Skip to content
Part 5 of 80 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Rukon da kaisar ya yiwa Nadiya shine abinda yafi yi mata ciwo domin kuwa tana ganin akwai raini ace wannan dan tsurut din ya rungume ta ya rungumi kirjin da take ganin ba kowane ya kamata da hakan ba face mutum daya wato show Wanda shine kadai yake rungumar ta ta yarda har da sumbar baki da wata irin azama Nadiya tayi nufin watsar da kaisar wanda take ganin ba zai mata wahalar watsar wa ba amma sai taji sab’anin zaton ta domin kuwa ta kasa kwatar kanta daga rukon da yayi mata bare har ta samu damar k’aska’ntar dashi ta hanyar kada shi amma sai taji tamkar wani ingarman namiji ne ya rike ta duk kokarin kwatar kai da taso ya kasa sakin ta sai wani takaici ya rufe zuciyar ta.

“Yauwa kaisar rike min yar banzar yarinyar nan don Allah kar ka bari na fita falon nan. Cewar Haj Aliya wacce take rike da bulaliyar hannun ta ta iso tana zubawa Nadiya da karfi.  “A yi mata hakuri mama ba zata sake.

“Za ta sake ne Kaisar ai wannan yarinyar tafi kama da ibilishiya ba mutum ba kaisar.

“Har wannan yarinyar ta san ta fita da dare sai sha dayan dare ta dawo? Ta finciko Nadiya daga bayan kaisar tana fadin, “Gidan uban wa kika je jiya sai dare kika dawo? har kin san zuwa wani party?  Ai ina zaune ina dakon zuwan ki sai sha dayan dare kika shigo munafuka kina sand’a duk akan idona aka yi.

Daddy ya soma saukowa daga saman benen shi saboda jin fadan haj Aliya.

“Me yake faruwa ne Aliya? Ya fada yana sauka inda Nadiya take zaune taki matsawa duk dukan da ake mata ko gezau wai sai an gaji an barta dama haka take da kafewa. duk dukan da ake mata ba shine damuwar ta ba irin sbu biyu. fati da ta fadawa Haj inda taje da kuma shigowar kaisar gidan su.

Daddy ne ya karbe bulaliyar dake hannun Haj Aliya yana bata hakuri.

“Daddy yarinyar nan tana shirin gajiyar dani Allah ya sani bata da hali me duniya zata dauke ni idan aka ga fati da kyakkyawar tarbiya ita kuma a watse? anya ko Kai zaka fahimce ni? Wallahi ni kaina ba zan iya yafewa kaina ba bare duniya. jiya fa da ka nemi yarinyar nan bata gidan nan wai sai da na tambaye fati take fada min kawayen ta ne suka gayyace ta wani party wai shi together sai sha dayan dare ta dawo gidan nan. duk wannan bai ishe ta ba sai da ta kaini kwano wai Nadiya ce kewa fati gori wai gidan su matsiyata ne in tana da zuciya ta koma misau anya kuwa zan iya Daddy? Anya kuwa ba zanyi nadama ba?

“Ba zaki yi ba Aliya Addu’a itace mafita kuma zanyi mata fada ba zata sake ba.

