Skip to content
Part 33 of 35 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“Al amarin Allah ne a kaina fati Ina Nadiya please? yaya jikin daddy?.

Wani yaji yajin kishi  da taji a idon ta saboda ambatar sunan Nadiya da yayi wanda yasa ta jin kwalla amma ta basar tana bashi amsa.

“Nadiya tana jama are wurin yakumbo halima basu jima da komawa ba don yanzu na tabbatar da basu Isa gida ba . Daddy kuma yaji sauki sosai sai dai heart failure da yake ta fama.

“Muje na duba jikin nashi sister.

Fati ta wuce gaba yana biye bayan ta

Alh iro yana zaune gaban shi da kayan fruit wanda aka ce yayi ta shan su suna taimaka wa zuciya shiyasa suka zame ko yaushe suna a gaban shi

ya zubawa kofar shigowar ido idon shi kyam akan Kaisar wanda yake takowa akan kafafun sa.

Har Kaisar ya Isa gaban Alh iro ya zube yana kare mishi kallo amma ya kasa cewa komai ya kuma kasa dauke idon shi daga Kaisar din.

Haj Aliya wacce Fati ta kwarma ta mata abinda ta gani ta bazamo da sauri har tana cin uban tuntube ta maze tana karasowa taja tayi turus kafin ta kwalawa sunan Kaisar kira.

Alh iro ya dago ya dubi haj Aliya yana fadin

“Aliya taho ki duba min nan shin abinda nake gani kina ganin shi? gizon da idona yake min ne ko kuwa ya fara bayyana a idanun kowa?.

“Na ganshi daddy nima shi nake gani amma ta yaya? mafarki? Ko kuwa siddabaru?.

Daddy ya mika hannu Akan fuskar Kaisar yana shafawa Kaisar ya soma fadin

“Daddy nine wallahi nine mama nine ba mafarki ko siddabaru ba . babu gizo Daddy zahiri ne.

“Ban yarda ba ! cewar alh iro

“Ba dai Kaisar ba sai dai shaidanin da yayi kama da suffar Kaisar. amantu billahi Rabba nayi Imani da Allah da ranar Alkiyama. nayi imani da mazannin Allah da mala ikun sa . haka nayi imanin mutuwa guda daya ce bata da komai bayan ta kuma wanda suka fi Kaisar daraja da kima da matsayi sune annabawa da manyan bayin Allah sun tafi basu dawo ba don haka Kaisar ma in ya mutu ba zai dawo ba tunda fiyayyen halitta ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam ma yayi wafati bai dawo ba  don haka ba dai Kaisar ba a dai fadi wani abun ba wannan ba amma bana in karin mutuwar a cikin ta ne abinda ya faru ya faru amma in dai an mutu to an mutu .

“Daddy Kaisar ne ba kowa ba a gaban ka ban mutu ba ko nace ba ni aka Rataye ba domin kuwa dan su da suke neman kadin ruhin sa bai mutu ba .

“Ta yaya zan yarda da hakan bayan akan idona akayi hakan ? har kabarin Kaisar an nuna min a Abuja ba zan yarda cewa Kaisar yana raye ba sai dai in an so a rikita min lissafi ko kuma ana son yaudara ta ne to azo a yaudare ni amma kar a fake da wannan hanyar don ina fatan tabbataccen Imani har zuwa lokacin da ruhi zaiyi bankwana da gangar jiki.

Jikin Kaisar yayi sanyi don ya rasa ta yadda zai ganar da daddy wanda yake fadin za a yaudare shi.

“Allazi wahidun Allah da GIRMA Yake.

Suka tsinci muryar dattijon a bakin kofa.

Su duka suka mayar da kallon su bakin kofar yayin da Kaisar ya mike da sauri ya nufi bakin kofar inda dattijon yake yana nufin shigowa da shi sai tsohon yace wa Kaisar.

“Sanar da mai gidan tukuna ai ba a shiga haular mai gida babu izinin sa

Alh iro da mamaki ya kashe shi daga zaune don ya gane muryar tsohon nan wanda Nadiya ta mara ne wanda yayi mamakin saurin bacewar sa har ya fara tunanin anya mutum ne?

“Shigo da shi

cewar haj Aliya wacce itama tashi daya ta gane tsohon

Kaisar ya shigo da tsohon wanda yake dogare da sandar sa har Kan kujerar da daddy yake zaune ya zauna

Haj Aliya ce ta soma gaishe shi kafin fati dukkan su sun shaida shi shima  duk ya san su ya kuma san alherin da sukayi mishi.

