Mafari.
“Baffa da daddy uwa daya uba daya ne su biyu iyayen su suka haife su a yan tagwaye kuma kafin su ba a haifi wani ba Bayan su ma ba a haifi wani ba shiyasa mahaifin su daddy wai suna Alh yaro wanda sunan sa yakubu ya saka musu suna iri daya wato ibrahim Ibrahim sai dai banbancin lakabi wato iro da halilu wato khalil.
Duk inda yan biyu suke a wancan lokacin zumunci ne da su da kaunar juna komai kayiwa hussain sai kayiwa hassan matukar kana son zaman lafiya
Haka su daddy suka taso Yan biyu masu kaunar juna ko ina suna tare har sukayi karatun bokon su suka kare suka tafi bautar k’asa inda tun da sukayi karatu ba su sami Rabuwa ba ko ina suna tare sai da suka tafi bautar k’asa ne suka sami rabuwa inda aka tura Baffa jihar ogun yayin da daddy kuma aka tura shi Plato wato Jos
Wannan itace rabuwa ta farko da sukayi mai tsayi ba s tare da juna ba.
Shekara daya cif suka kare bautar k’asa inda Baffa dama ya shirya maganar aure da innar mu wato Hajara don haka yana dawowa ya sami aiki da hukumar Aikin hajji ta jihar bauci don haka aka sha biki
Shi kuwa daddy bai samu aiki ba amma shima yana da wacce suka daidai ta wato mama Aliya shima Baffa ne ya kama akayi bikin daddy da mama ta tare a lokacin ma su suna da shekara uku da aure duk da basu haihu ba
Shekara biyar da auren Baffa wanda yayi daidai da shekara buyun auren daddy innar mu Hajara ta haife ni murna kamar me ? daddy shi yafi kowa murna don shi yace suna mahaifin su za a saka min
Baffa kam yace sai yadda yace haka za ayi
Mama Aliya ce take karba ta a lokacin ta goya ni bata barin Inna da aiki na da hidima ta kasancewar gida daya suke sai dai kowa da sashin sa yayin da iyayen su Baffa suke can tasu shiyyar duk da gida guda ne a nan misau
Kwanci tashi asarar mai rai har na shekera biyar innar bata kuma haihuwa ba mama ma zuwa lokacin bata haihu ba inda mama ta zamo uwa ta ta biyu don komai tana min har na mayar da komai nawa dakin ta yayin da daddy kuma ya koma jos don zuwan da yayi bautar k’asa ya hadu da wani mutumin bauci wanda yake da arziki a garin jos har ya zama uban gidan daddy don haka sai daddy ya koma can ya samu aiki a kamfanin Alh dan kyana wanda yake da kamfunna da yawa garuruwa irin su kaduna Legos da kuma sokoto don haka daddy ya koma jos ya samu siki a karkashin Alh dan kyana inda Allah ya sanya arzikin yana nan na daddy sai ga Alh dan kyana ya bude kamfanin sumenti da fulawa a garin bauci ya kuma bawa daddy Rukon kamfanin
Gaskiyar daddy da rukon amanar sa yasa Alh dan kyana ya bashi ragamar rukon dukkan kamfunna shi .
Daddy ya sami kudi sosai ya kuma ginawa Baffan su sabon gida ya kuma tallafawa dan uwan sa yayin ya biya kujera uku ta zuwa saudi Arabia Baffan su da mahaifiyar su sai Baffan mu suka tafi shi kuma ya gina gida a bauci ya kwsso mu muka dawo bauci don ni din na shi ne cewar Baffan mu
A lokacin da su mahaifin su suka dawo ne babu jimawa baban su ya komawa Ubangiji ciwon kwanaki uku abu in ya zamo na ajali ne babu wayo Babu dabara
Ya rage daga su sai haj maitan wato mahaifiyar su wacce daddy yaso daukar ta ya maida kusa da ita amma yana Jin kunyar dan uwan sa don kar yaga kamar ya gaza dole ya barta a nan misau amma kuma gata na duniya haj maitan tana ganin shi ba ga iron ba baga halilu ba ita kam sai sambar ka tsakanin ta da tilon ya’yan nata
A shekaran da ta zagayo ne daddy ya biya mana kujera da haj maitan har da innar mu da ni da mama muka tafi saudi.
