Skip to content
Part 78 of 78 in the Series Azurfa Da Zinari by Hadiza Gidan Iko

Haka suka fice da AlMustafa baici abincin ba inda Alhaji Sani ya tabbatar Almustafa ya hadiyo wani babban Al amari tunda kalubalen sa yayi yawa a rayuwa daga wannan sai wannan,?.

Ya mike da sauri ya dauki nashi abincin ya fita da shi ya karbi Al Mustafa ya saka shi a mota ya Bashi abincin ya soma ci ya kuma bashi madarar bobo ya sha ya kaishi makaranta da kanshi akasin su Salim da direba ne yake kaisu.

Tun daga wannan rana Alh Sani ya samo wata Mata mai suna hanne ya bata amanar kulawa da Al Mustafa abinda yasa dija tasha jinin jikin ta don haka sai Al mustafa ya samu sake sosai a gidan Alh Sani hanne kuma tana ji da Al Mustafa don yana bata tausayi musamman da ta gane bashi da gata irin na yan gidan.

Kawu garbati ya karbi takardar wacce ya karbar wa yarsa mariya wacce take gida da jimawa tana jawarci shine fa yaji ana bada takardar daukar mata zuwa k’asar Saudi Arabia don yin aikatau shine kuma ya saka sunan Rabi don Allah yayiwa kawu garbati mayatar son kudi musamman da yaji a kyauta za a kai mata kuma in suka gama aikin su kudi ake biya ba na wasa ba don haka kawu garbati ya rude ya rikice ya kuma bada sunan Rabi da Mariya.

Rabi tana gida taga mariya da takarda wai zasu tafi saudi Arabia abunda yayi matukar tayar mata da hankali har ta iske kawu garbati tana tambayar ba asi ya kuma Rattaba mata yadda abin yake Al amarin da Rabi ta gane Aikin nan ne wanda ake safarar mata amma sai a fake da aikatau don haka tacewa kawu garbati.

“Kayi hakuri kawu gaskiya ba na Ra ayin aikin nan ni kam aure zanyi amma wannan Aikin angulu ne da kan zabo ana kai mata suyi karuwanci ne ba Aikin kawai ba in ma aikin ne to aikin bauta ne mai kama da an saka kudi an siyi mutu tunda naje Saudi Arabia naga irin wadan Nan mutanen.

“Ai fa Abun arziki kuma ai Bai karbi kare ba yanzu duk jajircewar da nayi na shiga na fita na sama miki wannan takardar da aka hana dubun dubata aka bani shine kike neman watsa min k’asa a Ido ? kina son ki nuna min kece kika je Saudi Arabia ni banje har kike karanto min hakan ? amma ita mariya da yake tawa ce bata ja ba sai ke shine kike min shimfida da aure? To bani takardar aure kuma tunda kin shi kika zaba ai kin san maganar Alh mai dukiya ko? yo sai nayi mishi magana don tun lokacin da yaji alh yaro ya kwanta dama yake ta min zarya duk da Rashin alherin Alh mai dukiya sai da yake kullo wani Abu yana bani na kwantale shi sosai to tunda kin shirya ai sai na kira shi tuni naso hada shi da Mariya itama ja irar taki.

Da sauri Rabi ta dubi kawu garbati tana fadin

“Kawu tun tuni da ka kawo min maganar mutumin nan nace maka bana son shi gaskiya tunda kace min baya son haihuwa ni Kuma gaskiya yanzu na kara wani ilimi akan zaman aure musamman da na shiga gidan Alh yaro to don Allah don ANNABI kawu kayi min afuwa ka janye min maganar Alh mai dukiya gara ka sama min wani na yarda.

“Ai kuwa kinci uwar karya kin kwana da yunwa wallahi cikin biyu dole ki dauki daya ko dai tafiya Saudi Arabia ko kuma auren Alh mai dukiya don na gama gane idan na zuba miki ido sauran kad’an kice zaman Kai zakiyi tunda kika fake da sana ar nan to in tafiya Saudi Arabia to In kumay auren to ga mai dukiya Nan.

