Skip to content
Part 28 of 99 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Ya taho a mota yayin da wayar shi ke ta faman burari inda yaga matar shi Haj laila tayi mishi missed call fiye da goma Sha biyar da yake cike yake bai bi ta kan wayar ba yaki dauka ya wuce office din gwamna

Lokacin da ya koma gida Kuma bai iske Haj Laila ba kasancewar su yantaccin  mata yasa bai neme ta ba don ya san kiran da tayi ta mishi wani abun sai bai bi ta kanta ba ya shiga laluben mataki akan Sufi da irin wulakancin sa

Haka ya raba dare kuma har yanzu babu haj laila babu dalilin ta amma bai damu ba saboda yasan tana da damar ta

Washe gari kuwa karfee bakwai da rabi su daddy da Kaisar da alh sule da Yaya halilu suka dira filin jirgin Sir abubakar tafawa balewa kafin takwas sun daga samaniya zuwa birnin tarayya Abuja

Karfe takwas da arba in da biyar suka sauka Abuja amma a can suka iske distinguish Mukhtar Biro tare da manyan Alkalai wanda tuni aka gama tsara komai Wanda za ayi babu jeka ka dawo

Karfe Tara daidai aka shiga kotu yayin da Kaisar ya zubawa Nadiya idanu wacce ta gama futa a hayyacin ta tayi duhu tayi rama koman ta ya hargitse tamkar ba Nadiyar nan yar gaye yar kwalisa ba idanu kozai kozai hannu da kafa kuma cike da sasari ta sha dauri tamkar goro

Alkalin mai shari baba tunde unwela ya zauna akan kujerar sa yana sanye da kayan shari a da hular gashi tare da gilashin ido fari. Baki ne tutturna wanda kallo daya zakayi mishi kw gane daga kabilar da ya fito wato yoruba

Ba a bawa su Daddy damar daukar Lauya ba shiyasa aka yi abin a late don haka wani kwararren lauya ne ya fita don yiwa Nadiya tambayoyin ya fara da tambayar sunan ta ta sanar da shi Nadya ibrahim kafin ya soma tambayar ta abdulhameed Mukhtar da irin alakar dake tsakanin su

ta sakeyiwa kotu bayanin da tayi a kotun bauci na haduwar su da abdulhameed da irin yadda ya faru na wulakancin da tayi mishi da kuma shi yadda ya saka aka dauko mishi ita da yadda su keso suka cire mata kaya naked har zuwa inda Abdulhameed ya shige ta ita kuma ta soka mishi wuka.

Mai shari a baba tunde yayi rubutu a takarda yayin da lauyan ya juyo Yana magana cikin harshen turanci yake fadin mai laifi ta amsa laifin ta ita ta kashe abdulhameed Mukhtar don haka yana neman mata afuwa yayin yankee hukunci tunda bata batawa shari a lokaci ba

Abu ne da dama an gama tsara shi  shiyasa babu wani bata lokaci aka yankewa Nadiya hukuncin kisa ta hanyar Rataya tunda ta amsa da bakin ta itace ta kashe abdulhameed Mukhtar Biro.

Kaisar da yayi tsallen uwar kuturwa jin an yankewa Nadiya hukuncin kisa ya tsaya a gaban kotu yana fadin

” Opjectin My lod isome body can’t Replace criminal?

duka aka waigo ana kallon Kaisar da mamakin tambayar shi kafin mai shari a ya dube shi yayi murmushi yana fada mishi ba a yin hakan sai dai ana iya nema musu sulhu a gaba ko a dauka ka k’ara amma wanda bai da laifi ba zai karbi hukuncin mai laifi ba sai in ya gudu ne ka zama grantors nasa ne.

Da sauri Kaisar yace

“forgive me my lod I’m criminal Nadiya ibrahim is not criminal she walke to shadow to dangerous.

Da sauri Nadiya ta dubi Kaisar jin irin amsar da yake bayar wa.

