Skip to content
Part 17 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Tsagera ya fito da kwayoyin ya zuba a kofin gilashin yana tuttula ruwan da yake cikin kwalbar kafin ya dauka yana kaiwa baki yana kurba cike da son jin shi a duniyar gizo yana nunkaya.

Ya dubi Boss da ya tsurawa wuri daya ido tamkar mai kallon TV baya ko kiftawa.

Motar Tero ta shigo gidan a guje tamkar wanda yake daga sama . yaci burki har yana tayar da kura ya fito inda boss yake zaune tare da tsagera.

“Ya aka yi ne my Boss? Ya fada yana zama ya dauko kofi yana zuba ruwan barasar da tsagera ya rage.

“Tero wai ka san  a yau kwana nayi ina mafarkin yarinyar nan? ban san a ina zuciya ta ta adana min ita ba amma dai nafi jin zafin wulakancin yarinyar nan ashe  a duniyar nan akwai wata yarinyar mace da zata cire hannu ta tsinka min mari?

Ya fada yana shafa gefen fuskar shi.

Tero ya ajiye kofin gilashin mai dauke da barasar mai tsada wacce suke sha .

“Wallahi babu yar shegiyar da zatayi maka haka ta kwana lafiya Boss ba a haifi shegiyar ba . Ko ka san a yau na zuga daddy ya sa an sauke tsinannen shugaban can wanda ya mare ni ya zagi uba Na na kyale shi ya kwana lafiya? yanzu daga can office din sa nake tuni aka tsige kafiri har an aika sunan wanda zai maye gurbin shege don haka yanzu zan shiga farautar tsinanniyar yarinyar nan Boss so kawai nake kayiwa shegiya kace kaca har ta dauki ciki sai muga da abinda take takama.

“Kuwa ka gama burge ni Tero don babu abinda nake ji sai marin nan da tayi min ta tofa min yawu a fuska . to idan har ka samo min ita wallahi bayan nayi mata yadda kace zan dauke ta ne mu bar Nigeria don naga karshen rashin kunyar ta inda bata san kowa ba sai ni kadai nayi yadda nake so da ita na tab’a inda nake so na lashi inda nake son lasawa sai na kwakule shegiya kaf kafin na dawo da ita Nigeria sai na ga uban da ya tsaya mata.

Suka fashe da da dariya suna kwartsa ihu tamkar wasu yayen arna saboda muguntar da suka shirya wacce zata hadiye Nadiya har wuya.

“Wani hanzari ba gudu ba gidan su fa yana da tsoro ta yaya za ayi hakan,?

cewar tsagera.

“Ina ne gidan nasu?

Tero ya tambaya don bai san gidan ba.

“Yar gidan iro kudi ce fa baka san gidan nasu da matsara ba?.

“Ai ko yar gidan iro banki ce  yasin yau din Nan sai ta kwana ido biyu ita da bacci sai likita yayiwa shegiya dinki . tashi muje fantami na nemo dark space don ma kar ta shaida fuska ta don uban ta ai yarinyar nan ta zo min makoshi wallahi koma me akayi mata ba zan huce ba .

Suka mike zuwa mall din babban shagon da yayi shuhura a garin bauci

Tero ne mai jan motar wanda yake ta kara biyawa tsagera da boss yadda ya tsani yarinyar har suka iso amma abin mamaki tun kafin su fito idon su ya sauka akan Nadiya wacce take rike da sanda tana makawa wata mahaukaciya da take can daman motar tayi kwance dare dare a saman gilashin motar ga kayan jikin ta fata fata da datti bakin ta kuma sai sakin yawu take wanda duk ya bata gilashin motar.

Da sauri Tero da boss da tsagera suka fito suna kallon abin mamaki

sai kawai suka ga wani wawan duka da nadiya tayiwa mahaukaciyar wanda ya fashe mata kai jini yana tsiyaya har matar ta zamo daga saman ta fado kasa babu alamar rai bare numfashi yayin da jinin da yake zuba a jikin mahaukaciyar duk ya bata jikin ta ya kuma bata saman motar yayi faca face kai ka rantse wata babbar saniya aka yanka.

