“Haj wannan gida nawa ne ke kika ce kina son na siya miki dakin ta a hade miki da sashin ki haj baki san in ana son abun mutum ba matukar ba shi ya tashi siyarwa ba dole a bashi yadda ya yanka? to ni nace ayiwa dakin kudi na siya miki aka kuma yi na siya na bata kudin ta kuma na tallata mata wannan gidan ta siya na bata sauran kudin ta.
“Eh lallai ka iya waka shata !
Na gani kuwa ka bata kudinta har ta siyi fridge gashi nan tana ta sana a ko ? To wannan maganar taka akwai tsamin munafunci a cikin ta don haka ban yarda da kai ba wallahi wannan shegen dakin nata shine a madadin wannan gidan? to muje a bata dakin ta na fasa karbar dakin wannan gidan nake so ai Rabi batayi kudin mallakar gidan nan ba wallahi nafi son ta komawa garbati can su bata Aron soro ta zauna ko shago amma gida irin wannan me akayi har an fara cewa tafi mu ga zance ga magana? To ba haka nake son ganin ta ba nafi son na ganta Hajaran majaran .
“Subhallahi Haj don Allah ku Rika saka alheri sai kuga alheri ya fara saukar muku . da wanda yayi muku sharri da wanda yayi muku alheri duk ku yiwa mutum fatan alheri sai Allan ya fara baku alheri kafin wanda kuka nufa da hakan . Sau tari fatan da mukewa juna shine yake fara suka garemu yanzu haj dubi abinda kike fada saboda Allah? haj Rabi a matsayin yar ku take tunda ban tab’a ganin tayi miki wani abu ba hatta yaran gidan nan na San irin yadda suka ci mutuncin ta amma ban tab’a jin ta bude baki tayi magana.
“Kai ya ishe ka haka kaji ko? Kai dama Ina zaka san abunda ake min ? baka da labarin irin bak’in cikin da na hadiya halan? baka san yadda na sha wahalar kishiyoyi ba halan ? to babu shegiyar da zanyi wa sauki a cikin su babu wacce zan sake yarda ko ruwa tasha daga cikin arzikin ku dama Alh ne ya hada to ya Raba an kuma rabu don haka Rabi ta kwashe komatsan ta ta bar gidan nan taje ta karbi akurkin dakin ta na fasa so dama don in rika zuba shara a ciki suma su hauwa in sha Allah sai na siyi dakunan su na zuba tantabaru don su gane nice a Saman su .
“Haj Ina ake haka sai kace dai babu adalci? ta siyar an siya kuma sai a dawo ace an fasa,? Ai ko shari a bata yarda da hakan ba gara a bata magana in zata saida sai a siya shima sai an bata Riba ba wai a mayar mata da kudin ta ba.
“In dai na fahimce ka sai abinda Rabi take so za ayi ko Sani ? wai a me kake kallon Rabi ne ? ba yanzu nake gaya maka uban ka ne ya aure ta ya mutu ya bari ba? Ko kuwa zakayi gugar jigida da hurumin Uban ka? To in dai har haka kake nufi na kusa na la Ance ka wallahi.
“Ko kusa ba abunda kike nufi bane haj . nayi mamaki ma da kikayi min wannan fahimtar. to Bari na fada miki gaskiya Haj kafin Alh ya bar duniya ya bani amanar Haj Rabi da danta Al Mustafa na kuma yi mishi alkawarin rike mishi amana kema ki bani wata amanar ko bayan ranki wallahi zan Rike miki ita Haj don ki san na haihu gareku kuma haihuwa daya kikayi min .
“Oho fatan da kake min kenan na mutu na baka Amana? to in ka gaji da gani na kana iya kar ni don ka yi yadda kake so tunda fada maka gaskiya ke sawa kana min fatan na mutu don ka sakata ka wala.Kuma manar Rabi kawai Uban naka ya baka bai maka wasiccin auren ta ba ta yadda zaka ririta ta a daki ? to kayi duk yadda kake so kuma wannan gidan ba dai Rabi ta zauna cikin shi ba in ma hakan ne sai dai ta siyar ta sake wani kuma mu zuba mu gani shege ka fasa.
Kai kuma idan har ka cika ni zaka ga bacin Rai.
Ta mike ta fice daga gidan a fusace tamkar zata tashi sama inda ta bar Alh Sani yana dafe da kanshi idanu jajir yana jin yaddda zuciyar sa ta amsa da maganganun mahaifiyarsa .