Duk adda Rabi taso ta nunawa kawu garbati yaki fahimta da gangan sai tayi hikima tace mishi ta zabi tafiya saudi Arabia ba don komai ba kuwa sai don in sun tafi ta sulale ta nemi mafitar ta.

Tuni kuwa maganar tafiya ta kankama inda ana nan yankin nasu kusan mace bakwai zata tafi

Saura kwana biyar tafiya Rabi ta nufi gidan Alh Sani

tana zuwa da Al Mustafa ta fara cin karo ya Kuma dafe ta Yana mata oyoyo inna ta.

Tausayin Al mustafa ya kamata hawaye ya soma fita daga idon ta yayin da Al Mustafa ya dube ta yaga tana kuka amma babu fasahar ya tambaye ta damuwar ta sai yace

“Inna wani ya doke ki ne?

ta kada mishi kanta tana share hawayen ta ta kama shi  suka shiga cikin gidan Al Mustafa yana kiran hanne yana fadin

“Nani Inna ta tana kuka wani ya dake ta.

Hanne ta karbi Rabi suka gaisa inda Al Mustafa ya nufi dakin Alh Sani ya fada mishi ga innar sa tazo tana kuka .

Da sauri alh Sani ya fito ya sami Rabi da hanne suna gaisawa hanne ta tashi Alh Sani ya zauna suka gaisa yana fadin

“Al Mustafa yace min kina kuka lafiya kuwa?

Ta kuma share hawayen ta tana fadin

“Baban Fatima wani Al amarin ne kuma ya sake tasa ni a gaba Wanda nake jin kamar nayi bankwana da ku da Al Mustafa. ta kwashe labarin komai akan abinda ya faru tsakanin ta da kawu garbati wanda yayi nata attack din auren Alh mai dukiya ko kuwa tafiya saudi Arabia neman kudi har dai ta zabi tafiya saboda ta San matsalar da take gidan Alh mai dukiya to amma abinda ya tsaya Mata a rai shine Al Mustafa.

Ta yi kuka sosai har Alh Sani yace zai tsaya mata koma ta baro gidan kawu garbati ta dawo gidan shi kawai.

“Kayi hakuri Baban Fatima idan nace zanyi hakan zai ce babu ni babu shi to amma in Sha Allah idan muka je zan san mafitar da zata fissheni ga amana Nan ko ban dawo ba Allah ya Taya maka Allah ya kama maka.

Jikin Alh Sani yayi sanyi hakikatan yaji kalaman na Rabi yayin da hawaye ya sauka akan fuskar shi lokacin da yaji abinda Rabi take fadawa al Mustafa.

“Al Mustafa zan tafi wani wuri da nissan tazara zai shata layin tsakanin mu idan Allah ta ala yayi min dawowa zanyi farin ciki in Kuma rabuwa ce ta zo mana da haka ina maka fatan alheri a kulliyar Rayuwar ka Ubangiji yayi maka baiwa da daukaka Mai albarka ya kawo maka aminci mai yawa tare da Ya’yan musulmi baki daya.

Al Mustafa ya zubawa uwar tasa idanu babu wayo bare ya gane wani abu sai dai jikin  shi a sanyaye sukayi sallama Ashe rabuwar kenan inda ya bita da kallo har ta bacewa ganin sa .

sallamar kenan sai dai a darrussalam. inda a Ranar har gidan su haj kaltume taje tayi musu sallama ta nemi su yafi juna dukksn su sai da ta bisu gidajen su tayi musu sallama.

Ranar da suka tashi daga bauci zuwa saudi Arabia a filin jirgi jidda suka sauka inda tun a nan aka soma Rarraba su zuwa sauran kasashe da za a kaisu irin su Ethopia da Sudan wasu kuma kamaru kai kasashe dai masu makotaka da Saudi Arabia inda wasu kam aikatau din ne wasu Kuma karuwanci ne .

