Skip to content
Part 50 of 55 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Karaf wannan kalmar ta shiga kunnen king da yakumbo tace ya shiga su gaisa da Nadiya don ya soma kama mata mikawa kwastoma dan waken a waje suna ta labarin duniya don Yakumbo akwai son labari musamman ma ace akan abinda ta sani ne

King ya dubi Nadiya da take mishi wani banzan kallo yana fadin

“Sannu ya kike?

ta kawar da kanta bata tanka mishi ba .

King ya juya ya barsu ya koma wurin yakumbo halima don tafiye mishi komai a zuwa jama are.

“Me yasa kike haka ne sweetie? tare fa muka zo da shi amma yayi miki magana ki share shi.

“to ka dake ni mana uba na tanda na kasa amsa shi.

“Ba zan dake ki ba amma kar ki sake bana so wannan ai wulakanci ne .

Ya fada yana mikewa tabi shi da kallo cike da bak’in cikin yadda yake mata magana da karfin iko kamar wani uban ta.

Da haka sukayiwa Yakumbo halima sallama tana cewa king sai yaushe kuma? yace in sha Allah zasu dawo

Suna tafe king bai cewa Kaisar komai ba shima kuma yana jin kunyar wulakancin da tayi mishi duk da ya zabi zaman shi a mota amma ya hana sai gashi rabon yaja mishi wulakancin.

“Kayi hakuri don Allah king .

“Meye kake bani hakuri Kaisar?.

Kayi hakuri wkan abinda yarinyar nan tayi maka da na san hakan wallahi da nace kayi zaman ka a mota.

“Kar ka damu ni bani da damuwa akan hakan tunda kai kaji ka gani Kaisar ai dole nayiwa tare kara nima na koyi shanye wulakancin ta Ina maka ADDU AR Allah ya zaba maka alherin sa akan ta.

Distinguish Mukhtar biro yana ta faman kiran  wayar zarto wanda yake can yashe yana jiniyar sarar da maccid’o yayi mishi wanda saura kadan ya sauke mishi kafada idan kuma yace asibiti zaije ba za a karbe shi ba sai da hukuma to yace akan me yaji ciwon? sai kawai yaje ya sami masu dorin karaya aka shafa mishi magani da kuma daure wurin sai dai ciwo babu wani sauki ashe ciwo dai dole sai anje asibitin

Wayar zarto taki samuwa don ta ma fadi a gudun ceton rayuwa shiyasa ma ya kasa samun shi

Haj laila da abdulhameed sune suka fi kowa damuwa da son jin yaya aka kare amma har kwanaki bakwai babu amo bare labari inda suka kagu da zuwa yanzu sun bar Nigeria amma tamkar an aiki bawa garin su

Kullum distinguish Mukhtar biro cikin neman layin wayar zarto yake amma har yau a kashe

Haj laila ce tace ya cigita zarto a wurin wanda suka san shi mana don ya jiyo musu labarin shi

Ai kuwa distinguish ya soma neman zarto wurin yan uwan shi yan jagaliya har ya samo labarin shi yana asibiti kwance babu lafiya wai an sare shi da adda kad’an ya rage s sauke mishi kafada

Abinda ya nunawa distinguish Mukhtar biro cewa lallai aiki baiyi nasara ba a can ne ma aka samu matsala.

Keena da malam Ango ya hana sakat babu damar ta fito kamar mai madubin duba ko kasuwa ta shiga sai sun hade da shi ya kuma biyo ta duk da gudun hijirar da tayi daga hostel din su zuws na su surayya amma bata tsira ba

Surayya ta dube ta tana fadin

“Wai ni kuwa wannan mutumin kanshi daya kuwa keena ko ina yana biye yana sambatun kaunar ki ni fa ganin abun nake kamar wani sihiri wallahi.

Keena ta motse fuska tana fadin

“Fidda kamar nan surayya wallahi sihiri ne nayiwa wani sai ban dace ba ya fada kan tsohon nan wanda aka ce sai na kawo lambar waya ko ta mota ashe motar tsohon ce na ga gayen s ciki yanzu haka cikin tashin hankali nake surayya bokan da yayi aikin yace sai mun sadu ko ya aure ni ko kuma zina ni kuma babu daya da zanyi shine nake cikin wannan janhurun masifar na rasa yadda zanyi.