Suka dubi juna tsakanin Boss da Tero cike da mamakin zafin kan Nadiya .

“Wato yarinyar nan zuciyar ta irin ta kafuran farko ce dubi tana shirin kashe baiwar Allah.

Cewar tsagera wanda ya nufi taron mutanen da suka rufu akan baiwar Allah nan da take kife babu Alamar rai bare numfashi sai ma jinin da yake zuba a kanta.

“Yasin daga nan zan salhe shegiya Boss tunda gashi ma Allah ya takaita min dogon nema shegiya tunda har ta iya wannan wulakancin wallahi ba zan bari ka tausayawa shegiya ba har kwayar fills ma zan samo maka ta yadda zaka kassara tsinanniya marar albarka wannan kam uban ta ya haifo janhurun masifa amma ta gamu da mu yan jeki kya gani duk shegiyar da aka cewa jeki kya gani ba kowa zata gani ba sai mu  .

Jin ance mahaukaciyar bata numfashi har ma wasu suna cewa ta mutu yasa su Tero da boss suka nufi dandazon mutanen inda kuma Nadiya ta sulale ta gudu ta tare napep ta wuce.

Da sauri Tero ya juyo don gudun abinda ya riga ya faru wato bacewar Nadiya sai gashi kuma sama ko kasa tayi musu layar zana tare da batan dabo.

tuni aka taitayi mahaukaciya da wasu mutane suka wuce kaita asibiti teero kuma ya nushi iska da jin haushin saken da da yayi amma tunda ma har an san gidan nasu magana ta Kare. suka shiga ciki suka siyo abinda ya kawo su suka fice Tero yana shan mugun alwashi

*****

Daddy zaune yana kallon tashar arewa 24 inda suke saka wake waken su har suka shuga babin  sabbin wakokin hipop Wanda suka ishi daddy yaja tsaki yana shirin sauya tashar ne wani Abun mamaki ya sauka gareshi  wanda ya shiga shakku Anya kuwa idan shi daidai yake gani ko kuwa gizo idon yake mishi.

Wata matsiyaciyar rashin kirki ce aka sako mawakin yana rungume da wata da idon shi ke nuna mish kamar Nadiya.

Sabuwar wakar show ce wacce aka dauka a yankari tuni kuma ta fita da fitar ta har gidan TV arewa tana yayin ta.

Mama ta shigo ta ga Daddy wanda yabar kan kujera yaje gaban TV yayi tsaye idon shi kyam skan mawakin wanda ta tara wata banzar suma irin ta awilo yana rungume Nadiya har yana hada bakin su suna kiss.

“Daddy lafiya dai?

Mama ta tambaya.

“Yauwa Aliya zo ki taya Ni gani wani abun mamaki nake gani .

ya fada yana mata yarinyar da ke kwance jikin mawakin marar albarka wanda kayan jikin shi ma tamkar ba na musulmi ba ga suma marar tsari akan sa yana kuma ta shafa jikin Nadiya.

Mama ta kafawa TV idon ta tuni kuma ta gano abinda Daddy ya gano.

“Inna lillahi wa inna ilaihir raju un wannan ai nadiya ce Daddy.

“Anya kuwa Aliya ,? bana zaton itace sai dai ko kama Nadiya yar musumi da wannan lalacewar?.

“Wallahi itace Daddy ai in ta bacewa gani na na zama sha ka tafi kenan da dai fati kace to zan sha rantsuwa don bata da wannan tunanin amma Nadiya ko shakka babu wallahi itace.

“To Ni dai ina cike da shakku ne don kar na yanke hukunci yasa na matso sosai tunda kuma kin fidda ni shakku alhamdulillahi yanzu har yarinyar nan ta san irin wannan lalacewar? yaushe ma ta samu sararin fita wannan masha ar? .

“In ka duba sosai a yankari ne akayi vedion ta Ina akayi hakan ban sani ba ina can na shanya baki Ina bacci?

cewar haj Aliya.