Daddy ya dubi Nadiya yana fadin, “Wato ke kunnen ki ba mai daukar magana daya bane ko? me yasa kike da taurin kai ne? ban hana ki duban wani mutum ki Yi mishi wulakanci ba? hatta masu aikin gidan nan nasan suna hakuri da halin ki shin ke baki san rayuwa bane? wanda fa ka wulankata a yau ta iya yuwa gobe shine wanda zai taimake ka. kuma in don kin bude ido kingan ki a wannan gidan gobe na iya zuwa da sabon sauyi wanda ba wannan ba da talaka da mai kudi duka tsarin Allah ne ba zabin mutum ba  don haka ki shiga taitayin ki kar ki bari a kara kawo min karar ki akan kin zagi wani ko kinyiwa wani gorin talauci kin manta uban fati ciki daya muka fito hala? to fati itace gaba da ke ki kiyaye kuma uban fati shine uban ki ba ni ba kuma Ni fati itace diyar da zan gani a ranar Alkiyama ke kuma ranar Alkiyama uban fati shi zaki gani ba ni ba don haka wannan maganar ta zamo ta farko kuma ta karshe da za a kuma kawo min karar ki in ba haka ba kuwa zaki sha mamakin hukuncin da zan dauka akan ki tashi ki bani wuri mutuniyar banza. Ta mike tana jin kamar ta amaye zuciyar ta musamman da take ganin an watsa ta a gaban kaisar wanda ta watsa don kawai yace yana son ta sai gashi a cikin gidan su tsamo tsamo kuma a gaban shi anyi mata fita.

ta wuce tana jin bak’in ciki tamkar zai shake ta ta mace.

Daddy ya juyo yana duban kaisar yana fadin

“Kaisar ka tashi lafiya?

kaisar ya zube yana gaishe da Daddy inda mama ke fadin

“Karadin yarinyar nan ya tayar da shi na san ya taho kawo ceto

yayi murmushi yana gaishe da ita yana fadin dama ya tashi.

“bari na karasa kitchen yanzu za a kawo maka kayan kari tun da safe an saka ni hararrami .

ta juya zuwa kitchen inda fati ke soya dankali da agada mama kuma ta dora naman da ta fara dafawa jiya tana ta fada akan halin Nadiya

tuni suka kammala suka kawo kayan falo inda kaisar da daddy suke ta fira mama tace fati ta zubawa kaisar amma Daddy yace a kai mishi nashi sashin shi don ba lallai zai iya sakewa yaci ba

dole kaisar ya koma dakin shi inda mama ta shirya mishi a kwando fati zata dauka ta kai mama tace

“Kira  min wannan marar mutuncin taxo ta kai mishi ke kiyi wahalar girkawa kuma ki yi wahalar fita kaiwa? Ita zata Kai shi kuma duk aikin gidan nan na yau ita zatayi shi.

fati ta aje kwandon ta wuce daki inda Nadiya ke ta zagaye falon tana tambayar kanta ta ina wannan shegen ya biyo ya zo gidan su? Kuma me yazo yi a gidan su har ya samu shigar da ta kula ya samu har da ambatar sunan shi a bakin mama wai kaisar? meye manufar zuwan shi gidan?.

fati ta shigo tana fadin

“Mama na Kiran ki.

ta watsawa  Fati wani matsiyacin kallo .

“Wato duk kashedin da nayi miki akan fadawa mama inda na tafi baki ji ba da yake munafuka ce ke wacce ta gado munafunci wurin matsiyatan iyayen ki saida kika fesa mata na je together? to ki sani zaki ga abinda zai faru wallahi kuma nan gidan in dai ba na uban ki bane sai kin barshi  shegu matsiyata kaska masu rab’ar mai jini makwadaita kawai.

ta fada tana wucewa ta bar Fati da dauke kwallar idon ta . Ita kam da mama zatayi mata adalci da ta barta ta koma misau ko don ta huta da gorin talauci da ake mata.

mama ta dube ta tana harara tace

“Dauki wannan kwandon ki mikawa kaisar kizo duk aikin da kika san na gidan nan ne yau ke zakiyi shi wallahi sakarai dabba dake .

Nadiya taji wani wbu ya soki zuciyar ta kaisar din da mama take magana shine wannan gayen?.

tayi tsaye turus har sai da mama tace

“Ko baki ji abunda nace bane?.

“To Mama ina nasan inda zan ganshi baki fadi inda yake ba?

“Yana Nan a wancan sashin da aka shirya.

ta figi kwandon ta fice mama na fadin

“In kika zubar da wbu daya a ciki wallahi sai jikin ki ya gaya Miki.

ta shiga sashin da wata irin azama tana mamakin waye wannan da har ya samu matsayin bashi masauki a cikin gidan nasu? .

