Skip to content
Part 48 of 55 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

“Luba wallahi idan kika kuma min maganar nan zakiyi nadamar abinda kikayi kar ki kuma min maganar nan.

“An gama hajjaju sai wace magana kike so nayi miki?

“Ta yadda zamu koma nijar mu gyaro abinda muka bata.

“A yaushe zamu koma Niger din? Luba ta tambaya da sauri tana kallon keena.

“Yanzu mana kina zaton zan bari a dauki wani dogon lokaci ne?

“To ai gaki ga hanyar nan kina iya tafiya amma ni don nan da sati daya ma albarka wallahi ba zaw kuma dosar hanyar nan ba duk wannan gubalar da muka shi kina nufin mu sake dosar hanyar? toke kam kina da wannan damar amma ni kan wallahi banga mai mayar da ni waccan hanyar da tafiya tamkar ta mai yada shege ba tunda kinga wuri ai  shiyasa na nuna miki kin san hanya kin san dajin to ki tafi kawai ba dole sai da ni ba.

“Ai wallahi kinci uwar karya kin kwana da yunwa luba yadda muka je tare  haka zamu koma wallahi  don ba zan koma ni daya ba kuma wallahi sai kin koma gobe goben nan kinji na tantse miki.

Luba ta gwalalo idanu tana kallon keena da take rantsuwa akan komawar su Niger.

“Uhum to maji ma gani wai an binne tsoguwar da ranta hajjaju sakeena ungo awarar ki wallahi kici ko ba komai zata rage miki kaifin  yunwar da kikeji kuma kyautar masoyi ce.

“Uwar ku luba ke da shi har da awarar.

luba tayi murmushi ta aje mata ledar awarar ta fice tana fadin

“Ki daiyi istigifari don ba a zagin hatsi da abinci don wata rana sai kin neme su baki samu.

Keena ta kasa tsaye da zaune musamman idan ta tuno fuskar malam Ango mafita kawai take nema amma ta kasa samo ta sai fa ta ta juya Niger ta sako aiki amma da wane kudin ? A canja mata da kudin da ta fara biya tunda aiki bai ci ba ai kuma kudi basu ciwu ba.

Malam Ango kam dare ya raba amma shi idon shi biyu ya kasa rantsawa fuskar keena kawai yake gani da wani irin bege da soyayyar ta yake ji yana huda zuciyar sa har yayi ta sambatun kaunar ta a cikin baccin da ya kwashe shi  kuma matar shi taji abinda yake fada amma ta saka mishi ido tana mishi uzuri

Washe gari tun da safe kuwa malam Ango ya buga sammako ya nufi hostel din su keena ya faka motar shi yana jiran fitowar wani ko wata da zai tambaya keena amma har rana ta fito bai ga wanda ya gitta ba inda kuma a can gidan aikin shi ana ta neman shi babu shi dole aka kira shi ya kuma taho da burin komawa

A ranar dai har dare bawan Allah nan ya kai amma bai samu ganin keena ba haka ya zuba zarya sai fa in an kira shi ya tafi amma yana nan yana dakon Tsammani.

*****

Mai shari a justice Sufi biro yana zaune tare da Yan uwan shi abubakar da Usman da suka zo taya shi murna suna ta firar zumunci har zuwa lokacin da suka yi niyar tafiya ya kuma rako su wurin motocin su sai ga abdulhameed ya shigo da motar sa inda mai shari a ya soma mishi fads akan tukin mota alhalin ga ciwo a jikin shi .

“Baka da hankali ne Abdulhameed kake tukin mota a wannan yanayin da kake? Ina Mustafa ko shafik?.

“Kayi hakuri Baffa nayi kuskure amma zan kiyaye

Ya fada yana bashi hakuri kafin ya dubi su Baffanin shi abubakar da Usman yana gaishe su suka dube shi cike da mamaki suna hada baki wurin tambayar abinda ya same shi saboda basu san yaji ciwo ba kai duk ma wani tsalle da akayi abu daya suka sani a cikin shine sauke Sufi amma ciwon abdulhameed da shari ar sa babu abunda suka sani .

Usman ne ya ruko Abdulhameed yana fadin

“Abdulhameed sannu baka da lafiya ne?

Abubakar ma ya amsa yana mishi sannu yana kuma fadin bai sani ba.

