Skip to content
Part 69 of 71 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Yana gama fadar hakan ya tsinke wayar shi ya bar Nadiya da rishin kuka domin kuwa da gaske ta na cikin balaki musamman na farmakin mazan da suka same ta a arha a inda aka hada su domin kuwa an haska fuskar ta ta zama would wide shiyasa ta zamo ganima don shi Osting ma bai damu da inda yake ba da matsayin shi na wanted A a shi anan ma ya soma chaje Nadiya sukayi ta karba karba shi da abokan sa kafin wadan da suke a nan tsare shiyasa ta soma kiran balaki wanda ta so ceto amma ga abinda daddy ya fada mata wanda yayi matukar tayar mata da hankali .

me daddy yake son ce mata?

Ita din ba yar sa bace ? wace fatin yake nufi? Fatin da tasha gorantaww talauci da cewa sun zama kaska masu bin masu jini? hakika bata tab’a baje yawan kalaman da mama da daddy suke nanata mata ba sai a yau da daddy ya fito mata a mutum.

Kuka take tana nadamar abinda tayi yayin da kalaman daddy sake caza kwanyar ta matuka gaya.

Daddy ya dubi haj Aliya yana rattaba mata kiran wayar da akayi mishi da wanda Nadiya tayi mishi ta kuma karanta mishi matsalar ta na kama su da akayi  da wasu yan ta adda a can America.

“To kuma dama mana Daddy? Ai alhaki kwikuyo ba ga irin ta nan ba? yanzu da ta kira ka me take so ayi? wallahi ni dai ban baka shawarar shiga case din yarinyar nan ba a barta da wanda ta zaba take kuma ganin sune fuye da mu.

“Aliya da lamarin yarinyar nan bai zo da wulakanci da raini ba da na shiga lamarin ta saboda dukkan abinda mukayi munyi shine don zatin Ubangiji to amma ni a yanzu na gama da yarinyar nan ta kama wasu iyayen ba mu ba ko da kuwa ta dawo to bata da muhalli a gida na.

Vigo da show da duk masu ruwa da tsaki akan shirya show up venus tun lokacin da suka ga akwai tashin hankali a yarinyar nan har an soma b’arin wuta sai suka samu suka sulale  shiyasa ma basu San cewa Nadiya da Osting ya dauko sun fada hannu ba gashi kuma babu waya a hannun Nadiya bare ta kira show  shima ya kira ta bai same ta ba don haka aka tafka uban sab’ani.

Jimy da abdulhameed da suka biyo bayan su Osting sune kawai suka kula da tsautsayin da ya fada musu don haka jimy ne kan gaba wurin kulla yadda za a bullowa Al amarin

Abdulhameed ne da jimy suka shiga case din da neman yadda al amarin ya fara

Abdulhameed yasha mamaki da yaji abinda ake tuhumar su Nadiya da laifin su Osting ya shafa ya zamo bak’in fenti

Zarya ta kama abdulhameed da jimy wanda yake fadin

“Yanzu ne fa zakayi bajintar dauko yarinyar nan domin kuwa dole zata nemi taimako to kawai kayi maza ka shigar da wani percentage na kudin ka idan ka sami nasarar fidda ta sai kuyi tazoje kawai amma fa sai ka saki kudi ta yada zamu samu tayi free.

“Jimy nifa nafi son ya’ya na a yanzu da komai a Rayuwa da zan san ta yadda zan fidda ta amma da sharadin in fidda ta ita kuma ta yi alkawarin bani ya’yana zanyi hakan in ta yarda ma ni sai na aure ta tunda ina son ta.

Jimy ya kada kanshi yana fadin

“Muyi wani abu mu samu su barmu mu gana da ita muji abinda tafi bukata.

Cuku cuku jimy ya soma har ya samu wanda ya tsaya musu aka yarda su ga Nadiya.

An dauke ta daga cikin su Osting saboda ganin suna neman kashe ta da muguntar su wacce ta tabbatar mata da lallai America ta tara manyan bara gurbi kuma masu naci akan mata kamar wasu mayu.

Nadiya ta ga abdulhameed wanda bata tab’a zaton gani ba . ta tuna kalolin wulakancin da tayi mishi amma a yanzu Daddy ya goge mata harda ta soma tunanin mahadin AZURFA DA ZINARE da Kuma tambayar kanta wacece ita?.

Abdulhameed ya mika hannu yana shafa fuskar ta ya kuma rike hannun ta ta fada jikin shi tana kuka tana fadin.

“Please help me my brothe I need to helping you.

“Me kike so na taimake ki da shi? kina son na fidda ki a nan?.

Ya tambaye ta yana rungume da ita tayi maza ta amsa tana fitar da  hawaye.

“Zanyi duk yadda zanyi don ganin na fidda ki a nan amma fa da sharadi? kin amince?.

ta dube shi tana fadin

“Na amince amma wane irin sharadi ne?.

“Zan fidda ki in kika fita kuma ki bani ya’ya na da suke hannun ki in kin yarda shikenan na tabbatar da ba zaki kuma sati a nan ba.

“Na yarda in ma kace har da ni kaina duka zan yarda.