“What do you say?

cewar mai shari a baba tunde yayin da kallo ya koma sama wai shaho ya dauki giwa .

Hatta alh Sule da yaya halilu a firgice suka mike cike da rudani yayin da daddy kuma ya dafe kanshi yana mamakin wane irin so Kaisar yakewa Nadiya da har ya karbar mata haddi.

tuni kotu ta kaure da haya hayar kafin mai shari a ya buga wani kwagiri akayi shiru inda lauyan nan ya mike yana duban Kaisar yana tambayar shi ta yaya akayi hakan?

Kaisar ya dubi su Daddy da su alh Sule da yaya halilu yana juyo da ganin shi ga distinguish Mukhtar Biro yana fadin

“Na san abubuwan da sukayi ta faruwa tsakanin Nadiya da Abdulhameed duk da ban san ta yaya suka hadu ba amma na tab’a gani sau Daya a gold and silver inda suka zo shi da wancan Gayen

Kaisar ya nuna Mustafa ya na fadin

“A ranar ne kuma naga ta mari Abdulhameed har ta saka aka kama wancan.

ya kuma nuna Mustafa Wanda ya tambaya anyi hakan ? ya kuma amsa da kwarai anyi hakan.

Lauyan ne ya kira mustafa Tero ya iso gaban kotun Yana tambayar shi .

“Kun tab’a zuwa gold and silver ne kuka hadu da Nadiya?

Mustafa ya amsa da kwarai kuwa anyi hakan kuma zai iya tunaww da fuskar Kaisar din shima ya tab’a ganin shi a gold and silver.

“Da gaske ne kuma Nadiya ta ari marigayi abdulhameed har ta saka aka kama ka Kai din?

Lauyan ya tambaye Mustafa Tero ya kuma tabbatar mishi da anyi hakan babu karya .

“Kenan dai duk abinda Kaisar ya fada zai iya zama gaskiya?.

Distinguish ne ya amsa da cewa kwarai kuwa tunda lokacin da aka nemi yarinyar shi Kaisar ne ya boye ta da yaji za a gurfanar da uban su ya fiddo ta sai yanzu ya gano lallai akwai makirci a cikin lamarin yaro Kaisar.

“Kaisar yayi wani murmushi mai  ciwo yana fadin

“wannan kadai na sani  ban san sauran abinda ya biyo bayan hakan ba  sai na ranar da na taho daukar Nadiya naga motar wannan  ya Kuma kuma nuna Mustafa Tero wani  ya ja Nadiya cikin motar da karfin tsiya sun sheka a guje abinda ya sa ni bin bayan su har gidan da suka kai ta inda na samu da kyar na samu shiga ciki na Kuma samu Abdulhameed yana keta haddin Nadiya ni kuma na soka mishi wukar har ya mutu don da mamaki ta iya kashe shi  don mace ba zata iya jarumtar soka wuka har ayi kisa ba kuma da Abdulhameed yana raye zai tabbatar muku da ni ne na kashe shi ba Nadiya ba .

Distinguish Mukhtar Biro ya mike yana nuna Kaisar yana fadin

“Shiyasa ka boye yarinyar nan lokacin da ake neman ta kayi gum da bakin ka sai  da nace za a tsare uban ku a madadin ta shine ka ce zaka kawo ta ka kuma kawo ta? lallai na yarda Kaine ka kashe abdulhameed tunda ka boye yarinyar nan da tunanin ko zaku tsira .

Kaisar yaji dadin yadda karyar da ya shirga ta zauna daram tamkar an zana .

“Kayi hakuri ranka ya dade nayi zaton za a duba mace ce ayi mata sassauci shiyasa ban fadi gaskiya ba don haka a hada laifuka na duka biyun ayi min hukuncin su da na kisan da na boye gaskiya da nayi .

Da sauri Daddy ya mike yana fadin

“Wannan yaron fa karya yake bai san komai akai ba kuma yana da ciwo bashi da cikakkiyar lafiya.