Na gama primary ne daddy ya fidda ni waje karatu inda nayi kukan Rabuwa da mama da daddy don haka na tafi malaysia karatu inda acan na kwashe shekaru masu yawa
Ina can ne mama ta haife ki sai dai hotuna aka tura min wanda shine yasa ni dawowa ba tare da na shirya hakan ba
Kallo daya nayi miki fati naji a raina Allah yayi min wani Abu duk da ban san ko meye ba. A haka rayuwa ta tura inda Allah yayiwa haj maitan rasuwa bayan ta dawo daga Saudi rasuwar da ta gigita su daddy da Baffa . haj itace Idon da ta rage musu kuma ta zama alfarma a garesu ko babu komai ADDU AR ta garesu da take lullube su da tarin akhairai yau gata babu dole suka dauki hakuri irin wanda mutanen da mutuwa ke bari da kewa da jimami .
Inna ta kasance mai son ki fati har ta kan zo bauci ne kurum don ke ta dauke ki kuje misau kiyi kwanaki ta dawo da ke yayin da mama kuma take kwakume da Nadiya har bata son abunda zai taba ta amma Inna kam Fati ce ta wajen ta don haka Baffan mu ne yaxo shi yaceww mama shi kam Hajara yaxo daukarwa yarta don haka suyi hakuri fati tashi ce ta Hajara ce.
Mama kuwa ta hado miki kayan ki fati tace ai dama yaya Hajara bata so bane tunda sai da nace ta tafi da yarta tace Alkunya .
Tun daga wannan rana Fati zaman ki ya dawo misau har zuwa lokacin da na kammala karatu na na dawo na same ki kina primary inda kuma Inna ta samu haifar hamza . Fati al amarin mu Allah ne ya zana shi dawowa ta gida Baffa ya bude kamfani a misau Wanda ya danka min ragamar komai naci gaba da tafiyar da komai inda kuma lokaci zuwa lokaci Baffa na cewa Inna ayiwa Aliya kara yarta take zuwa koda mako biyu uku ne take yowa tunda yanzu ga hamza tana gani a gaban ta don shi a zaton shi yara Inna ke son gani a gaban ta bai sani ba kaunar ku a jini take . ni kuma a lokacin da kikayi min nisa sai al amarin ya tsananta a gare ni Ina so nazo ni bauci amma sai tarin ayyukan da suke nan su sha kaina sai lokacin da na samu kai Baffa ko wani al amarin ya kawo ni . naso boye abinda ke zuciya ta amma labarin zuciya a tambaye fuska don ma baki da ilimin so mai yawa fati ai da tuni zaki gano yayan ki amma baki san hakan ba ne. lokacin da Daddy yace zai hada ni aure da Nadiya naji zan fada mishi gaskiya amma kuma na san akwai abinda yake boyewa shiyasa na kame duk da an samu tuntube tsakanin Baffa da Inna to amma sai Allah ya juya Al amarin sai gashi ashe tuni daddy yayi imagin din mu a matsayin couple har kuma Allah ya tabbatar bayan na fasa marurun zuciya ta ya kuma tabbatar min da yaso hakan amma gudun Kar ya shiga hakkin dayan mu sai gashi alkawarin Allah ya cika akan mu fati kinji yadda alakar mu take da halaccin auren mu ina fatan kin fahimci komai yanzu,?.
Fati da ta zubawa yaya Alabo Ido ta sauke ajiyar zuciya tana fadin
“Na fahimta yaya yanzu ni din yar mama ce amma Nadiya take min wannan wulakancin da gorin? ko da yake na fahimce karamcin mama da Daddy wata kil don Nadiya tana yar fari shiyasa suke mata kara da Alkunya. amma ka sani Yaya Ina kaunar Inna ta da Baffa na kai din ka zama jinin jiki na tunda ka zamo jinin Baffa na da Inna ta wallahi Ina son ka Ina kaunar ka ka rike wannan a ranka har abada bani da kamar Inna ta da Baffa na yaya Alabo duk yadda kake so kayi dani .
ya rungume ta yana fadin
“Duk yadda nake so fa Kika ce?
ta kada mishi kanta tana fadin
“Ina nufin abinda na fada Yaya alabo ko ba komai Ina fatan ni da kai muyi zumuncin da yafi wanda muka gada gun iyayen mu kai sunan baban su Baffa ne da kai ni kuma mama tace min sunan haj maitan ne dani kaga mun zama madubi gun iyayen mu to yaya Ina mai tabbatar maka da bani da kamar ka a yau dun mijina kuma dan uwa na da kake da matsayi biyu a gareni .
