“Allah ya gafarta malam Aiki fa yayi kyau don tunda matar sa ta tafi wankan gida nice nake nasa girki kuma duk taimakon da ka bayar na jaraba su kuma Alhamdulillahi bukata ta biya . Sai dai in da gizo Yake sak’ar shine matar tasa yar uwar sa ce wacce na gane hadin gida ne kuma akwai zumunci nai karfi a tsakanin iyayen su to Ina tsoron abinda zai biyo baya idan maganar auren mu ta fito don har ya fara maganar auren mu nice ban bada kai ba na kuma tabbatar da in ya kawo maganar auren mu iyayen su ba zasu yarda ba shine nake so malam ya dan yi min wani abu wanda da ya kawo maganar auren namu su yarda babu wani kace nace don gaskiya malam na matsu na shiga gidan shi ko babu komai yana da sakin aljihu kuma komai iyalin sa ta nema tana samu wannan shi ya sa naji nima zan shiga a dama dani kuma Allah da ikon shi gashi nayi nasara don kullum yana kofar mu nagode sosai malam da kokari Allah ya kara haske.
Malamin ya dubi ladidi yana fadin
“To Alhamdulillahi tunda bukata ta biya wannan din ma in dai za ayi yanka in sha Allah komai zai zama labari don yadda yake jin ki a zuciyar sa babu abinda ba zai iya aikata wa ba don haka auren ku ma zai zamo nan kusa in dai za ayi yanka.
“Kowane irin yanka ake so malam ai sai ayi tunda yana sakin aljihu me ake da bukata?
Malamin ya shafi gemun sa yana fadin
“Akwai bukatar a yanka bak’ar akuya da bak’ar tunkiya in aka zubar da jini to zaki sha mamaki.
“Ai malam tafe nake da hatsi na a buga a kwashe ne ga wannan dubu hamsin ne jiya na wanke su hannun shi a fara da su idan ma ba zasu Isa ba to zan kawo sauran gobe ko jibi idan yazo.
Malam ya karba yana Fadin
“Lallai sai kin karo kamar wadan nan don ance dabbobin ma yanzu babu k’asa da na dubu tamanin.
“Babu matsala malam ko na nawa ya kama a siya zan ciko kudin tunda ma yana kwantaluwa ai babu damuwa.
da haka tayi mishi sallama ta wuce.
Tun farkon zuwan fati unguwar nan lokacin auren su da alabo da ladidi ta soma shigowa gidan ta kula da irin rayuwar da alabo da fati sukeyi wacce ita ko kwatankwacin ta bata samu a gidajen auren da tayi har biyu ba gata kuma tana jawarci na uku
tun daga lokacin da ladidi taga Alabo taga irin daular da yake ciki ta hada mishi yawu musamman ma da ta gane babu abinda yake tattali kamar matar sa fati sai taji ta tsani Fati a rayuwar ta duk da tarin akhairai da fatin take kan yi mata don ta gane a gidan su ladidi ma abinci da kyar ake samu bare kuma sutura sai take taimaka mata amma ds yake dan butulu ne kana mishi alheri yana saka yadda zai maka sharri.
To daga nan fa ladidi ta soma shiga malamai da son samo zuciyar alabo ga alama kuma tana dab da samun hakan don har gidan take shiga tayi mishi girki ayi fira a sha soyayya shi kuma yana sakar mata kudi dama abinda take mayata kenan kudin shi da hidimar.
Kwanaki kusan ashirin da wani Abu alabo bai kuma zuwa ba yayin da Fati ta gama gane akwai sanwar da ya saka tsakanin sa da ladidi sai take ta ADDU A Allah ya kiyaye koma meye
Kaisar kam duk bayan kwana uku ko biyar yana misau ganin mamy Siyama inda kuma yake ganin girman fati da yadda take kula mishi da yar sa shiyasa komai ya suyo to na su biyu ne Siyama da khalifa .
Har fati tayi arba in alabo bai kuma zuwa misau ba inda Inna ta soma gane akwai wani abu ta kuma soma tohumar fati abinda yake faruwa a tsakanin su don ta kula ko waya baya kira.
Fati ta soma kuka tana fadawa Inna Hajara dukkan abubuwan da suke faruwa.
Ai kuwa Inna Hajara ta daga waya ta kira alabo tace koma me yake yau yau yazo tana kiran shi.
Ya samu zuwa Inna Hajara kuwa ta rufe shi da masifa tana fadin
“Me kake nufi ne halan da har sai na kira ka kake zuwa? dama ka shirya wani abu ne halan? to so nake ka fada min abunda binta tayi maka kake mana wannan wulakancin fada min da bakin ka yau inji ko kuwa don ka same ta a arha ne kake ganin bata da daraja? .
“Nifa inna babu abinda tayi min aure dai nake so na kara .