“A a daddy ka bari na fadi gaskiya lafiya ta lau  yau laraba sha shida ga watan biyar kuma nan Abuja ce ba bauci ba ka yarda lafiya ta lau Daddy? ba bari kawai na bayyana gaskiya in na bari aka kashe Nadiya na zalunce ta tunda na san ba ita tayi laifin da za ayi mata hukunci kanshi ba.

Tuni kotu ta hargitse har tana kiran likitan kwakwalwar ta ya kuma duba Kaisar lafiyar shi lau don haka aka nemi Kaisar da ya biya Nadiya  kudin tara da bata sunan da yayi mata har aka tsare ta na tsayin lokaci inda shi kuma aka maida shi makwafin Nadiya tare da biyan kotu Tara ta wahalar da shari a da yayi musamman kotun bauci da ta yankee hukunci a bai bai saboda boye gaskiya.

Kaisar ya amsa da zai biya yana kuma neman afuwar kotu akan abinda yayi

Kan kace me? An kwance Nadiya daga sarkar da take an mayar ga Kaisar abinda yayi matukar firgita daddy ganin ana shirin wucewa da Kaisar gwarumfa.

Da sauri ya rike Kaisar din yana kuka magana yake so yayi amma ya kasa saboda tashin hankali da firgici .

Ganduroban ya ja hannun Kaisar suka wuce kukan daddy ya tsananta tamkar zai shide .

Haka kotu ta tashi kowa yana shurin ficewa amma daddy kuka yake tamkar zai hadiye zuciya ya mace.

Kuka daddy yake riris irin kukan nan na sallamawa Rayuwa .

Yaya halilu da Alh Sule ma sun kasa cewa dashi komai bare suce yayi hakuri ko wani ban baki da magana.

Da sauri daddy ya mike yana duban alh Sule da yaya halilu yana fadin

“Yanzu yaya halilu da Kai Alh Sule kuna kallo yaron nan ya daurawa Kansa janhurun masifa amma a kasa samun wanda zaiyi wani Abu saboda Allah? to meye amfanin tahowa tare da ku zaku barni ni kadai Kuma a kasa fahimta ta? ta yaya kuna kallo yaron nan zai jawa Kansa masifa saboda so ya rufe mishi ido ya kasa gane alfarmar sa da amfanin zaman sa a duniya ? wallahi tallahi bai san komai Akan abunda ya fada ba ko ya sani karya tafi yawa a cikin abinda ya fada . A tare aka kawo mu da shi kuma fati ta fada min Nadiya ta tafi rakiyar kawayen ta ne da aka neme ta aka rasa kuma ai ni da ku  ai duk munga yadda Al Amarin ya faru a CCTV camera ta ina wani Kaisar yazo yayi kisa? kuma bayan Nadiya da bakin ta ta amsa itace ta kashe yaron suma masu shari ar kamar dai basu da hankali da tunani?.

Ganin yadda daddy ya fututtuke yana zuba masifa ne yasa Alh Sule ya dafa kafadar shi yana fadin

“Iro yaya zamuyi bayan yaro ya gama dab’awa cikin sa wuka? ya fa fadi abinda yayi daidai da Al amarin nan kai da kanka kace ba ya da lafiya duk don ka kautar da maganar tashi amma ya zana maka rana kun mako ya kuma tabbatar da lafiyar sa kalau an kuma auna shi lafiya lau to iro me kake so muce bayan ya gama damalmala abun,? Idan har akwai mai laifi a cikin hakan to Nadiya ce don nasha mamaki da tayi gum da bakin ta bata ce komai. A yadda naga hankalin Kaisar y tashi Akan tsare ta da yadda yake shiga da fita akan ta na zaci ba zata iya bari ya cutu ba amma tana ji tayi shiru abinta anya kuwa mutane suna da burin mayar da alheri da alheri?