“Amma yaya Mukhtar baya kyauta mana ko a labari bai fada ba?.

“Kuyi hakuri hidima ta mishi yawa ne ku biya ta gidan sai ku jajanta mishi

cewar mai shari a justice Sufi biro .

“Sauri nake gaskiya ba zan iya biyawa abdulhameed Allah ya baka lafiya kaji sai na shigo zan zo na duba ka   cewar abubakar da shima yake zazzafa kamar dan uwan shi  Mukhtar biro shiyasa ma idan akwai wanda Mukhtar ke shakka a cikin yan uwan sa to abubakar ne .

Sukayi sallama da mai shari a justice Sufi suka wuce

Baffa alkali ya kama hannun abdulhameed yana fadin

“Yaya ne D’ana akwai damuwane a fuskar ka har bata boyu ba meye?

Suka wuce cikin falon nashi suka zauna abdulhameed na fadin

“Baffa Allah ne ya jarrabe ni da kuinar yarinyar da nayiwa abin nan shine naje na samu baban ta na roke shi ya bani auren ta smma ya hana nayi mishi zarya yafi a kirga amma yaki shine Daddyn nata yake fada min tana da ciki sakamakon abinda nayi mata don haka ba zai bani auren ta ba ni kuma Baffa a wannan ciwon da na hadu da shi ance ba zan iya haihuwa ba shine Daddy ya rude yace dole sai ya karbo yarinyar saboda Daddyn ta yace mishi zai zubar to daddy yaje amma ya dame Al amarin don ya sa hukuma ta kama baban yarinyar har ana kulle su kaga ya kara lalata abun shine nazo wurin ka  don Allah Baffa kaje min ko kai zaiga kimar ka ya yarda ba zai zubar mata da cikin ba.

Mai shari a ya gama sauraren Abdulhameed yana sauke ajiyar zuciya yana fadin

“Abdulhameed in fada maka gaskiya zaka yarda,?

ya amsa da sauri yana fadin

“Eh Baffa.

“To gaskiya abinda akayiwa uban yarinyar nan ba ayi mishi adalci ba . Abdulhameed an dauki yarsa an keta haddin ta don ta nemi Kare kanta aka tozarta uban ta shin kana ganin uban ta a yanzu zai kalli wanda ya tozarta shi da kima? duk ba wanna ba yaya Mukhtar yaci mutuncin uban yarinyar nan da nuna mishi madafun iko suna hannun sa hukuncin da na yankee ma daga shi yayi ya kai shi Abuja inda sukayi mishi yadda yske so aka kashe wani wanda ya fanshi rayuwar yarinyar da cewa shine yayi kisan alhalin shaidu sun tabbatar da cewa ba shine yayi kisan ba . sai bayan an rataye shi ne ya mutu kai kuma gakk ka bayyana. to abdulhameed duk ba wannan ba mu aje wannan maganar gefe daya mu koma Akan wacce kazo da ita . shin a yanzu me kake son mallaka cikin yarinyar ko kuwa auren ta kake so?

Ya fada yana duban abdulhameed

“Baffa ni duka ina son na mallake su da auren nata da kuma cikin in zai yarda.

“to ni kuma zan iya zuwar maka neman auren ta amma ba zan iya tsayawa gaban uban ta nace fan cikin ta nake maka begin ba saboda cikin yarinyar nan Abdulhameed sunan kai kayi shi ne amma nata ne ita daya sai in taso ne zata baka amma ba iko irin wanda yaya Mukhtar ke son nuna wa ba. na wa aka basu kudin sadakin auren yar su? ce min babu sai kawai a keta mishi alfarmar yarsa kuma a tilasta shi bada dan don dai milkin mallaka ake abdulhameed? ba zan iya tsaya maka a wanna ba amma auren ta kam nine dama mai nema maka shi amma cikin ta babu kotun da ta Isa ta karbe shi daga garesu ta baku Abdulhameed sai fa in kotun zalunci ce amma nak da hurumi akan cikin da fan ta tunda ba auren ta kayi ba aure shi yake bawa miji ya’ya smma haduwar titi to rabuwar titi ne ya’ya sun zama na mace shine ake cewa shege to ni na san gaskiya ba zan yi abinda babu gaskiya ba don haka auren ta Kam ni ne mai nema maka shi kuma ba a yanzu ba sai ta haihu shine ta fita idda amma yanzu neman auren ta zai iya zama laifi amma idan ta haihu ka fada min a ranar ma ana iya daura auren ku  ina fatan ka fahimce ni abdulhameed?.

