Skip to content
Part 25 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Distinguish Mukhtar Biro kuwa kullum Suna mutuware shi da haj Laila suna tashe da gawar abdulhameed suna gurzar kuka

Haka zasu kare wuni a mutuware su dawo gida kamar yanzu da suka dawo gida ana dab da Kiran sallar magaruba inda mai gadin kofar gidan distinguish Mukhtar Biro wanda aka turowa da firiskoton kotun kawo sammaci ya kuma bawa mai gadin shine suna shigowa ya auna a guje yana bude musu kofar ya kuma basu takardar sammacin

Distinguish ya karbi takardar yana budewa sai kawai yaga sammacin ya dubi mai gadin yana fadin

“Waye ya kawo takardar nan?

da sauri ya bashi amsa da cewa firiskoton kotu ne

Distinguish Mukhtar Biro bai kawo akan case din su day iro bane sai ma wani hasashen da yayi don haka yaja tsaki yana wurga takardar sammacin a cikin mota saboda ganin kowace kotu ce wato babbar kotun jihar wacce kanin distinguish din takardar sammacin ta fito daga hannun shi sai yayi murmushi don koma waye wannan a k’asa yake .

ya shiga gida yayin da tuni Haj laila ta wuce cikin gida

Ranar litinin itace ranar shiga kotu don haka tuni Kaisar ya gama tabbatar da komai har da lauyan su wanda shima ya gama saita komai

A can kotun suka iske Nadiya jami an tsaro na tsare da ita don haka Haj Aliya da Fati da Kaisar da Daddy duk sun zo har da Yaya halilu da alabo duk sun hallara a kotun shima Alkalin ya iso wanda bai ma iso ba shine distinguish Mukhtar Biro don sai sha biyun rana yazo inda yazo yaga dan uwan nashi ne Alkalin da zaiyi shari ar a matsayin  na chief judge a babbar kotun don haka sai distinguish Mukhtar Biro yayi murmushi mai ciwo don duk kwanakin babu abunda Yake ji irin tazarar da mutuwa ta shata musu layi tsakanin sa da abdulhameed ba  shiyasa maganar farin ciki babu shi a tare da shi sai dai kuka

Shari ar da akeyi ta wani mutum ce da matar shi take K’ara akan munafuntar ta  da yayi yayi auren sirri bata sani ba  shine ta kawo shi kara akan ya biya ta bashin da take binsa tunda har yana da kudin da zaiyi aure bai sanar mata ba . shine fa shari ar ta dauki lokaci har karfe biyu inda Alkalin ya dage shari ar har zuwa sati biyu masu zuwa.

Aka soma karanto karar su alh iro GIDAN KUDI wanda sai a lokacin distinguish Mukhtar Biro ya lura da mai laifin da aka shigo da ita wato Nadiya ya kuma soma daga kanshi don ya hango alh iro sai kuwa gashi ya gano shi can tare da alh sule.

Mamaki ya kama distinguish Mukhtar Biro akan kokarin su na kawo shi K’ara . suyi mishi laifi kuma su Riga shi kuka da kawo k’ara ? to sun san yadda suke da Alkalin ne ma? ai kuka suka kawo gidan mutuww domin kuwa zasu fadi k’asa warwas ne .

Kafin ya gama jerawa kanshi tambayoyin ne yaji firiskoton kotu yana karanto karar da alh sule da alh iro suka shigar da  karar distinguish Mukhtar Biro wanda yake ikirarin kashe ahalin alh iro GIDAN KUDI saboda yarsa ta kashe mishi dan shi .

Alkalin ya dubi firiskoton da sauri don shi kam bai san da wannan maganar ba ta kashe Dan dan uwan nashi a yaushe akayi hakan?. kafin yace idan wanda ake kara yana kusa ya fito shima wanda yake kara ya fito suyi wa kotu bayani.

Tuni kuwa lauyan da Kaisar ya daukar wa Nadiya ya fito ya tsaya a gaban kotu ya soma rattaba bayani

Ko su daddy basu san Kaisar ya daukar wa Nadiya lauya ba sai dai ganin sa sukayi

Distinguish Mukhtar Biro kuwa wayar shi ya dauka yana Kiran lauyan shi wanda ya bukaci gani a yanzu yanzu ba a rufa minti talatin ba kuwa ya karaso

Lauyan Nadiya ya soma gabatar da kanshi da sunan shi kafin ya koma ya zauna

Alkali ya dubi dan uwan shi yana radin

“Ko wanda ake kara yana da Lauya?

tuni lauyan na distinguish ya mike yana gabatar da kanshi gaban kotu 

Alkali ya soma magana akan karar da alh Sule da alh iro suka shigar akan baraza da Rayuwa da distinguish Mukhtar biro yakewa alh iro da bindiga yana fadar zai kashe shi ya kashe ahalin sa saboda yarsa ta kashe mishi dan shi don haka ko lauyan wanda ake k’ara yana da abin cewa.