“Kayi hakuri Baban Fatima idan lamari na zai zama bacin rai tsakanin ka da mahaifiyar ka don Allah kar ka bari ranta ya baci ba gida take magana akai ba? wallahi zan tashi sai a nemi wani .
“Ba zai yuwu ba Haj shari a ma in ta tayar da ciniki to aibu ne ta gani a ciki amma bayan haka babu abinda yake tada ciniki in dai an kulla shi da ka siya na saida maka .
Duk yadda Rabi taso ya fahimci kalaman mahaifiyar sa na cewa ba dai ta zauna gidan ba Alama ta nuna bata yarda ba ba kuma zata yarda ba to me ma take nufi?
Da haka alh Sani yayi Mata sallama ya wuce.
Haj kaltume kuma ta wuce gida da bak’in cikin daukakar Rabi musamman yadda taga Yan tallar ta suna ta shiga da futa don kafin ta baro gidan har wasu sun saido sun dawo don haka aka shiga sak’a da mugun zare.
Kwanaki goma sha biyar da yin wannan takaddama Rabi ta wayi gari gidan su ya buwaye su don daren jiya kam ita da Mustafa basuyi bacci ba an kwana ana basu tsoro banda ma tasirin ADDU AR da ta kwana tanayi wata kil da ba haka ba.
Washe gari bata zaci abin na gaske bane sai da dare yayi taji abubuwan da suka saka ta dole ta hakura da zaman gidan nan matukar ba gware sukayi suka zo duniyar ba.
Ta kira alh Sani ta fada mishi abinda yake faruwa daga shekaran jiya zuwa yau din inda har layu dai ta gani a taskar gidan wanda bata san da wanzuwar su ba.
Alh Sani yayi shiru kafin ya dube ta yana fadin,
“Babu komai bari kawai a fita daga cikin sa ba dai za a siyar da shi ba Haj ko zai tabbata a haka in sha Allah kuwa babu mai saida shi bari na saka cigiya a sama miki wani amma yanzu ko zaki koma gidan kawu garbati ne kafin a samu wani gidan?
Ta amsa mishi da dama ita kam ta tsorata da gidan ga mustafa jiya da zazzabi ya kwana baiyi bacci ba gara ta koma gidan kawu garbati duk da kalubalen da yake damfare a gidan.
“To amma zaki tafi da fridge din Sana ar ki sai almajiran suke zuwa suna dauka talla ko ? don in aka bari kasuwar zata mutu.
“Eh to bari sai na tafi dashi can sai na fada musu
Haka kuwa akayi Rabi tayi parking din kayan ta Alh Sani kuma ya turo mata motar kwasar kaya ta kwashe mata kayan ta zuwa gidan kawu garbati wanda ya ganta kamar daga sama ya kuwa sha kunu kamar bai tab’a dariya ba wai shi an zo gabar da zaiyi wulakanci.
“Sai yanzu ne da rana ta baci kika tuna da ni din ina da amfani? cewar kawu garbati wanda yake mata wani shegen kallo.
Ta soma koro mishi abun da ya faru har ta dawo gida kafin a samu wani gidan.
“Ai ke kam Rabi butulu ce wallahi mai manta alheri tunda kika shiga gidan Alh yaro ni zan iya tuna wani Abu na jinkai ma da kika tab’a nufa ta dashi? har akayi muku Rabon gadon amma baki neme ni na tsaya miki ba amma yanzu da gidan ya sami matsala kin wani kwaso tab’ai tab’ai kin nufo ni ga wanda bai san ciwon kansa ba mai gidan wofi.
Idon Rabi da hawaye ta dubi kawu garbati Wanda aike ma yake mata ta bada kudi a kawo mishi kuma mariya yake turawa ta kuma saki magana ko a gaban uban wa amma dubi abinda yake fada?
Ta ce,
“Kawu ? lokacin da za ayi Rabon nan ni nazo na fada maka kace ba zaka bar aikin gonar ka ba kuma ga mariya nan ba zan iya kirga adadin abinda na bayar a kawo maka ba. Ba sana a nake ba duk abinda kaga ni tasrifin Ubangiji ne amma kayi hakuri in sha Allah zan baka .
“To tuna min tunda na manta har kike zama gaba na kina zana min abunda Kika bani. Yi maza kiyi min gori Rabi ko ki tara mutane ki fada musu abinda kika bani.
