Kwanaki biyu distinguish Mukhtar Biro yana faman kiran wayar mai dakin nashi haj laila amma bays samun ta sai kuma hankalin shi ya koma akan meye dalilin kiran da tayi ta jera mishi ? kuma ina ta tafi?
Ranar yana zaune a gida ake sanar dashi an Rataye yaron nan a shekaran jiya yau za a nuna yadda akayi ratayar a NTA news a ranar kuma sai ga shi distinguish yana zaune aka nuna yadda akayi Ratayar Kaisar ya Kuma gani da idon shi inda yaji ba haka ya so ba a yadda yaso irin kisan da akayiwa dan sa irin sa yaso ayi mishi amma dai tunda ya mutu shikenan
Ya jawo kwalin tissue paper ya yago yana goge kwallar idon sa don kuka kam ya kasa daina shi na rashin Abdulhameed
Yana zaune yana goge ido da kwalla yaji wayar shi na tsuwwa ya jawo ta ya duba yaga daga office din gwamna ne ya dauka inda ake sanar dashi an tura mishi sako ta watsapp ya duba an saka hannu a takardun shi
Rabon shi da hawa online tun kafin ya tsinci mutuwar abdulhameed don haka sai yanzu da ya bude datar wayar yaga sakonni suna ta shigowa har da wanda aka turo daga office din gwamna amma sakon da yafi daukar hankalin sa shine sakon hoto mai motsi da mai dakin nashi ta tura mishi wanda ya yi saurin Danna budewa don yaga meye kuma ya tambaye ta tana ina?
Yana bude hoton mai motsi wato vedio sai yaga hoton abdulhameed wanda aka sakalawa wayoyin computer sun zagaye shi a sashi sashi na kanshi da sauran jikin shi .
Da sauri ya duba sai yaga kamar yana saukar da numfashi sai yaga laila tana online sai ya danno yi mata voice yana fadin.
“Wai laila Abdulhameed ne nake gani haka kamar yana numfashi? kina ina ne naga nomber ki bats shiga ga kuma inda nake ganin abdulhameed ba Nigeria bane don Allah fada min yaya akayi ? Abdulhameed bai mutu ba ? urgently please .
Yana tura mata yaga har ta bude shi ta saurara ta Kuma dawo mishi da hoton gwai gwai mai alamar rawa kafin ta yi mishi sakon murya.
“Nayi ta kiran ka a lokacin da na fahimci akwai sauran numfashi s tare da Abdulhameed amma baka dauka ba shine na karbe shi muka taho washing ton yanzu haka ya soma fidda numfashi.
Da wani irin sauri ya mike yana sauraren abinda haj laila ke fada mishi kafin ya soma fadin.
“Da gaske ne laila ko kuwa mafarkin da nake yi kullum ne? don Allah ce min ba mafarki bane gaske ne.
“Nima na jima distinguish ina imagine. wallahi na dade ban yarda ido biyu bane kaima zaka yarda da hakan idan kazo kaga abdulhameed yana fidda numfashi duk da dai har yanzu bai san wanda yake kanshi ba amma sun bada tabbaccin tree day’s zai bude idon shi har ya soma fahimtar inda yake .
Ya danna maida Reply yana fadin
“Gani nan zuwa laila dole na tashi jirgi zuwa washing tone a yau din nan gani nan zuwa.
Kan kace me? ya tashi shirin tafiya gadan gadan ya kuma samu visa kan kace me? jirgin ya daga dashi zuwa ingila .
*****
Ciwo ya kwantar da Daddy ganga ganga Al amarin da ya nuna damuwa ce sanadin ciwon daddy wanda yake fama da hauhawar jini da kasawar zuciya
Gado a ka basu a federal medical center na bauci inda haj Aliya take cike da tashin hankali musamman ganin halin da daddy yake ciki ga fati itama lafiyar taki dadi kuma duka ciwon duk na rashin Kaisar ne
Yaya halilu da alabo har da Inna Hajara suka taho bauci duba iro inda alh Sule yake tsaye kan komai na lafiyar aminin sa
Yaya halilu ya dubi iro da yake matukar jin jiki ya tausaya mishi matuka gaya yana fadin
“Allahu yash feekha Ibrahim Allah ya tada kafadar ka ka saka damuwa da yawa a ranka amma kuma damuwa dole ce Allahu yash feekha
Inna Hajara ma ta tausayawa halin da iron yake ciki tana duban haj Aliya tana fadin
“Anya kuwa Aliya babu hawan jini a cikin ciwon nan? al amarin da ban tsoro yake kuma shi wannan ciwon mugun ciwo ne yanzu kinji an fadi da kuma an fadi sai an rasa hannu ko kafa Allah dai ya raba mu da mugun ji da gani amma in dai akwai hauhawar jini to na san mai magani sadidan a yar leman sai a samo mishi.