Kaisar yana cire rigar shi zai sauya da jessi wacce yake motsa jiki da ita nadiya ta shigo babu ko sallama ya juyo Yana fadin.

“Wa alaikissalam

tabi jikin shi da yake lullube da gashin gargasa tana yamutsa fuska cike da wulakanci da son ta keta shi.

ya miko mata hannu yana murmushi yana fadin

“Assalamualaiki ya habibaty.

“Nabi habibaty da gudu ba we. kai tsaya da Allah waye kai? me ya kawo ka gidan mu? waye uban ka da her ka samu masauki a gidan KUDI?.

ya tako zuwa gaban ta tamkar zai rungume ta yana fadin

“Baba na Allah ya yi mishi rasuwa tun jimawa . ni ba kowa bane maraya ne kuma nazo gidan ku don na nemi aiki na kuma samu zan rika yi miki wanki da guga in kuma zama dan aiken ki duk yadda kike so dani haka zakiyi amma ki sani ina nan ina kaunar ki ba kuma zan daina ba don Ina ji a jiki na ke matata ce to be.

bai rufe baki ba ta auna mishi mari.

“Idan ka kuma hada kanka dani wallahi zakayi nadama banza kawai .in ma wani abu ka shiryo ka shigo gidan mu da wannan munafuncin to zan fadawa daddy ya sallame ka kuma wannan kayan abincin kayi kad’an wallahi nayi maka dakon abincin da zaka ci baka isa ba matsiyaci da kai .

ta suri kwandon ta fice tana fadin gara ta kaiwa karnukan gidan su . ai kuwa can ta nufa ta juyewa karnukan abincin ta wuce tana huci.

fati da ta fito farfajiyar gidan ta zauna ta hade kai da tafukan hannun ta taga fitowar nadiya da kwandon ta nufi dakin Karen ta juye abincin da naman ga karen ta wuce abinta sai ta gane halin Nadiya kam sai lahira ba dai a duniya ba.

fati ta mike zuwa kitchen ta hada wani abincin ta nufi kofar kaisar wanda ta iske yana motsa jiki duk ya hada zufa . wani abu ya sauka a zuciyar fati wacce bata san ko meye ba amma dai tana jin wani abu akan kaisar.

ta ajiye mishi abincin ta juya bata ce ko uffan ba shima shima ya bita da kallo bai tanka ba .

Mama da ta tabbatar da sai Nadiya tayi wani abu akan kai abincin nan sai ta bi bayan ta sai gashi kuwa taga ta fito da kwandon abincin duk da bata ji maganganun da ta zubar ba

tana kallon ta har dakin karen da ta juye abincin ta juyo dole mama ta juya inda Nadiya ta shigo da kwandon bata ce komai ba.

“Bakiyi tunanin kin bar error ba ta dawowa da komai ? In na tambaye ki sai kice min ya cinye komai kenan a lokaci daya? ke yanzu kin fi gane ki bawa kare da ki bawa dan adam? to wallahi kinji na rantse sai kin girkawa kaisar dukkan abinda kika bawa karen nan maza ki shiga kitchen ki dora girki  dama zuciya ta ta bani sai wani abu ya faru to maza wallahi dukkan abinda kika san yana cikin kwandon nan sai kin sake girka shi ni kam an jarrabe ni da kaddara Allah yasa na cinye wannan kaddara.

“A rude Nadiya ta juyo Jin abinda mama ke fadi Wai sai ta sake girkawa kaisar wani abincin.

“Wallahi mama ba zan girkawa wancan katon wofin abinci ba dan aiki ne fa wanki zai mana da guga mama salon kisa ya raina ni zanyi mishi girki? ai ni nafi karfin na taka na Kai mishi abinci har dakin shi bare kuma ace ni zan yi mishi girki wallahi mama ba zanyi ba.

<< Azurfa Da Zinari 4Azurfa Da Zinari 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×