Duka yakumbo tana kuka take rattaba wannan bayanin kafin ta juya kan Nadiya ta cacumo ta tana fadin
“Munafuka dama kinyi nufin kunyata ni ne a gaban yar uwa ta? A kawo min ke lami lafiya sai kawai aji kina shirin sauke dan dakan kuka a gaba na me kenan? to gara kawai ta kashe ki na kashe banza wofi in yaso nace kin mutu da dai iyayen ki suji abinda yake faruwa wallahi banda idon duban su na basu ba asi . .
Irin shakar da yakumbo halima tayiwa Nadiya irin wacce ke neman makasa ce don ga alama ta hau hanyar kisan da gaske don haka likitan ya mike da sauri Yana kwatar Nadiya daga hannun yakumbo wacce ta kara fashewa da kuka kashirban bil hakki.
“Barni likita na kashe yarinyar nan in kashe wofi cikin shege a gida na ina ina akayi hakan? yarinyar nan ko kofar gida bana barin ta fita saboda amana na dauko amma da yake ta iya munafunci har ta iya fita ta kunso cikin shege? gyaran tarbiyar ta fa aka kawo mini don an san ni din zazzafa ce yau Ina zafin nawa da har hakan ta faru? ban gyara ba sai ma b’atawa da nayi ? in dubi iyayen ta da wane idon ko da wace kamar? ba dai wannan ta halima da nake da ita ba wallahi sai dai ko na koma sadiya.
“to Inna ba ta haka zaki tuhume ta ba ki bari ku koma gida cikin hikima zaki tambaye ta ya akayi hakan ? amma in Kika ce ta wannan hanyar ta zafin naki ai zaki kashe ta ne kuma a koma sabon babi wanda duka za ayi nadamar sa abinda ya faru ya riga ya faru sai a nemi hanyar gyara .
yakumbo ta mike tana duban Nadiya da take mayar da numfashi tana fadin
“Sai ki wuce muje gidan ki bani bayani ai dole ma na sanar da iyayen ki halin da ake ciki don su san ki wuce sanin su kuma ni ba a hannu na kika watse ba
Da haka suka fice suka bar asibitin yakumbo sai kuka take tana share hawaye da fyace majina
Suna zuwa gida kuwa yakumbo ta mayar da kofa ta rufe ta ritsa Nadiya da wuka tana fadin
“Ai gara kawai na cewa iyayen ki kin mutu da dai na Kai musu wannan mugun labarin wallahi fada min ta Ina kika kwaso min wannan janhurun masifar?
A tsorace Nadiya take ja baya tana fadin
“Wallahi ban sani ba yakumbo ni ban san komai ba wallahi.
“Karya kike wallahi ai shi cikin ba a ruwa ake shan sa ba sai an bi ta kunji kunji na kuma tabbatar da kunji kunjin kika bi don in a ruwan ne da tun a gaban iyayen ki zakiyiwa shi kuma da hafsa ta riga ki haifewa.
Makociyar yakumbo ce mai koko da ta gama Jin komai ta katanga ta soma buga mata kofa tana fadin
“Ke dai baki da hankali wani sa in halima In kikayi hakan anya ba kin dab’awa cikin ki wuka ba? asiri rufe ake maganin komai kafin duniya ta dauki labarin ku da Allah bude ki nemo wata hanyar ba wannan ba
jin wannan matashiya da mai koko makociyar yakumbo take mata yasa ta bude gidan don Nadiya ta cika gidan da ihun kukan ta.
Mai kokota kama hannun Nadiya tana fadin
“yi shuru haka Nadiya kwantar da hankalin ki kinji .
Yakumbo kuka take tana fyace majina tana fadin
“Mai koko ina zan tsoma rayuwa ta? lami lafiya iyayen ta suka kawo min yarinyar nan gashi za a saka ni zance da karkace kai ko da kunyar Alhaji Garbebe aka barni ai na bani na lalace yace na san lalatacciya ce nake shirin lika mishi,? .
“Duk fa ba wannan ce mafuta ba gara ki sake shiri dole ne iyayen yarinyar nan zasu san abinda baki so su Sani ko kuwa sai ta haihu ne zakije kice musu ta haihu? .