“Subhallahi keena me ya Kai ki bin boka da hankalin ki? duk fa wanda yaje gun boka ko wani mushriki babu shi babu Allah har tsayin kwana arba in yanzu ke in aka tambaye ki wace riba kika samu a zuwa wannan wuri kice me?.

“Surayya duk ba wanna nake ba yanzu tunda naje ai sai dai a tarbi gaba kawai. ni yadda zan karya sihirin mutumin can shine damuwa ta don wallahi baki ji yadda nake ji ba idan naga tsohon can yana biye da ni.

“to Allah ya sauwake amma karya shi ba zai zama wahala ba ga al kur Ani nan ki lazimce shi akwai ayoyin karya sihiri bari na nemo miki su ki jaraba in sha Allah kikayi amfani da su ke da mutumin can zaku wanye lafiya duk da ni Shi ya fi bani tausayi kuma kece kika dauki alhakin sa sai Kuma Allah ya saka mishi  tsoho kamar wancan ko ya aure ki ai sai dai yayi ta fada miki yana son ki amma lafiya ma bata ishe shi ba me zai miki?.

Surayya ta ganowa keena syoyin karya sihiri ta kuma fada mata abubuwan da zata nema har ta samu ta sha ta kuma bawa malam Ango shima in sha Allah zata Karya ko wane irin sihiri ne.

Anyi biki na girma a k’asar Senegal harka irin ta masu kudi har aka Kare bikin da ya dauki Sati biyu cur ana shagulgula . bayan nan kuma uban amarya yace su alh iro ba zasu taho a cikin satin ba sai sun huta gajiya.

A takaice dai sai da sukayi sati hadu cur kafin sukayi sallama da iyayen amarya suka dauko hanyar Nigeria

Kaisar suna waya da daddy da mama fati ce basa waya don haka ranar da zasu taso Daddy ya fadawa Kaisar wanda ya tafi tarbar su a filin jirgi ya dauko su suka taho gida

Sai washe gari Daddy yace yaje ya dauko Nadiya a jama are inda cikin ta yake cikin wata na tara tayi wani irin kiba cikin ta ya fito sosai ga kumburi da tayi sasur takalmi ma baya shiga kafar ta  idanu sun shige can ciki sunyi loko yayin da hancin ta ma ya kara girma Kai komai na jikin ta ma ya girma duk wanna gayen da i ili yanzu babu ta zama kayan nauyi .

Kaisar ma ya kare mata kallo cike da tausayawa ta shigo motar tana numfashi don dole ka tausaya mata ciki yayi girma na ban mamaki.

Haka suka taho yana Jan ta da labari amma bata kulawa don tafiyar motar ma ji take kamar ana wurwura ta kamar ta ce ya tsaya ta huta.

Da kyar suka iso bauci ta kasa fitowa motar sai da Kaisar ya kamata amma Kuma wata sabuwar baya da kugu duk suka rike ta kasa motsi.

Ya dube ta ganin yadda take hada zufa yasa ya tambaye ta.

“Yaya dai ,?

sai kawai ta fashe da kuka tana shirin bajewa k’asa amma da sauri Kaisar ya tallabe ta a jikin shi azaba ta ishe ta ta soma kuka wiwi don gaba daya kugun da kafafun sun rike ga kuma mara da ta soma daukar nata ciwon tamkar zata tarwatse.

“Zan mutu wayyo zan mutu baya na .

ta soma kuka da kwararato inda Kaisar ya dauke ta cik duk nauyin ta da kuma K’arantar shi in ace zai iya daukar ta a misali  ne zaka karya ta musamman ka kalle shi dan kad’an sai gashi yayi sama da ita duk da ko a zahirin ta tafi shi tsayi bare kuma ga nauyin ciki ga na kumburi.

Yana tallabe da ita tana kara kwarmata ihun ta don ciwo kam kamar jira ake ta iso gidan nasu yayi Mata sallama.

Haj Aliya da taji ihun da ake kwarawa ne ta taso da sauri sai taga Kaisar tallabe da Nadiya.

“Subhallahi Kaisar lafiya?

“Wallahi mama  muna zuwa nan ta soma kuka ban san me yake damun ta ba.

