“Kar ka samu damuwa Abdülhamid, Mukhtar dan uwa na ne kuma abinda yayi kusukure ne muna nan da kai zai gane kuskuren sa ni yanzu Allah yayi min wata daukakar ma Abdulhameed gidan gona ya zame min alheri kaza da kwai dai a garin nan babu na daya na duk wani gidan abinci da yake a bauci hannu na yake karbar kaza kwai kuwa har fidda shi ake makotan jihar nan don haka kar ka damu abdulhameed wani hani ga Allah baiwa ni yaya Mukhtar ma gaba ya kaini wallahi ba baya ya mayar da ni ba.
“Nagode Baffa Allah ya kara maka daukaka yasa kafi haka.
Ya amsa yana jin dadin ADDU AR abdulhameed din ya mike zai tafi gidan gona yace su karbi key din dakin su daya ke gidan wanda shi ya ware musu shi tun tuni in sunzo suke yada zango duk da dan Baffa Sufi din abdurrahaman ba halin su daya da su Hameed din ba shiyasa ba sosai suke jone ba kamar yadda suke da mustafa da Tsagera wanda shima dan ummulkhairi ne kasancewar abdulhameed shi daya ga iyayen sa sai Allah ya zuba mishi kawa zucin yara yana son yaga yaro a gidan su yayin da Haj laila kuma ta kayyade iyalin a shi daya Tak take so ya isheta rayuwa sai abdulhameed yake son su Mustafa da shafik wato Tsagera har suka hadu wur daya suka dunkule kowane kuma da sunan da yake amsawa na tantiranci .shi dai Abdulhameed shine Boss saboda iya rike girma da kuma harkar girma.shi kuma Mustafa Tero saboda iya hada mugunta . shi kuwa shafik Tsagera akwai dagiya da kuma safawa idon sa kwalli ya Kuma fege mutum da rashin. kunya shiyasa yaci sunan Tsagera.
Wannan itace haduwar ukun su Abdulhameed Mustafa da shafik wanda iyayen su suke ciki daya uwa daya uba daya amma sun fi zama gidan distinguish Mukhtar don can ne suke yadda suke so gidan su mustafa da shafik kuwa sai dai aje ayi gaisuwa ga ummulkhairi da abubakar da Usman sai fa yanzu da suka yada zango a gidan Baffa alkali.
Haj safiya ta kawo musu key din dakin wanda yake tas babu datti sai kayan kallo da gadaje da komai na bukatar matasa irin su ga kuma mai aiki da zai gyara musu dakin don haka sai suka lafe gidan Baffa alkali wanda kaji ba sa yankewa a gidan tabbaccin dai mai gidan gona ne da gidan.
Kwanaki biyu suna gidan Baffa alkali a yau kuma Abdulhameed ya matsawa Tero ya raka shi gidan Alh iro ya kai kanshi ya yankee mishi kowane irin hukunci kuma ya roki auren Nadiya.
Tero ya dauki makullin dayar motar Baffa alkali suka fice zuwa gidan Alh iro gidan kudi.
Washington.
Da safe Haj laila take ta kiran wayar abdulhameed taji yaya ya kwans? amma sai taji wayar a kashe duk da can suke nufin zuwa da sun shirya amma ka ida ne sai ta fara kiran shi taji lafiyar sa amma sai taji wayar a rufe.
A gaggauce take shirin tana fadawa distinguish wayar Hameed a rufe .
Suka taho suna kara magana akan yadda za ayi a dawowa da Abdulhameed lafiyar sa ko ta wane hali ne in dai kudi suna magana to zasuyi amo
Sai dai me? suna shiga dakin da Hameed din yake suka tara’s da babu kowa sai filin gadon yayin da hatta kayan asibiti da suke jikin sa ya cire ya watsar akan gadon.
A Rude Haj aila ke lekawa toilet da sauran dakunan tana son gano abdulhameed amma yayi batan DABO.
tashin hankali mai tsanani ya wanzu ga Haj laila da distinguish wanda ya futa yana neman majinyaci da mai jinya a nan ne ake sanar musu da tafiyar su jiya da dare.
Haj laila ta sauke ajiyar zuciya tana fadin
“Ni na san akwai abinda yaron nan yake sakawa a ranshi tunda yace ya gama kwana Nigeria na san hakan yake nufi damuwa ta kar zaman jirgi ya mayar mishi da ciwon baya.