Lauyan distinguish Mukhtar Biro ya mike yana fadin

“Kwarai kuwa ya mai shari a ai mai kara ma yayi kokari matuka Gaya da yin wannan riga malam massalaci da karfin hali . yarsa ce tayi kisa ta kashe dan wanda suke kara kuma su kawo shi Kara? to a jinjina musu gaskiya shi kuma a me suke so kotu ta yanke mishi hukunci? ga yarsa nan itace ta kashe mishi dan sa kuma saboda rashin adalci ace sun kawo karar sa? to shima yana shigar da kara akan jinin dan sa Abdulhameed.

“Objected my lod lauyan Wanda ake kara yana wuce iyakar sa.

“Zai kiyaye

cewar Alkalin

Lauyan distinguish ya dubi Alkalin yana fadin

“Ya mai shari a ina so kotu ta bani dama nayiwa mai laifi tambayar

“An baka

Cewar Alkalin

Lauyan distinguish ya matsa inda Nadiya take wacce hawaye kewa zarya a fuska yana fadin

“Meye sunan ki?

“Sunana Nadiya Ibrahim.

“Shekarun ki nawa?

“Shekara ta ashirin da uku

“Ko kin san Abdulhameed Mukhtar Biro?

“Eh na san shi

“Meye alakar ku da shi?

“Bani da wata alaka dashi illa mun hadu kamar sau uku a wurare daban daban yace yana sona ni kuma na ce bana son shi .

“To daga cewa yana son ki kin ce baki son shi shine kika kashe shi,?.

“Objected my lod lauyan wanda ake kara yana cin mutuncin wanda ake zargi ya daina keta alfarmar ta da sunan tambayoyi.

“A kiyaye

“To nagode ya mai shari a

Ya sake duban Nadiya yana fadin

“Ko kina da labarin mutuwar shi Abdulhameed Mukhtar Biro?

Ata amsa da

“Eh na sani

“Ana zargin kece wacce kika kashe abdulhameed  me kika sani a Kai?

“Hakika ni na kashe shi

Ta fada kanta tsaye babu kwana don lauyan ta yace kar ta karyata tace itace ta kashe shi don kuwa tana da babbar hujja a hannun ta.

Haj Aliya da alh iro da yaya halilu da alabo da fati har da Kaisar sai da kansu ya sara jin amsar da Nadiya ta bayar ta cewa itace tayi kisan Abdulhameed Mukhtar Biro

Daddy ya dafe kirji yayin da alh sule ma ya shiga tashin hankali.

“To alhamdulillahi Nadiya Ibrahim kin kawo karshen komai tunda baki bawa shari a wahala ba kin amsa kece kika kashe abdulhameed to babu wani sauran ja sai a barwa mai shari a damar yankee miki hukunci.

Da sauri lauyan Nadiya ya mike yana neman izinin magana ga mai shari a ya kuma bashi.

“Ya mai girma mai shari a lauyan Wanda ake kara Bai kamata ace ya rufe babin tambayar shi ba tare da yaji dalilin da yasa Nadiya tayi kisa ba shin dama ana kashe mutum babu dalili? me ya hada Nadiya da abdulhameed har ta kashe shi ? shine abinda ya kamata barrister ya duba amma ni bari na tambayar mishi  abinda ya manta bai duba idan mai shari a ya bani dama.

“Kotu ta baka dama

cewar Alkalin mai shari a

lauyan Nadiya ya matsa kusa da ita yana fadin

“Nadiya a lokacin da Abdulhameed yace yace yana son ki kika ce ba kya son shi sai kuma me ya faru a tsakanin ku shin kun sake haduwa ne a wani wuri?

Nadiya ta share hawayen ta tana fadin

“Gaskiya bamu sake haduwa dashi ba bayan haduwar da mukayi kamar sau uku.

“To ta yaya kuma kuka hadu gashi kince ke kika kashe shi?.

“Eh akwai wani dan uwan sa gashi a can

ta fada tana nuna mustafa Tero da hannun ta tana fadin

“Wancan da nake ganin su a tare shine kwanaki biyu da suka wuce ina tsaye a bakin hanya sai kawai naji an jawo ni mota da karfi wani ya dora min wuka a makoshi suka kaini wani gida a makera G R A inda a can na ga abdulhameed wanda ya ke cewa shine ya saka a dauko mishi ni don ya ga abinda nake takama dashi da zaice yana sona in wulakanta shi don haka ya saka wanda suka dauko ni suka fince min kaya har ya keta min haddi ni kuma na soka mishi wuka.

