Skip to content
Part 67 of 68 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Washegari kuwa Keena tayi nufin komawa Niger duk da ban bakin da luba take mata akan ta hakura amma bata ji kamar zata kyale tsinannen tsohon can ba ga mari ga tsinka jaka?.

“Dama kin bar bata yawun bakin ki luba in ma ba zakije ba ki sha zaman ki amma ni kam sai na koma munyi uwar watsi da shegen can.

“Ina zan barki ki tafi ke daya bayan na san mutumin can babu I’mani s tare da shi? ai dole na biki ko don na kashe wutar da kuke shirin tayarwa.

Haka suka koma niger inda Keena ke ta shan mugun alwashin ta akan ba I’mani wanda tayi nufin nunawa rashin I’mani.

Dariyar ba I’mani ya saki har tana amsa amo a dajin ya soma fadin.

“Ke ga karamar tsinanniya kinga rashin I’mani ne shiyasa kika zo bada hakuri? to kinyi kad’an ar banten uba sai na gasa ki kafin ki gane barno ba gabas take ba shegiya tsinanniya ni zaki mara ? ba gara ki fada wuta da ranki har ki kone ba? ai baki gama ganin rashin I’mani ba don sai na karar da komai naki da wuta sai kinzo nan kin bani hakuri  .

“Ai kai kanka ka san kaci uwar karya  ka kwana da yunwa kaci kudi na babu biyan bukata kuma don na mare ka don uwar ka ka jona min wuta na kuma yin wata asara to gani nazo  ne  tsakanin ni da kai daya ya kashe daya  muga mai rashin I’mani tsakanin ni da kai  don nima zan nuna maka nawa rashin I’manin don wallahi sai na saka kayi nadamar abinda kayi kayana da ka jona wa wuta  kayi ta rayuwar ka wallahi don kai da kanka ka san ba zan barka ba ko waye uban ka sai na ganshi sai naga uban sa shima bare kai dan ta shegiya dan ta tsinanniya wallahi sai dai ko ni ko kai .

Keena ta fada tana zuge jakarta ta fita da wata shareriyar wuka wacce luba bata ga lokacin da ta dauko ta ba.

Keena ta nufi ba I’mani da wukar nan wacce bai san ta fito da ita ba tunda ba gani yake ba ai kuwa keena ta laftawa ba I’mani wukar nan a wuya .

Wata irin k’ara da ba I’mani ya fasa itace ta sa ya soma jawo wasu k’iri k’iri Yana watsowa Keena wacce ta kauce k’irin ya fada Kan kwaryar shi sai ga wuta ta Kama inda Keena ta gane da ita yaso ya konewa.

Ai kuwa keena ta jawo k’irin ta watso mishi a jiki  sai gashi  wuta ta soma bin jikin shi amma da yake ya iya surkullen tsiyar sai ga wutar ta soma sauka tamkar wacce aka zubawa ruwan sanyi.

Keena ta soma daukar duwatsu tana rosawa kan  ba I’mani wanda yake ta neman hada abinda zai kashe Keena.

ganin Yana mika hannu ya na furta wasu maganganu sai ga wuta ta biyo hannun shi ya kuma nuna keena wacce auna a guje luba ta bi ta baya  suka fice daga dajin yayin da suka bar ba I’mani jini yana bin jikin shi inda keena ta yankee shi da inda tayi mishi rotse har ta fasa mishi Kai ga kuma inda ta yankee shi ta fidda mishi jini .

Ya shafi wuyan nashi da zafi ya ishe shi yaga jini yana bin hannun sai ya yi dariya yana yage baki  tamkar mai yunkurin amai sai ga wata katuwar kunama ya amayo ta kuma fada cikin kwaryar da ke gaban shi yayi dariya yana fadin

“Kin shiga uku kin lalace sai dai uwar ki ta sake haifar wata amma ke dai kam kin gama.

Ya hade hannuwan sa wuri daya yayi wata mika sai ga hayaki yana zagaye shi sai da ya hade shi duk kafin ya bace b’at daga gindin bishiyar kukar.

Duk wata hanya da Nadiya ta bi don zubar da cikin nan abu ya gagara hatta da ruwan nakudar da taje aka jona mata karshe ganin zata mace a banza a wofi babu kuma biyan bukata yasa ta fincike shi da kanta sai da kyar ta gane kanta dole ta sallamawa kaddarar nan har zuwa lokacin da watannin cikin suka cika tara daidai .