“Muje mu yanki tikitin komawa nigeria tunda ya dakin ya tashi me ragaya zata tsaya jiran?
A Ranar su distinguish Mukhtar Biro suka hawo jirgi suka nufo Nigeria ina direban gidan distinguish din ya iso filin jirgi jiran saukar su har jirgin ya sauka suka shigo mota haj laila na tambayar isah yaya jikin abdulhameed din bai kuma tashi ba ?
Isah ya dube ta yana fadin, “Haj wane Abdulhameed din ? Ai yanzu nake shirin tambayar ku nace Ina mai jiki haj?
Distinguish ya cabe zancen yana fadin
“Yo bai zo gidan bane Isa? tun jiya ya taho fa?
“Wallahi ranka ya dade bai zo ba ko dai ba Nigeria ya taho ba?.
A zabure haj laila ta zaro wayar ta tana kiran Mustafa amma wayar shi a kashe shima abdulhameed din wayar shi a kashe.
“Na shiga uku Ina yaron nan ya shigs? me yake nufi ne da hakan ? sai Haj laila ta saki kuka hankali a tashe shima distinguish Mukhtar Biro hankali a tashe don sun san akwai abinda abdulhameed yake nufi. Da sauri distinguish ya lalubo wayar shi yana kiran shafik ya kuma sami shafik din yana tambayar shi Ina abdulhameed yake shafik?.
Shafik din ya amsa da baiga abdulhameed ba.
Hankalin distinguish Mukhtar Biro da haj laila yayi masifar tashi na rashin sanin inda Abdulhameed ya makale, “Wannan yaro yana saka min ciwon kai wallahi . Yaro ba a Isa a saka shi ko a hana shi ba? yanzu me yake nufi kenan?
cewar distinguish Mukhtar wanda yake cike da tashin hankali.
Haj laila ma ta zuba hannaye saman kanta kamar mai shirin saka kuka ko da yake taki kad’an za a wuce da ta rusa kukan.
“Duk ma inda suke suna tare da mustafa amma Ina suke shi da ba lafiya ba? kar dai yana gidan su yarinyar nan? bana ko shakka yana can tunda ya mayar da ruhin sa gidan su.
Cewar Haj laila wacce tayi maganar da tabbacci
“Don yana mahaukaci sai yaje gidan su ya tare ? To yaje ya tare din in ma yace uwar yarinyar ce uwar sa yaje ana haka ai.
“Yaya kake wannan maganar distinguish? ba haukan shi ne abun ji ba sai lafiyar sa don Allah ka je gidan nasu ka gani ko Yana can .
“Ni zan bishi a can din don uban sa ? yaje ya tare ya dade bai mayar da iyayen ta madadin mu ba .
“Ni bari na bi shi tunda ba zaka fahimci abinda nake fada maka ba yanzu idan da ajali ba shikenan ya zama tarihi ba ? mun samu ya dawo kuma kana auna mishi ashar sai kace ba daga asibiti ya taso ba,? Ta mike kenan sai ga Tsagera ya shigo yana fadin
“Daddy kunji abdulhameed yana gidan Baffa alkali yanzu na gamu da mustafa yake fada min hakan.
Distinguish ya dubi Tsagera yana fadin
“Gidan Sufi kace shafik? Ai kuwa zanci mutuncin yaron nan wallahi me yake nufi wai?
bai san cewa Sufi shine babban mak’iyin sa a duniya fiye da mutuwar da ya soma?.
Ya dubi haj laila yana fadin, “Kinji iskancin yaron nan? duk gidajen yan uwa ya rasa wurin sauka sai gidan Sufi? me wannan yaron yake nufi da ni ne?
“To shi Sufin ba dan uwan ka bane da in yaje can yake laifi?.
“Ba kin san muguntar da ya nuna min ba? ni na saka aka sauke shi sai kawai yaje can gidan shi ya tare? yaja min abin magana da gori wurin Sufi?
“Ni dai yanzu tunda yana can alhamdulillahi kuma yanzu bari naje na duba shi naga jikin nashi.