“Ai kin san ke din ma na so ki amma uban ki ya nuna mana shi jan wuya ne to har da ke din ma zanso na siye ku na biya kudin cajin da za ayi miki don Nan ba irin Nigeria bane manyan kudade ake batarwa don tseratar da rayuwa in kuma ba haka ba zasu kashe ku ne kinga tunda kina da kaddara gara ki siyar da ita ki cece rayuwar ki don nan dai mahaifin ki bashi da kudin fansar ki.

Jimy ne ya kuma shiga da fice wurin ganin an tsaya wa Nadiya duk da an soma bincike don gano alakar su da Osting aka saki kudi sosai har Allah ya sa Nadiya ta kubuta daga sharrin kisan da take passing.

Abdulhameed ne ya taho da ita zuwa gidan sa kafin zuwa lokacin da zasu taho Nigeria. Nadiya kam jikinta a sanyaye yake babu abunda take so irin ta hadu da faddy da mama a yau domin su fidda ta daga wannan bak’in duhun da ta samu kanta don bata tab’a baje zancen daddy da mama ba irin na daddy wanda ta tabbatar abinda ya fada shi yake nufi.

Rayuwa ta sosai abdulhameed yake shirin sauya mata don komai yi mata yake yayin da sumayya ta iso gidan tayi Ido hudu da Nadiya wacce bata san fuskar ba amma hakikatan ta san sunan don haka ba karamar kaduwa sumayya tayi ba da ganin Nadiya a gidan abdulhameed amma da Yake ilimi yana aiki sai ta tarbi Nadiya suka zama tamkar kawaye har suka soma sabo.

Wayar Abdulhameed da ya kira haj laila yake fada mata dukkan abubuwan da suka faru da Nadiya da irin kudin da ya zube ya samo ta da kuma sharadin da sukayi .

Haj laila ta kwalla gud’a tana fadin

“Alhamdulillahi Abdulhameed kayi min daidai in har suna son yar su a hannun mu to su fanshe ta da Ya’yan ka kayi min hikima kwarai wallahi maza kira daddyn ka ka sanar mishi.

Ya kira distinguish Mukhtar biro yana fada mishi abinda ya faru shima yaji dadin hakan ya kuma ce suyi komai a Rubuce idan uban ta yana son ta to ya basu yan biyu in kuma yace ba zai bayar da yan biyu ba to za a mayar da ita america ne akashe ta yasan Alh iro ba zai yarda a kashe mishi yarsa ba dole ya basu Ya’yan su .

Wani al amari mai ban tsoro da ya soma faruwa da fati da Alabo wanda ya zama abin mamaki . domin kuwa tunda akayi haihuwar nan alabo ya soma nunawa fati wani abu wanda bata tab’a sanin shi ba amma duk dai tayi mishi uzuri don gaskiya bai tab’a nuna mata haka ba.

Akayi suna yaro ya amsa sunan Baffa halilu wato Ibrahim khalil suka kuma nufi misau don Inna Hajara tace a dawo mata da binta nan ta gyara ta

Fati tana son siyama wacce take bawa no-no yarinyar kuma tuni ta warware ta daina rashin lafiya

Sati biyu da zuwan Fati misau amma yaya alabo bai zo ba kuma bai kira ta ba. abinda ya dame ta matuka gaya.

Ranar da ya zamo sati na uku bai zo ba ne Inna ke fadin

“Wannan yaron kuwa lafiya har yau bai zo ba ? ko kunyi waya ne wani Abu ya tsare shi ya hana shi zuwa?

Fati tace mata aiki ne yayi mishi yawa.

Da dare fati ta kira wayar shi inda taji muryar mace ta dauka tana fadin ya manta wayar ne.

Muryar wacce tayi maganar bata boyu ga fati ba don haka tace

“Wai ladidi ce?

Da sauri ladidi tace

“Itace wacce?

fati tayi mamakin abunda ya kai wayar Yaya Alabo wurin ladidi.

Ladidi yar makotan su ce bazawara ce da auren ta ya mutu kuma tana shigowa gidan fati wani lokacin ma har aiki sukeyi tare  ta bata kwancen kayan ta ta Kuma bata abunci wani lokaci ma idan Yaya Alabo yayi tafiya fati ta kan kira ladidi taxo ta taya ta kwana .kai ladidi dai ta zama kamar Yar gida duk da yaya Alabo yasha fada mata baya son ladidi tana shigo mishi gida amma sai ta bashi hakuri tace mishi tana da kirki ba don ya so ba ya bar ladidi tana shigowa kuma wai yanzu da ta kira wayar shi taji ta a hannun ladidi shine abinda yayi matukar bats mamaki me ya kai wayar sa a hannun ta?.

ta sake kira amma taji wayar a kashe don haka da safe ta sake kira ya kuma dauka.

“Yaya Alabo wani laifi nayi maka tunda nazo misau ko ka kira ni?.

“To meye na sai na kira ki tunda kuna lafiya?

Ya bata amsa a fusace.

“Allah ya baka hakuri amma naga ko baka kira ni ba don ni kaina zaka kira don Khalifa.