“Ranar juma a da safe ta wayi gari da nakuda wacce tun kafin ma ta fita hayyacin ta ya gane tana bukatar agajin asibiti amma da ya nemi ya kaita sai ta dube shi a lalace tana fadin .

“Ai gara na mutu ni da koma wane shege ne zan haifa da dai na yarda ka kwashe ni ka Kai asibiti gara duk mu mutu.

Bai tsaya nuna jin zafi ko haushin maganar ta ba ya fita da mota ya kuma fadawa mama halin da badiya take ciki da sauri kuwa mama tace ya kamo ta ya fito da ita su tafi asibiti.

Ya fita ya koma sashin su inda kukan kyakkyawwr yarinyar yayi mishi marhabin.

Ya danna kanshi dakin Nadiya inda ya same ta tana kallon kyakkyawwr yarinyar wacce take cikin jini tana tsilla kuka yayin da take nata kallon fuskar Kaisar sak sai dai ita kam ba yar kad’an bace da girman ta amma fuskar ta babu inda ta baro uban ta tamkar ya tofar.

Mamakin ta wannan yarinyar ce dama ta rike nata wuya? kamar ta da Kaisar yasa mata jin tsanar yarinyar fiye da tsanar yan biyu da tayi.

Kaisar ya dubi Nadiya da irin kallon da takewa yarinyar wacce take ta tsala kukan ta iso duniya lafiya ya kuma tabbatar da ba zata iya yi mata komai ba sai kawai ya juya ya sanarwa Haj Aliya an ma haihu.

Haj Aliya ta biyo shi inda ta iske Nadiya ta bar wurin ta kuma bar yarinyar tana ta tsala kuka.

bata fahimci komai ba ta kira Ade ta gyara yarinyar ta nade ta a tawul tana fadin

“Masha Allah yarinya bata baro gida ba Allah ya raya ta da I’mani.

Kaisar yana rungume da yarinyar ya futo ya haura saman daddy ya kai mishi Siyama wacce zata taci sunan mahaifiyar sa nai Rasuwa wato Amina.

Daddy ya karbi yarinyar yana murmushi yana fadin

“Masha Allah Kaisar wannan ai copy ce da namiji ce kam za a jima ba a gane ku ba amma jinsi ya nuna ku Allah ta ala ya raya ta da I’mani anyi mata huduba ko? .

Ya amsa yana murmushi yace.

“Anyi mata daddy Siyama ce tunda tana bin Ramadan don na daidai ta musu sahu zata amsa Siyama amma sunan marigayiya na saka mata .

“Masha Allah Allah yasa tayi halin mai sunan bari na tashi na shiga kasuwa.

Kan kace me? Daddy ya hado wa Kaisar kayan barkan Siyama kaya kuwa masu daraja akayi ta yankan nama amma mai jego ta shiga lissafin sauran satittikan da zata fece America wurin Venus din ta don sun gama shiryawa da show lokaci kawai ake jira su haye jirgi su wuce America.

Daddy yayi ta hidima fiye da wacce akayi a haihuwar yan biyu don yana ganin Kaisar ne nashi yar Kaisar itace tashi amma su Ramadan na Kaisar ne.

Kwana biyu da haihuwar ta gama yanke hukunci don haka ta nufi daddy ta zube a gaban daddy y wanda yabi ta da kallo yana jin tamkar ya make ta .

“Daddy don Allah a taimaka mini a raba ni da auren Kaisar don gaskiya ni  kam ana cutar dani  bai iya komai ba fa na auratayya yadda yake min ba haka baban yan biyu yayi min ba yafi shi iya komai to  a raba mu kowa ya nemi wani.

Wani irin tsoro da firgici ya shigi daddy jin kalaman Nadiya na kunya da nuna rashin d’a A.

“Ana cutar ki ? to mutane nawa ne aka cuta a duniya? ko kuwa sai kece ba za a cuta ba? to bari na fada miki anzo gabar da komai zai bayyana matukar kika tsallake auren yaron nan wallahi ba zaki saka min hawan jini ba idan magana ta bugi magana wata kil zakiyi ladabi.

“Daddy ka fahimce ni don Allah nifa dama ba son yaron ban nake ba kuma ni gaskiya ina son shiga Venus kuma gaskiya Kaisar yayi min kad’an baya iyawa dani  dole na cutu tunda ba ya iya gamsar dani sai dai ya barni da bak’in ciki to in ba a raba mu  ba akwai matsala don gaskiya na gaji daddy  baya iya min baban yan biyu yafi shi iyawa.