Sai kuma ta juya da sauri ta nufi dakin su nadiyar ta figo ta suka iso falon ta kuma dire ta a gaban TV n tana fadin

“A gidan uban wa kika san wannan wayewar da lalacewar ?  wannan ai tabad’ewa ce Ashe ni ban sani ba duniya na can na zagi na akan aninda bani da sani ko alhaki? yanzu wannan tayi kama da yar musulmi a tsarin tarbiya da addini?.

Nadiya ta dubi TV tana kallon wakar da show yake rerawa yana kuma rungume da ita da kayan marar albarka wanda duk suka bayyana surar ta.

“Ni kam a yau nayi kaico har fiye da yawan shekarun iyaye na wallahi wannan yarinyar ba mutum bace.

Sai mama ta rufe nadiya da duka tamkar zata aike ta kiyama saboda takaici tana dukkan nata tana kuka .

“Wace irin jarabawa ce na hadu da ita ni kam?.

Daddy ya rike hannun mama yana fadin

“Kyale ta Aliya muyi mata ADDU A Allah ya shirye ta Amma babu abinda dukan zai mata .

Mama ta zauna tana rera kuka tana fadin

“Astagfurullah Allah astagfurullah Allah mun tuba

Daddy ya dubi Nadiya yace ta tashi ta basu wuri

ta mike da sauri tana Jin da ta sani akan sakin wakar da show yayi da ta san zai sake ta a yanzu da bata barshi sakin ba Amma kuma bata ji tayi nadamar hakan ba

“Gara da Allah yasa kayi hikimar bayar da sadakar auren yarinyar nan Daddy tunda har ta iya wannan bad’alar ta rungume rungume da katon Allah ta ala bana ko shakka zata iya yin film din banza tunda har ta san tayi irin wannan shigar suna rawa har da tsotsar baking juna  Daddy meye ba zai faru ba? don Allah ka rage kwanakin da ka sanya sati biyu yayi min yawa Daddy yarinyar nan ta fita a kaina wallahi .

“Nima naga dacewar rage kwanakin Nan Aliya na kuma rage su rana irin ta yau zan daura auren yarinyar nan na mikawa maccid’o su wuce Niger ko hankali na zai kwanta don a yanzu ban yarda da yarinyar nan ba . tuni kuwa shirye shirye suka koma na rana irin ta yau

Babu wani shiri da Daddy keyi bare kuma Ango maccid’o shiyasa bikin babu wani da ya dan ga lokacin sai fa da Daddy ya sanarwa maccid’o ya rage sati daya a yadda yadda ya saka

Keena da lubabatu da safina suka iso gidan Don kwana biyu  Nadiya bata zuwa ko ina mama ta kasa ta tsare

Keena ta dube ta tana fadin

“Wai kawata Ina motar ki ne ita nazo aro don ina da biki na kece raini ne ke kuma yanzu naga kin zama wata matar kulle duk wuraren shakatawar ma kin daina zuwa ko kin koma islamiyar ne,?.

Safina ta kyalkyale da dariya tana fadin

“Haba dai islamiya hutu dai ke kin san mutuniyar yar hutu ce.

“Ke ni kuwa na kalli sabon album din show a arewa 24 mutuniyar kinyi wuta fa wallahi ba karya sai maganar rigar Nan taki ake.

Nadiya taja tsaki tana fadin

“Luba ai ni ban san abinda nayiwa mama da Daddy ba . yanzu fa ko waje bani da damar fita sai an sani wulakanci kala kala mota kuwa ai Daddy ya karbe ta ni na rasa ma me yake damu na wallahi bakin ciki ishe ni.

“Yo ke Kuma zaki zauna ne haka ayi ta miki wulakancin sai kace ba yar zamani ba? halan don sunga wakar ku da show ne ?.

“Bama shi bane keena wai kin san aure ma suke shirin yi min da kaskantacce irin maccid’o mai gadin kofar get din gidan mu?.

“La ilaha illallah Muhammadur Rasulullah sallalahu alaihi wassalam.

Suka hada baki su duka suna fada cike da nuna alhini da tashin hankali.

“Wai auren wasa ne za ayi muku ko kuwa dai mafarkin hakan kikayi?.

