“A a mama kisan kai kenan idan aka zubar babu wanda ya san abinda Ubangiji yake nufi a bar Nadiya ta haife cikin ta ni in duk duniya babu mai son dan ko diyar ni ina son shi kuma zan amsa sunan uban sa ta iya yuwuwar Allan ya yafe laifin samun cikin tunda ta karfi akayi mata amma laifin kisan bawan Allah ya kasa yafe shi don Allah kar a zubar.
Nadiya ta mike tana mishi wani shegen kallo tana fadin
“Ni ce zan haifi shege? wallahi sai na zubar da shi ba zan haifi shege ba.
Daddy ya kifa mata mari yana fadin
“Sai yaushe ne yaron nan zai y’antu wurin ki? sai yaushe ne zaki yarda son ki yake da zuciya daya? Ina ce yanzu ya dawo da ke da wannan kayan Kuma na tabbatar asibiti ya kaiki tunda ga magunguna nan? anya kuwa ke din yar halal ce Nadiya? .
“Shine zai tsara min yadda zanyi ne Daddy? .
Yakumbo halima ta kuma kifa mata mari tana fadin
“Ban zaci hakan ba kam wallahi don wannan yaron dai shine dan halal din da har yanzu baiga mugayen ayyukan ta ba yana nan yana son ta amma ita kam ni kam Ina tausayin sa wallahi Allah ya dauke mishi wahala.
Daddy yace
“Halima ki koma da ita can ta zauna a wurin ki har zuwa lokacin da zata haihu.
“A a Alh ka gafarce ni ka san halin karkara mu a can kyamar wannan abun ake kuma ka san ina yan sana oi na da anji anyi hakan har kayan sana a ta za a daina siya gara dai ta zauna a nan kune babu masu kunji kunji da yawa amma ni yanzu yadda zamu karke da Alhaji Garbebe nake don shi in ya nemi aure bai samu ba duk abinda ya kashe lissafi yake sai an biya shi to bare kuma yaji ga abinda tayi mu fa can macen da ta kashe miji tafi mai cikin shege farin jini don karshen abin kunya shine cikin shege don haka alh ka yafe ni ba zan koma da yarinyar nan jama are ba duk dai abunda ake ciki zan Sanar maka daga shi can Alhaji Garbeben.
“Kar ki damu Halima ko yace a biya shi abinda ya kashe mata da wanda ya baki duk ki fada min zan biya shi mun ga kaddarar da tafi wannan Allah ya sa mu ga bayan al amarin.
Da wannan yakumbo Halima ta wuce jama are Nadiya kuma ta dawo gida da zama tana cike da takaicin yadda daddyn yake goyaww Kaisar baya akan duk yadda yake so ita ya za ayi ta raini cikin gayen nan hat ta haife? A yadda ta tsara ma ko a can jama are ne sai ta zubar da shi gashi wancan matsiyacin Kaisar din daga cewa kar a zubar daddy ya hau ya yarda.
Babu abinda ya rage ba daga wulakancin Nadiya ba ga fati ba baga yan aikin gidan nasu ba.
Laulayi mai zafi take wanda komai taci sai ya dawo ta amayar.
tana duke tana kwara amai Kaisar ya shigo ya ganta shi ya kama ta suka fice ya nufi asibitk da ita inda aka bude mata file wanda zata fara awo
ya dauko ta suka dawo gida ya shiga zaryar kawo mata abubuwan da take bukata irin kwadayin masu ciki
Haj Aliya tana zaune tana kallon shi ya shigo da leda wacce ya siyowa Nadiya kayan kwalama . Haka yake zagewa yayi mata duk abunda take so in kuma ya kama da abin shiga kitchen ne kamar su wainar fulawa ko dan malele sai ya roki fati tayi mata. Amma duk wannan kar kuce Kaisar Yana da wata kima a idon Nadiya a watse ma take kallon shi ko wanda ya kwarewa naci da son cusa kai, a gareta kallon matsiyaci take mishi kuma baran gidan su wanda dole ne ma yayi mata yadda take so shiyasa har gobe Kaisar bai da wata k’ima wurin ta ba kuma zaiyi ta ba.