“Ni tsoro na ma kar ace Alhaji Garbebe ne tunda shi kadai yake zuwa wurin yarinyar nan.
“Tambayar ta zakiyi ai cikin ruwan sanyi ba wai kina nuna ta da wuka ba kowaye ai zata fada miki in ma shine duk da bana zaton garbage don baiyi suna akan hakan ba .
yakumbo halima ta dubi Nadiya tana fadin
“kun tab’a yin wani abu ne da garbage ?
Nadiya ta kad’a kanta tana fadin
“Bai tab’a nuna min komai ba ni kaina ban san komai akan hakan ba .
” To kuma ke mai koko yaushe zan nufi iyayen yarinyar nan da wannan maganar? ai gara kawai na hada kudi na kaita asubtin da suke zubar da ciki su zubar mats da shi baki na alaikum.
“Idan kuma ta mutu a wurin zubar da cikin kice me ? su gane yarsu ta lalace a hannun ki kin kuma kashe ta wurin zubar da cikin? to ki fada musu gaskiya kawai babu boye boye in Kuma kina ganin hakan shine mafita dabara kafa !
mai koko ta juya ta fice ta bar yakumbo halima da canki canka sai kawai ta kuma saka kuka wiwi hawaye da majina.
*****
Abdulhameed wanda ya tashi zaune yana cije baki saboda a yanzu ne yasha wuya saboda famin da yayiwa kanshi amma dai ya na samun sauki kasancewar asibitin mai kyau da likitoci masu kwarewa
yana zaune haj laila ta taho tana mishi sannu amma bai ko kalle ta ba bare ya amsa. Distinguish kuma hannun shi ya kama zai duba illar da yayiwa kanshi amma ya zare hannun shi daga rikon da uban nashi yayi mishi fuska a daure yana motsi da baki amma babu wanda yaji me yake fada
Haj laila ta hada mishi ruwan tea tana fadin
“Daure ka sha mai zafi kasha magani jikin ka yayi kyau abdulhameed don ma baka cin abinci.
yasa kafa ya har bar da kofin yana kara gimtse fuska inda haj laila da distinguish suka bishi da kallo baki sake .
“Meye haka abdulhameed?
cewar haj laila .
“Ni fa ku kyale ni mom kuyi tafiyar ku tunda babu mai son abinda nake so to ku kyale ni don Allah bi na san hanyar da zanbi na samawa kaina abinda nake so. wallahi mom duk wanda ya nuna baya sona da Nadiya zan barshi kowaye wallahi to a barni kawai ni na kashe wa kaina nama tunda babu mai sona . .
“Haba abdulhameed wai ba ni nace maka nayi maka alkawarin hakan ba ? ka bari mana ka kara samun sauki da an sallame mu muka koma Nigeria maganar da za ayi kenen .
“Mom ke kika yards da hakan shi daddy kinji ya yarda ne ? mace bata neman aure dole sai uba namiji shi kuma daddy yana saman ki duk yadda yace haka zakiyi kuma abinda ya fada yake nufi shiyasa ni zan shiga na fita na samawa kaina abinda nake so duk na hutar da ku ke da daddy mom.
ya mike yana kiran Mustafa Tero ya shigo yana fadin
“Kaje kayi mana bicking flying Tero yau nake son komawa Nigeria ba zan kara kwana a asibitin nan ba ina son sanin halin da Nadiya take ciki don jiki na yana fada min na saka ta a cikin matsala da tashin hankali to so bai zama cutarwa ba gara na cutar da kaina fiye da ta cutu.
“Kayi hakuri har a sallame ka abdulhameed ni nayi maka wannan alkawarin ko yar waye zan nemo maka kaji? kai kadai ne gareni ta yaya kake zaton ba zan so abinda kake so ba,? cewar distinguish Mukhtar Biro wanda ya rungume dan nashi abdulhameed yana rarrashi sai kace dan yaro har yana bubbuga bayan shi .
“Daddy kar ka yaudare ni in har hakan kake nufi to nema min sallama kawai mu koma Nigeria ka nema min auren Nadiya kawai in dai abinda kake fada min gaskiya ne ba yaudara ba don ni fa ba zan kuma kwana a garin nan ba sai Nigeria.