Kunya tayi matukar kama Daddy jin abinda take fada wai Kaisar yayi mata kad’an

Haj Aliya da ta shigo ganin zuwan Nadiya ta kuma ji kukan da Nadiya ta kawo sai ta kame baki sake take kallon su da yardarwa kanta Nadiya tana iya tashin duniya baki daya da mugayen halayen ta .

“Tashi daga gabana tun ranki bai baci ba yar iska marar tarbiya Allah ya wadaran halin ki Nadiya na gaji da halin ki kullum kara lalacewa kike maimakon ki daidai ta sahu to ki rike wannan a ranki kin jawo wata magana matukar baki bi auren ki sau da kafa ba wallahi Nadiya dab da kike da ki kunya ta ki je ki baje wannan maganar a faifai ki fahimci me nake nufi ki saka hankali da lura in kuma baki gane ba ki nemi sani akan hakan.

ta mike tana ficewa dama don kar a ga laifin ta yasa ta zuwa neman izinin tunda kuma ba a fahimce ta ba to ba za a ki fahimtar yaren da zata ganar da su ba don haka ta soma da aikin farko.

Kwanaki bakwai yarinya ta amsa sunan ta aminatu amma sl kunyar ta Siyama saboda sunan mahaifiyar Kaisar ne mai rasuwa Allah ya musu Rahama

tunda Nadiya ta haifi Siyama bata kuma zuwa hannu ta ba Kaisar ne koman ta har ya dora ta akan nadarar da ya jima da zama costumers a siyan ta wato nan don haka tuni Siyama ma da bata san yaya dandanon nonon uwar ta ayke ba don ita kam tazo ne a lokacin da ake tsaka da son gayun da zai fito da martabar kirji yaushe kuwa za a bata shi ta kayar da shi da tsatso? yan biyu ma nadamar basu ake bare wata Siyama da sam ba ayi baraba da zuwan ta ba.

Siyama Kan kukan dare gareta akasin su yan biyu da suke da hakuri ita kam Siyama kuka gare ta don haka ta soma cika cikin Nadiya da kukan daren ta wanda yake hana ta bacci har tayi ta kwarawa yarinyar ashar musamman ma da ta gane bai son a zagi Siyama ita Kam sai ta kama sunan ta na yanka ta kwara mata ashar.

Kamar yau dai da cikin yarinyar ya ke mata ciwo tana ta kuka Kaisar yana rurrugata  amma taki shiru abinda ya hana Nadiya bacci  yayin da Kaisar yake bawa Siyama maganin ciwon cikin don ya fahimci yara da lalurar su don haka ya bata greiy water ta kuma sami sauki har tayi bacci don haka da safe sai yayi nufin kaita asibiti don a duba mata kalar magani

Nadiya Kam da taji yau yarinyar nan ba zata kuma hana ta bacci ba zatayi maganin ta don haka Kaisar yana shiga toilet da nufin yayi wanka  Nadiya kuma ta yankewa Siyama hukunci na daukar ta da sauri ta nufi tank din ruwan su yayin da Ramadan ya fasa kuka don shi nan wasa yakewa Siyama to daukar da Nadiya tayi mata yasa shi kuka don ba sa son a dauke ta sai su sai Kaisar don haka jin kukan Ramadan yasa Kaisar ya fito da sauri don bai fara wankan ba yaji kukan yaron sai kawai yaga Nadiya rike da Siyama tana nufar tanki abinda ya nuna mishi cikin tankin take nufin kai Siyama ta jefa sai yaji wani irin tashin hankali mai tsanani ya sauka akan zuciyar shi da wani irin sauri ya bi bayan ta don ya karbo Siyama amma yana zuwa tana saka yarinyar a cikin tankin.

Jirgin Us citizen mallakin k’asar amurka ya sauke a babban birnin k’asar amurka wanda yayi dakon Nadiya da show .

Karon farko da Nadiya ta tako garin amurka don babu yadda batayi ba daddy ya fidda ita waje karatu amma yaki saboda sanin hali yafi sanin kama don haka ya barta a bauci tayi karatun du har ta kare shi sai gata yau a garin da yake yak’ar ta wato America.

Babban hotel show ya Kama ya sauke ta tun a ranar da suka sauka kuma vigo ya iso don yaga kyawun Nadiya da show yake ta kambama shi.