Kwanaki goma sha biyu ciff yakumbo Halima tana duban hanyar zuwan Alhaji Garbebe wanda take son yazo taji da me zai zo? amma har yau kwanan Nadiya goma sha biyu da komawa jama are amma bai zo ba abinda kuma bai tab’a yi ba don tunda ya fara kaunar Nadiya baya rufe kwana uku bai zo ba. abinda kawai yakumbo halima ta kawowa ranta labari ya ishe Alhaji Garbebe yaji komai.
Ranar laraba da dare sai ga Alhaji Garbebe ya sallama wa yakumbo Halima ya kuma coge a kofar gidan bai shigo ba kamar yadda ya saba sai dai yaro ya tura yace ace anawa halima sallama
Yakumbo ta fito sai tayi arba da Alhaji Garbebe.
“A a Alhaji Garbebe kaine ka tsaya a waje sai kace wani bak’o,?.
“Eh ai yau kam na zama bak’o halima tunda har akwai manuba a cikin abinda kika so jona min, haba ni fa nayi mamakin abinda ya kawo kyakkyawar yarinyar nan gidan ki ashe abunda ya koro b’era daga rami ya fada wuta yafi wutar zafi. Banda Allah ya so ni ashe da haka zaki lika min janhurun masifa yarinya tazo min da dan wani in yi magana ace ba haka ba? Ashe mugun abu yarinyar nan ta kunso har ta kasa zama a birni shine aka hada kai da ke za a cuce ni Halima? To Allah ya tona asirin ki naji abunda yake faruwa kuma maimakon ki kira ni ki fada min sai kikayi gum da bakin ki duk tsawon lokacin nan da banzo ba ai na dakata ne in ga ko zaki neme ni ta yadda zan gane baki da sani amma sai kikayi gum to Allah ya tona asirin ki naji komai don haka dukkan abinda kika san na bayar s dawo min da kaya na Allah bai dora min kaddara ba saboda ban fasa rokon alherin sa ba.
“Kai garbage dube ni nan kar kazo har kofar gida na ka fada min zancen banza da wofi kaji ko? ni anya ma babu hannun ka a cikin yarinyar nan,? kai kadai ke zuwa wurin ta to zaka amsa kira alkali kayan da ka bayar kuma dole na biya ka komai ka san ka kawo to ka lissafa shi amma ni ma zan nemi hakkin yarinya a gaban kuliya .
Alhaji Garbebe ya dubi yakumbo halima a zabure yana fadin
“Har da sharri kuma don nace a biya ni kayan da na kawo? to kuje kunci banza halima .
“A a wallahi sai an biya ka garbebe kaine dai zaka gane baka ci banza ba duk garin nan babu wanda yarinyar nan take kulawa sai kai don haka da anga ciki jikin ta ai naka ne don haka ka saurari kiran alkali tunda hat zaka zo ka zare min Ido ni ban zare ma idanu ba kai ka zare min har kana fadar Allah ya tona min asiri to zaka ga Wanda asirin sa zai tonu wallahi.
Da sauri Alhaji Garbebe ya wuce ya bar kofar yakumbo halima don in akwai abinda yake tsoro to kotu ce don sun tab’a shari a da wani aka kalace shi tas yan kudin sa suka kare a shari a ya sha wuya da kyar ya samu ya kubuto . daga nan ya shiga tsoron shari a . gane hakan da yakumbo tayi yasa tayi mishi wannan barazanar don ta san ba zai tsaya jiran a biya shi ba zai bar maganar amma da batayi mishi hakan ba hatta da tattasai da tumatur din da ya kaiwa Alhaji Iro sai ya saka su a lissafi bare kuma wanda Yakumbo ta karba itama sai ta buya amma ko da yaji tace su hade kotu shine yayi maza yace taci banza ya kuma wuce bai tsaya bin kadi ba.
Yakumbo Halima tayi dariya ganin yadda Alhaji Garbebe yayi saurin bacewa daga kofar gidan ta da yanzu yana nan ya tara mata mutane kuma ba zai saurari kowa ba sai an biya shi.