Ta mike tana daukar jakar ta ta kira Tsagera ya taho tace ya dauko mota ya kaita gidan Baffan su alkali mai shari a Sufi
Tsagera ya kwaso ta a mota suka nufi gidan Baffa alkali
Tero ya kawo abdulhameed har kofar gidan iro ya faka motar inda Tero ya fito zuwa wurin masu gadin yayi musu sallama yana neman ganin mai gidan wanda yace bakin sa ne
Zubairu ne yayi musu sallama da shi ya kuma bude musu kofar get suka shiga da motar su
Alh iro yana saman sa aka sanar dashi yana da bak’i don haka ya sauko ya fita ya bude falon da ya ke saukar bak’in
Abdulhameed yana dafa sanda yana tafiya a hankali don har yanzu akwai sickness a tare da shi amma muhimmancin Nadiya a gareshi ya wuce na lafiyar tashi don ruhin sa ne daidai da darajar Nadiya
Alh iro ya dubi abdulhameed da Mustafa da suke shigowa da sallama ya kuma boye mamakin da tunda dama Kaisar yace mishi bai mutu ba har zai bayyana gashi kuma Yana bayyana.
Ya amsa sallamar su yayi musu nuni da mazaunin manyan kujerun suka zauna Abdulhameed yana zama da kyar mustafa na Taya shi zaman
“Sannun ku da zuwa Babu lafiya ne ?
cewar daddy Alh iro wanda ya fada da tausayawa a fuskar sa Mustafa ne ya amsa mishi da cewa bashi da lafiya.
“Ayya Allah ya kara lafiya yasa zakkar jiki ne.
Suka amsa su duka a tare kafin Abdulhameed ya zamo daga saman kujerar yana gaishe da Daddy shima mustafa ya zube a gaban shi yana gaishe shi ya amsa yana Kara yiwa Abdulhameed ADDU AR samun sauki
Sukayi shiru sun rasa ta inda zasu fara Alh iro ne ya katse shirun da fadin
“Ban gane ku ba yara daga ina ? kune ai bak’in da ake maganar suna son gani na ko?.
Da sauri abdulhameed ya amsa da cewa
“Kwarai kuwa Daddy mune ni sunana abdulhameed Mukhtar wannan kuma sunan shi Mustafa dan uwa na ne .
“Masha Allah sannun ku in ce dai lafiya ko,?
“Eh to Daddy lafiya lau qmma wata alfarma nazo nema wurin ka .
“Kar ka damu abdulhameed in dai ina da wannan alfarmar sai nayi maka ita in sha Allah sai dai in bani da ita ne .
“Alhamdulillahi Daddy nagode dama nine yaron da yayiwa Nadiya yarka fin karfin da nayi mata har al amura da yawa suka faru shine nazo in baka hakuri in roki gafarar ka don Allah ka yafe min abinda ya faru wallahi Allah Daddy nayi nadama ba kad’an ba .
“Ayya abdulhameed kar ka damu kaji na yafe maka Allah ya baka lafiya wallahi na yafe maka kowane bawa cikin kuskure yake ni ma ina da kuskuren da nayiwa Ubangiji nake kuma son ya yafe min in nace ba zan yafe ma abdulhameed nayi yaya da abinda ke tsakani na da Ubangiji na? don haka na yafe maka .
Abdulhameed ya sunkuya a gaban Alh iro yana fidda kwalla yana fadin
“Nagode Daddy Allah ya yafe maka ya yafe mana don Allah ka sake yi min wata alfarma ka bani auen Nadiya don nine nafi cancantar na aure ta tunda na Karbe budurcin ta nine ya kamata na aure ta .
“Banda wannan alfarmar Abdulhameed don ba zan iya yi maka ita ba gaskiya don ba zan baka auren Nadiya ba don kar nayi maka karya don maganar gaskiya ma Nadiya na gama fidda mata miji yana nan gefe Daya kaga bai kamata na yaudare ka ba don na san abunda ba zai yuwu bane to ni yadda bana son ayi min karya haka bana yinta don aji dadi.
A tsorace abdulhameed ya dubi Alh iro cike da tsoro da tashin hankali don yadda ya zaci saukin al amarin bai zaci akwai turjiya ba.
“Kayi hakuri daddy don Allah. na zaci karimci daga gareka tun kafin nazo sai da nazo kuma na gane kallon Karimcin da nayi maka na rage ka Akan yadda kake to don Allah don ANNABI kar ka rike ni da laifin da nayi maka ka hana ni auren Nadiya idan kace ba zaka bani auren ta ba daddy sai naga kamar ba ka yafe min rokon da nayi maka ba wallahi Allah shine daya an jarrabe ni da son Nadiya fiye da irin son danakewa ruhi na matukar zan rasa ta to zan roki Allah ya gajece min numfashi don na huta.