Daddy ya dube shi yana Fadin

“Sannu baba sannu da zuwa.

“Sannu alh ya jikin ? Allah ya kara lafiya.

duk suka amsa da ameen ameen

“Wata kil ku shaida ni wata Kil kuma ku manta ni to amma ni bana manta alheri amma har ga Allah ina yafe sharri amma alheri duk wanda yayi min shi Ina rama masa amma sharri Kam na Kan bar mutum da kayan sa .

“Kuna ta mamakin wannan yaron ? to ku bar mamaki Allah yana taimakon wanda ya taimaki bawan sa. hakikatan wannan yaro yayi bajinta duk da zuciyar sa ce take rike da wani Al amari akan abinda yayi amma duka lokaci ne Alkali to Allan ya  taimake ni ni kuma ya bani ikon taimakon sa kuma ina mai tabbatar muku ban da dan lokaci wancan yaron da aka ce ya mutu zai bayyana don Bai mutu ba yana can waje yana karbar magani don haka Allah ne Allazee wahidun shi kadai yake da GIRMA ku bar tantama ku bar kokonto.

Daddy ne ya dauke ajiyar zuciya yayin da haj Aliya kuma ta cikawa tsohon gaban shi da kayan abinci da na sha duk da ita da fati basu fahimci abinda daddy ya fahimta ba na tsohon ba bil adama bane.

“Alhamdulillahi baba Allah ya kara lafiya muna godiya ga abinci nan ka saka albarka.

“Ayya nagode Alh ina axumi yau litinin nagode nima Allah ya kara lafiya.

ya mike zai tafi yana cewa daddy Alh iro

“Ga magani nan wurin Kaisar in Allah ya yarda zaka sami saukin ciwon zuciya.

Kaisar ya mike zai mishi rakiya amma ya dakatar da shi yana fadin

“Yi zaman ka Kaisar zauna ka kula da uban rikon ka sai wata rana.

Da haka ya fice yana dogara sandar sa daddy da ya gama gane al amarin dattijon ya raka shi da kallo har ya fice

Haj Aliya ta zauna tana yiwa Kaisar barka shi kuma yana tambayar jikin daddy ta kuma sanar dashi komai

Kaisar ya fiddo maganin da dattijon nan ya bashi na daddyn ya fada mishi a jika da zuwan zam zam a bashi yasha tuni kuwa Haj aliya ta tashi malam Ango ya nemo zam zam

Daddy ya rage daga shi sai Kaisar yake fadin

“Kaisar dattijon nan kuwa bil adama ne? nayi mamaki fa tun ranar da ya shigo gidan nan da kuma irin neman da nayi mishi ban ganshi ba tun a ranar zuciya ta ta darsa min wani abu.

Kaisar yayi murmushi yana fadin

“Ai Daddy da kaga al amarin da ya faru tsakanin mu da ka kara mamaki don ni da kaina da farko tsorata nayi amma sai ya karanto min cewa alheri ne ya hada mu ba mugunta ba da yana rama mugunta da Nadiya bata tsira. ya kuma fada min shi din musulmi ne shiyasa ba barwa Allah komai na inda a zaman sarkar da aka saka ni ma a ranar Daddy ina so nayi salla amma babu ruwa kuma ko abinci ba a bani ba babu ma wanda ya tuna da ni din  mutum ne sai ga bawan Allah nan Daddy wani masallaci da ban san ko na ina bane a can nayi salla . Daddy in takaice maka ma a ranar da akayi hanging din a saman wata bishiya na ganni har komai y faru kan idona. A bakin sa naji baka da lafiya kuma a bakin sa naji ka mayar da Nadiya jama are Daddy me yasa?.

Alh iro ya sauke ajiyar zuciya yana fadin

“Kaisar dole nayi nesa da yarinyar nan domin kuwa idan Ina ganin ta a cikin gidan nan ko kusa dani to hakikatan itace ajali na shiyasa na kaita can jama are wurin halima ko ba komai halima akwai displing zata saita ta kuma ta gane rayuwa kuma Ina so a can ta samo miji wanda zai ganta a gidan talakaww Wanda ba zata gorantaww talauci ba .

“Kayi min afuwa daddy in roki wata alfarma mana Daddy? ADDU A itace abinda zakayi mata amma mai bada hali ya riga mai mada horo.