Yakumbo ta kuma kyalkyale wa da dariya tana fadin
“Wa ya fada maka barno gabas take ? Da yanzu kana nan kana min zayyana amma yanzu na san wannan hanyar ma ka soke binta garbebe.
Sak’on takardar mai dauke da mugun Albishir ya riski mai shari a Sufi biro ta gidan akwatin gidan waya wato inbox wanda motar ma aikatar ta isko shi har gida ta kawo mishi, baya gida a lokacin da sak’on ya iso don haka matar sa ce Haj Safiya ta karbi takardar wacce take da tambarin stamp din government al amarin da yaja hankalin haj Safiya wacce tayi abinda ba aikin ta ba wato duba sak’on da ba nata ba ta fito da takardun daga cikin Emblam tana son ganin abinda ta kunsa sai kawai tayi Karo da takardar dakatar da mijin nata ko ace saukewa daga mukamin sa na judge.
Ba karamin tashin hankali Hajiya Safiya ta shiga ba don hakikatan tasan mijinta da tsayar da gaskiya a gurbin ta abinda kuma yazo ranta ya tsayar da gaskiya a inda ba a so hakan ba don bata san komai akan abinda ya faru tsakanin sa da dan uwan sa ba .
Hankali a tashe take kiran wayar mijin nata Sufi mai shari a amma ta dami wayar a kashe don haka ta wanzu cikin tashin hankali akan wannan bak’on al amarin
Sai dab da magariba mai shari a ya iso gida daga saukar karatun Al kur Ani mai girma da aka gayyace shi na yan makaranta
Bata sanar da shi komai ba sai da ya kintsa kafin Haj Safiya ta dube shi tana fadin
“Mai shari a kayi shari a da wani ne a makon nan? Ya dubi matar tashi yana fadin
“Wani abu ne? Ko kuwa waiting later aka kawo min? Ta yi mamakin tambayar da ya mayar mata da amsar gaskiya.
“An kawo takarda ne daga inbox har nayi karambani don na san Sak’o daga inbox cikin biyu yake ko alheri ko akasin sa shine naga waiting ce .
“Na san da zuwan ta dama Safiya Ina kuma dakon zuwan ta duk abinda na gani daga Allah ne kuma akwai hikima daga hakan.
“Haka ne Allah yasa hakan ya zama silar wata daukakar .
“Ameen ya Rabb Safiya duk lokacin da bawa yaji wani zafi ko Rad’ad’i to akwai wata daraja da Ubangiji yake nufin kara masa na san da zuwan takardar nan shiyasa abin bai bani mamaki ba .
“Har ga Allah raina ya bani ka tabbatar da gaskiya gurbin ta ga wanda bai so hakan ba ni kam aikin nan don kaine kake son shi amma Ina tsoron wani abu tunda mutane sun siyar da I’manin su wa wulakantacciyar don Allah ka barshi ka sake wani tunda kana da damarmaki da yawa a hannun ka.
“Ba zanyi nadamar tabbatar da gaskiya a gurbin ta ba Safiya ko babu komai ana batawa Alkalai suna wasu suna batawa wasu suna kulb’a na barna ana cewa jab’a ce shiyasa ban damu da komai ba in dai na fita hakkin gaskiya alhamdulillahi na san Allah ba zai barni haka ba sai ya tabbatar mini nima da tawa gaskiyar Allah muna jiran taimakon ka
Shikenan magana ta tabbata mai shari a Sufi biro ya sauku babu maganar zuwa kotu sai dai da yake yana dan tab’a kiwo na kajin agric gidan gona sai ya mayar da hankalin sa gidan gonar sa Kuma har yau din matar sa bata san dan uwan sa ne silar sauke shi ba. haka sauran Yan uwan su ma babu wanda ya sani sai dai kawai y sanar da su an sauke shi daga judge.
