiji na yayi min akan mugayen ayyukan ta da halayen ta.

“Ki dubi abinda tayiwa tsohon nan? wai kin san shine ma tsohon da ta banke? kuma fa ganin shi kawai akayi a cikin gidan babu wanda yaga shigowar shi.

“Wallahi daddy ban tab’a muzanta irin yau ba. Akan idona tayi wa tsohon nan haka. me duniya zata dauke ni in ba wacce taso kanta ta watsar da amanar Allah ba? ni dai kaina ba zan yafewa kaina ba matukar duniya zata shaida rashin kirkin nadiya takuma yabawa fati ni da kaina ba zan iya yafewa kaina ba to ina aikin me?.

“Na rasa yadda zanyi da yarinyar nan Aliya na sani mai bayar da lali ya riga Mai bada horo . bana ganin laifin ki Aliya akan mugayen ayyukan yarinyar nan tunda akan ido na kike komai  tunda yadda kike mata wuta wuta ma ni bana mata Amma me yasa ta zama haka maimakon abin sha awa da Ya’yan musulmi suke zama? don Allah Aliya me zanyi na samu zama lafiya?.

“ADDU A zamuyi in sha Allah Allah ba zai kunyata mu ba kuma ba zakayi nadama ba.

“Dole yarinyar nan ta nutsu Aliya ko kuma na nesanta ta daga ni tunda ta soma zagin kaisar da wulakanta shi naji ba zan barta ta wulakanta yaron nan ba duk da na lura da yaron yana son cewa wani Abu Akan ta in ma na fahimce shi akwai kanshin soyayyar nadiya a idanun kaisar wanda ba zan so hakan ba Sam don babban goro sai magogin karfe ZINARE ne shi da yafi karfin AZURFA sai dai ZINARIYA kamar sa amma ba dai Nadiya ba.

“Na fahimci hakan nima amma in har hakan ne Ina ganin gara ayi mata auren ka bawa kaisar din ita ina ganin kamar hakan ma shi yafi.

“Ba zan bashi ita ba Aliya don na tabbatar da tashin hankali na hada shi da shi . ke kin san yarinyar nan sai tsayayyen namiji wanda take shakka da tsoro shine kawai zai saita ta amma kaisar da ya na iya biye ra ayin ta yayi mata yadda take so ai kin ga cutar da shi kawai zatayi.

“Eh to kuma haka ne Allah ta ala ya shirye ta ya kuma zaba abinda yake shine alheri amma kuwa na tausayawa yaron nan in dai son yarinyar nan yake da gaske don na san zai wahala ne yadda take a haka ban zaci zai samu abinda yake so ba musamman yadda Take daukar kanta tamkar wata yar mistar president ni ai zanso ganin jajirtaccen namijin da zai mulki zuciyar yarinyar nan. .

“Nima abinda nake son gani kenan

cewar daddy

Washe gari tun da safe show ya kira wayar nadiya yana fada mata karfe sha daya na safe zasu fita.

ta tashi tana tunanin ta yadda za ayi ta fita don bataji zata fasa fitar nan ba

Da sauri ta mike tana shiga toilet tayi wanka tayi shirin fita kiran show bata kuma yarda mama ta Sani ba ta fice da sauri

Da karfi ta soma buga kofar dakin Kaisar tamkar zata jijjige kofar

Yana zaune rike da alkur ani yaji dukan kofar

Ya mike yana bude kofar inda yaga nadiya wacce take rike da kugun ta tana hararen kofar.

“Samun wuri ne kana Jin Ina dukan kofar kayi banza dani tamkar gidan Uban ka ne?.

“Yi hakuri masoyiya da girman kijerar ki .

“Ban ce maka kar ka kuma ce min masoyiya ba? Ni ai sai dai baban ka Amma nafi karfin nayi soyayya da kai sai dai gyatumin ka don haka daga yau in har zaka ce min masoyiya to sai dai kace min momy matsiyacin banza da kai.

“An gama in dai sunan momy din kike so wallahi sunan ki daga yau momy koma nace my momy yayi haka?.

“Yi maza ka nemo matsiyaciyar uwar ka a can kauyen ku bani key din mota zan fita kuma wallahi idan ka sake ka fadawa daddy na karbi key din Nan wallahi sai ka bar gidan nan in dai ba na baban ku bane.

“Ayya ai daddy ya hana ki tukin mota my momy amma bari nazo na kaiki inda zakije don ba zan tab’a yin abinda daddy y hana ba.

“Kai wai da me kake takama ne da har zance ga yadda nake so kace ba haka ba waye uban ka ? da Allah malam ka dauko min key ko kuwa yanzu nayi maka abinda baka zata ba wallahi.

“Ok to ina zuwa.

Ya juya dauko key din motar ya fito da waya wacce ta gane daddy yake shirin kira.

“Bance ka kira min daddy ba in ka sake ka kira shi wallahi ranka zai baci.