Haj Aliya ta muskuta tana fadin
“Wallahi yaya Hajara hawan jinin ma shine gaba kuma in dai akwai yadda za ayi a samu maganin don Allah a sama mana don ni nafi yards da maganin hausa akan na asibitin nan wanda kullum jiya iyau.
“Ai bari ma na tashi alabo ya tafi can yar leman din ya karbo.
Ai kuwa alabo da yake tare da fati yana tambayar abinda yake damunta tayi wannan ramar sai ga sakon tafiya yar leman wanda ya nemi fati tayi mishi rakiya amma tace bats jin dadi yaje ya dawo
Abinda ya tsayawa fati a rai shine kallon da ta ga yaya alabo yana mata wanda ya canja da komai har ta soma tunanin suna uwa daya uba daya amma tana hango soyayya a kwayar idanun sa ? ko kuwa dai itace take hasashen hakan?
Sai yamma alabo ya dawo daga yar leman ya kuma dawo da magunguna kala kala amma dai wanda yake sadidan din na hawan jini shi aka soma hadawa wanda yake na bak’in zoborodo tare da garin gero aka zuba maganin cika aka dama kamar kunu aka bawa daddy yasha sosai don ka idar maganin dama cika ciki ake taf to in sha Allah duk yadda jini ya hau zai sauka
Ai kuwa sau uku aka damawa daddy sai gashi ya soma samuwa.
Yakumbo halima tana bakin murhu tana soya gyadar kuli kuli ta kalli Nadiya da ke zaune bayan ta saka ta surfen wake .
“Wai surfen ne haka kikewa lakwai lakwai haka ? ni fa ban son iya shege kinji gara ma ki saki jiki wallahi surfen wake sai kace mai surfen masara? ai kar ma ki yarda na gane akwai langwai a lamarin ki don na kula baki iya komai ba sai sahalci to ni bana shirin da raggaye gara ma kiyi kamar kinayi don aiki ne a gida na kamar Ya’yan carbi wancan biye da wancan duk wanda baki iya ba dole ne ma ki koye shi.
Kuka ya kwacewa Nadiya ta soma fadin
“Ni kam duk wanda ya cuce ni wallahi Allah ban yafe mishi ba wuta bal bal ni ina na iya wani surfe ko a labarin sa ban tab’a jin shi ba.
“Iyye zagi na kike don Uban ki? to bari na cuce ki da hujjar kai wa Allah kara banyi lalacewar da yaro zai zage ni na saka mishi ido ba kowaye uban sa kuwa.
Ai kuwa yakumbo hali ta zari iccen geza ta kuma rufe gida don ma kar makociyar ta ta shigo kawo ceto dama haka yakumbo take hukuncin Ya’yan ta wanda take rufe gida har Allah yasa sukayi aure dama Ya’yan nata uku ne duka mata kuma tayi musu aure sai Ya’yan su ake kawo mata don ko yanzu akwai jikoki biyu a gaban yakumbo halima yar shekara goma da yar sha biyu sune suke mata aiki amma zuwan Nadiya da ta fi su shekaru sai yakumbo take ganin aikin Nadiya zai fi nasu hafsa din abinda bata sani ba gara su hafsa sau fin dubu da Nadiya don bata iya komai ba sai kwalliya da rashin mutunci
Ai kuwa yakumbo ta rufe Nadiya da duka da icce tana dukan tana kwara mata asher.
“Ni ? ki zage ni ki kwana lafiya? ai kuwa kinci uwar karya har da uban ta kin kwana da yunwa wallahi ke ni ko yaya Aliya tana shakka ta bare ke kayan wofi wallahi da girma na da komai ki bude baki ki zage ni don kawai na saka ki aiki? to a me kike nufi ? na saka miki ido yadda iyayen ki suka zuba miki ido nima nayi hakan? to haram giyaa gidan liman wallahi ba zan zuba miki ido ki rashe min ba sai dai na miko miki karya kenan uban kuturu ma yayi kad’an bare na makaho da baya gani sai kin motsa wallahi sai na more ki kinyi aiki wallahi .