Yaya halilu ya gyada Kai yana fadin

“Sule barni da wannan kayan bak’in cikin Kaisar bashi da hankali ai in so cuta ne to hakuri magani ne . wane irin so ne wannan wanda baya duban gabas? wace rana wannan tsinannen son ya tsinana mishi bayan bai mori komai ba sai ta Rayuwa da yayi? Ita kuma shegiyar yarinyar nan da tayi shiru me take nufi ne? tayi laifi haddi ya hau kan wani ? .

Daddy ya soma dauke kwallar idon sa da tissue paper yana jin ba zai iya bari a kashe Kaisar akan abinda ba shi ne yayi ba ba zai ci amanar yaron ba.

Nadiya suka hango ta taho cikin kayan ta na gida da tazo da su akasin na gidan sarkar da aka sauya mata zuwa nata na gida

Daddy da suke cikin mota suka hango Nadiya tana nufo su alh iro ya tsura mata ido Yana Jin bai tab’a jin ya tsani yarinyar nan ba sai ayau da yake ganin rashin adalcin da ta shuka

cike take da murna da farin cikin samun yancin nan na fansar yancin da Kaisar yayi mata

Daddy ya ji hawaye yana shirin fito mishi amma yayi maza ya goge su daidai da nadia tayi sallama ta bude motar ta shige .

Daddy ya dauki wayar shi yana kiran wayar lauyan da Kaisar ya daukar wa Nadiya amma baiji wayar ta shiga ba

Ya dubi Alh Sule yana bashi key din motar yana fadin

“Ba zan iya komawa gida a yanzu ba Alh Sule sai dai kaja yaya halilu ki koma gida amma ni kan sai naga abinda Allah zaiyi ba zan iya barin Kaisar a cikin wannan halin ba in har haka ne ni ne zan fanshi Rayuwar Kaisar ni nafi kamatar kashewa ba shi ba nine zan mutu.

Alh Sule ya bude motar ya fita yana fadin

“Ai komaw bata kamace mu ba iro mu koma gida mu bar Kaiser a nan ? wallahi ba zai yuwu ba bari na kira alh garba ya hada ni da wani Alkali a nan Abuja muga yddaa za ayi

Ai kuwa Alh Sule ya kira wani abokin shi Alh garba ya tura mishi lambar wani babban Alkali suka kuma neme shi ya fada musu inda zasu same shi a garki don haka suka tashi mota suka nufi garki gidan alkali wanda ya tarbe su da tarba ta mutunci bayan gaisawa suka Rattaba mishi halin da ake ciki da kuma kuskuren da Kaisar yayi akan abinda bai da Sani akan shi ya daurawa kansa musifa

Alkalin ya dube su yana fadin

“Da dai ace bai furta da bakin shi cewa yayi ba to da an san abinyi amma gaskiya indai har ya amsa da bakin shi to magana ta kare tunda ma har wata ce ake zargi ya wanke ta ya bayyana gaskiya to kar ku wahalar da kanku.

Daddy yayi shiru cike da tashin hankali kafin yace

“Ranka ya dade yanzu Babu wani Abu da za ayi? don Allah a taimaka mini wallahi yaron bai san komai ba ya dai fada ne kawai wallahi ko me ba zai gagara ba a duba don Allah ranka ya dade wallahi yaron nan amana ce s gare ni .

“To bari na kira daga can kotun Alkalan idan akwai abinyi sai ayi.

nan take ya kira waya yana neman alfarma akan yaron da ya amsa laifin da ake zargi kan yar uwar sa ko za ayi wani Abu?.

“Maganar nan an rufe babin ta rana kawai za a saka ta kashe yaron nan ta hanyar rataya tunda ya fadi shine yayi kisan Abdulhameed Mukhtar Biro don haka an gama Rattaba hannu a kan case din sa har anyi off din sa don haka babu wani abinyi sai dai ko a saurari ranar da za a saka ta Rataye shi. Cewar wani na kusa da Baba Tunde a can kotun Alkalan.

<< Azurfa Da Zinari 27Azurfa Da Zinari 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×