“Ba zan iya baki key din motar ba sai na sanar dashi tunda ya fada min ya hana ko aro na baki to amma babu abinda ba zaki nema na kasa yi miki shi amma ba zan iya tsallake umurnin daddy ba .

Wani irin tsoro da firgici suka dirar mata idan daddy ya san zata fita me kenan? bayan daddy ya saka mata takunkumi.

Wayar ta tsinke daddy bai dauka ba ita kuma girman Kai ya hana ta nemi sulhu.

“Kai malam in motar nan ba ta Uban ka bace ka bani key in kuma ta uban ka ce sai ka fada min.

“Muje na kai ki masoyiya sai na fadawa daddy Ni na kai ki.

“Yaushe kayi wannan isar ? ni zan tsaya ka tuka ni ? haka da Kai kamar an roko baka ko iya ganin gilas? da Allah malam ka bani key kaji kana bata min lokaci.

Wayar kaisar ta dauki tsuwwa ya dauka Yana gaishe da daddy.

Ko da ta fahimci da daddy yake wayar sai tayi maza ta fice don ta tabbatar daddy ba zai barta fita ba ita kuma ta sha alwashin fita daukar vedion wakar nan .

“Ya akayi ne kaisar?

cewar daddy.

“Daddy dama nadiya ce zata fita shine tazo karbar key din mota shine nace sai na sanar da kai tunda kace ba zata kuma fita da mota ba.

“Kar ka sake ka bata kaisar bani ita naji inda zataje da sassafen nan .

“Ta fita ai amma bari na bita na kai mata wayar.

yabi bayan nadiya da sauri wacce ta fice tana kiran sarkin gida wanda ya taho a huge don yana kiyaye mutuncin shi akan wulakancin yarinyar.

“Da Allah dauko mota zaka kaini wani wuri.

da sauri sarkin gida ya dauko motar nadiya ta shige suna shirin fita kaisar ya iso yana ce mata

“ga Daddy a waya yana magana.

tayi mishi wani shegen kallo Kafin taja tsaki tana fadin

“Kai da Allah muje sarkin gida kana bata min lokaci.

haka sarkin gida yaja motar a guje suka fice duk daddy yana Jin abunda take fada.

“Daddy sun tafi .

“Babu komai kaisar barta zata dawo ta same ni ai naji abinda ta fada.

Sarkin gida ya kai Nadiya  studion show daga nan kuma suka nufi yankari inda za  ayi album din yayin da nadiya ta sauya shiga da wasu damammun kaya wanda suka fidda mata surar ta aka kuma dauki vedion wakoki irin na rashin tarbiya wanda akayi show yana rungume da ita ana rawa irin ta mawakan turai  . Kaya kala kala ta sauya yayin daukar wakar don haka sai hudu na yamma suka dawo gida bayan ta cire kayan ta maye da hijabi

Daddy Zaune a falo yayin da Fati da kaisar suke karkashin inuwar Umbrella suna karatu

tana shiga falon da daddy ta soma karo wanda ya kira ta ta Isa a tsorace ta zube  a gaban shi.

“Daga ina kike? .

“Daga karbo dinki nake.

“ban hana ki fita ba a gidan nan? wa kika tambaya da kika fita aliyw tace min bata san kin fita ba? .

“Kaisar ya kira ni da safe yace kinje karbar key din mota ban fada miki mota tashi ce ba taki ba? nace a baki waya Ina ji kina mishi tsaki raina Ni kikayi ne ? da wace motar kika fita?.

“Da tawa ce na fita.

“shi kuma sarkin gida mafarkin an ga ya  tuka ki akayi?.

“Ba tare da shi na fita ba daddy karya yake maka .

daddy ya dauki wayar shi yana kiran sarkin gida wanda ya shigo yana zubawa a gaban daddy.

“Ina ka Kai nadiya sarkin gida?

ya juyo yana kallon nadiya wacce take mishi kashedin da idon ta inda ya gane ta tashi.

“tambayar ka nake kayi min shiru.

“Yallabai yankari na kaita kuma daga nan ban san komai.

“tashi kaje sarkin gida daga yau kar ta kuma ce maka zata wani wuri ka kaita ko kofar gida ta gama fita kaji na fada maka? .

“An gama yallabai.

tashi kaje

sarkin gida ya mike ya fice

Haj Aliya tana zaune daddy ya dube ta Yana fadin

“Ko kofar gida kar yarinyar nan ta kuma takawa Aliya zan nemo wani na bashi kyautar auren ta ina ganin wanna shine kawai abinda zanyi na huta da takaicin yarinyar nan.

wani irin duka da nadiya taji ya sauka a zuciyar ta tare da wani bak’on tashin hankali shi ya sa ta gani biji biji aure? take Kara jiyo amon sautin daddy na cewa zai nemo wani ya bashi kyautar auren ta  wane irin wulakanci daddy ya shirya yi mata?

<< Azurfa Da Zinari 12Azurfa Da Zinari 14 >>Azurfa Da Zinari 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×