Abdulhameed ya gyada kanshi hawaye suna taruwa a idon shi sai dai a yau kam bai fahimci Baffa slkali daidai ba don yadda yaso baiyi mishi ba dama nan ne kawai yake da tabbacci amma sun samu kuskuren fahimta shi da Baffa alkali duk nasiha da nuni da yayi mishi da kuma ayoyin al kur Ani da yayi ta kawo mishi misslai amma zuciyar soyayya ta rufe idon ganin abdulhameed har s yau ya soma jin hushin. Baffa alkali.

Ya jima kafin ya ja jiki ya shiga motar shi ya bar gidan yana zubar da hawaye don a mayen son abu biyu yake Nadiya da dan cikin ta  duk yadda ya kyauta ta zato ga Baffa alkali yau dai ya bashi kunya.

Ya iso gidan su cike da damuwa haj laila ta tarbe shi tana tambayar abinda ya faru.

Ya soma zubar da hawaye bai ce mata komai ba yayin da distinguish ya sauko yana kallon shi yana zubar hawaye .

Cike da tashin hankali haj laila ke tambayar shi amma bai dago ba bare ya bata amsar tambayar ta tayi tambayar duniya amma bai fasa zubar da hawaye ba kuma bai dago ya ce musu uffan ba

Distinguish Mukhtar ya rike hannun shi yana fadin

“Fada min abdulhameed me faru ne? kaje gidan Sufin ne?.

Sai a nan Abdulhameed ya dago yana kallon uban yana fadin

“Naje Daddy amma Baffa alkali yayi min abinda ban zata daga gareshi ba domin kuwa bai goya min baya akan komai ba sai ma ya nuna min cikin Nadiya ba nawa bane nata ne kuma ba zai iya tsayawa a gaban uban ta ya nemi alfarmar a bani ciki ba tunda ba auren ta nayi ba amma zai nema min a auren ta shima ba yanzu ba sai ta haihu wallahi daddy ban zaci hakan daga Baffa alkali ba nayi zaton alheri daga gareshi .

“Ai da nace maka kar kaje baka yarda ba abdulhameed amma ta ina Sufi ya zama masoyin ka mutumin da ya nuna bare yafi dan uwa? yanzu da yayi maka haka ai ka dane ba masoyin ka bane tunda bai karbi daya daga cikin bukatun ka ba don haka a yau zan saka a sato yarinyar nan mu fice abroad da ita ba zamu dawo ba sai ta haife cikin ta in yaso mu dawo duk matakin da uban ta zai dauka ya dauka ya dauka amma yau din nan in sha Allah ko gidan iro nake so a dauko min akwai yan jagaliyar mu na siyasa yan a mutu zasuyi min yadda nake so don haka kwantar da hankalin ka zama cikin shiri don zamu bar Nigeria ne soon na zabi alkali ya yankee min kowane irin hukunci ne matukar dai na tsira da dan cikin yarinyar can abdulhameed ace komai na yarda don na zama gane hakan kawai zanyi na zauna lafiya na kuma karbi dan ka cikin sauki amma in ba hakan ba wancan mutumin zaija ni k’asa ne to ya shirya kaini kotun koli akan na saci yarsa zan karbi haddin hakan matukar dai na tsira da dan dan ka Abdulhameed.d

Haj laila da abdulhameed sukayi murmush don sun gamsu da hakan sai kawai distinguish Mukhtar biro ya jawo wayar shi yana Kiran wayar wani dan jagaliyar siyasa mai suna zarto wanda har kisa yana iya yi. Zarto ya iso kofar gidan distinguish Mukhtar biro ya kira wayar shi ya fito yana sauke zarto a karamin falon shi don yana ganin zarto bai Kai matakin zuwa babban falo ba bare kuma seat room saboda abun matsayi ne iya girman kan iya girmamawar da za ayi maka.