“Don Allah nema mana sallamar ban mu koma gida kar ya jawo wa kanshi wani ciwon na kuma shiga uku tunda yace ba zai kuma kwana ba ka san ba zai kuma kwana ba karbo mana sallamar
cewar haj laila wacce take son a cikawa abdulhameed burin shi ta kuma san abunda ya fada shi yake nufi .
Dole distinguish ya nufi office din likitan don karbar takardar sallama. likitan ya tarbe shi ya zauna yana koro mishi abun da yake so wato takardar sallama.
likitan yayi shiru kafin ya soma yiwa distinguish bayani akan cewa ba yanzu ya kamata a sallami abdulhameed din ba don akwai matsala ne tare da shi .
Wace irin matsala kake magana likita? banda wanna ciwon akwai wata matsala ne? yaron ne ya matsa da son komawa Nigeria. likitan ya soma jawo file din abdulhameed ya bude ya fito da doguwar takardar yana duban distinguish cike da tausayin abinda zai fada mishi.
“Fada min matsalar da kake magana likita ? meye matsalar Abdulhameed kuma a yanzu?
.Likitan ya sauke ajiyar zuciya yana duban distinguish Mukhtar Biro da tausayin halin da yaron nashi yake ciki don dole za a tausaya musamman ma idan aka dubi tarin kauna da soyayyar da suke nuna mishi kad’ai ya Isa ya nuna suna ji da shi to yaya zasu karbi kaddarar da take tashi ce tun ran zanen sa? Kuma ma tunda ya mutu ya dawo ai zasu rayu ne da shi haihuwar ce dai ba zaiyi ba tunda yanzu ai da sun share makokin mutuwar sa.
“Kayi shiru Dr kace akwai matsala kuma ka kasa fada min ? fada min kawai in wacce kudi zasu magance min ce ina da kudin da zanyi komai don rayuwar Abdulhameed ba kuma zanji komai ba don kudi na sun tafi gareshi.
Likitan ya kuma sauke ajiyar zuciya yana fadin
“Kayi hakuri ranka ya dade al amarin babu dadin fada ne kuma na lura da tarin kauna da soyayyar da ke tsakanin ku da yaron shiyasa nake alhinin sanar maka amma dai dole zan fada maka shiyasa nace maka ba yanzu ya kamata ace an sallami abdulhameed ba saboda wannan matsalar da zan fada maka a yanzu.
“Sakamakon yankan wukar da yake a gefen cikin shi wanda yayi sanadiyyar datse wata jijiyar Kai sako daga inda take zuwa k’asan marar shi wacce take jone da jijiyar da ke fidda kwayayen hallitta wanda suke bayar da kwan haihuwa.
“Me kenan ?
cewar distinguish Mukhtar Biro wanda ya tambaya a rikice .
“Matsalar da ta kara rikita al amarin shine fincike plaster da yayi ne a lokacin da ya fusata don aikin farko an samu anyi nasarar aikin duk da babu tabbataccin jijiyar ta koma bakin aikin ta don irin matsalar da ta samu ba zai bashi damar haihuwa ba saboda ta tsinke ne an dasa ta sai kuma ya mayar da aikin baya ta hanyar cire plaster inda kuma ta kuma tsinkewa kuma har yanzu bata hadu ba. smma rashin hadewar ta ba zai zamo matsala a Rayuwar sa sai dai ba zai tab’a haihuwa ba zai rayu ne babu ya’ya shiyasa nace bai kamata a sallame shi a yanzu ba ga kuma ciwukan jikin shi ma basu gama warkewa ba.
Wata irin zufa da ta soma wanke distinguish Mukhtar Biro har tana saukowa dokin wuyan sa.
ya cire hular kanshi yana ambatar kalamar .
“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un likita? shi kadai na haifa bashi da wa ko kani ta yaya zan rayu ba tare da naga jinin sa ba? sai kuma ya saka kuka yana dafe kanshi abinda ya bawa likitan matukar tausayin sa.