Haj Aliya ta ruko ta kallo daya tayi mata ta gane nakuda ce don hannun tar yana dafe da marar ta  ga uwan zak’in nakuda da ya soma bin kafar ta.

” Subhallahi Kaisar maza haura saman benen ka kira min Daddy ai nakuda ce take maza ka fada masa ka zo ka kai mu asibiti.

Ya haura saman da sauri yayiwa daddy bayanin da mama tayi mishi suka sauko tare inda Daddy yace da Kaisar yayi maxa ya fidda mota su tafi asibiti.

Tuni kuwa haj Aliya da Ade suka kama Nadiya zuww mota Kaiser ya gyara mota aka saka Nadiya wacce nakuda ta tahowa gadan gadan  a guje Kaisar taja motar suka nufi asibiti.

Shigar su asibitin yayi daidai da zuwan su Abdulhameed wanda gefen cikin ke wa ciwo dama a cikin bayanin likita yace zai rika yin ciwon time by time to har da ma dai damuwar Rashin tabbas akan Nadiya da cikin ta sai kuma ga ciwon dole Tero  ya dauko shi a mota suka nufo asibitin sai kuma ga motar Kaisar ta faka inda ake cewa ga mai haihuwa nan jama a su danyi hakuri .

Tero da abdulhameed wanda yake dafe da gefen ciki yaga an shigo da Nadiya rirrike da ita gaban shi yayi wata matsiyaciyar sarawa haihuwa? Nadiya ? ya’yan shi?  sai yaji ciwon nashi ma ya neme shi ya rasa.

tuni kuwa aka shiga da Nadiya dakin haihuwa yayin da aka bar Kaisar a mota haj da Ade sune jiran tsammani yayin da Tero kuma yake duban abdulhameed yana fadin

“Yarinyar nan ce fa da ka lailaya wa aiki gata nan zata zaro aikin da ka bata homework anya ba zaka shiga ka taya ta nakudar ba?.

“Tero ai ni sa a ce ma ta kawo ni asibitin nan ko ba komai zanga dana da ake neman yi min fin karfi kuma a nan din za a zuba a kwashe kai dai mu karanta salati sha daya ga ANNABI Allah ya sauke ta lafiya.

Abdulhameed ya soma Karanta salatin ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam da fatan Nadiya ta sauka lafiya yayin da Tero yake mishi kallon  ba lafiya  gareka ba.

Nas din da ta karbi  labour din Nadiya ta fito da sauri tana karasowa wurin su haj Aliya da ke tsaye cikin jiran tsammani tana fadin

“Haj ku kawo kayan tarbar haihuwar ta sauka ta baby boy.

Abdulhameed da ya zubawa nas din ido har ta karaso ya kuma ji abinda tace sai yaji wani irin farin ciki yana sauka a zuciyar sa baby Boy? mai sunan daddy ya iso kenan.

Da sauri Haj Aliya ta juya tana fadin

“Yi hakuri don Allah nas wallahi duk a rude nake ban ma iya tunawa da wasu kayan haihuwa ba Bari na shiga bakin asibiti sai na samo .

ta juya da sauri ta fice yayin da Kaisar yake a cikin mota ya hango haj Aliya ta fito da sauri ya fito yana son yaji mama tace mishi Nadiya ta sauka.

“Mama wani abun ake so ne?.

“Kayan haihuwa ne bamu zo da su ba Kaisar gashi har ta haihu.

Yayi murmushi yana fadin

“Alhamdulillahi kaseeran mama mai ta samu?

“ta samu namiji inji nas din .

“Mama muje mu samo kayan tunda ta sauka alhamdulillahi.

Suka fito nan bakin asibitin wani shagon baby care suka shiga suka hado komai Kaisar ya biya kudin suka dawo ciki haj Aliya ta bawa nas din kayan ta nufi ciki.

Abdulhameed da yaga wautar shi har aka kawo kayan baiyi wani motsi ba abinda ya kamata ace shine ya siyo ya kawo.

Nas ta sake dawowa tana rungume da baby boy nade a tawul ta mikowa haj Aliya shi wacce ta karbe shi tana kallon fuskar shi masha Allah yaro kato jajir da shi mai kyau.

Idon abdulhameed akan yaron yana kallon shi da wata irin kauna da soyayya ya kuma saita wayar shi yana daukar yaron hoto ba tare da Haj Aliya ta fahimci abinda yake ba.