Ya kara rike ta yana kai bakin shi a bakin ta yana fadin
“Nagode da wannan matsayin dear in sha Allah sai munyi zumuncin da ya zarce na su daddy da Baffa sai mun aje musu Ya’yan da zasu zama farin ciki a garesu da mu da kuma musulunci.
Yana rungume da ita Yana kissing din ta ta Kuma bishi da duk yadda yake so .
tun daga wannan rana Fati da Alabo suka shimfida wata irin rayuwar auren su bisa soyayya da kauna mai yawa wacce ta fito da su a wasu ma aurata da suka zama abin so da koyi yayin da alabo baya jin wahalar ya aje komai don ya tarairayi matar sa da nuna mata babu ya ita a gareshi. Itama bata Jin wahalar yi mishi komai Yake so da kuma jurewa bukatar sa a komai shiyasa suka shiru abun su kowa yana jin dan uwan sa a bugun numfashi har ta kai basa son suyi nisa da juna in ma sunyi din to suna like da juna a waya.
Don haka siyayyar da ake ta sha tuni aka samo baby amma basu san hakan ba don bata laulayi bata ciwon komai shiyasa sai dai ta Kara haske yayin da shi kuma ya kara dafe mata don ta sauya mishi irin canjin cikin da ya samu a tare da ita wanda a yanzu ne yake jin ta da wani irin sirrin da ya kara mata wata daraja ta musamman.
Wani irin matsiyacin tsamin ruwan wine din nan ya budade falon har hawa kai yake.
Da sauri Kaisar ya toshe hancin sa yana mikewa tsaye yana kallon kwalbar wine din da ta baje a kan tiles tayi watsa watsa yayin da ruwan cikin kwalbar ya soma fidda hayaki irin tafasar da lemu mai gas yake yana fidda kumfa .
Ya dubi fasasshiyar kwalbar ya kuma dubi Nadiya wacce babu ko darr a tare da ita sai takaicin fashewar kwalbar da rasa wannan damar a yanzu wacce take ta tsumayi.
“Giya? A nan gidan? me kike nufi ? kece da wannan aikin ko kuwa wa?
Kaiser ya jera mata tambayoyin duka a rude amma bata ko nuna taji abinda yake fada ba bare ta bashi amsa.
“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un
Kaisar ya fada yana jin wani irin abu mai kama da nadamar auren yarinyar nan itace take shan giya ko kuwa me zatayi da ita?.
“Me idona yake gani Kaisar?
suka juya su duka a tare inda suka ga daddy tsaye a bakin kofar kuma ga alama ba yanzu yazo ba ya jima a wurin wata kil ma duk abinda ya faru akan idon shi ya faru.
Tun lokacin da Nadiya ta shigo tana zuba sauri Daddy yaga napep din da ya aje ta yaga yadda ta shigo ya zuba mata ido yana zaune a karkashin inuwar umbrella amma ita bata ganshi ba don haka yabi jakar da take zugewa da kallo inda ya hango wani abu mai Kama da bakin bindiga shine abinda yaja hankalin sa har ya bi bayan ta zuwa cikin sashin nasu don bai yarda da yarinyar nan ba sai ga komai ya faru akan idon sa.
Tsoro mai tsanani ya kana Nadiya ganin daddy a bakin kofar su.
Kaisar da yake toshe da hanci ya yi maza ya saki hancin da ya toshe ya iso gaban daddy yana fadin
“Daddy dubi Nadiya? giya a kwalbar yarinyar nan Daddy Ina aikin me har ta soma shan wine? ban tab’a zaton zatayi wannan wayewar ba .
“Kaga a yanzu kai kanka zaka yarda Allah ya amsa rokon da nayi mishi na ya bude min abunda yake a lullube gashi kuma ya amsa min Kaisar na gani .