Da sauri Inna Hajara ta daki kirji tana fadin
“Kai kace me? Aure? to kaci uwar karya ka kwana da yunwa wallahi in ma mafarki kake ka farka kuma ko bayan raina baka Isa ba wallahi ba mutumin wofi kai in har dan kirki ne ka dubi Aliya da wace kamar? Da Allah tashi ni a gaba na tun ban sharara maka mari ba sakarai shashasha da kai baka Isa ka bani kunya ba wallahi .
sai kuma ta fasa kuka tana share hawaye da gefen zanin ta don idan akwai abunda ya tab’a hada ta da dan nata mai tsanani to wanna ne .
Baffa halilu ma ya girgiza da maganar da Alabo ya kawo mishi ta karin aure amma shi bai ga abin tashin hankali a ciki ba don haka yace yaje yayi ADDU A abinda Yake alheri Allah ya tabbatar da shi.
Alabo yana shirin tafiya ne Inna Hajara ta tare shi da fadin
“To me kake nufi ne ? baka kawo min kudin kitso da wankin zannuwa ba zaka wuce babu ko neman kadi.
A nan alabo ya bada kudin kitson da na wankin zannuwa irin na wacce tazo wankan gida idan zata koma shine miji ke bada wannan kayan ayi shirin komawa.
Tunda alabo ya zo misau da kwana biyu yaji Fati ta fita a ranshi babu wacce yake so da gani irin ladidi wacce ta maye gurbin Fati don haka ya ji babu sauran muhallin da Fati zata zauna a gidan shi sai ladidi.
Ladidi kuwa da ta koma wurin malam ta kai mishi cikon kudin yankan da akayi ya bata magani yace ta zubawa alabo a acikin abinci to zaiji ya tsani matar sa tsana irin wacce ba a tab’a yi ba.
Ai kuwa ladidi tazo ta auna magani ta bawa alabo ya kuma ci shine fa ya shiga wannan halin
Tun kwana biyu Inna Hajara ke duban hanyar zuwan alabo amma shiru har aka ci sati inda Baffa yayi mishi magana nan ma bai zo ba . washe gari sai ga Daddy yazo don alabo kam ta can ya bulla ya fadawa Daddy yana so zai kara aure daddy kuwa ya goya mishi baya ya kuma ce zaizo isau yaji dalilin da za a hana shi aure
Inna Hajara ta rike baki tana jin abinda iro yake fada wai gobe goben nan za aje mishi neman auren .
Hatta da yaya halilu bai aminta da auren nan ba amma yafi Inna Hajara fahimta amma kam uban nasu ya na shirin basu mamaki.
Washe gari kuwa Daddy da alh sule suka nufi nemawa alabo aure aka kuma gama komai sati hudu masu zuwa za a daura auren. amma me? Inna Hajara tace a mayar da fati dakin ta tunda shi ba zai zo ba ta kira shi ta kira shi amma bai dauka ba yama daina daga wayar ta.
“Uba na yana shirin bada ni Hajara . shi kuma iro da yake ya iya daurewa karya katara shine har da shige mishi gaba? dubi yarinyar nan uwa ta ko bata fada ba bak’in cikin sa ne yake k’arar da ita daga tsaye anya lamarin uba na na lafiya ne?.
“Na lafiya ne mana malam namiji kuma ai ya wuce da irin haka in baiyi hakan ba ashe a sauya mishi suna daga namiji zuwa maza maza.
Ladidi kam da ta gama kama Alabo shine take fada mishi ba zata zauna da matar sa ba in ma yana son ta to dole ya saki matar sa don ita bata zama da kishiya ko a bayan ta kishiyar zata zo to ita zata fice bare ace iskewa zatayi don haka ko dai ya raba musu gida ko kuma ya sahale mata .
Shi da kanshi ya ke Jin kamar baiyiwa Fati adalci ba amma kuma wani abu da yake danne zuciyar sa ya ana shi farkawa daga mayen da Yake ji akan ladidi.
Inna Hajara ce ta shirya da kanta zata maida Fati dakin ta amma affa Halilu yace
“Ke da kanki Hajara? ai Alabo yayi kad’an da kiyi mishi wannan aikin shi da kanshi zai zo ya dauki matar shi babu mai kai mishi ita anyi mishi na farko da karshe.
Shi ya kira alabon yace yazo yau ya dauki matar sa sai akayi kai da Kai don a yau din yayi nufin zuwa Misau din.
Shigar yamma yayiwa misau don haka a taskar gida ya samu Baffa ya zube yana gaishe shi Baffa ya zuba mishi ido bai tanka mishi ba ya ci gaba da sauraren shi.
“Sai yau kazo? ko da yake ai kiran ka nayi baka zo don kanka ba amma ai shikenan.
“Kayi hakuri Baffa dama yau din zanzo don na kasa jurewa abinda nake ji
Ya zaro takardar yana mikawa Baffa wanda gaban sa ya sara da karfi amma ya shanye ya karbi takardar Yana fadin.
“Ta mece ce wannan ? Alabo ya kasa motsi don shi da kanshi yaji kunya ta Kama shi.
“Nace ta mecece? Ko da Yake ga kai ga fata meye dalilin tambayar me aka yanka?
ya warware takardar wacce ke dauke da Rubutu na jar biro layi daya tak amma mai dauke da tashin hankali fiye da akirga.