“Uwar ki keena ya Ina fada miki wulakancin da ake shirin yi mini kina fadar wani MAFARKI?.

“To ai abin ne da mamaki ace za ayi miki irin wannan auren na tozarta duk mazan duniya a rasa wanda za a baki sai mai gadin kofar gidan ku ke kuwa wace irin lalacewa ce ta same ki haka?.

luba tana rike da baki safina tace

“Ai laifin ki ne Nadiya kuma sai ki zauna ki rungume hannu bakiyi wani motsi ba? Ai ba zaki xuba ido a cuce ki ba sai ki amo mafita.s

“Wace irin mafuta zan samo luba?.

“Yauwa idan har kika tabbatar da gaske suke Shirin aura miki mai gadin kofar gidan ku a ranar da aka daura auren sai kawai ki fice kiyi tafiyar ki kiyi kwana biyu ko uku ana neman ki sai kin tabbatar da maganar ta mutu zaki bayyana ina me tabbatar miki su da kansu zasu neme ki ba ke kadai ce suka haifa ba?.

Nadiya tayi murmushi tana gyada kanta tana fadin

“Wallahi ni kadai ce Yar mama da Daddy wmma basu bari na nayi yadda nake so  .

“Kece baki so kiyi yadda kike so ba ga Alama waccen agolar tafi ki iya manuba shiyasa tafi ki fada babba.

“Ke ba agola bace yar yayan Daddy ce ta dai iya munafunci da tsugudidi ga kwadayayya ce haka ma iyayen ta makwadaita ne komai Daddy ne yake musu kaskoki ne.

“To kin dai ji wallahi idan kika bari aka aura miki wani kaskantacce irin mai gadin gidan ku ai kin fado wallahi wai wanene ma Ango daga cikin su wannan mai wuyan kamar yasha ruwan zafi ko mai jajayen idanun?

Cewar keena.

“Mts duk ba su bane wani fa shirgege na nan mai manyan hantuna mai kama da an aiko mishi sakon mutuwar iyayen shi biyu.

Safina da lubabatu suka kyalkyale da dariya suna tabowa keena na fadin

“Lallai kinyi market wanna kam ai da ganin shi banijare ne ko?

Nadiya ta ja tsaki tana fadin

“Koma dai uban waye ni ai in ba show ba wallahi sai rijiya mai kwalabe kuma keena kin bani data wallahi dama tuni zuciya ta take fada min na gudu kawai amma sai nace to ina zanje?.

“Kizo gidan mu mana.,

cewar keena da take duban Nadiya.

“Ai fa an gama keena barni da su ko ban zo gidan ku ba zan nufi wurin show kawai nayi zamana har ranar da su Mama zasu saduda.

Keena ta ce

“Kar kije wurin show kizo gidan mu kawai kiyi zaman ki amma naji miki zafin rasa motar nan ke fa kadai ke da irin ta a garin nan?.

“Bari bani haushi keena .

suka mike da shirin tafiya saboda shigowar Fati wacce take musu sannu da zuwa

Nadiya ta mike don tayi musu rakiya inda safina ke fadin

“Mu kam a nuna mana angon mu gaisa kafin muzo karbar kudin yan mata .

“Kudin yan matan uwar ki.

cewar Nadiya wacce tayi zagin a fussce .

suka nufi motar keena da suka zo cikin ta inda kaisar ya fito don suyi bitar karatu shi da fati sai kawai keena taga kaisar shima kuma ya gansu alamma yayi kamar bai gansu ba.

“Ke gayen can me ya shigo dashi gidan ku?

cewar keena wacce tun kallon farko da tayiwa kaisar ta ji ya sace mata zuciya.

“Dan Aikin GIDAN mu ne wani abu ne mayya?

cewar nadiya wacce ke jifar keens da wani shegen kallo.

“Alhamdulillahi wallahi tun da ido na ya hango min gayen nan zuciya ta ta yafe kowane namiji tunda ma har aiki yake a nan gidan ni kam ciwo na ya warke don haka zan dawo yakin soyayya sai naga abinda ya turewa buzu nadin sa wallahi.

<< Azurfa Da Zinari 16Azurfa Da Zinari 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×