“Yanzu da kika kwaso kika taho a nan gidan kike nufin zama ? sai yanzu ne kika san ni naki ne? To ai yanzu walkiya ta haska in zaki iya kwana a soron farko to bismillah amma in dai dakin can ne ba zan baki shi ba yan haya zan saka na karbi kudin sa in kuma zaki karbi hayar bismillah dubu biyar duk wata ba Kuma zaki shiga bashi ba sai kin aje min ita.
Idon Rabi cike da hawaye take kallon kawu garbati kafin ta share hawayen ta ta bude jakar ta ta fito da dubu biyar ta mika mishi ya kuma karbe ya kalmashe .
Ta shigar da kayan ta ta kuma jona wayar fridge din ta ta soma sana ar ta wacce tasha suka da kushe amma da yake raba bawa da arziki sai Allah haka yan tallar ta suke ta jidar mata kayan sana ar ta har ta kai ana zuwa sarin k’ank’ara wacce take badawa da sauki sai masu kayan ruwa suke ta zuwa sari . Kan kace me? Rabi tana cikin suturar Ubangiji kuma tana bawa kawu garbati da matan sa hasafi duk da babu gode bare an gode.
Alh Sani ya iso gidan kawu garbati yazo kawowa Rabi kayan abinci don bai fasa wannan hidimar ba.
Al Mustafa ya rugo da gudu yana makale Alh Sani yana fadin
“Oyoyo baba na . Alh Sani ya cabe shi ya daga sama yana jin tausayin Al Mustafa wanda ya maida shi Uba don tunda ya daina ganin mahaifin sa ya kama Alh Sani yana ce mishi baba na. Yayin da shima sanin yake kallon Al Mustafa dan shi ba dan uwa ba .
Al Mustafa da yake da naci akan makaranta ya soma fadin
“Baba yaushe zanje makaranta? Uncle na can makaranta yana cewa Ina Al Mustafa bai zo makaranta ba?.
Alh Sani ya dubi Al Mustafa yana fadin
“Ka daina zuwa makaranta ne Al Mustafa? na Sani nan kunyi nisa da makaranta kana son zuwa ne?
Yayi saurin kada kanshi Alh Sani yace to kayi hakuri zan san yadda za ayi kaji? jeka ka fadawa maman ka nazo.
Ya sheka aguje ya fadawa Rabi sai gata da tabarma ta fito tana mishi sannun da zuwa
Ya zauna suka gaisa yana tambayar ta mutanen gida da kuma karatun Al Mustafa. Ta amsa mishi da Al Mustafa tunda suka dawo nan baije makaranta ba saboda babu wanda zai kaishi ya maido shi duk da tana jin ciwon rashin karatun.
“To ko zan tafi dashi ne can gida na sai ake kaisu tare da su Salim ?
tayi murmushi tana fadin
“Nagode Baban Fatima Allah ta ala ya shirya maka zuriar ka na Sani kai din uban Al mustafa ne ba dan uwa ba Allah ya jikan lahirar malam yasa ka gama da haj lafiya.
Ya amsa da ameen kafin ya sauke mata kayan abincin da ya kawo mata ya Kuma karbi kayan Al Mustafa don zai tafi dashi can cikin ya’yan sa ake kaisu makarantar tare
Ta kawo mishi kayan Al mustafa yana ta daga mata hannu wai bye bye yake mata ashe Rabuwar kenan tsakanin Al mustafa da mahaifiyar sa sallamar bankwanan kenan.
Kawu garbati tunda yaga kayan abincin da aka saukewa Rabi yace ya daina awo sai dai aje ace ta bayar ta kuma bayar a dafa a cinye
Al Mustafa ya kum samun wani katon kalubalen ga matar alh Sani wato dija wacce sam batayi maraba da zuwan Al mustafa gidan ba akasin ya’yan ta da suke son yaron musamman babbar su Fatima tana son Al Mustafa sai Kuma su salim da yan uwan sa .
Dija ta soma nunawa Al Mustafa bak’in halin ta ne ta hanyar hana shi abinci ta kuma kasa cire mishi Riga bare ta watsa mishi ruwa da sunan wanka haka zata shirya Ya’yan ta amma Al Mustafa sai dai ko Fatma ta bashi a boye ko tayi mishi wankan a boye don in uwar tasu ta gani ba zatayi mata da dadi ba.
Ranar da Allah ya nunawa Alh Sani muguntar dija ta zuba abincin ta bawa su salim abin yaro Al mustafa yazo zai saka hannu yaci dija ta buge hannun shi tana zare mishi idanu tana kwara mishi tsawa wacce ta sa ya koma baya ya lafe yana b’ari yana kallon yan Uwan sa suna cin abincin.