“Na saki matata saki uku.
Baffa halilu ya saki takardar yana fadin
“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un.
“Ni kake dosa da wannan tashin hankalin Alabo? ni a matsayin uban Fati kake dosa da takardar saki har uku don uban ka?
Abunda Baffa bai tab’a yiwa alabo ba wato zagi.
“Dauki takardar ka kaiwa iro shi sai ya kawo mini .
Fati da taji kalmar da Baffa ke fada sai taji wani irin duka ya naushi zuciyar ta .
Inna Hajara kuwa buta ta figa ta shige bandaki a guje saboda tashin hankalin da taji tuni ta soma zawayi a band’aki tana kuka.
Alabo da yaji kamar wanda ya farka daga bacci ya kuma ji lallai akwai tashin hankali a cikin abinda yayi mai kama da mafarki .
“Kayi hakuri Baffa dole ta sa ni sakin nan.
Baffa ya kwashe shi da mari ya kuma maska mishi mari yana fadin
“In ka kuma kira na da sunan Baffan ka zan la Ance ka wallahi ni kam a yau nayi nadamar sanin ka A rayuwa ta Alabo don ban tab’a muzanta irin yadda kake shirin muzanta ni ba tashi daga nan tun ban yi abinda zai baka mamaki ba kuma ka tabbatar da ka kaiwa iro takardar nan don wallahi idan baka kai ta ba fushi na zai tabbata akan ka ina jiran zuwan ta daga shi iron don naga karshen rashin kirkin ku kai da shi ni in ga mai kawo mini takardar nan.
Alabo ya mike yana ganin jiwa na shirin kada shi .
Ya fice daga gidan yayin da ya shiga mota amma ya kasa tashin ta ya tafi
Ya dubi takardar wacce ke dauke da saki uku Rigis ya kuma ji mai ya kai shi wannan sikin? yaushe yayi hakan?sai ya tuna da ladidi wacce itace ta rubuta da sunan shi kuma yaji hakan ba nadama a ciki.
Inna Hajara da ta fito daga bandaki taga baya nan sai ta dubi Baffa tana fadin
“Tafiya yayi ne? Ai ba zan iya da kunyar Aliya da iro ba tunda bashi da kunya wallahi ba zai kai takardar nan ita kadai ba sai ya hada da binta ya mayar nan ne zan san ya shirya wulakanci mai daraja.
Ta fita kofar gida don bata ji tashin motar sa ba sai ta ganshi a mota zaune yana hada uban gumi don haka ta dawo ta kama hannun Fati tana fadin
tashi binta kuje tunda ya zama dan iska ni bani da idon duban ki bare Aliya da iro .
Ta saka mishi fati a mota hannun ta rike da muciya tana fadin
“Maza ka bar nan ko yanzu na bare maka kai wallahi dan iska mutumin wofi .
A guje Alabo yaja mota ya wuce yayin da Inna Hajara ta manta da khalifa da Siyama a dakin sai da ta shigo tayi kukan ta ta gaji kafin khalifa ya farka yana kuka sai a nan ta tuna da baya da k’urar da ta bari .
tun daga misau har bauci babu wanda yayi wa dan uwan sa magana tsakanin fati da Alabo. Ita dai kuka ma take tun daga misau har bauci shi kuma yana ta kama channel.
Suna isowa Fati ta fice daga motar ta nufi cikin gidan inda sukayi kicibus da Haj Aliya wacce Fati ta rungumebta tana sakin kukan ta. Haj Aliya kuwa ganin babu goyon yaran yasa ta rude tana tambayar Fati lafiya?
Kukan fati ya kara karfi har daddy da yake sama ya jiyo shi ya sauko yana tambayar fati abinda ya faru.
Alabo ya shigo shima cikin tashin hankalin inda haj Aliya tace babu lafiya kam.
“Uba na ya akayi ne ? me yake faruwa?
Alabo ya soma share zufa yana tadin
“Daddy ban san abinda Yake faruwa dani ba wallahi daddy ban sani ba .
ya fito da takardar sakin yana fadin
“Ku gafarta mini daddy Baffa yace na kawo maka ko ya la ance ni ban san me ke faruwa dani ba daddy na saki Fati ne sakin da ban san ta yadda akayi nayi shi ba.
Ya fada yana fidda hawaye .
“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un uba na wane irin saki kake magana? ka saki wa tukuna?.
Alabo ya soma Mika mishi takardar wacce Yake jin tayi mishi nauyi tamkar dutsen uhudu.
“Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un wa ce ka saki ? uwa ta? ya subhallahi Uba na.
Ya karbi takardar yana warewa yayi arba da Rubutun na jar biro wanda yayi matukar kad’a shi matuka gaya har ya zauna akan kujera ragwaf.
Saki uku shi yake ta maimaitawa a kwanyar shi yayin da haj Aliya tayi mutuwar tsaye.
“Ina yaran kika baro su?
Haj Aliya ta fada tana duban fati wacce ta mance ma da wasu yara sai fa yanzu da aka tambaye ta .