Allah da ikon shi ana sauke su a jidda Rabi ta sulale ta gudu ba tare da an snkara da guduwar tata ba har garin sauri ta Ratsa tsakiyar titi ba tare da kul da motar da ta danno ba ai kuwa tayi gaba da Rabi wacce take neman mafaka.

Wani irin zafi da Rad’ad’i ne ya ratsa ta Wanda ya tabbatar mata da an banke ta

Matar da tayi bankar ce ta fito taga halin da Rabi take ciki ta kama ta mata sannu cikin harshen larabci suka nufi asibiti.

A nan asibiti Rabi ta kwana ana bata kulawa har ta samu dauki matar tazo tana duba ta da Yake tana jin turanci sai sukayi ta magana da Rabi wacce itama ta san yaren sai matar ta tausayawa Rabi da aka sallame ta ma sai suka nufi gidan matar mai suna jawahir inda Rabi ta zayyana mata komai tun daga farko har zuwan su Saudi Arabia da yadda ta sulale ta gudu har tsautsayin ya faru ta gujewa yan tafiyar su.

Jawahir ta gama sauraren bayanan Rabi ta kuma tausaya mata don har a ranta da ta ga Rabi mutuniyar kirki ta gani ta kuma ji zata iya taimaka mata har karshen numfashi. ALLAH kenan !

Jawahir bata Jin hausa daga turanci sai larabci don haka da turanci Rabi take fada mata komai har ta kare bata labarin Rayuwar ta.

Jawahir ta bata hakuri ta kuma fada mata In zata iya zama da su babu matsala sai dai su din ba mazauna garin Saudi ba ne asalin sune nan din iyaye da kakani duk suna nan hasali ma suna da alaka da masarsutar Saudi amma aiki ya mayar da mijin jawahir din k’asar Syria don haka in sun shigo Saudi to hutu suka samu ko wani dalilin daban don haka yanzu ma saura kwana biyar su koma can Syria din amma jawahir ta bawa Rabi zabi idan zata zauna dasu to zasu wuce Syria idan kuma tafi son Saudi to zasu mayar da ita can family house din su da ke daular masarsutar Saudi ta king abdulazeez ta zauna a can in ma zata yi aikin ne to aikin masarautar zaifi mata aminci kuma zata zauna babu fargabar kake ko rashin takardar zama wato ighama

Rabi ta dubi jawahir da wannan karimcin nata tana hawaye tana mata godiya tana cewa duk inda ta ajiye ta tana Godiya kuma har ta mutu ba zata manta ba

Jawahir tayi murmushi tana fadin

“To yanzu kinga saboda yanayin jikin ki ki fara zama a can masarautar in yaso idan Allah ya dawo damu tunda muna zuwa aikin hajj idan mun zo sai mu tafi tare Amma yanzu jikin ki bai gama warkewa ba in anjima sai mu tafi na kaiki wurin ummu nauwal na gabatar dake

Rabi ta jinjinawa kudurar Ubangiji na irin tagomsshin alherin da yayi mata

Babu abinda ke Ranta sai Al Mustafa wanda take jin ina ma yana nan tare da ita? Da babu abinda zai sata tunawa da Nigeria da su kawu garbati sai dai tayi waya su gaisa da alh Sani amma yanzu gata a Saudi cikin Rahamar Allah amma zuciyar ta na Nigeria tana bulayin neman Al Mustafa Amma sai ta aike mishi da ADDU AR fatan alheri da Aminci mai yawa

Rabi tasha mamakin gidan da suka iso ita da jawahir. gida ne Wanda zuciya Bata isa fassarw yadda yake da kyau ba bare kuma baki da Alkalami su zayyana abinda kawai ta Sani shine gidan sai sarauta kuma sarautar ma mai girman matsayi don yadda taga hadiman gidan duk larabawa ne kuma cikin tssri da aminci ba irin sarautar da ta saba gani ba