“Wanna sharri ne objected my lod har ta fara gogawa wasu sharri?

cewar lauyan distinguish wanda ya mike yana zanzana.

Lauyan Nadiya yace yana son ganin Mustafa Tero ya kuma fito zuwa inda ake tsayawa yana kallon mahalarta kotun .

Lauyan Nadiya ya dube shi yana fadin

“Yaya sunan malamin?

ya amsa da sunan shi Mustafa.

“Mustafa ko ka san wannan ?

Ya nuna Nadiya

“Eh kwarai na san ta .

“Me ka sani tsakanin ta da dan uwan ka abdulhameed?.

“Eh to na san dai yana son ta ita kuma tana mishi wulakanci ta mare shi ta kuma tofa mishi yawu a fuska da maganganu iri iri dai  babu wanda bata fada mishi ba .

“Kenan dai tayi mishi wulakancin kamar yadda ta fada?

lauyan ya tambaye Tero .

“Kwarai kuwa tayi mishi.

“To maganar da tace har da kai a cikin wanda suka dauke ta a mota zuwa wani gida a makera G R A shima duk anyi hakan kenan?.

“Eh .na am?

ya fada yana in ina.

“Objected my lod lauyan mai laifi yana son zurma wanda yake tambaya don meye zai rika yi mishi tambayar wuce hankali.

“A kiyaye

cewar mai shari a

Lauyan Nadiya ya amsa yana juyawa ga Tero yana fadin

“Malam Mustafa da gaske ne Nadiya ta kashe abdulhameed a gidan mahaifin sa dake makera G R A?.

Da sauri Tero ya amsa da cewa

“Kwarai kuwa ta kashe shi a can ne.

“To wa ya gayyace ta gidan ko dama tana zuwa?

Tero ya gano ramin da akayi mishi sai kuma yayi shiru.

“Napep ce ta kai Nadiya gidan ko kuwa wani daga cikin yaran abdulhameed?.

“Eh da motar gida ne ba napep bane gaskiya don Bata tab’a zuwa gidan ba .

“Da gaske kenan an kamo Nadiya ba don ta shirya ba?

Tero yayi shiru har lauyan ya kuma maimaita abinda ya fada ya amsa da haka ne.

“Lokacin da Al amarin ya faru kana gidan ko baka nan?

Tero ya amsa da baya nan sai da ya dawo ya tara’s da kisan kuma bai iske Nadiya ba.

“Su waye wanda suka sukayiwa Nadiya fit da kayan jikin ta?

Tero ya amsa da cewa  baya nan akayi amma dai yasan su kilin ne.

“Mustafa ka san abunda ake nufi da domin Allah?

lauyan ya tambaye shi ya kuma amsa da eh ya sani

“To ka fada min domin Allah har da kai a cikin wanda suka dauko Nadiya a mota ?.

Tero yayi k’asa da kanshi yana Fadin

“Eh har dani da su kilin saboda nayi alkawarin kawo mishi ita don ya rama wulakancin da take ta mishi  kuma wallahi itace ta kashe abdulhameed ina da shaidar hakan a cikin CCTV camera akwai yadda ta kashe shi da wukar don kotu ta fita a zargi don haka ina so na kawo CCTV camera din a nan na nuna yadda tayi ta kashe shi.

Lauyan Nadiya ya dubi Alkali yana fadin

“Ya mai girma mai shari a shaidu da hujjoji sun bayyana akan Nadiya ce ta kashe abdulhameed amma tayi kisan ne don ta kare kanta ina ganin a bada damar kawo CCTV camera din don ta Haka ne Alkali zai bawa kowane bangare hakkin sa .

Alkali yayi Rubutu a takardar shi yana duban Mustafa yana fadin

“A kawo CCTV camera din gidan a gobe don itace shaida ta karshe da zata zamo yankee hukunci

Alkali ya buga gudumar sa akan wani abu dake gefen sa kafin mahalarta kotun suka hada baki wurin fadin kotuuiu. Inda kowa ya soma ya soma mikewa alkali ma ya fice daga kotun  aka wuce da Nadiya zuwa gidan dutse saboda Alkali  yace a mayar da iita sai gobe in za a sake zama .

su Sule da alh iro da haj Aliya ma suka mike suka fice amma distinguish Mukhtar Biro ya kasa tashi daga inda Yake zaune Mustafa yazo zauna kusa da distinguish wanda Yake hararen Mustafa don ya cika mishi ciki matuka gaya da in valid amsar da ya bayar sai kawai distinguish ya kifawa Mustafa mari cike da fusata yana nuna Tero da yatsa amma ya kasa cewa komai.

<< Azurfa Da Zinari 24Azurfa Da Zinari 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×