Daddy ya fada a gusace ya daga kafa zuwa inda Nadiya take kame amma tana ganin fuskar daddy ta san sauran zancen don haka ta daga kafa zata matsa amma kafin tayi hakan ya saka kafar shi ya tad’iye ta ta zube a kasa ya kuma kifa mata mari ya sake kifa mata wani ta soma kwarara Uban ihu abinda ya sanya haj aliya ta bazamo don karar kai da ji ka San ba ta lafiya bace.
Haj Aliya taja tayi turus tana kallon daddy da ya saka belt din Kaisar yana laftar Nadiya ta san hakikatan al amarin mai girma ne don daddy Yana da hakuri matuka gaya akan Al amarin Nadiya.
“Har kinyi wannan wayewar? Wallahi tallahi baki Isa ba ba dai a nan ba ni kam Allah ya sani na soma nadamar abinda nayi wannan yarinyar.
Haj Aliya da ta rike shi tana fadin
“Kayi hakuri nima yau dai na tuna maka abinda kake tuna min kar ka zube ladar ka don Allah kayi hakuri.
Daddy ya dago kanshi Yana fidda hawaye ya dubi haj Aliya yana fadin
“Aliya naga jarrabta Allah ya sa ta tsaya iya yarinyar nan dubi fa yarinyar nan da giya Aliya ? har ta san rayuwar giya? ta yaya Allah zai barni bayan na san tana nan tana cutar da bawan Allah maraya wanda bashi da kowa san Allah sai ni sai jama ar ANNABI? .
Ido a warwaje haj Aliya take rufe bakin da tabude tana mamakin maganar da taji Wai giya ga Nadiya.
“Giya? ke kike shan giya ?
Ta fada tana kallon Nadiya wacce ta girgiza kanta tana fadin
“Nifa mama ban tab’a sha ba zan sha ne don cikin nan ya zube ance in aka sha wine yana zubewa shine zan sha don gaskiya ba fa zan haifi cikin nan ba wallahi.
mama ta kuma kifa mata mari tana fadin
“Ke kam Allah ya wadaran halin ki wallahi ban zaci kina da wani kyakkyawan asali ba wallahi Nadiya ke kam ba yar halal bace duk yadda akay.
“Ga kwalbar wine din nan kin ganta ni kuwa yanzu me zancewa Allah?.
“Daddy wallahi yarinyar nan ba zata dora maka ciwo ba wallahi bata isa ba ni kam na zame hannu na a koman ta ciki kuma da take maganar zubarwa Kaisar duk irin hukuncin da yayi maka kayi wallahi ba zamuji komai ba kai karshe ma igiyar auren yarinyar nan don Allah don ANNABI ka sauwakewa kanka ita.
Daddy ya nufi hanyar ficewa yana fadin
“Yarinyar nan tafi karfi na amma kamar yadda nace zan bata mamaki to hakan ne zai faru Kaisar hukunci ma yana hannun ka matar ka ce ikon ka ce sai yadda kaso zakayi.
“Ni dama zakayi zuciyar nan ka sauwake min wahalallen auren ka da har godiya nayi maka.
Ya dube ta bayan mama da daddy sun fuce yana fadin
“Ba zan iya yin hakan ga zuriar daddy ba . ko babu komai shine komai na kuma albarkar sa kike ci ba kuma zan gajiya da yi miki alfarma ba saboda shi ni fa tun da na shimfide ki na ga koman ki na kuma yi yadda nake so da koman ki ai babu wani abu kuma . to meye ma? meye ban gani ba? meye banji yadda yake ba? shima cikin zan so naga irin kokarin ki Akan sa amma kar ki wahalar da kanki alkawarin Allah mai cika ne.
“Ni kuma wallahi wannan cikin ba zai kuma kwana bakwai a jiki na ba zanje a cire min shi don bana bukatar sa kuma idan kace ba zaka sake ni na ba? to in kaki ji wallahi ba zaka ki gani ba “Amma kuma kar ka ga laifin kowa idan kaga abinda zai same ka akan rashin sakin nan don wallahi kofofin balaki ne ka budewa kanka in ka shirya sai nace maka Bismillah amma in ka so ka sauwake min shine kawai zaman ka lafiya don har abada bani da hadi da matsiyaci irin ka babban goro sai magogin karfe muna da nissan tazara a tsakanin mu gara kawai ka nemo daidai kai amma ni wallahi nafi karfin talaka irin ka fakiri kana da zabi na Rayuwar ka ko mutuwar ka akan rike aure na ko sakin