“Kaisar bakayiwa kanka adalci ko kuma zuciyar ka bata maka adalci wane irin so kakewa yarinyar nan? ka dan yarinyar nan tunda Al amarin ka ya faru bata nuna wani emotion ba? ko ka san saboda wannan zaluncin da tayi maka ta fita a raina? kaita jama are da nayi saboda ina son nayi ness da ita . ban tab’a jin na tsani yarinyar nan ba Kaisar sai na shirun da tayi bata karya ta ka cewa itace tayi kisa ba. ko ka san cewa da nayi mata magana akan hakan cewaa tayi ba ita ta saka ka ba kai kayi ra ayin hakan? Anya Kaisar kana da zuciya a kirjin ka kuwa? don Allah ka manta da Nadiya a rai da zuciyar ka. yau dai bari na so kaina na tallata maka gati wacce itace daidai da kai a kamanni  da halayya har da dabi a amma zanso zuciyar ka ta manta da Nadiya don allah ka bawa zuciyar ka magana.

“Daddy ina son Nadiya ne saboda jinin ka ce . so irin son da banayiwa rayuwa ta saboda kawai ta zamo jinin ka daddy. Ina son fati amma ba son aure ba sai son yan uwan taka ba zan iya yiwa fati adalcin bata soyayya ta ba saboda  Nadiya kadai na bawa wannan zuciyar tawa Daddy don Allah Ina nema mata afuwa kayi hakuri ka dawo da ita gidan nan ba zata iya rayuwar kauye ba kuma ba maccid’o zaka bata ba daddy kake cewa ta samo miji talaka?.

Daddy yaji hawaye suna ciko idon sa saboda jin abinda Kaisar ya fada na gaibu.

“Kaisar ai maccid’o tun da iyayen sa sukaji mugun abun da ta tafka magana ta watse na kuma yi nufin hada ta da alabo shima na gane fitina zan hada don yarinyar nan a nan cikin gari dai ba zata auru ba sai ta dangana da kauyen shiyasa.

“Daddy to ni fa ? ka manta daddy ina son ta? akwai wani da ya kamaci auren ta iri na ? nayi maka alkawarin kowann irin Hali ne da Nadiya ins son ta kuma zanyi kokarin ganin na saita ta.

“Ba zaka iya ba Kaisar kuma auren Nadiya a gareka cutarwa ce babba ni kuma abinda zai cutar da Kai na xabi ya cutar da ni fiye da kai shiyasa nake ganin kun barranta da juna don Allah mu bar maganar nan in baka son fati to nemo wata na aura maka amma banda Nadiya don Allah.

“Daddy kar nayi maka karya wallahi babu wata mace a raina sai Nadiya shiyasa nace maka ba zan iya yiwa fati adalci ba to kowace mace ma ba zan iya duban ta ba bare naji wani abu a game da ita .

Kaisar ya fada yana mikewa ya fice daga dakin daddy abinda ya nunawa daddy Kaisar yayi fushi

yabi shi da kallo har ya fice yana murmushi

Can da yamma sai ga Alh Sule ya zo yana mamakin bayyanar Kaisar wanda yaje ya kai mishi karar Daddy

Daddy yayi shiru yana sauraren alh sule wanda ya ke son sanin yadda akyi Kaisar ya bayyana.

Daddy ya yi murmushi yana fadin

“Al amarin Kaisar sai shi Alh Sule wai yaron da ake case din mutuwar sa ne bai mutu ba shine Allah ya kawo mishi dauki amma duk ba wannan ne abin mamakin ba Alh Sule sai ta yadda idon yaron nan ya kasa hango aibun Nadiya shi fa a dole son ta yake ni kuma Ina gano mishi cutuwa a auren nan don yarinyar nan ba matar kwarai bace amma ya kasa gani har yana kai kara?.

“to lallai yaron ya shiga da yawa amma mu roki Allah ya zaba abinda yake shine alheri in auren ne alheri Allah ya tabbatar in kuma babu Allah ya kawo mafita.

Suna rabuwa da alh Sule ya kira kaiser ya iso yana fadin

“In banda abinka Kaisar ai ba sai ka sanar da alh Sule ba ni ina hango maka abinda zai faru a gaba ne kamar ka mace ta gari wacce zata samar maka da nutsuwa ta kuma tallafawa maraicin ka ya kama ce ka ba irin Nadiya ba saboda idan na baka auren Nadiya Kaisar tashin hankali na hada ka da shi.

“Daddy ai naji na gani sai Allah ya juya Al amarin muga sab’anin zaton mu tunda Ubangiji mai juya Al amura ne ni yanzu damuwa ta ma halin da take a jama are ne don na san wahala take ta  sha don Allah don ANNABI daddy kayi min izini na dawo da ita nan ba zata iya Rayuwar kauye ba.