“Allah ya kauda makiyan ka shugaban k’asar gobe sai kayi wallayi ko Nigeriar ba kowa cauuu uban gidan mu maganin kukan mu Allah dai Allah dai mai daraja uban mara’s uba mai uban ma kaine uban sa kaine kakan sa don kutumar uwar su aha Eh aha Allan dai Allah dai .

Distinguish Mukhtar biro yayi murmushi yana fadin

“Zarto aiki nake so kayi min duk runtsi kar ka dawo min kace ba a dace ba don zamu muguwar matsala da kai don haka nutsu ka kama kanka kuma kar ka sake ka sha shegun kayan ku na shaye shaye bare ta fada maka karya ka gane? .

“Ai mai gida na aje kwaya wiwi kawai nake dan  hayak’awa itama in gari yayi zafi bana samun damar tsotsa ta bare kwaya da roci.

“to yayi maka kyau karbi nan ka dubi hoton nan da kyau bari na auna lafiyar kwanyar ka me idon ka ke nuna maka a hoton nan?.

Zarto ya karbi hoton yana zube idanun shi akai ya kuma hango kyakkyawar fuskar Nadiya da surar ta .

“Na san yarinyar nan mai gida yar gidan iro GIDAN KUDI ce na tab’a ganin ta a wani wuri lokacin da wani mutum s garin Jos yazo nan ana ce mishi shaid’an yace yana son ta amma yarinyar nan tayi mishi wani irin wulakanci bata san shaid’an bane da ta san shi da bata fara abinda tayi ba .

“Na yarda kwanyar ka so fresh now zarto ka san me nake so kayi min?.

“Sai ka fada mai gida.

“wannan yarinyar nake so ka shiga gidan iro ka sato min ita duk runtsi duk wuya kar ka bari a wuce kwana biyu kana da ladar aikin ka har dubu dari biyu da hamsin idan ka kawo min ita. tashi kaje kar ka kawo min uzuri bare tsautsayi ko sab’ani nasara kawai nafi so da ganewa ka San Hakan.

Zarto ya kwartse da ihu yana fadin.

“Ita kadai kake so na kawo maka mai gida ko har da yan gidan duka? kai idan gidan ma dukkan shi kake so a dauko maka shi dungurun gum daga mazaunin sa za ayi hakan bare wannan jaririysr anyi an gama ne yasin.

“Ita kadai ma nake so jeka sai naji ka kome kenan ka kira layin da na kira ka da shi in baka same ni ba ka turo min text message.

“Ban iya massage ba mai gida sai dai kawai na kira ka.

“To jeka ina jiran ka.

“Ba zan samu wani abu ba mai gida ?

cewar zarto wanda yayi request din wani abu. Distinguish Mukhtar ya kirko kudi dubu ashirin ya bashi ya karba yana gwama mishi hannuwa yana sarawa.

“Sai an bi ta taka oga koko aji duka wallayi.

Ya fice a guje ya bar gidan distinguish Mukhtar biro.

tafiya ta kama Alh iro da haj Aliya zuwa Senegal zuwa bikin yar wani abokin kasuwancin su wanda zai aurar da yarsa tafiyar da akayi ta da Fati dama an shirya ta don a yaddda aka shiryya ta har da Nadiya sai kuma ga al amarin cikin ta don haka daddy yace da Kaisar ya kai Nadiya jama are wurin yakumbo halima har zuwa lokacin da zasu dawo  sai ta dawo

A washe gari kuwa Kaiser ya dauki mota ya yiwa su daddy da mama da fati fatan alheri da ADDU AR Allah ya kai su lafiya ya dawo da su lafiya.

Nadiya kam kuka take na zaman jama are da zatayi har na kwana bakwai  don ta so tafiyar nan Senegal don an shirya ta tuni don har da alh sule da iyalsn shi aka wuce Senegal

A ranar zarto da yan tawagar sa suka damfaro gidan Alh iro har suka sami nasarar shigar sa don sun hauro ta baya ne amma ga mamakin su gidan babu kowa hatta yan aikin babu kowa sai fa masu gadin kofar wanda suka san suma da shirin su don haka a ranar zarto ya sanarwa Distinguish wanda yace mishi duk dare suke zuwa har masu gidan su dawo in ma basa nan to kullum su kaiwa gidan ziyara.

*****

<< Azurfa Da Zinari 47Azurfa Da Zinari 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×