“Ai na san inda kuke in naso na ganku ba zan zo bane?

wannan maganar tayi matukar bata mamaki amma sai tayi mishi uzurin wata kil wani ya tabo shi a can sai ta sauya maganar da cewa

“Jiya na kira wayar ka sai naji ladidi a layin.

Ai fadar hakan ke da wuya dan bawan Allah ya rufe ta da masifa tamkar zai zuro hannu ya mare ta.

masifar da yake ta zuba mata ne tasa ta kuka amma bata bari Inna ta sani ba don ta san ba zasu shawo ta da dadi ba.

Kwanaki suka gangara ranar wata asabar sai ga ladidi wai tazo duba Khalifa

fati bata kawo komai a ranta ba ta karbi ladidi suna ta fira tana tambayar ta mutanen gida da sauran makota .

Ladidi tana rike da khalifa tace da fati

“Yayan ki kuwa yazo tunda Kika zo gida?

fati tace

“Sai dai waya don yace min ayyuka sunyi mishi yawa.

“Na ce mishi ne in zai zo mu taho tare amma na gane ba zai zo ba shine na taho .

Wani irin duka ya naushi zuciyar fati don sai yanzu ta tuna da kiran da tayi mishi taji wayar shi a gun ladidi.

Ta na hada uku da biyar sai suka bata takwas amma sai ta bar abin a zuciyar ta ta kuma barshi a matsayin zato zunubi.

Wayar ladidi da take a kasa kira ya shigo inda lambar alabo ta shigo duk da sunan da ta saka mishi ba nashi bane star ce guda uku ajere amma lambar da ke k’asa ta nunawa fati lambar sa ce .

Da sauri ladidi ta dauka tana fadin

“Hello ?

sai ta mike tana futa waje don amsa wayar ta abinda kuma ya jefa fati a cikin rudani domin kuwa ta gane wata kulalliyar alaka tana shirin kulluwa tsakanin Yayan ta Alabo da makira ladidi koma ta kullu bata sani ba.

Me ya kai wayar Alabo gun ladidi? me ya kai shi kiran ta a yanzu? me ya sa ladidi ta ce taso in zai zo su taho tare? me yake faruwa ne bayan ta baro gida? anya kuwa babu wani mugun kulli a k’asa? meye dalilin kiran ladidin da kuma manufar zuwan wayar shi gareta.

Ladidi ta jima a waje tana waya kafin ta shigo tana fadin

“Kinji yayan ki yana hanyar zuwa misau kinga kudin mota ta ya huta sai mu koma tare.

Fati ta zubawa ladidi Ido tana jin anyi mata na mutumin duniya amma bari taga idon yaya Alabo a yau da kuma irin kallon da zaiyiwa ladidi shine zai nuna mata kowace irin alaka ce tsakanin su .

Au kuwa dan bawan Allah bai rufe awa daya ba sai gashi a misau ya faka motar shi ya fito da kayan siyayyar da yayiwa fati ita da khalifa ya shigo gidan yana fatan ya hango ladidi sai kuma gata ya ganta goye da khalifa ya sha mur wai don kar ya bada kanshi yayin da fati ta zuba mishi ido taga ya zuba uwar kibar shi alamar bashi da wata damuwa. Ladidi tayi kamar bata tab’a sanin Alabo ba shima kuma haka . kai al amarin yan duniya ma da wahala yake . ko da yake ban zaci akwai Allah a cikin lamarin ba.

Yana rike da khalifa wanda ladidi ta kwanto daga bayan ta ta bashi ta fice daga dakin wai ta basu wuri su zanta.

ta zuba mishi ido yana gyarawa yaron rukon da yayi mishi yayin da take rike da Siyama tayi bacci.

“Fatan kana lafiya Yaya kwana biyu.

Ya dago kai ya kalle ta Yana fadin

“Ina lafiya mana in kaji shiru ba lafiya ba? ko kuwa zanyi ta zarya hanyar garin nan ne don dai nine wanda matar sa ta tafi wankan gida.

Ya fada Yana gintse fuska

Karshe ma sai ya mike ya bar mata dakin ya fita wurin inna Hajara

Fati taji ruwan Hawaye Yana sauka a fuskar ta amma tayi karfin halin share su tana zubawa Siyama Ido  tankar mai kidaya harbawar sakan da minti.

Inna Hajara ta dube shi tana fadin

“Wai aiki ne ya rike ka halan da ban ganka ba? Yayi maza ya karbe da fadin aiki ne yayi mishi yawa. da wanna ya rufe bakin iyayen sa da suka soma tuhumar rashin zuwan sa

Ya kawo musu kaya sosai bai jima ba yace zai koma inda ladidi take fadin

“Matar yayan ta don Allah ce mishi ya rage min hanya.

Fati tayi mishi magana yace ta taho

Yayi musu sallama suka dauki hanyar bauci ladidi uwar makirci tana tunanin Fati ta kusa ta gano wani abu amma kuma ba zata gane ba don al amarin a lullube Yake Kuma a lulluben  zaizo sai dai taji har anyi an gama.

*****

<< Azurfa Da Zinari 68Azurfa Da Zinari 70 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×