Kayataccen gida mai abin hawan isar da mutum sama ( lifter) ya mika sama ko ya sauko da Kai haka jawahir tayi ta shiga da ita har suka Isa kuryar gidan inda ake ta gaishe da jawahir tana amsawa har tana bada kyautar Riyalai

Unmu nauwal itace kamar jakadiyar gidan don haka a sashin ta suka sauka ta gabatar da Rabi da kuma irin Al amarin da ya faru da ita inda jawahir tace a sama mata aiki wanda za a rika biyan ta

Ummu Nauwal ta karbi Rabi ta kaita dakin sajida ta sauke ta a nan inda zatayi aiki da sajidar ne a matsayin mai aikin girkin abincin  gargajiya

Jawahir ta bata lambar wayar ta tace duk abinda take ciki ta sanar mata  sukayi sallama ta wuce zuwa kuryar gidan gun iyayen su

Tunda Rabi ta shigo gidan nan sai ta samu kanta da samun nutsuwa babu wani aikin wahala aikin girkin ma sai suyi kwana bakwai basuyi ba sai dai suci abinda suke so Kan naman kaji da kayan itace kan madarar laban kai lallai AZURFA DA ZINARE tana Saudi kafin Kuma a matsa madeena

Kan kace me? Rabi tayi wani irin sauyi tayi kiba tayi jajir ga hutu ga cima mai kyau ga sutura irin ta matan larabawa

Lokaci zuwa lokaci tana kiran Alh Sani su gaisa ya tambaye ta yaya take ciki?

Ta fada mishi Rahamar da Ubangiji yayi mata baiwa da ita daga tsautsayi ya gitta an banke ta sai gata a tsakiyar gidan sarautar Saudi babu Aikin komai sai cima mai kyau

Yaji Dadin hakan yayi Mata ADDU AR Allah ya kara sutura

Ta tambaye shi Al mustafa ya tashi ya nemo shi can cikin yara ya bashi wayar Yana ce mishi ga Inna.

Ya kwakume wayar yana Fadin

“Inna ta Ina kika tafi baki zo ba?

Tayi murmushi tana Jin tamkar ta miko hannu taja shi ta kawo shi Saudi yasha irin dadin da Ubangiji ya mata kyauta dashi amma ina ! Alkalamin kaddarar haka ya zana.

“Al Mustafa na kana lafiya? Ina su Salim da Fatima da su muhd?.

“Inna sunan lafiya Lau yaushe zaki zo ?

“To Al Mustafa sai Allah ya nufa amma ni ma ba zan ce maka ga lokacin ba amma in sha Allah mun kusa mu gana kaji?

“To Inna ki siya min mota da jirgi In zaki taho baba yace zai siya mana keke.

“Masha Allah to kayi ta kokari a makaranta in sha Allah ko ban zo ba zan samu wanda zai zo na bashi sak’on mota da jirgi a kawo muku har da su Salim da muhd.

“To Inna mun gode ki hado mana har da ibon da biescut.

Sun jima suna magana da Al mustafa kafin Alh Sani ya karbi wayar sukayi sallama

Wata rana lokacin sun yi shekara da zuwa burnin Saudi jawahir sun zo Saudi Rabi tana tare da jawahir sun shiga kasuwa sai ga wata haduwa tsakanin rabi da Mariya wacce take rike da gumama tana talla sai kawai taga wata balarabiya mai kama da Rabi.

Rabi taga mariya inda ta nunawa jawahir ita tana fada mata yar uwar ta ce da suka tare daga Nigeria.

Mariya ta zubawa Rabi Ido don Bata yarda Rabin bace tafi yarda da kama ce kawai smma sai taga Rabi na nufo ta har ta iso inda take ta rungume ta tana ambatar sunan ta.

“Yar uwa ashe da Rabon ganawa?