Haj Aliya da Ade suna ta yaba kyan jariri  yayin da haj Aliya ta fita kaiwa Kaisar yaron ya gani .

Ya karbi yaron ya rungume yana mishi so irin wanda uba yakewa dan sa  yana ta murna yana fadin

“Allah ta ala ya raya su da Imani mama yaya ita Nadiyar babu dai wata matsala ko?.

Haj Aliya ta ce

“Kaga ni ban ma tambayi nas din yaya uwar ba? amma dai lafiya tunda in da akwai wani abu da ta fada amma dai bari na koma sai naji yaya ita uwar yaron

Ya mika mata yaron ta karba ta koma cikin asibitin inda sukayi taho mu gama da nas din nan ta taho da sauri tana fadin

“Haj a sake kawo wasu kayan ashe twins ne ga can tana shirin sauke wani ayi sauri da Allah.

Abdulhameed ya mike yana shirin bin bayan nas din jin tace twins ne sai kuma ya koma ya zauna yana hango twins a hannun sa.

Da sauri Haj ta mikawa Ade yaron ta fice tana kwalawa Kaisar kira ya fito mota yana fadin

“nama lafiya?.

“Kudurar Ubangiji kenan Kaisar shi kadai yasan abinda ya shirya a lamarin yarinyar nan dubi dai yadda abubuwan nata suka faro tamkar dai ace kirkirarren labarin hikaya  wai twins ne zata haifa ga ta can tana nakudar wani sai an kuma kawo kayan tarba.

“Alhamdulillahi mama bari na je na hado ai naga yadda kika hado sai a bani kamar su.

“To karbi katin ATM card din nan Kaisar sai a cire a ciki.

“Haba mama Ya’ya na ne fa  har zanji wahalar hidimar su da dawainiyar su ? abinda yafi haka ma zanyi musu ba tare da na gaji ba Allah ya raya su Akan sunnar ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam.

Ya juya da sauri ya bar haj Aliya sake da baki tana mishi rakiya da idanu tausayin shi na kamata.

ta juya ta koma minti biyar Kaisar ya kawo mata kayan ta karba ta mikawa nas wacce tuni ta gyara shi ta nad’o a tawul ta kawowa Haj Aliya.

Identical twin masu tsananin kama da juna har ta kai zaiyi wahalar banbancewa sai fa ga Wanda ya kalle su na farkon wanda yake da dan d’igon baki a kunnen shi qmma fa ba kowa ya gane hakan ba sai wanda aka nunawa.

Idon Abdulhameed akan yaran har bai san idaniyar shi tana fidda hawaye ba ba komai yake tunani ba sai yadda iyayen Nadiya zasu nemi nuna mishi bashi da hurumin komai Akan ya’yan shi wanda kallo daya zakayi mishi ka gane shine sak basu baro komai nashi ba.

“Masha Allah Allah kaine Allah Ubangijin ANNABI Musa da Harun Kuma Ubangijin ANNABI MUHD da SULAIMAN har da ibrahim. Allah ka sa yaran nan su zama cikon addinin musulunci ne ka kautar da su asalin su da hanyar yadda suka wanzu  cikin duniya Allah kar ka tabbatar da su akan asalin su amma ka tabbatar da su bisa turbar ANNABI MUHD sallalahu alaihi wassalam.

Hawayen idon Abdulhameed ya kara gudu saboda jin irin ADDU AR da ake musu na kar su tabbata akan asalin su na shegun da aka samar ta wata hanya ba ta aure ba.

Ya mike ya fice don ya koma gida ya fadawa haj laila haihuwar Nadiya.

Tero ya biyo bayan shi yana fadin

“Kai billahilazi la iha illallahu sai mutanen can sun bayar da identical twin din ko gidan uban wa aka kalli yaran can copy din ka ne sak Boss ko makahon da bashi da Ido ya shafa su zaiji kamanin ku .

Bai tankawa Tero ba sai shafa sumar kanshi yake yana furza huci a bakin shi har Tero yaja motar suka fice daga asibitin aguje tamkar masu shirin zuwa sama ta bakwai.

“Yaya ita nai jegon take babu dai wata matsala ko? Cewar haj Aliya wacce ta tambayi nas din.

<< Azurfa Da Zinari 49Azurfa Da Zinari 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×