Duka na gaske yakumbo tayiwa Nadiya wanda bata shan irin shi ba abinda ya sa ta zage ta yi surfen wake kafin ta gama ta shiga wanke shi duk da bata san yaya ake ba amma tanayi yakumbo na kwara mata ashar duk ta watsar da shi dole hafsa ta kama mata aka yi wankin waken yakumbo sai masifa take ana gamawa kuma yakumbo ta bata aikin burbushe gyadar da ta soya .
Kan kace me? Nadiya ta soma iya tarin ayyukan da suke jibge a gidan yakumbo hali tamkar ya’yan carbi kana gama wanna zata kirkiro maka wani tamkar da gayya ma take hakan amma ba gayyar bace yakumbo macece mai zafin neman kudi komai da ruwan ka ce tayi kuli kuli tayi kosai da koko da safe da rana kuma dan wake take jifa shiyasa duk garin na jama are aka san yakumbo hali shiyasa kuli kulin ta in tayi dake shi ake ayi yajin kosai da dan wake kuma gata da injin nikan ta wanke take markade waken ta ta kuma murza gyadar ta amma fa kuli kulin sai dai a daka shi a turmi kuma Nadiya ce mai wannan aikin na dakan yaji tun tanayi tana gunguni in yakumbo taji ta ta bugi banza wofi har ta kai tana tsananin jin tsoron yakumbo kamar yddaa su hafsa suke tsoron ta
Kan kace me? Nadiya ta koma Allah sarki wata ran domin kuwa bata ma samun lokacin kanta bare ta yi wanka da gayen da ta saba kayan ta ma tunda ta ajiye jakar bata Kuma duba su ba domin kuwa yakumbo ta ware mata kayan aiki wanda ko yaushe cikin aikin wake ko gyada suke ko kuma aikin garin dan wake
Don haka gidan yakumbo babu yunwa don da safe idan ta dama kokon ta cewa take su debi wanda zai ishe su su kuma debi kosai shima iyacin su . da rana ma ga dan wake su ke dibar yadda zai ishe su su kuma zuba nai da yaji bata da tsegumi akan ka duba da yawa wani lokacin ma ita ke cewa su kara man ko yajin ko kuma dan waken ko kosai ko kokom . kuma bata da keta don duk wannan Aikin nan da suke Mata tana saidawa ta dafe kudin ta zasu basu wani abu tace su saka a bankin su . haka kuma idan an kawo tallar gwanjo zata tsirtar musu ta siya musu kuma bata nuna banbamci tsakanin jikokin ta da Nadiya Kai dai barta da masifa ko ta saka ka aiki kayi mata gunguni yanzu ne kuwa zaka ji a jikin ka don tafi tari rashin hakuri kana cewa kulle zata ce maka cass
Sai dai duk wanna bai sa Nadiya ta saduda ba abinda take gani ta yaya daddy zaiyi mata wanna wulakancin ya maido ta nan tana ta shan wahala don kawai ana son ganin laifin ta? Ita ina Ruwan ta da wani Kaisar can ? In don abinda yayi ne yass suke ganin ta a marar kirki har suna ce mata butulu ai na cewa tayi yayi abinda yayi ba har suke korar ta saboda wani matsiyaci irin wannan gayen? Ita kam ysnzu mafita kawai take nema ta yadda zata gudu daga jama are ta koma bauci ta samu show kawai suyi auren su ta manta da su daddy tunda basa son ta sai kowa ya tsaya wurin sa kawai .
don haka sai ta soma tara yan kudin da yakumbo take basu idan suka yi yawa zata balle ko cikin dare ne tayi tafiyar ta amma ina ita Ina iya zaman jama are? ai in su keena ma suka ji dariya zasuyi mata suce tayi karkon kifi ta fara rayuwa a birni a kuma gidan kudi amma ta Kare a kauyen jama are? Ai ta fadi babu nauyi wallahi.
A ranar taji mama ta yiwa yakumbo hali waya tana fada mata daddy babu lafiya har an kwantar da shi a asibiti . yakumbo ta dauko salati tana sallamewa tana tambayar me yake samun iron ? mama fada mata hawan jini ne yakumbo tace in sha Allah kuwa zata zo ta duba shi jibi jibin nan .
Wannan magana da Nadiya taji bata komai ba na ciwon daddy a ranta ma cewa take Allah ya kara mishi duk son wannan matsiyacin banzan ne ya taso mishi hawan jini ko? sai taji itama yakumbo na tafiya itama zata balle tayi tafiyar ta taje suyi auren su ita da show ba sai sun sake ganin ta ba?
*****