“Kayi hakuri ranka ya dade munyi iyakar iyawar mu amma al amarin yafi karfin mu haka kaddara take bata da gurbin sauka sai dai in ba a zanowa bawa ita ba.
“Likita shi kadai fa na mallaka duk duniyar nan banda abun so sama da shi ka kuwa san yadda na zana ganin ya’yan Abdulhameed? ka san daular da na shiryawa jikoki na ya’yan Abdulhameed? don Allah likita kace min MAFARKI nake .
“Kayi hakuri ranka ya dade ba mafarki bane gaske ne .
“Yanzu babu wani abun yi likita? Idan akwai yadda za ayi don allah ayi bana jin tsadar kudi ko nawa ne zan biya wallahi .
“Ranka ya dade duk wanda yace maka akwai abin yi ma kudin ka zai karba ina da kwarewa ta wannan fannin ba alfahari ba wannan jijiyar bata son bak’o ma ana bata son a taba ta da an tab’a ta matsala ake samu bare kuma ta datse . magungunan da Yake a kai sune zasu rage mishi Rad’ad’in ciwon don zai rika dama da ciwon ciki ne akai da Kai da kuma matsalar kullewar inda yankan yake shiyasa nace ba yanzu ya kamata a sallame shi ba a bari ya Kara kwana biyu tukuna.
Distinguish Mukhtar Biro ya rike kanshi yana jin duniyar tana katantawa da shi
ya mike ya dauki hular shi ya mayar ya fice daga office din likitan yana hango balakin da ya same shi
Haj laila da take zaune tana lallaba Abdulhameed ya sha ruwan tea yana mazewa har dai ta samu ta ciwo kanshi ya karbi ruwan shayin mai hade da kayan hadi madara da oveltin yana sha
Distinguish Mukhtar Biro ya shigo dakin abdulhameed na shan tea ya zauna kusa da haj laila wacce take duban shi jiki a sanyaye.
“Yaya ne my distinguish?
ya ajiye hular shi jiki a sanyaye yana fadin
“laila matsala ta kuma samun mu wacce bamu da maganin ta .
“Banda wannan kuma da muke ciki distinguish wata ka ke kira mana? mye kuma ya faru?
ta fada a rude.
“likita yace min abdulhameed ya samu matsalar da ba zai iya samun haihuwa ba sai dai ya rayu a haka ni kuma Ina hango ta yadda na dora rayuwa ta akan ya’yan Abdulhameed shi kadai muka mallaka laila ya ya zamuyi da wannan kaddarar?.
“Daddy nifa ba wannan ce damuwa ta ba don Allah ka gane hakan mutum nawa suke rayuwa babu ya’ya? ni fa gida Nigeria nake so na tafi ba wannan maganar ba Nadiya ce damuwa ta Ina son na ganta na ga halin da take ciki .
“Haba Abdülhamid bakaji abinda muke magana akai bane ? da ya’yan ka muka dora dukkan burin mu sai kuma ace mafarkin mu ba zamu ga hakan ba ? .
“Daddy wannan ai laifin ku ne da kuka zabi iyakar abinda kuke so ku haifa yanzu da na mutu ba dole kuyi hakuri ba? In da ina da dan uwa ko yar uwa ai ya ishe ku ganin shi da ahalin sa ba lallai sai na mutum daya ba ni yanzu ya bada sallamar ? ya tambaya yana kallon Daddy.
“Yace ka bari ka gama shan magani tukuna saboda akwai yuwuwar ciwon ciki yake taso maka time by time.
Abdulhameed ya aje kofin tea din ya koma ya kwanta ya juyawa iyayen baya ya barsu da maimaita zancen na likita yayin da Haj aila ke kuka kashirban bil hakki saboda ita kam tafi distinguish Mukhtar shiga damuwa ba don komai ba sai tsara iyalin da sukayi na zabar D’a daya tilo a matsayin dan da zasu rayu da shi amma a yanzu ta hango katon kalubale ko babu komai Mukhtar yana da damar auro wata matar ta haifa mishi ya’ya amma ita kam sai dai ta gani anayi jikokin ma da ta kallafa ranta akan su ma ba zasu samu damar zuwa ba tunda mai kawo su babu lafiyar kawo su.