“Ka daije ka gano ta amma ba yanzu nayi nufin ta dawo ba dama akwai kayan ta da za a kai mata kayiwa malam Ango magana idan zai je kuje tare ka gano ta idan lokaci yayi zata dawo amma yanzu tayi ta zama can.

ya mike ya fito ya kira malam Ango yana sanar dashi zasu tafi jama are yanzu

Mama ta bashi kayan Nadiya da za a kai mata 

Kayan kawai ya duba himili guda ya gane da gaske daddy yake ya mayar da rayuwar Nadiya kauye don haka malam Ango ya fito da mota aka loda kayan suka dauki hanyar jama are yana cike da alhinin yadda zai riski rayuwar Nadiya a gidan yakumbo hali a jama are  a yadda ya san rayuwar Nadiya a bauci yaushe zata iya rayuwar kauye ?

.Tun a hanya Kaisar yake ta jerawa malam Ango tarin tambayoyin duka akan Nadiya da halin da take a kauye  a jama are.

Malam Ango yayi murmushi yana fadin

“Uban gida na ai jama are ba kauye bane kawai dai karamar hukuma CE jerin kana nan hukimomin jihar bauci kuma Nadiya ai dama kyan ta hannun wanda zazzafan mutum wanda zai koyar da ita tarbiya shiyasa matar nan ta burge ni wallahi yakumbon nan  tasu babu wargi a tafiyar ta na tabbatar da a hannun ta yarinyar nan ta taso da ba a zagi iyayen ta ba suna yi bakin kokarin su amma tana sawa duniya na zagin su bata ko gudun bakin duniya yarinyar nan wulakanci kala babu wanda bata iya ba har da mai kalar ruwan hoda kwanaki fa tafasasshen ruwan zafi ta kyarawa Ade don kawai ta kawo mata shayi bai mata ba don Allah in ba don iyayen ta karimai bane kana zaton Ya’yan aden zasu yarda? ai talauci b hauka bane  Allah kadai ya san yawan yan aikin da yarinyar nan ta kora a gidan nan da wulakancin ta kasan kuma ba kowa ne ke iya jurewa wulakanci ba duk wanda kaga ya jima a gidan nan to hakurin say ya kai wallahi ko kuma yanayin uxuri ne saboda iyayen ta mutanen kirki ne kuma albasa ce batayi harlin ruwa ba amma yanzu kam ai ta soma hankali tunda aka kai ja ira jama are duk tayi sanyi ranar nan da aka aike ni na samu tana murjin gyadar kuli kuli tayi dawan dawan da ita Kai baka ce itace mai izzar nan da dagawa ba . kai ai yarinyar nan tayi wulakanci wallahi ta zaga ta mara don kuwa banke mutum da mota yadda ka san ta take kwadi haka take take mutane ni na rasa abinda yarinyar nan ta dauki rayuwa shin ta manta ko bata mutu ba dole aure zai raba ta da gidan su da take homa da barazana da shi ? kuma mijin da zata aura ba lallai ne ya zama kalar gidan da ta baro ba amma take mantawa? amma kaga yanzu mai gida yayi maganin ta Ashe shima ya san ta kan tsiya kyale ta kawai yake yanzu kuwa ai ta gane Allah daya ne . Kaga ita ita yar uwar ta babu ruwan ta da izgili Fatima ba? Ita kam ko dan aikin gidan su girmama shi take  rayuwar ta babu Allah wadarai irin ta waccen ja irar ranar da na kawo ta jama are fa babu kalar zagin da yarinyar Nan ba Tayi min ba Akan na aje ta wai tayi tafiyar ta ashe mai gida ya san halin kayan sa shiyasa yace kar mu tsaya ko ina sai gidan yakumbo halima wacce yace ta karbe wayar hand set din ta ta kuma hana ta fita ko ina haka kuma aiki ko wane iri ne a saka ta shi. don haka aikin koko yanzu yarinyar nan ta iya haka aikin kosai bare murjin gyadar kuli kuli ta iya komai na mata yanzu amma da bana zaton ko ruwan shayi ta iya dafawa.

A fussce Kaisar ya dakatar da malam Ango daga zayyanar da yake babu ko burki.

“Kace don a azabtar da ita aka kaita jama are malam Ango? Sai kace jaka duk wadan nan ayyukan da ka zayyanar? wannan ai ba tarbiya bace mugunta ce waye bai san kuruciya ba? dole sai munayiwa juna uzuri malam Ango yarinyar nan yarinya ce kuma kowane mutum da irin yadda kuruciyar sa take zuwa.

<< Azurfa Da Zinari 33Azurfa Da Zinari 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×