Vigo kam ya kad’u da ganin surar Nadiya don tana cikin danyen jego shiyasa ta kara fita a kyau kuma koman ta ya cika ya batse .

Show ya gabatar mata da vigo a matsayin wanda Yake daya daga cikin agent na masu shirya venues kuma wanda zai tsaya mata. abinda Nadiya bata sani ba shine abinda aka fada mata akwai coge da manuba da yaudara a cikin sa kuma da ace a iyakar film din shedancin kawai suka tsaya wata kil ace da sauki . don har manyan yan ta adda akwai a cikin masu shirya venues din wanda yake cike da fasadi da yada alfasha .

Vigo ya rungume Nadiya yana mata highly welcome yana kare mata kallo da ganin lallai ta mallaki matanci.

Suka gaisa tana mishi godiya duk da harshen turanci suke maganar kasancewar su Vigo black American .

Atun washe gari aka soma kai Nadiya manyan shagunan yarfa make up irin na garari don gyara mata fata da kuma gashi  hatta da gashin ta sai da aka saka mata shi cikin wani inji ya sauya mishi kala ya koma jaja jaja aka kuma yi mishi salon da ya koma tamkar irin na matan America kafin fatar jikin ta wacce ake shafawa mayuka da kayan gyara.

Hatta da kayan sakawar Nadiya sun sauya zuwa guntayen siket da matsattsiyar riga masu fidda sura

Cikin kankanin lokaci Nadiya ta zama women Americans kuma one in town domin gashin ta ma ya zama abin kallo saboda bata saka mishi komai bare wai dan kwali bare kuma surar ta da kullum cikin saka kayan da suke nuna ta suke. Kayan da take sakawa da takalma classical ne kuma duk Vigo ne ya dauki nauyin siya mata da sunan venues ne take bawa duk matan da suka shiga

Abdulhameed da yake nan American ya samu sauki ne Haj aila da sumayya da suke tare da shi distinguish bai san tarayyar sumayya da abdulhameed ba wacce ita sumayya a k’asan zuciyar ta son Abdulhameed take har ta lallaba shi da bashi shawarar ya kama karatu a nan American koma wace irin damuwa ce da shi karatu zai tafiyar mishi da ita .

Haj laila ma taji dadin shawarar sumayya wacce tayi hakan don kafa gwamnatin ta kuma tayi sa a shima abdulhameed din baya son komawa Nigeria a yanzu saboda mikin da yake ranshi dole ya yarda ya koma karatu Haj laila kuma ta sanarwa distinguish Mukhtar biro cewa abdulhameed ya koma karatu ba zai dawo a nan kusa ba har suga abinda hali yayi.

Distinguish yayi maza yace

“Yayi mishi kyau gara mishi hakan amma kinja kunnen sa akan yar gidan Sufi da take can ko? babu shi babu ahalin Sufi na raba su sun kuma rabu don ni da Sufi ko A LAHIRA bana fatan haduwa to haka shi da duk ahalin Sufi sunyi hannun riga da na san ma abdurrahaman zaije can wallahi da ban taho ba don naci uban sa da kyau amma ko yanzu zan je gidan Sufi na zubar da kaya uban kowa ya taka don a kiyaye ni ni da ahali na tunda Sufi ya zama na gurbi shegen dangi  to Allah yasa nagan shi ko wani nashi a cikin abunda ya shafe ni yaga yadda zan yage shi irin yagewar da akewa takardun bogi.

Sumayya kam tayi nasarar dora zuciyar Abdulhameed akan yadda zai so ta don yana yawan fada mata ya rufe babin soyayya amma tana kokarin dawo mishi da bara bana   ita dai sai dai tayi murmushi tana fadin

“In ka rufe babin soyayya baka tunanin akwai zuciyar da take bukatar ka fiye da irin sanin da kayi ana so?  ka taimaka min kar ka rufe babin soyayya don na kusa na kawo maka sak’o mai nauyi wanda yake bukatar bude babin soyayya. Ranar da ta kama ta daya ga watan sabuwar shekara itace ranar show up Venus don haka Nadiya taga mata Kyawawa ta kuma ga karshen kwalliya da sura ga Mata kimanin dari da tamanin da suka Shiga Venus Wanda dukkan sw suka kasance yaruka daban daban in ka cire Nadiya ita daya kwallin kwal da take ausa fulani  sauran duk yare ne na sauran kasashe masu makotaka da American.

<< Azurfa Da Zinari 66Azurfa Da Zinari 68 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×