yana gidan gona albarkar kaji ta yi wata irin hab’aka tamkar ana sako kajin daga sama . Kwan da ake fidda wa a sati sune ake fitar wa a wata . Agwagi talo talo da tantabaru tamkar zubo su ake har mamaki yake amma al amarin Allah wanda baya toshewa bawa hanya matukar bawan ya yarda da Allah da gaskiya daya
Al amarin Sufi sai ya zama alheri daga wannan sai wannan har ya mayar da hankalin sa gidan gona. da kanshi yake kwasar kaji da zabi da kwayaye ya nufi gidan Yan uwan shi ya kai musu ayi zumunci a ciki kuwa har da ummulkhairi da take kanwar sa ba ya jin wahalar zuwa gidan ta su sha firar zumunci ya dawo.
Gidan Mukhtar ne dai yaje yafi a kirga sai ace mishi baya nigeria matar tashi ma wai suna can a ingila
Daga baya ne yake samun labarin shari ar da Mukhtar ya mayar Abuja aka Kuma yanke hukuncin ratayar.
Bayan kwanaki kuma ya samu labarin bayyanar Abdulhameed wanda ya samu tagomsshin numfashi har yake karba magani ya kuma gane Mukhtar da matar sa suna ingila ne wurin neman lafiyar Abdulhameed.
Wanna shine abunda ya faru tsakanin distinguish Mukhtar Biro da dan uwan sa mai Shari a Sufi biro.
*****
Jirgin da ya dauko su Abdulhameed da Mustafa Tero ya sauke su a filin jirgi saman sir abubakar tafawa balewa a birnin bauci inda Tero yake rike da abdulhameed wanda mikewa takewa wahala saboda dunkin da yake manne a gefen cikin sa dole sai da sanda ko kuma ya rab’a jikin Mustafa ya rike shi su tafi
Napep Tero ya tsayar musu suka shiga Tero na fadin inda za a kaisu wato gidan su Abdulhameed amma hameed din yace ba zai iya zuwa gidan can ba gidan Baffa Alkali zai zauna wato Baffa Sufi shi suke kira da Baffa Alkali.
Haka kuwa napep yaja su zuwa unguwar ta su Baffa Alkali
Sufi yana shirin fita zuwa gidan gona ya fito yana duba motar shi da yaji tana kara sai ganin Napep yayi ta shigo farfajiyar gidan sai kuma yaga abdulhameed yana fitowa da sanda ya nufo shi.
Da sauri Sufi ya rufe motar ya nufo abdulhameed Wlwanda suke da wata irin shakuwa da kauna kasancewar Sufi mai son yayi musu nasiha yasa suke kunar sa.
“Alhamdulillahi Abdulhameed Kaine nake gani akan kafafun ka? dukkan godiya tana ga Ubangiji shi kadai.
Sufi yana rungume da Abdülhamid suka koma cikin gida inda Mustafa ke ta fadin
“Baffa ni baka ganni ba sai ta hameed kake?
“Yi hakuri Mustafa na ganka Ina murna ne da Allah ya raya min Hameed ne.
Sukayi dariya suka shiga ciki haj Safiya tana fadin
“Subhallahi Abdulhameed babu lafiya ne na ganka haka?
Baffa Alkali ne yake bata amsa ta soma jajantawa abdulhameed har tana kawo musu abinci da dambun naman kaji da dafaffen kwai
Suna zama abdulhameed ya zamo kasan kujera a gaban Baffa Alkali yana fadin
“Baffa hakuri nazo na baka naji abinda Daddy yayi maka akan abinda ya faru ni da kaina na san banyi wa yarinyar nan adalci ba Baffa shi Daddy bai faye son gaskiya bane ko ni zanyi shari ar mu da Nadiya nine bani da gaskiya saboda na sato ta na kawo ta gida na kuma keta haddin ta Baffa idan kanwa ta akayiwa hakan ba zan nemi hakki ba? Nima shaidan ne ya ingiza ni ga hakan Baffa amma Allah da ikon shi an jarrabe ni da son yarinyar tunda na tab’a ta na kasa zama lafiya Baffa don Allah kayi hakuri kar ka kalle mu da laifin Daddy wanda ya saka aka sauke ka daga mukamin ka.