Mariya ta yarda Rabi ce ba kama ba don haka ta watsar da kayan gumamar da suke hannun ta tana fadin

“Rabi kece haka ? don Allah fada min Rahamar da Kika samu haka dare daya Allah Kanye bature.

Rabi ta dubi mariya tana tambayar ta labarin gida da su kawu garbati mariya tace mata suna lafiya anan take bata labarin kamun da akayi musu na farko aka watsa su Nigeria saboda an gano bad’alar da suke ta Shashanci amma Kuma sukayi cuku cuku suka dawo amma a yanzu Kan karuwanci Babu ci dole ta koma saida gumamar.

Rabi bata ji dadin abinda mariya tayi ba don ta san ta kuda ce bata haram sai dai kuma ta san in da laifin ta to laifin kawu garbati yafi yawa shi da ya turo zaurawa Saudi neman kudi

Rabi ta sanar da Mariya Al amarin ta da guduwar da tayi da yadda suka hadu da jawahir da irin taimakon da tayi mata ta kaita gidan sarautar Saudi take aikin ta cikin aminci

Jawahir ta dubi mariya tana fadin idan Babu damuwa zasu tafi da ita taga masaukin Rabi

Ai kuwa mariya ta shiga motar mai feshin sanyin ac har gidan su ummu Nauwal Mariya taga daula taga Rayuwa kamar ba zata taho ba inda Rabi ta cika ta da alheri mai yawa har take ce mata tana son tura sako Nigeria amma bata San yadda za ayi ba mariya ta sanar da ita yadda ake sukayi sallama

Rabi ta turawa Alh Sani sak’o da nashi da na su salim da Al mustafa wanda ta siyawa kayan wasa na  yara motoci da jirage da kayan askar din Saudi masu kyau kaya rakataf ta tura ta Kuma bada na kawu garbati shima hatta da su haj kaltume Rabi sai da ta bayar a basu

Alh Sani yayi mamaki ko da yake bai zama abun mamaki ba dama haka Allah yake a lokacin da ake nufin cutar da kai in Allah yaso sai ya sanya wannan cutar da zama alheri gashi dai Rabi anyi mata abubuwan da yawa da sunan a dakushe ta Ashe takin arziki ake mata

Ya kira ta yayi mata godiya sosai yayi mata ADDU A har ta fada Mishi tana nan zuwa bayan aikin hajj in sun kare zata zo ta tafi da Al Mustafa da salim ta saka su wata makaranta ta haddar Al kur Ani ce da ake bawa ya’yan da suka Rasa iyaye ilimi kyauta wato marayu.

Wannan shine burin Rabi ga Al Mustafa amma ashe Allah bai nufi cikar sa ba

Lokacin aikin hajj Rabi ta kuma samun tagomsshin aiki ta rokawa iyayen ta Rahama da gafara ta rokawa Alh yaro da dukkan musulmin duniya ta kuma roki Allah alherin sa mai yawa ga Alh Sani da danta Al Mustafa da dukkan Ya’yan musulmi ita kuma ta Roki aminci da kyakkyawan karshe da kyakkyawar makoma

Lokaci zuwa lokaci Mariya tana zuwa su gaisa har ma ta sanar da ita labarin gida

Dukkan wani Abu da Rabi take son yi ko ayi mata sai taji kamar wacce ake umurta don haka ta gabatar da komai ta Kuma yi komai.

Gaba daya ta tattare komai nata Wanda ya danganci kudaden ta ta turawa Alh Sani tace ya hada ya Siyawa Al mustafa wani Abu da zai amfane shi.

ta turawa kawu garbati kudi tace yayi mata ADDU A da yake mayatar abin duniyar gareshi ai kuwa yayi ta mata ADDU AR da bata tab’a sanin ya iya ta ba ita da iyayen ta sun sha ADDU AR don haka taji dadi ta godewa Allah.

<< Azurfa Da Zinari 77

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×